Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 12/15 pp. 18-22
  • Ruhun Allah Ya Yi Wa Masu Aminci Na Dā Ja-gora

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ruhun Allah Ya Yi Wa Masu Aminci Na Dā Ja-gora
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ruhun Allah Ya Ƙarfafa Musa
  • Ruhu Mai Tsarki Ya Sa Bazalel Ya Cancanta
  • Ruhun Allah Ya Taimaka wa Joshua Ya Yi Nasara
  • “Ruhun Ubangiji Ya Shiga Cikin Gideon”
  • “Ruhun Ubangiji Ya Sauko Ma Jephthah”
  • “Ruhun Ubangiji Ya Zo ma [Samson]”
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Dogara ga Jehobah Kamar Samson
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yana da Muhimmanci a San da Aikinka Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 12/15 pp. 18-22

Ruhun Allah Ya Yi Wa Masu Aminci Na Dā Ja-gora

“Ubangiji -Yahweh ya aiko ni, duk da ruhunsa.”—ISHA. 48:16.

1, 2. Mene ne ake bukata don a kasance da bangaskiya, kuma wane ƙarfafa ne za mu samu ta yin la’akari da masu aminci na dā?

KO DA yake mutane da yawa a zamanin Habila sun nuna bangaskiya, amma “ba duka ke da [bangaskiya] ba.” (2 Tas. 3:2) Me ya sa mutum yake kasance da wannan halin, kuma mene ne zai taimaka masa ya kasance da aminci? Mun san cewa idan muna bukatar bangaskiya, wajibi ne mu samu sani daga Kalmar Allah domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Bangaskiya daga wurin ji ne.’ (Rom. 10:17) Sashe ne na ’yar ruhu mai tsarki na Allah. (Gal. 5:22, 23) Saboda haka, muna bukatar ruhu mai tsarki don mu nuna da kuma kasance da bangaskiya.

2 Ba a haifan mutane da bangaskiya. Maza da mata masu aminci da muka karanta game da su a Littafi Mai Tsarki mutane ne da suke da “tabi’a kamar tamu.” (Yaƙ. 5:17) Sun yi shakkar wasu abubuwa da rashin tabbatawa da iyawarsu kuma suna da kasawarsu, amma “aka ƙarfafa su” da ruhun Allah don fuskantar ƙalubale. (Ibran. 11:34) Za mu samu ƙarfafa don mu ci gaba da nuna bangaskiya ta yin la’akari da yadda ruhun Jehobah ya yi musu ja-gora, tun da yake muna zama ne cikin zamanin da abubuwa da yawa za su iya raunana bangaskiyarmu.

Ruhun Allah Ya Ƙarfafa Musa

3-5. (a) Ta yaya muka sani cewa Musa ya aikata da taimakon ruhu mai tsarki? (b) Mene ne misalin Musa ya koya mana game da yadda Jehobah yake ba da ruhunsa?

3 Musa ne ya fi dukan mutanen da suka rayu a shekara ta 1513 K.Z., ‘tawali’u ƙwarai.’ (Lit. Lis. 12:3) An danƙa wa wannan bawa mai tawali’u hakki mai girma a al’ummar Isra’ila. Ruhun Allah ya ƙarfafa Musa ya yi annabci da shari’a da yin rubuce-rubuce da shugabanci da kuma yin mu’ujizoji. (Karanta Ishaya 63:11-14.) Duk da haka, akwai lokacin da Musa ya yi kuka cewa aikin ya fi ƙarfinsa. (Lit. Lis. 11:14, 15) Sai Jehobah ya ɗiba “daga cikin ruhun da ke” bisa Musa kuma ya ba wa mutane saba’in don su taimaka wajen yin aikin. (Lit. Lis. 11:16, 17) Ko da yake Musa yana ganin yana yin ayyuka masu wuya ainun, ba shi kaɗai ba ne yake yin ayyukan ba kuma mutane 70 da aka naɗa su taimaka masa ma ba su kaɗai ba suke yin aikin ba.

4 An ba Musa isashen ruhu mai tsarki don ya yi aikin. Bayan canjin da aka yi, Musa har ila yana da dukan ruhun da yake bukata. Ruhu mai tsarki da Musa yake da shi bai masa kaɗan ba kuma bai cika yi wa dattawa 70 ɗin yawa ba. Jehobah yana ba mu ruhun da muke bukata daidai da yanayinmu. “Yana bada Ruhu ba da aunawa ba” amma “daga cikin yalwatasa.”—Yoh. 1:16; 3:34.

5 Kana jimre gwaje-gwaje ne? Kana jin cewa hakkokinka suna daɗa ƙaruwa kuma suna cinye lokacinka? Shin kana ƙoƙari ne don ka yi wa iyalinka tanadin abinci na ruhaniya da na zahiri yayin da kake jimrewa da abubuwa da suke daɗa tsada ko kuma alhini saboda rashin lafiya? Kana ɗauke da hakkoki masu yawa a cikin ikilisiya? Ka kasance da tabbaci cewa Allah zai iya ba ka ƙarfi ta wurin ruhunsa mai tsarki don ka iya jimre wa yanayin.—Rom. 15:13.

Ruhu Mai Tsarki Ya Sa Bazalel Ya Cancanta

6-8. (a) Mene ne ruhun Allah ya taimaka wa Bezalel da Oholiab su yi? (b) Mene ne ya nuna cewa ruhun Allah ne ya yi wa Bezalel da Oholiab ja-gora? (c) Me ya sa misalin Bezalel yake da ban ƙarfafa a gare mu a yau?

6 Labarin Bezalel na zamanin Musa ya nuna yadda ruhun Allah yake aiki. (Karanta Fitowa 35:30-35.) An zaɓi Bezalel don ya yi ja-gora wajen yin wasu gyare-gyare a mazaunin. Shin Bezalel ya san yadda ake ƙera abubuwa kafin a soma wannan babban aikin? Wataƙila, aiki na ƙarshe da ya yi shi ne yi wa Masarawa tubala. (Fit. 1:13, 14) To, ta yaya Bezalel zai yi wannan aiki mai wuya? Jehobah “ya cika shi da ruhun Allah, cikin hikima, da fahimi, da ilimi da kowace irin sana’a; domin ya tsiro da salo na gwaninta . . . shi yi aiki cikin kowace irin sana’a ta fasaha.” Allah ya kyautata iyawar Bezalel da Oholiab ta wajen ba su ruhu mai tsarki. Babu shakka cewa sun koya da kyau, domin sun yi aikin kuma sun koya wa wasu yadda za su yi shi.

7 Wani tabbaci cewa ruhun Allah ya yi wa Bezalel da Oholiab ja-gora shi ne ingancin aikin da suka yi. An ci gaba da yin amfani da abubuwan da suka yi bayan shekara 500. (2 Laba. 1:2-6) Yawancin mutane da suke yin abubuwa a yau suna rubuta sunayensu a jikin abin da suka yi don mutane su san cewa su suka yi shi kuma a daraja su. Amma Bezalel da Oholiab ba su yi haka ba, suna son a yabi Jehobah don dukan abubuwa da suka yi.—Fit. 36:1, 2.

8 A yau, muna iya yin aikin da ke bukatar iyawa na musamman, kamar gini da buga littattafai da shirya taron gunduma da taimakon ’yan’uwanmu bayan wani tsarar bala’i da kuma bayyana wa likitoci da ma’aikatan asibiti abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yin amfani da jini. A wasu lokatai, waɗanda suke da iyawa na musamman ne suke yin waɗannan ayyukan, amma yawancin lokaci waɗanda suka ba da kansu da ba su san aikin sosai ba ne suke yin sa. Amma ruhun Allah ne ke taimakonsu su yi aikin da kyau. Ka taɓa jinkirin karɓan wani aiki a hidimar Jehobah domin kana ganin wasu za su fi ka iya aikin? Ka tuna cewa ruhun Jehobah zai iya kyautata iliminka da iyawarka kuma ya taimaka maka ka cika kowanne aikin da ya ba ka.

Ruhun Allah Ya Taimaka wa Joshua Ya Yi Nasara

9. A wane yanayi ne Isra’ilawa suka samu kansu bayan sun bar ƙasar Masar kuma wace tambaya ce ake bukatar a ba da amsarta?

9 Ruhun Allah ya kuma yi wa wani bawan Allah ja-gora, wanda ke zamanin Musa da Bezalel. Ba da daɗewa ba bayan Isra’ilawa suka bar ƙasar Masar, Amalakawa suka kai wa mutanen Allah hari. Ko da yake Isra’ilawa ba su saba yin faɗa ba, amma yanzu za su yi yaƙinsu na farko a matsayin mutane masu ’yanci. (Fit. 13:17; 17:8) Ya kamata wani ya yi musu ja-gora a yaƙin. Wane ne zai zama?

10. Me ya sa Joshua da Isra’ilawa suka ci yaƙin?

10 An zaɓi Joshua, amma bai taɓa ja-goranci runduna a dā ba. Mene ne ya san game da yaƙi? Shi bawa ne a dā wanda ya yi tubala, kuma a cikin jeji ya tattara manna don abincinsa na yini. Hakika, Elishama kakan Joshua ya ja-goranci ƙabilar Ephraim kuma shi ne shugaban rundunar sojoji guda 108,100. (Lit. Lis. 2:18, 24; 1 Laba. 7:26, 27) Amma, Jehobah ya gaya wa Musa kada ya zaɓi Elishama ko kuma ɗansa Nun, amma ya zaɓi Joshua ya ja-goranci rundunar don su halaka magabtansu. An yi yaƙin kusan dukan ranan, kuma domin Joshua ya yi biyayya ga Allah kuma ya amince da ja-gorar ruhun Allah, Isra’ila ta ci yaƙin.—Fit. 17:9-13.

11. Ta yaya za mu iya yin nasara a tsarkakkiyar hidima kamar Joshua?

11 Bayan haka, Joshua “cike da ruhun hikima,” ya ɗauki matsayin Musa. (K. Sha 34:9) Ruhu mai tsarki bai sa shi yin annabci ko kuma yin mu’ujizai kamar Musa ba, amma ya taimaka wa Joshua ya ja-goranci Isra’ila a yaƙe-yaƙe masu yawa da suka yi don su ci ƙasar Kan’ana. A yau, muna iya jin cewa ba mu da ilimi ko iyawa na yin wasu abubuwa a tsarkakkiyar hidimarmu ga Allah. Duk da haka kamar Joshua, muna da tabbaci cewa za mu yi nasara idan muka yi biyayya sosai ga umurnin Allah.—Josh. 1:7-9.

“Ruhun Ubangiji Ya Shiga Cikin Gideon”

12-14. (a) Mene ne nasarar da sojoji 300 suka ci a kan Midiyanawa ya koya mana? (b) Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa Gidiyon? (c) Wane taimako ne muke sa rai Allah zai yi mana a yau?

12 Jehobah ya ci gaba da nuna yadda ikonsa yake ƙarfafa mutane masu aminci bayan da Joshua ya rasu. Za mu iya karanta game da mutane waɗanda “daga cikin rashin ƙarfi aka ƙarfafa su” a littafin Alƙalawa. (Ibran. 11:34) Da taimakon ruhu mai tsarki, Allah ya sa Gidiyon ya yi yaƙi a madadin mutanensa. (Alƙa. 6:34) Rundunan Midiyanawa sun fi na Gidiyon yawa, za a iya raba sojojin Midiyanawa huɗu huɗu ga kowanne sojan Isra’ila. A idanun Jehobah wannan ƙaramin rundunar Isra’ilawa sun yi yawa sosai. Sau biyu yana gaya wa Gidiyon ya rage sojojinsa har sai sun kai yadda za a iya raba Midiyanawa 450 ga kowanne sojan Isra’ila. (Alƙa. 7:2-8; 8:10) Jehobah ya amince da adadin da ya rage. Da hakan, idan Isra’ilawa suka ci yaƙin ba wanda zai iya yin fahariya cewa ƙoƙarce-ƙoƙarce ko kuma hikimar ’yan Adam ne suka sa aka ci yaƙin.

13 Gidiyon da rundunarsa sun kusan gama shiri. Da a ce kana cikin wannan ƙaramin rundunan, za ka iya kasancewa da kwanciyar rai cewa an aika waɗanda suke jin tsoro gida ko kuma waɗanda ba su yi hattara ba? Ko za ka ɗan ji tsoron abin da zai iya zama sakamakon ne? Muna da tabbaci cewa Gidiyon ya dogara ga Allah. Ya yi abin da aka gaya masa ya yi! (Karanta Alƙalawa 7:9-14.) Jehobah bai tsauta wa Gidiyon ba don ya nemi alama ya tabbata cewa Allah yana tare da shi. (Alƙa. 6:36-40) Maimakon haka, ya ƙarfafa bangaskiyar Gidiyon.

14 Ikon Jehobah na yin ceto ba shi da iyaka. Zai iya ceton mutanensa daga kowanne irin yanayi mai wuya, kuma yana iya yin hakan ta wurin yin amfani da mutanen da suka raunana ko kuma waɗanda ake ganin ba za su iya taimako ba. A wasu lokatai za mu iya jin cewa mutane da yawa suna gāba da mu ko kuma muna cikin mugun yanayi. Ba za mu sa rai cewa Allah zai nuna mana alama kamar na Gidiyon ba, amma zai iya yi mana ja-gora da kuma ta’aziyya ta wurin Littafi Mai Tsarki da ikilisiya da ruhu ke wa ja-gora. (Rom. 8:31, 32) Alkawuran Jehobah na ƙauna da ya yi mana suna ƙarfafa bangaskiyarmu kuma suna ba mu tabbaci cewa Jehobah ne mai cetonmu!

“Ruhun Ubangiji Ya Sauko Ma Jephthah”

15, 16. Me ya sa ’yar Jephthah ta kasance da hali mai kyau, kuma yaya hakan ƙarfafa ne ga iyaye?

15 Ka yi la’akari da wani misali. Sa’ad da Isra’ilawa suke son su yi yaƙi da Ammonawa, ruhun Jehobah “ya sauko ma Jephthah.” (Alƙa. 11:29-31, 34) Tun da yake ya yi ɗokin ya ci nasara don yabon Jehobah, Jephthah ya yi alkawari na wani abu mai tamani. Ya yi alkawari cewa idan Allah ya sa ya ci nasara a kan mutanen Ammonawa, duk abin da ya fara fitowa daga gidansa sa’ad da ya dawo zai kasance na Jehobah. Sa’ad da Jephthah yake dawowa daga yaƙin, ’yarsa ta fito ta tarbe shi. (Alƙa. 11:29-31, 34) Hakan ya sa Jephthah mamaki ne? Babu shakka, don ita ce kaɗai ’yarsa. Ya cika alkawarinsa ta wurin ba da ’yarsa don yin hidima a wuri mai tsarki na Jehobah da ke Shiloh. Da yake ita mai yin bauta ga Jehobah da aminci ce, ’yar Jephthah ta yarda cewa a cika alkawarin da Mahaifinta ya yi. (Karanta Alƙalawa 11:36.) Ruhun Jehobah ya ba dukansu ƙarfin da suke bukata.

16 Ta yaya ’yar Jephthah ta kasance da irin wannan hali na sadaukarwa? Babu shakka, ƙwazon mahaifinta da kuma ibadarsa sun ƙarfafa bangaskiyarta. Iyaye, yara suna lura da misalinku. Shawarwarinku suna nuna cewa kun yarda da abin da kuke faɗa. Yaranku suna sauraran addu’o’inku da kuma koyarwarku haɗe da misalinku na bauta wa Jehobah da dukan zuciyarku. Dukan waɗannan za su taimaka musu su kasance da sha’awar bauta wa Jehobah. Wannan zai sa ku farin ciki sosai.

“Ruhun Ubangiji Ya Zo ma [Samson]”

17. Mene ne ruhun Allah ya taimaki Samson ya yi?

17 Ka yi la’akari da kuma wani misali. Sa’ad da Isra’ilawa suke bauta a ƙasar Filistiyawa, “Ruhun Ubangiji kuwa ya soma motsa” Samson ya ceci Isra’ila. (Alƙa. 13:24, 25) An ba wa Samson ƙarfi mai ban mamaki da babu wanda yake da shi. Sa’ad da Filistiyawa suka zuga Isra’ilawa ’yan’uwan Samson su kama shi, “sai ruhun Ubangiji ya zo masa da iko, igiyoyin da ke a hannuwansa suka zama sai ka ce flax da aka sa masa wuta, maɗauransa suka narke suka zube ma hannuwansa.” (Alƙa. 15:14) Ko a lokacin da ya raunana a zahiri domin ya tsai da shawara da ba ta dace da ya sa ya yi hasarar ƙarfinsa, an sa Samson ya yi ƙarfi “ta wurin bangaskiya.” (Ibran. 11:32-34; Alƙa. 16:18-21, 28-30) Saboda yanayin, ruhun Jehobah ya taimaka wa Samson a hanya ta musamman. Har ila, waɗannan abubuwa da suka auku a tarihi suna da ban ƙarfafa sosai a gare mu. Ta yaya?

18, 19. (a) Ta yaya misalin Samson ya ƙarfafa mu? (b) Ta yaya ka amfana ta wurin tattauna misalan masu aminci a cikin wannan talifin?

18 Muna dogara ga wannan ruhun da ya taimaki Samson. Muna yin hakan yayin da muke yin aikin da Yesu ya ba mabiyansa, wato, “mu yi ma jama’a wa’azi, mu [yi] shaida kuma.” (A. M. 10:42) Yin wannan aikin yana iya yi mana wuya. Saboda haka, muna farin ciki cewa Jehobah yana amfani da ruhunsa don ya taimaka mana mu cim ma ayyukan da aka danƙa mana! Saboda haka, yayin da muke cika aikinmu, mun yarda da annabi Ishaya wanda ya ce: “Ubangiji Yahweh ya aiko ni, duk da ruhunsa.” (Isha. 48:16) Hakika, ruhun Allah ne ya aike mu! Muna yin wannan aikin da tabbaci cewa Jehobah zai kyautata iyawarmu yadda ya yi wa Musa da Bezalel da kuma Joshua. Muna amfani da “takobin Ruhu, wato maganar Allah” da tabbaci cewa zai ba mu ƙarfi yadda ya ba Gidiyon da Jephthah da kuma Samson. (Afis. 6:17, 18) Idan mun dogara ga Jehobah, zai iya ba mu ƙarfin yin aikinsa kamar yadda ya ba Samson ƙarfi na zahiri.

19 A bayane yake cewa Jehobah yana yi wa masu bauta masa da gaba gaɗi albarka. Bangaskiyarmu tana daɗa ƙarfi sa’ad da muka bar ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora. A cikin Nassosin Helenanci na Kirista, da akwai misalai na waɗanda ruhun Allah ya yi musu ja-gora. Za mu yi farin cikin koya a talifi na gaba yadda ruhun Jehobah ya taimaka wa bayinsa masu aminci a ƙarni na farko kafin Fentakos na shekara ta 33 A.Z., da kuma bayan hakan.

Me ya sa ka ƙarfafa don sanin yadda ruhun Allah ya taimaki . . .

• Musa?

• Bezalel?

• Joshua?

• Gidiyon?

• Jephthah?

• Samson?

[Bayanin da ke shafi na 22]

Ruhun Allah zai iya sa mu kasance da ƙarfi a ruhaniya yadda Samson yake a zahiri

[Hoto a shafi na 21]

Iyaye, misalinku mai kyau zai taimaka wa yaranku su so bauta wa Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba