Ka Yi Koyi da Misalin Yesu na Yin Tsaro
“Ku yi tsaro, ku yi addu’a.”—MATT. 26:41.
YAYA ZA KA AMSA?
․․․․․
Ta yaya addu’o’inmu za su nuna cewa muna yin tsaro?
․․․․․
A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna yin tsaro a hidimarmu?
․․․․․
Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tsaro sa’ad da muke fuskantar gwaji, kuma yaya za mu iya yin hakan?
1, 2. (a) Waɗanne tambayoyi za a iya yi game da misalin Yesu na yin tsaro? (b) Shin ’yan Adam masu zunubi suna iya yin koyi da misali mai kyau na Yesu? Ka ba da misali.
KANA iya yin mamaki: ‘Zai yiwu kuwa mu yi koyi da misalin Yesu na yin tsaro? Ballantana ma, Yesu kamili ne! Ban da haka ma, a wasu lokatai Yesu yana iya sanin abin da zai faru a nan gaba, har fiye da shekaru dubbai! Shin yana bukatar ya yi tsaro?’ (Mat. 24:37-39; Ibran. 4:15) Bari mu fara tattauna waɗannan tambayoyi don mu ga yadda wannan batun yake da muhimmanci da kuma gaggawa.
2 Shin ’yan Adam masu zunubi za su iya yin koyi da misali mai kyau? Hakika, domin ɗalibi yana koya daga misalin ƙwararen malami. Alal misali, ka yi la’akari da mutumin da yake koyon yadda ake harbi da kibiya a lokacinsa na farko. Da farko ba zai iya harban dabbar da yake so ba, amma sai ya ƙara koyo kuma ya ci gaba da ƙoƙari. Don ya iya harbin da kyau, sai ya bi misalin malaminsa sosai, wanda ƙwararren maharbi ne. Ɗalibin zai mai da hankali ga yadda malamin yake tsayawa da ajiye hannunsa da kuma amfani da yatsunsa. A hankali, zai koya yawan yadda zai ja tsirkiyar bakar da kuma yadda iska za ta shafi kibiyar. Idan ya ci gaba da yin ƙoƙari da kuma yin koyi da malaminsa, zai koya yadda zai saita dabbar da yake son ya harba kuma ya same ta. Hakanan ma, muna ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu zama nagargarun Kiristoci ta wajen bin umurnin Yesu da kuma yin koyi da misali mai kyau da ya kafa.
3. (a) Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana bukatar yin tsaro? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 Shin Yesu yana bukatar ya yi tsaro? Hakika! Alal misali, a dare na ƙarshe kafin Yesu ya rasu, ya aririci mabiyansa masu aminci: ‘Ku yi tsaro tare da ni.’ Sai ya daɗa: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jarraba.” (Mat. 26:38, 41) Ko da yake Yesu yana yin tsaro a ko da yaushe, amma a waɗannan sa’o’i masu wuya, yana bukatar ya yi iya ƙoƙarinsa don ya yi tsaro kuma ya kasance da dangantaka na kud da kud da Ubansa na samaniya. Ya san cewa mabiyansa suna bukatar su yi tsaro ba a wannan lokacin kaɗai ba amma a nan gaba. Saboda haka, bari mu tattauna abin da ya sa Yesu yake son mu yi tsaro. Bayan haka, za mu bincika hanyoyi uku da za mu yi koyi da Yesu a yin tsaro a rayuwarmu ta yau da kullum.
DALILIN DA YA SA YESU YAKE SON MU YI TSARO
4. Me ya sa muke bukatar mu yi tsaro?
4 Yesu yana son mu yi tsaro domin abin da ba mu sani ba da kuma abin da muka sani. Sa’ad da Yesu yake duniya, shin ya san kome da zai faru a nan gaba ne? A’a, gama ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Mat. 24:36) A wannan lokacin, Yesu, wato, “Ɗa,” bai san ainihin lokacin da ƙarshen wannan mugun zamani zai zo ba. Mu kuma fa? Shin mun san kome game da nan gaba? A’a! Ba mu san lokacin da Jehobah zai aiko da Ɗansa don ya kawo ƙarshen wannan mugun zamanin ba. Idan mun san wannan ranar, shin za mu bukaci yin tsaro? Kamar yadda Yesu ya bayyana, ƙarshen zai so farat ɗaya ba labari, saboda haka, muna bukatar mu yi tsaro fiye da dā.—Karanta Matta 24:43.
5, 6. (a) Ta yaya sani game da Mulkin Allah zai taimaka mana mu yi tsaro? (b) Me ya sa sani game da Shaiɗan zai sa mu yi tsaro sosai?
5 Yesu ya san abubuwa da yawa masu ban al’ajabi game da nan gaba da yawancin mutane da suke tare da shi ba su sani ba. Ba mu san abin da Yesu ya sani ba, amma ya koya mana abubuwa da yawa game da Mulkin Allah da abin da zai yi a nan gaba. Yawancin abokan makarantarmu da abokan aikinmu ko kuma waɗanda suke yankinmu ba su san waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi ba. Wannan wani dalili ne da ya sa za mu yi tsaro. Kamar Yesu, muna bukatar mu riƙa yin hattara don neman zarafin gaya wa mutane abin da muka sani game da Mulkin Allah. Wannan zarafin yana da tamani, kuma muna son mu tabbata cewa mun yi amfani da shi. Mutane suna bukatar taimako don kada a halaka su!—1 Tim. 4:16.
6 Dalili na biyu da ya sa Yesu ya yi tsaro shi ne don ya san cewa Shaiɗan ya ƙudiri aniya ya gwada shi da tsananta masa da kuma sa ya daina bauta wa Allah. A kowane lokaci, wannan mugun magabci yana neman “wani zarafin” don ya gwada Yesu. (Luk 4:13) Yesu ya yi tsaro a ko da yaushe. Yana son ya kasance a shirye don kowane gwaji, ko jarraba da hamayya ko kuma tsanantawa. Mu ma muna cikin irin wannan yanayin. Mun san cewa har ila Shaiɗan yana “kamar zaki mai-ruri, . . . yana neman wanda za ya cinye.” Shi ya sa Kalmar Allah ta gargaɗi dukan Kiristoci: “Ku yi hankali shinfiɗe, ku yi zaman tsaro.” (1 Bit. 5:8) Amma ta yaya za mu iya yin hakan?
YADDA ADDU’A ZA TA TAIMAKA MANA MU YI TSARO
7, 8. Wane gargaɗi ne Yesu ya ba da game da addu’a, kuma wane irin misali ne ya kafa?
7 Littafi Mai Tsarki ya nuna nasaba da ke tsakanin yin tsaro a bautarmu ga Jehobah da kuma yin addu’a. (Kol. 4:2; 1 Bit. 4:7) Ba da daɗewa ba bayan Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi tsaro tare da shi, ya ce: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jarraba.” (Mat. 26:41) Shin yana nufin cewa sa’ad da suke fuskantar yanayi mai wuya ne kaɗai suke bukatar su yi addu’a? A’a, gargaɗinsa ƙa’ida ce da ya kamata mu bi kullum.
8 Misalin Yesu ya nuna mana amfanin yin addu’a. Kana iya tuna cewa akwai daren da Yesu bai yi barci ba domin yana addu’a ga Ubansa. Bari mu yi tunanin yanayin. (Karanta Luka 6:12, 13.) Wataƙila Yesu yana kusa da garin Kafarnahum. Yayin da dare ya yi, Yesu ya hau kan ɗaya cikin duwatsu da ke kusa da Tekun Galili. Sa’ad da ya kalli ƙasa, wataƙila ya ga wutar a-ci-bal-bal a garin Kafarnahum da kuma ƙauyuka da ke kusa. Amma, sa’ad da Yesu ya soma addu’a ga Jehobah, ya natsu sosai. Sa’o’i suka wuce, kuma Yesu bai lura ba sa’ad da mutanen da suka kunna a-ci-bal-bal a ɗakunansu suka karkashe su. Kuma bai lura ba sa’ad da wata take zagaya a sama kuma bai lura da kukan dabbobi da ke kusa ba. Wataƙila yana addu’a game da shawara mai muhimmanci da yake son ya tsai da, wato na zaɓan manzanni 12. Ka yi tunanin yadda Yesu ya shaƙu cikin addu’a yayin da yake gaya wa Ubansa dukan ra’ayinsa da kuma damuwarsa game da kowanne almajiri yayin da yake roƙonsa ya yi masa ja-gora da kuma ba shi hikima.
9. Mene ne za mu iya koya daga misalin Yesu na yin addu’a dukan dare?
9 Shin misalin Yesu ya koya mana cewa dole ne mu yi sa’o’i da yawa muna addu’a? A’a, gama ya faɗa game da mabiyansa: “Ruhu lallai ya yarda, amma jiki rarrauna ne.” (Mat. 26:41) Duk da haka, muna iya yin koyi da Yesu. Alal misali, muna addu’a ga Ubanmu na samaniya kafin mu tsai da shawara da za ta shafe mu da iyalinmu ko kuma yadda ’yan’uwanmu Kiristoci suka bauta wa Allah? Shin muna addu’a game da ’yan’uwanmu masu bauta wa Jehobah? Shin muna faɗan abin da ke zuciyarmu ko kuma muna maimaita tsarin kalmomi da ke rubuce? Ka lura cewa Yesu yana son yin magana da Ubansa shi kaɗai. A yau da mutane sun shagala da aiki, yana da sauƙi a manta da abin da ya fi muhimmanci. Za mu fi yin tsaro idan mun ba da lokaci sosai ga yin addu’a na kanmu. (Mat. 6:6, 7) Za mu kusaci Jehobah, kuma za mu yi ɗokin ƙarfafa dangantakarmu da shi da kuma ƙin yin kome da zai ɓata dangantakarmu da shi.—Zab. 25:14.
YADDA ZA MU YI TSARO A AIKIN YIN WA’AZI
10. Wane misali ne ya nuna yadda Yesu ya kasance a faɗake ga neman zarafin yin wa’azi?
10 Yesu ya yi tsaro a aikin da Jehobah ya ba shi. Da akwai wasu ayyuka da za su sa mutum ya yi tunanin wasu abubuwa sa’ad da yake aiki kuma hakan ba zai jawo masa matsaloli masu tsanani ba. Amma da akwai ayyuka masu yawa da za su bukaci a mai da hankali kuma a kasance a faɗake, aikin wa’azi yana cikin irin waɗannan ayyukan. Yesu ya kasance a faɗake a aikinsa, yana neman zarafi na yi wa mutane wa’azi. Alal misali, sa’ad da shi da almajiransa suka isa garin Sukar bayan sun yi tafiya mai nisa, almajiran suka tafi su saya abinci. Yesu ya zauna a bakin rijiya da ke garin don ya huta, amma ya kasance a faɗake, kuma sai ya samu zarafin yin wa’azi. Wata mata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Da Yesu ya zaɓa ya ɗan yi barci a wannan lokacin. Da ya nemi hujjoji na ƙin yi mata magana. Amma ya soma tattaunawa da ita, kuma ya ba da shaida sosai da ya taimaki mutane da yawa a birnin Sukar. (Yoh. 4:4-26, 39-42) Shin za mu iya ƙara yin koyi da misalin Yesu na yin tsaro, wataƙila ta yin ƙoƙari mu kasance a faɗake ga neman zarafin yi wa mutane da muke haɗuwa da su kullum wa’azin?
11, 12. (a) Ta yaya Yesu ya bi da waɗanda suke son su janye hankalinsa daga aikinsa? (b) Yaya Yesu ya kasance da daidaita a hidimarsa?
11 A wasu lokatai, mutane masu manufa mai kyau sun nemi su janye hankalin Yesu daga aikinsa. Mutanen birnin Kafarnahum suna son Yesu ya kasance da su domin mu’ujizojin da ya yi na warkarwa. Hakan daidai ne. Amma, aikin Yesu shi ne yin wa’azi ga dukan “ɓatattun tumaki na gidan Isra’ila,” ba ga waɗanda suke cikin birni ɗaya ba. (Mat. 15:24) Saboda haka, ya gaya wa waɗannan mutanen: “Dole in kai Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk 4:40-44) A bayyane yake cewa abin da ya fi muhimmanci a rayuwar Yesu shi ne hidimarsa. Bai bar kome ya janye hankalinsa ba.
12 Shin Yesu ya shagala ga aikinsa da har ya zama mai tsattsauran ra’ayi ko kuma marar son jin daɗi ne? Ko kuwa ya shagala ainun a hidimarsa da har bai san abin da mutane suke bukata ba? A’a, Yesu ya kasance da daidaita a hidimarsa. Yana more rayuwa kuma ya more cuɗanya da abokansa. Ya daraja iyalai kuma ya nuna juyayi ga bukatunsu da matsalolinsu, kuma ya nuna yana ƙaunar yara.—Karanta Markus 10:13-16.
13. Ta yaya za mu yi koyi da misalin Yesu na yin tsaro da daidaita game da aikinmu na wa’azin Mulki?
13 Yayin da muke yin koyi da misalin Yesu na yin tsaro, yaya za mu yi ƙoƙari mu kasance da daidaita yadda ya yi? Ba za mu bar duniya ta janye hankalinmu daga aikinmu ba. Har ma abokai da dangi masu manufa mai kyau suna iya gaya mana mu rage hidimarmu ko kuma mu biɗi abin da suke ɗauka rayuwa ta yau da kullum ne. Amma idan muna koyi da Yesu, za mu ɗauki hidimarmu a matsayin abinci. (Yoh. 4:34) Hidimarmu tana sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma tana sa mu farin ciki. Duk da haka, ba zai dace mu zama masu rashin daidaita muna nuna adalcin kai ko halin marasa son jin daɗi ba. Kamar Yesu, muna son mu zama bayi masu farin ciki da daidaita na “Allah mai [farin ciki].”—1 Tim. 1:11.
YADDA ZA MU YI TSARO A LOKATAN GWAJI
14. Wane hali ne muke bukatar mu guji sa’ad da muke fuskantar gwaji, kuma me ya sa?
14 Sa’ad da Yesu yake fuskantar gwaje-gwaje ne ya ba mabiyansa gargaɗi mafi gaggawa. (Karanta Markus 14:37.) Sa’ad da muke cikin yanayi mai wuya, muna bukatar mu tuna misalin Yesu fiye da dā. Sa’ad da mutane da yawa suke fuskantar gwaji, suna manta da wata gaskiya mai muhimmanci da aka ambata a littafin Misalai sau biyu saboda muhimmancinta: “Akwai hanya wadda ta ke sosai bisa ga ganin mutum, amma matuƙarta tafarkun mutuwa ne.” (Mis. 14:12; 16:25) Idan muka dogara ga fahiminmu, musamman sa’ad da muke fuskantar matsaloli masu tsanani, za mu sa kanmu da ƙaunatattunmu cikin haɗari.
15. Wane gwaji ne shugaban iyali zai iya fuskanta a lokacin da ake rashin kuɗi?
15 Alal misali, shugaban iyali yana iya fuskantar matsi mai tsanani na biyan bukatun iyalinsa. (1 Tim. 5:8) Yana iya karɓan aikin da zai sa ba zai riƙa halartan taron Kirista a kai a kai ba ko kuma yin ja-gora a bauta ta iyali ko kuma yin wa’azi. Idan yana yin abin da yake gani daidai ne, karɓan aikin zai zama kamar abin da ya dace ne. Amma zai iya rasa abotarsa da Jehobah da kuma juya masa baya. Ya fi kyau a bi gargaɗin da ke Misalai 3:5, 6! Sulemanu ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: a cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”
16. (a) Mene ne muka koya daga misalin Yesu na dogara ga hikimar Jehobah? (b) Ta yaya magidanta da yawa suke yin koyi da misalin Yesu na dogara ga Jehobah a lokacin wahala?
16 Sa’ad da Yesu yake fuskantar gwaji, ya ƙi dogara ga nasa ra’ayi. Ka yi tunani! Mutum mafi hikima da ya taɓa rayuwa a duniya ya ƙi dogara ga nasa hikima. Alal misali, sa’ad da Shaiɗan ya jarabce shi, Yesu a kai a kai ya amsa da kalmomin nan: “An rubuta.” (Mat. 4:4, 7, 10) Ya dogara ga hikimar Ubansa don ya yi tsayayya da gwaji, ta hakan Yesu ya nuna tawali’u da Shaiɗan ba shi da shi. Shin mu ma muna yin hakan? Shugaban iyali wanda yake yin koyi da Yesu a yin tsaro yana barin Kalmar Allah ta yi masa ja-gora, musamman a lokacin wahala. A dukan duniya, magidanta dubbai suna yin hakan. Suna saka Mulkin Allah da bauta ta gaskiya gaba da bukatunsu na zahiri. Ta hakan, suna kula da iyalansu sosai. Jehobah yana albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na yi wa iyalansu tanadi, kamar yadda Kalmarsa ta yi alkawari.—Mat. 6:33.
17. Mene ne ya motsa ka ka yi koyi da yadda Yesu ya yi tsaro?
17 Babu shakka, Yesu ya kafa misali mafi kyau na yin tsaro. Misalinsa yana taimaka mana kuma yana ceton rayuka. Ka tuna cewa Shaiɗan yana son ka yi sanyi a bautarka ga Jehobah. Kuma yana son ya raunana bangaskiyarka da kuma sa ka daina yin ƙwazo kuma ka daina bauta wa Jehobah. (1 Tas. 5:6) Kada ka sa ya yi nasara! Ka yi tsaro kamar Yesu. Ka keɓe lokaci don yin addu’a, ka yi tsaro a hidimarka kuma ka dogara ga Jehobah sa’ad da kake fuskantar gwaje-gwaje. Ta bin wannan tafarkin, za ka more rayuwa mai farin ciki da mai gamsarwa har ma a yanzu yayin da kake gani cewa ƙarshen wannan muguwar duniya tana daɗa kusa. Idan ka yi tsaro, Yesu zai tarar da kai a faɗake sa’ad da ya zo halaka wannan muguwar duniya. Jehobah zai yi farin cikin ba ka ladar kasancewa da aminci!—R. Yoh. 16:15.
[Hoto a shafi na 6]
Yesu ya yi wa matar da ke ɗiban ruwa a rijiya wa’azi. Waɗanne zarafi kake samu don yin wa’azi kullum?
[Hoto a shafi na 7]
Taimaka wa iyalinka su bauta wa Jehobah yana nuna cewa kana yin tsaro