Nathan—Ya Ɗaukaka Bauta Ta Gaskiya da Aminci
Ba shi da sauƙi a gaya wa mutum mai iko cewa abin da ya yi ba shi da kyau kuma yana bukatar gyara. Shin za ka samu gaba gaɗi ka gaya wa mutumin idan ka san cewa ya kashe wani don ya rufe asirinsa?
Sarki Dauda ya yi zina da Bath-sheba kuma ya yi mata ciki. Don ya rufe asirinsu, Dauda ya sa aka kashe mijinta, kuma ya ɗauki Bath-sheba a matsayin matarsa. Dauda ya ci gaba da yin hidimarsa a matsayin sarki na watanni masu yawa kuma bai gaya wa kowa game da zunubinsa ba. Amma Jehobah bai ƙyale hakan ba. Ya aiki annabi Nathan ya gaya masa kuskurensa.
Wannan aikin ba shi da sauƙi. Ka yi tsammani cewa kai ne Nathan. Da me za ka yi? Amincin Nathan ga Jehobah da kuma gaba gaɗin bin ƙa’idodin Allah ne ya sa shi ya tuna wa Dauda zunubin da ya yi. Yaya annabin zai yi hakan kuma ya sa sarki Dauda ya gane cewa yana bukatar tuba?
MALAMI MAI BASIRA
Ka ɗauki ’yan mintoci ka karanta 2 Sama’ila 12:1-25. A ce kai ne Nathan, kuma kana gaya wa Dauda wannan labarin: “Dā akwai mutum biyu a cikin wani birni; ɗaya mai-arziki ne, ɗayan kuwa talaka ne. Mai-arzikin nan yana da garkunan tumaki da na shanu da yawa ƙwarai: amma matalaucin ba shi da kome, sai dai wata yar tumkiya wadda ya saya ya yi kiwonta kuma: ta yi girma tare da shi da ’ya’yansa kuma; ta kan ci daga cikin nasa rabon abinci, ta sha daga wajen nasa ƙoƙo, ta kwanta a ƙirjinsa, ta zama masa daidai kamar ɗiya. Sai kuma wani mai-tafiya ya zo wurin mai-arzikin, shi kuwa ya hana a ɗauka daga cikin nasa garken da cikin nasa shanu abin da za ya shirya wa mai-tafiyan da ya zo wurinsa, sai ya ɗauki yar tumkiya ta talakan nan, ya shirya ma mutumin da ya zo wurinsa.”—2 Sam. 12:1-4.
Da yake Dauda makiyayi ne a dā, ya gaskata cewa wannan labarin gaskiya ne. Wani mai ba da ƙarin bayani ya ce, “Wataƙila Nathan ya saba zuwa wajen Dauda ya yi roƙo a madadin waɗanda aka yi musu rashin adalci kuma ba su da mai taimako.” Ko idan hakan gaskiya ne, Nathan yana bukatar ya kasance da aminci ga Allah da kuma gaba gaɗi don ya yi wa sarki magana haka. Labarin da Nathan ya ba da ya sa Dauda fushi ƙwarai. Dauda ya ce: “Na rantse da ran Ubangiji, mutumin da ya yi wannan ya isa mutuwa.” Sai Nathan ya ce masa: “Kai ne mutumin nan.”—2 Sam. 12:5-7.
Ka yi tunanin dalilin da ya sa Nathan ya zaɓa ya gaya wa Dauda wannan matsalar a wannan hanyar. Ba shi da sauƙi mutum ya fahimci yanayin abokinsa na kud da kud haka ba. Dukanmu mukan ba da hujja don mu bayyana ayyukanmu. Amma labarin da Nathan ya ba da ya sa Dauda ya yanke wa kansa hukunci ba tare da saninsa ba. Sarkin ya fahimci dalla-dalla cewa abin da Nathan ya kwatanta ya yi muni sosai. Sai sa’ad da Dauda ya yanke hukunci ne Nathan ya gaya masa cewa wannan kwatancin game da Dauda ne. Haka ne ya sa Dauda ya fahimci yadda zunubinsa yake da tsanani. Wannan ya taimake shi ya kasance da ra’ayi mai kyau ya karɓi horo. Dauda ya yarda cewa ya “rena” Jehobah ta abin da ya yi da Bath-sheba, kuma ya karɓi horon.—2 Sam. 12:9-14; Zab. 51.
Mene ne muka koya daga wannan? Manufar malamin Littafi Mai Tsarki ita ce ya taimaka wa masu sauraro su yi tunani game da batutuwa kuma su fahimci abin da ya dace. Nathan ya daraja Dauda kuma ya yi masa magana cikin basira. Nathan ya san cewa Dauda yana ƙaunar adalci da kuma gaskiya. Saboda haka, ya yi amfani da labarin da ya san zai shafi mutumin da yake da irin waɗannan halaye masu kyau. Mu ma za mu iya taimaka wa mutane su fahimci ra’ayin Jehobah. Ta yaya? Ta wajen yin amfani da abin da suka san ya yi daidai ba tare da sa su ji cewa mun fi su ko kuma muna gaya musu abin da za su yi ba. Littafi Mai Tsarki ne yake gaya mana abin da ya dace da kuma abin da ba shi da kyau, ba ra’ayinmu ba.
Amincin Nathan ga Allah ne musamman ya taimaka masa ya tsauta wa sarki mai iko. (2 Sam. 12:1) Hakazalika, amincinmu ga Allah zai ba mu ƙarfin zuciyar kāre mizanan adalci na Jehobah.
YA ƊAUKAKA BAUTA TA GASKIYA
Kamar dai Nathan da Dauda abokai ne sosai, gama Dauda ya ba wani cikin ’ya’yansa maza sunan nan Nathan. (1 Laba. 3:1, 5) A lokaci na farko da aka ambata Nathan a cikin Littafi Mai Tsarki yana tare da Dauda. Dukansu suna ƙaunar Jehobah. Babu shakka cewa sarkin ya tabbata da ra’ayin Nathan domin ya gaya wa annabin cewa yana so ya gina wa Jehobah haikali. Dauda ya ce: “Ga shi yanzu, ni ina zaune cikin gida na cedar, amma sanduƙin Allah yana zaune cikin makarai na zane.” Da hakan Nathan ya gaya wa sarkin: “Je ka, ka yi dukan abin da ke a ranka; gama Ubangiji yana tare da kai.”—2 Sam. 7:2, 3.
Nathan mai bauta wa Jehobah ne da aminci, kuma saboda haka, yana shirye ya goyi bayan shirin Dauda na gina haikali na farko na bauta ta gaskiya a duniya. Amma a wannan lokacin, Nathan ya faɗi ra’ayinsa ba abin da Jehobah ya gaya masa ba. A daren nan, Allah ya gaya wa annabinsa ya kai wa sarkin wani saƙo dabam cewa, Dauda ba zai gina haikalin Jehobah ba. Ɗaya cikin ’ya’yan Dauda ne zai yi ginin. Amma, Nathan ya sanar cewa Allah ya yi alkawari da Dauda cewa kursiyinsa “za ya tsaya har abada.”—2 Sam. 7:4-16.
Ra’ayin Nathan game da wanda zai gina haikali bai jitu da nufin Allah ba. Amma ba tare da yin gunaguni ba, wannan annabi mai tawali’u ya amince da ja-gorar Jehobah kuma ya ba da haɗin kai. Wannan misali ne mai kyau da ya kamata mu bi idan Allah ya yi mana gyara! Nathan ya ci gaba da samun amincewar Allah domin yadda Jehobah ya yi amfani da shi bayan hakan a matsayin annabi. Kamar dai Jehobah ya hure Nathan da Gad mai ganin wahayi su ja-goranci Dauda wajen tsara mawaƙa 4,000 a hidimar haikali.—1 Laba. 23:1-5; 2 Laba. 29:25.
YA GOYI BAYAN SARAUTAR
Nathan ya san cewa Sulemanu ne zai zama sarki bayan Dauda. Saboda haka, Nathan ya aikata nan da nan sa’ad da Adonijah ya yi ƙoƙari ya yi wa Dauda juyin mulki sa’ad da ya tsufa. A wannan lokacin kuma, Nathan ya nuna basira da aminci. Da farko ya aririci Bath-sheba ta tuna wa Dauda alkawarin da ya yi na naɗa ɗansu Sulemanu sarki. Sai Nathan da kansa ya je wurin sarkin don ya tambaye shi ko ya zaɓe Adonijah ya zama sarki bayan shi. Da yake ya fahimci yanayin, sarkin ya umurci Nathan da wasu bayi masu aminci su naɗa Sulemanu sarki kuma su sanar da hakan. Adonijah bai yi nasara ba a ƙullinsa na naɗa kansa sarki ba.—1 Sar. 1:5-53.
ƊAN TARIHI MAI TAWALI’U
Mutane sun gaskata cewa Nathan da Gad ne marubutan Sama’ila na ɗaya surori na 25 zuwa 31 da kuma littafin Sama’ila na biyu. Waɗannan littattafan da aka hure sun ce: “Ayyukan Dauda sarki fa, da na farko da na ƙarshe, ga shi, an rubuta su cikin labarin Sama’ila mai-gani, da cikin labarin Nathan annabi, da cikin labarin Gad mai-gani.” (1 Laba. 29:29) Littafi Mai Tsarki ya kuma ambata cewa Nathan ya rubuta game da “ayyukan Solomon.” (2 Laba. 9:29) Hakan yana nufin cewa, wataƙila Nathan ya ci gaba da hidima a fadar sarki bayan rasuwar Dauda.
Wataƙila annabi Nathan ne da kansa ya rubuta abubuwa da yawa da muka sani game da shi. Amma muna iya koyan abubuwa da yawa game da shi daga abin da bai rubuta ba. Babu shakka, Nathan ɗan tarihi ne mai tawali’u, kuma ba shi da burin zama sananne. Wani ƙamus da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce, an ambata shi cikin Littafi Mai Tsarki ba tare da “gabatarwa ba kuma ba a ba da bayani game da iyalinsa ba.”
AMINCI GA JEHOBAH NE YA MOTSA SHI
Daga ɗan abubuwan da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki game da Nathan, mun san cewa shi mai tawali’u ne da kuma mai ƙwazo wajen goyon bayan mizanan Allah. Jehobah Allah ya ba shi ayyuka masu yawa. Ka yi bimbini a kan halayen Nathan, kamar su aminci ga Allah da kuma ƙaunar mizanan Allah. Ka yi ƙoƙari ka yi koyi da irin waɗannan halayen.
Wataƙila ba za a gaya maka ka tsauta wa sarakuna da suka yi zina ba ko kuma hana ƙullin da wani ya yi na zama sarki ba. Amma da taimakon Allah, za ka iya kasancewa da aminci ga Allah kuma ka ɗaukaka mizanansa na adalci. Za ka iya zama mai gaba gaɗi da malamin mai faɗan gaskiya da kuma mai goyon bayan bauta ta gaskiya.
[Hoto a shafi na 25]
A matsayin mai goyon bayan sarautar, Nathan ya yi magana da Bath-sheba cikin basira