Ka Koya Daga Kalmar Allah
Mene Ne Zai Faru da Addini?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Dukan addinai ne suke da kyau?
Akwai mutanen da suke son su faranta wa Allah rai a dukan addinai. Allah yana ganin mutanen nan kuma ya damu da su. Amma, abin baƙin ciki shi ne, wasu mutane suna aikata mugunta da sunan Allah. A dā, shugabannin addinai sun azabtar da waɗanda suke hamayya da su. (2 Korintiyawa 4:3, 4; 11:13-15) A yau, daga rahotannin da ake samu a labarai, wasu shugabannin addinai sun ƙarfafa ta’adanci, wasu sun goyi bayan yaƙi ko kuma sun yi lalata da yara.—Karanta Matta 24:3-5, 11, 12.
Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa akwai addinai iri biyu, akwai addini na gaskiya da kuma addinin ƙarya. Addinin ƙarya ba ya koyar da gaskiya game da Allah. Amma, Jehobah Allah yana son mutane su san gaskiya game da shi.—Karanta 1 Timotawus 2:3-5.
2. Mene ne zai faru da addini?
Allah ba ya son addinai masu da’awar cewa suna ƙaunarsa amma ba sa koyar da gaskiya game da shi su ruɗi mutane. Hakika, mabiyan waɗannan addinan suna son abuta da duniyar da ke ƙarƙashin Shaiɗan Iblis. (Yaƙub 4:4; 1 Yohanna 5:19) Kalmar Allah ta kamanta addinan da suke yin ibada ga gwamnatocin ’yan Adam maimakon Allah da karuwa. Littafi Mai Tsarki ya kira karuwar nan “Babila Babba,” wadda ita ce suna tsohon birnin nan inda addinin ƙarya ya samo asali bayan Rigyawar da aka yi a zamanin Nuhu. Ba da daɗewa ba, Allah zai kawo halaka na ba zato ga addinai masu ruɗin ’yan Adam kuma suna zaluntar su.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2, 5, 17; 18:8, 23, 24.
3. Ta yaya Allah zai sa mutane a dukan duniya su yi murna?
Hukuncin da za a zartar a kan addinan ƙarya a nan gaba albishiri ne. Hakan zai kawo ƙarshen zaluncin da ake yi a faɗin duniya. Addinan ƙarya ba za su sake ruɗin mutane kuma su raba kansu ba.—Karanta Ishaya 11:9; Ru’ya ta Yohanna 18:20, 21; 21:3, 4.
4. Mene ne ya kamata sahihan mutane su yi?
Jehobah bai manta da sahihan mutanen da suke cikin addinan ƙarya a dukan duniya ba. A yanzu haka yana haɗa kan waɗannan mutanen ta wajen koya musu gaskiya.—Karanta Mikah 4:2, 5.
Jehobah yana marabtar waɗanda suke son su bauta masa zuwa cikin iyalinsa. Ko da abokanmu da dangoginmu ba sa farin ciki da matakin da muka ɗauka na bauta wa Jehobah, ba za mu taɓa yin asara ba. Za mu ƙulla abuta da Allah, za mu samu sabon “iyalin” da ke ƙaunar mu kuma za mu kasance da begen yin rayuwa har abada.—Karanta Markus 10:29, 30; 2 Korintiyawa 6:17, 18.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 15 da 16 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 24]
The Complete Encyclopedia of Illustration/J. G. Heck