Kana Daraja Aure A Matsayin Baiwa Daga Wurin Allah Kuwa?
“Ubangiji shi yarda maku ku sami hutawa, kowace ɗayanku a cikin gidan mijinta.”—RUTH 1:9.
KA NEMI AMSOSHIN WAƊANNAN TAMBAYOYIN:
Me ya sa za mu iya ce bayin Allah na zamanin dā sun daraja aure a matsayin baiwa daga Allah?
Yaya muka san cewa zaɓin da muka yi na aboki ko abokiyar aure yana da muhimmanci ga Jehobah?
Wace shawara game da aure ce kake son ka yi amfani da shi a rayuwarka?
1. Mene ne Adamu ya yi sa’ad da Allah ya ba shi mata?
“WANNAN yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana: za a ce da ita Mace, domin daga cikin Namiji aka ciro ta.” (Far. 2:23) Adamu mutum na fari ya yi farin ciki sosai domin Allah ya ba shi kyakkyawar mata! Kuma shi ya sa ya furta waɗannan kalmomin. Allah ya sa Adamu ya yi barci mai zurfi sosai, sai ya cire haƙarƙarinsa kuma ya yi mace da shi. Daga baya Adamu ya kira ta Hauwa’u. Allah ya ɗaura musu aure. Domin Jehobah ya yi amfani da haƙarƙarin Adamu don ya halicce ta, Adamu da Hauwa’u sun fi kowanne ma’aurata a yau kusantar juna.
2. Me ya sa namiji da ta mace suke son juna?
2 Jehobah ya halicci namiji da ta mace don su so juna. Kuma wannan soyayya ce take haɗa namiji da ta mace. Mutane da yawa suna sa rai cewa idan sun yi aure, soyayyarsu za ta dawwama. Kuma hakan ya faru sau da dama tsakanin Shaidun Jehobah da yawa.
SUN DARAJA AURE A MATSAYIN BAIWA
3. Ta yaya Ishaƙu ya samu mata?
3 Ibrahim mai aminci ya daraja aure sosai. Saboda haka, ya aiki babban bawansa zuwa ƙasar Mesopotamiya don ya samo wa ɗansa Ishaƙu mata. Wannan bawan Ibrahim ya yi addu’a ga Jehobah kuma hakan ya sa ya samu sakamako mai kyau. Ya samo wa Ishaƙu mata mai suna Rifkatu kuma tana tsoron Allah. Kuma tana cikin waɗanda Jehobah ya yi amfani da su wajen cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim cewa dukan al’ummai za su sami albarka ta zuriyarsa. (Far. 22:18; 24:12-14, 67) Mutane da yawa a yau suna zaɓan mata ko mijin da za su aura. A wasu lokatai, wasu suna samo wa abokansu mata ko miji. Amma bai kamata mu yi hakan ba idan ba su ba mu izini ba. Kuma Allah ba ya zaɓar wa mutum mata ko miji. Amma idan Kiristoci suna son su yi aure ko kuma suna son wasu abubuwa, Allah zai iya taimaka musu. Kuma hakan zai yiwu idan sun yi addu’a ga Allah cewa ya taimake su kuma sun bi ja-gorar ruhunsa.—Gal. 5:18, 25.
4, 5. Ta yaya ka sani cewa Bashulammiyar da makiyayin suna son juna?
4 Akwai wata kyakkyawar budurwa ’yar Shulem a ƙasar Isra’ila ta dā. Wannan budurwar ba ta son ƙawayenta su tilasta mata ta auri Sarki Sulemanu wanda yake da mata da yawa a lokacin. Ta ce: “Ina yi maku kashedi, ku ’yan matan Urushalima, kada ku tada ƙauna, kada ku falkar da ita, sai ta yarda tukuna.” (W. Waƙ. 8:4) Bashulammiyar da wani makiyayi saurayi suna son juna sosai. A cikin tawali’u ta ce: “Ni ne furen rose na filin jejin sharon, ni ne kuma lily na kwari. Kuma sai makiyayi saurayin ya ce: “Kamar furen lily cikin ƙayayuwa, haka nan masoyiyata cikin ’yan mata take.” (W. Waƙ. 2:1, 2) Ƙwarai, suna bala’in son juna.
5 Bashulammiyar da kuma makiyayi saurayinta za su ji daɗin aurensu domin suna ƙaunar Allah. Bashulammiyar ta ce wa masoyiyanta makiyayi: ‘Sa ni kamar hatimi a bisa zuciyarka, kamar hatimi a hannunka: gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa: kishi yana da mugunta kamar kabari, harshensa harshen wuta ne, harshen wuta mai-tsanani na Ubangiji. Ruwa mai-yawa ba shi da iko shi ɓice ƙauna, rigyawa ba ta da iko ta dulmaye ta. Ko da mutum za ya miƙa dukan dukiyar gidansa, shi sayi ƙauna, sai a yi masa reni matuƙa.’ (W. Waƙ. 8:6, 7) Hakazalika, irin ɗabi’a da amana da bayin Allah za su bukaci daga abokin aurensu ke nan.
ZAƁINKA YANA DA MUHIMMANCI GA ALLAH
6, 7. Ta yaya muka sani cewa zaɓin da muka yi na matar da za mu aura yana da muhimmanci ga Jehobah?
6 Zaɓinka na matan da za ka aura yana da muhimmanci ga Jehobah. Alal misali, Jehobah ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi game da mutanen ƙasar Kan’ana. Ya ba Isra’ilawa umurni cewa: “Ba za ka yi surukuta da su ba; ɗiyarka ba za ka ba ɗansa ba, ba kuwa za ka ɗauka ma ɗanka ɗiyatasa ba. Gama za shi juyadda ɗanka ga barin bina, domin su bauta ma waɗansu alloli: hakanan fushin Ubangiji za ya yi ƙuna a kanku, ya hallaka ka farat ɗaya.” (K. Sha 7:3, 4) Shekaru da yawa bayan haka, Ezra firist ya ce: “Kun yi laifi, kun yi auren mata baƙi, da hakanan kun ƙara laifin Isra’ila.” (Ezra 10:10) Bayan haka kuma, manzo Bulus ya ce wa Kiristoci: ‘Mata a ɗaure ta ke muddar ran mijinta; amma idan mijin ya rasu, a sake ta ke ta auri wanda ta ga dama; sai dai cikin Ubangiji.’ (1 Kor. 7:39)
7 Mashaidin Jehobah da bai auri Mashaidiya ba ya yi rashin biyayya ga Jehobah. Isra’ilawan zamanin Ezra sun yi rashin biyayya sa’ad da suka auri matan da ba sa bauta wa Jehobah. Nassosi sun bayyana wa Kiristoci dalla-dalla wadda ya kamata su aura. Bai dace Kirista ya nemi hujja don ya karya dokar Jehobah ba. (Ezra 10:10; 2 Kor. 6:14, 15) Saboda haka, Kirista da ya auri wadda ba ta bauta wa Jehobah bayan ya yi baftisma zai iya rasa gatansa a cikin ikilisiya. Kuma ba zai dace Kirista ya yi addu’a cewa Jehobah ya albarkace shi sa’ad da ya yi masa rashin biyayya ba, yana cewa: ‘Jehobah na yi maka rashin biyayya da gangan, amma duk da haka, ina son ka yi mini albarka.’
UBANMU NA SAMA YA SAN ABIN DA YA FI DACEWA DA MU
8. Ka bayyana dalilin da ya sa ya kamata mu bi shawarar da Jehobah ya ba da game da aure.
8 Mutumin da ya ƙera inji ya san yadda yake aiki. Zai iya ba da shawara a kan yadda za a yi amfani da shi. Kuma idan ba a bi shawarar ba, za a iya ɓata injin. Ko ba haka ba? Hakan ma yake da aure, dole ne mu bi shawarar da Jehobah ya ba da tun da shi ne ya kafa aure.
9. Me ya sa Jehobah ya kafa aure?
9 Jehobah ya san kome game da ’yan Adam da kuma aure. Yana son mutane su ‘yalwata da ’ya’ya, su riɓu,’ shi ya sa ya halicci mutane da sha’awar yin jima’i. (Far. 1:28) Allah ya san cewa mutane za su iya kaɗaitawa, shi ya sa kafin ya halicci mace ta fari, ya ce: “Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” (Far. 2:18) Jehobah yana son ma’aurata su yi farin ciki.—Karanta Misalai 5:15-18.
10. Mene ne ma’aurata za su iya yi don su faranta wa Jehobah rai?
10 Babu auren da ba a samun matsala a ciki, domin dukanmu mun gaji ajizanci daga iyayenmu na fari, wato, Adamu da Hauwa’u. Amma, idan bayin Jehobah sun bi shawarar da ke Kalmar Allah a rayuwarsu, za su yi farin ciki sosai a aurensu. Alal misali, manzo Bulus ya ba da shawara dalla-dalla game da jima’i a aure. (Karanta 1 Korintiyawa 7:1-5.) Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba cewa sai sa’ad da ma’aurata suke son su haifi yara ne kaɗai za su sadu da juna. Kuma hakan zai iya gamsar da bukatansu na zahiri da kuma na motsin rai. Amma yin jima’i da ba bisa ƙa’ida ba tsakanin ma’aurata yana ɓata wa Allah rai. A wannan sashe mai muhimmanci na rayuwa, ya kamata miji ko mata da Kiristoci ne su bi da juna da kirki kuma su nuna cewa suna ƙaunar juna da gaske.
11. Ta yaya aka albarkaci Ruth don ta yi biyayya ga dokokin Jehobah?
11 Ya kamata aure ya sa mutane murna da kuma farin ciki. Kuma ya kamata kwanciyar hankali ta kasance a iyalin Kirista. Ka yi la’akari da abin da ya faru shekara dubu uku da ta shige. Wata tsohuwa mai suna Naomi da surukanta Orpah da Ruth gwauraye ne. Sa’ad da za su koma ƙasar Yahuda daga ƙasar Mowab, Naomi ta gaya wa Orpah da Ruth su koma gida. Amma Ruth ta bi Naomi zuwa ƙasar Yahuda. Kuma ta ci gaba da kasancewa da ita da kuma bauta wa Allah na gaskiya. Boaz wani dattijo ne da ke bauta wa Jehobah. Ya gaya wa Ruth: “Ubangiji ya sāka miki aikinki, ki karɓi cikakkiyar lada daga wurin Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kika zo neman mafaka ƙarƙashin fukafukansa.” (Ruth 1:9; 2:12) Tun da yake Ruth ta daraja aure, sai ta amince ta auri Boaz. A nan gaba sa’ad da za a mai da duniya aljanna kuma a ta da matattu, Ruth za ta yi farin cikin sanin cewa ta zama kakar Yesu Kristi. (Mat. 1:1, 5, 6; Luk 3:23, 32) Ta kasance da aminci ga Jehobah kuma ta samu albarka sosai.
SHAWARA MAI KYAU DON YIN FARIN CIKI A AURE
12. Daga ina ne za mu iya samun shawara mai kyau game da aure?
12 Allah ya gaya mana abin da ya kamata mu yi don mu yi farin ciki a aurenmu. Babu ɗan Adam da ya kai shi ilimi. Amma, mene ne zai faru da mutumin da ya yi aure sau da yawa kuma ya kashe auren? Ba zai dace mu nemi shawara daga wurinsa ba. Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya ba mu shawara mai kyau game da aure. Saboda haka, ya kamata kowanne mutum da zai ba da shawara game da aure ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki. Alal misali, manzo Bulus ya rubuta: “Sai ku kuma kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” (Afis. 5:33) Ya kamata kowanne Kirista da ya manyanta ya fahimci wannan ayar, tun da a bayyane take. Amma babbar tambayar ita ce: ‘Shin za su bi wannan shawarar da ke cikin Kalmar Allah?’ Za su yi hakan idan suna daraja baiwar da Jehobah ya ba mu na yin aure.a
13. Mene ne zai iya faruwa idan maigida bai bi shawarar da ke 1 Bitrus 3:7 ba?
13 Ya kamata miji wanda Kirista ne ya ƙaunaci matarsa. Manzo Bitrus ya ce: “Haka nan kuma ku mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi, da kuma masu-tarayyan gado na alherin rai: domin kada addu’o’inku su hanu.” (1 Bit. 3:7) Idan miji bai bi shawarar Jehobah ba, Jehobah ba zai amsa addu’arsa ba. Hakan zai iya sa su yin alhini sosai, su riƙa cin musu kuma su riƙa yin fushi da juna.
14. Wane alheri ne mace mai ƙauna take yi wa iyalinta?
14 Matar da ta bi shawarar da ke Littafi Mai Tsarki kuma ta ƙyale ruhun Allah ya yi mata ja-gora za ta shaida farin ciki da lumana a cikin iyalinta. Ya dace maigida Kirista ya ƙaunaci matarsa kuma ya kāre ta. Matar da Kirista ce tana son a ƙaunace ta kuma hakan yana sa ta kasance da halayen da za su sa maigidan ya ƙaunace ta sosai. Littafin Misalai 14:1 ya ce: “Kowace mace mai-hikima ta kan gina ɗakinta: amma mai-wauta ta kan rushe shi da hannuwa nata.” Mace mai hikima da ƙauna tana yin abubuwa da yawa da za su sa iyalinta ta yi farin ciki kuma ta samu ci gaba. Tana kuma nuna cewa tana daraja baiwar aure da Allah ya tanadar.
15. Wace shawara ce ke littafin Afisawa 5:22-25?
15 Mata da miji suna nuna cewa suna daraja aure a matsayin baiwa daga wurin Allah ta wajen bin misalin Yesu na yadda ya bi da ikilisiyarsa. Suna nuna ƙauna da kuma daraja juna. (Karanta Afisawa 5:22-25.) Ma’auratan da suke ƙaunar juna suna da tawali’u kuma ba sa ƙin yi wa juna magana ko kuma su ƙyale wasu halaye marasa kyau su ɓata dangantakarsu. Jehobah yana yi wa irin wannan iyalin albarka.
KADA KOWA YA RABA SU
16. Me ya sa wasu Kiristoci ba su yi aure ba?
16 Ko da yawancin mutane suna son su yi aure wata rana, amma wasu bayin Jehobah ba su yi aure ba domin ba su samu macen da suke so da kuma take ƙaunar Jehobah ba. Wasu kuma ba su ga damar yin aure ba. Kuma kasancewa marasa aure yana ba mutum damar yin abubuwa da yawa a hidimar Jehobah kuma yana iya sa su samu gamsuwa yayin da ba su yi aure ba.—Mat. 19:10-12; 1 Kor. 7:1, 6, 7, 17.
17. (a) Mene ne Yesu ya ce game da aure? (b) Idan Kirista ya soma sha’awar matar wani ko mijin wata, kuma wane mataki ne ya kamata ya ɗauka nan da nan?
17 Ya kamata mu yi la’akari da kalaman Yesu da ke gaba ko mun yi aure ko a’a: “Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su, har ya ce, saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne wa matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:4-6) Yin sha’awar matar wani ko mijin wata zunubi ne. (K. Sha 5:21) Idan Kirista yana yin wannan sha’awar, ya kamata ya ɗauki mataki nan da nan don ya kawar da irin wannan sha’awar daga zuciyarsa. Kuma wajibi ne ya yi hakan ko da hakan zai jawo masa baƙin ciki da yake ya ƙyale wannan sha’awar ta mamaye shi. (Mat. 5:27-30) Ya wajaba mutum ya kawar da irin wannan tunanin kuma ya daina wannan zunubin.—Irm. 17:9.
18. Yaya ya kamata mu ji game da baiwar yin aure da Allah ya tanadar mana?
18 Mutane da yawa da ba su san Allah ba ko kuma baiwar aure suna daraja aure. Amma mu kuma fa? A matsayinmu na bayin Jehobah “mai-albarka” da suka keɓe kansu, muna farin cikin nuna cewa muna daraja aure a matsayin baiwar da Jehobah ya tanadar.—1 Tim. 1:11.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da aure, ka duba babi na 10 da 11 na littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”
[Bayanin da ke shafi na 6]
Aure mai kyau yana daraja Jehobah kuma yana iya sa kowa a cikin iyalin farin ciki
[Hoto a shafi na 5]
Ruth ta daraja baiwar Allah na yin aure
[Hoto a shafi na 7]
Kana nuna cewa kana daraja baiwar Jehobah na yin aure?