Ka Kasance Da Ra’ayi Mai Kyau Idan Kana Fuskantar Matsala A Aurenka
“Ga waɗanda sun rigaya sun yi aure ina umurni ba kuwa ni ba ne, Ubangiji ne.” —1 KOR. 7:10.
ZA KA IYA BAYYANAWA?
A wace hanya ce Allah ya gama ma’aurata?
Ta yaya dattawa za su iya taimaka wa Kiristocin da suke fuskantar matsaloli a aurensu?
Yaya ya kamata mu ɗauki aure?
1. Yaya ne ya kamata Kiristoci su ɗauki aure? Me ya sa?
SA’AD DA Kiristoci suka yi aure, suna yin wa’adi a gaban Allah kuma ya kamata su ɗauki wannan wa’adin da muhimmanci sosai. (M. Wa. 5:4-6) Jehobah ne ya kafa aure, saboda haka, shi ne ya haɗa ko kuma “gama” ma’aurata. (Mar. 10:9) A wasu lokatai, dokar ƙasa game da aure da kuma ta Littafi Mai Tsarki suna saɓawa da juna. Amma, ya kamata bayin Jehobah su bi dokar da Allah ya kafa game da aure. Ya wajaba bayin Jehobah su kasance da ra’ayin Jehobah ko da a lokacin da suka yi auren ba sa bauta wa Jehobah.
2. Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifin?
2 Aure zai iya sa mu farin ciki sosai. Mene ne za mu iya yi idan ba ma jin daɗin aurenmu? Shin za a iya gyara irin wannan auren ne? Mene ne zai iya taimaka wa ma’aurata idan ba sa zaman lafiya a aurensu?
ZA A JI DAƊIN AUREN NE KO A’A?
3, 4. Me zai iya faruwa idan ba a tsai da shawara mai kyau sa’ad da ake zaɓan abokin aure ba?
3 Idan auren Kirista yana da daɗi, yana sa shi farin ciki kuma yana daraja Jehobah. Idan ba haka ba zai kawo baƙin ciki. Kiristocin da ba su yi aure ba za su iya yin aure a hanyar da ta dace idan suka bi ja-gorar Allah. Amma, mutumin da bai tsai da shawara mai kyau sa’ad da yake zaɓar wadda zai aura ba zai iya samun matsala da kuma baƙin ciki a aurensa. Alal misali, wasu matasa suna soma fita zance tun ba su yi shirin ɗaukar ɗawainiyar da ke tattarre da yin aure ba. Wasu sukan samu abokiyar aure daga Intane. Nan da nan sai su yi aure kuma su fara baƙin ciki. Wasu sukan yi aure ko da sun yi zunubi sosai sa’ad da suke fita zance, kuma hakan zai sa ba za su riƙa ɗaukan juna da daraja ba.
4 Wasu Kiristoci ba su yi aure “cikin Ubangiji” ba, saboda haka, sun soma baƙin ciki domin abokin aurensu ba ya bauta wa Jehobah. (1 Kor. 7:39) Idan ka sami kanka a wannan halin, ka nemi gafara da kuma taimakon Allah ta yin addu’a. Jehobah ba zai kawar da matsalolin da suka taso don kurakuren da muka yi a dā ba, amma yana taimakon waɗanda suka tuba su jimre da matsalolinsu. (Zab. 130:1-4) Ka yi iya ƙoƙarinka ka faranta wa Allah rai kuma “farinciki na Ubangiji” zai ƙarfafa ka.—Neh. 8:10.
IDAN AURENKA YANA CIKIN HAƊARI
5. Idan aure yana cikin haɗari, wane irin tunani ne bai kamata ka yi ba?
5 Idan wasu ba sa jin daɗin aurensu, za su iya yin wannan tunanin: Neman magance matsalar da muke fuskanta a auren nan ba ɓata lokaci ba ne kawai? Wataƙila zan fi farin ciki idan na auri wata! Suna iya yin tunanin barin abokiyar aurensu don suna ganin za su samu sakewa. Zai fi dacewa mu kashe auren ne? Ko da ba zan iya kashe aure bisa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba zan iya barin abokiyar aurena don in soma jin daɗin rayuwata kuma. Maimakon yin irin wannan tunanin ko yin da-na-sani, ya kamata Kiristoci su yi iya ƙoƙarinsu su magance matsalar ta wajen bin ja-gorancin Allah.
6. Ka bayyana abin da Yesu ya faɗa a Matta 19:9.
6 Kirista da ya kashe aurensa ba shi da dama ya sake yin aure sai dai idan abokiyar aurensa ta yi fasikanci. Yesu ya ce: “Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.” (Mat. 19:9) A wannan ayar, “fasikanci” ya haɗa da zina da kuma sauran zunubin lalata. Yana da muhimmanci Kirista ya yi addu’a don Allah ya ja-gorance shi idan yana tunanin kashe aure ba tare da wani a cikinsu ya yi zina ba.
7. Mene ne mutane za su ce idan Kiristoci ma’aurata suka kashe aurensu?
7 Idan Kirista ya kashe aurensa, hakan zai nuna cewa ba shi da dangantaka mai kyau da Jehobah. Manzo Bulus ya yi wannan tambaya mai muhimmanci: “Idan mutum ya rasa yadda za shi mallaki nasa gida, ƙaƙa za ya goyi ekklesiyar Allah?” (1 Tim. 3:5) Hakika, idan Kiristoci ma’aurata suka kashe aurensu, mutane za su ce ba sa bin ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki.—Rom. 2:21-24.
8. Idan Kiristoci ma’aurata suka yanke shawarar kashe aurensu, mene ne matsalarsu?
8 Idan Kiristoci ma’aurata suna shirin rabuwa ko kuma kashe aurensu kuma hakan bai jitu da abin da Nassi ya ce ba, suna da matsala a dangantakarsu da Jehobah. Zai iya zaman cewa ɗaya daga cikinsu ko kuma dukansu biyu ba sa bin ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki. Idan dukansu biyu sun dogara da Jehobah da dukan zuciyarsu, za su iya magance matsalolin da ke aurensu.—Karanta Misalai 3:5, 6.
9. Ta yaya wasu Kiristoci suka samu albarka don ƙoƙarcen-ƙoƙarcensu na magance matsalolin aurensu?
9 Ma’aurata da yawa sun yi nasara wajen magance matsalar aurensu ko da cewa da farko kamar hakan ba zai yiwu ba. Allah yakan albarkaci ma’aurata da suka ƙi yin watsi da aurensu saboda matsaloli. Alal misali, ka yi la’akari da abin da zai iya faruwa idan mijin ba Mashaidi ba ne. Manzo Bitrus ya ce: “Ku mataye kuma, ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.” (1 Bit. 3:1, 2) Mutumin da ba Mashaidi ba ne zai iya soma bauta wa Jehobah saboda halin kirki na abokiyar aurensa! Kiristoci da suka magance matsalolin aurensu kuma suka ci gaba da kasancewa tare suna girmama Allah kuma za su samu albarka.
10, 11. Waɗanne abubuwa ne za su iya jawo matsaloli a aure, amma wane taimako ne Kiristoci za su iya samu?
10 Kiristoci da yawa da suke son su faranta wa Allah rai suna auran Shaidun da suka keɓe kansu ga Jehobah. Duk da haka, yanayi yakan canja a yadda ba su zata ba. Alal misali, mijin ko matar za ta iya soma gwagarmaya da matsaloli na motsin rai. Ko kuma abokiyar aure za ta iya daina wa’azi har na tsawon wata shida. Abin da ya faru da Linda ke nan,a wata mai shela da ƙwazo wadda mahaifiya ce mai ƙauna. Ba ta ji daɗi ba ko kaɗan sa’ad da mijinta ya fara yin abubuwan da ba su da kyau. Ya ƙi tuba sai aka yi masa yankan zumunci. Mene ne ya kamata Kiristoci da suke irin wannan yanayin su yi idan suna gani ba za a iya ceton aurensu ba?
11 Kana iya tunani: ‘Ina bukata in riƙa ƙoƙarin ceton aurena duk da cewa ba ma jin daɗin auren?’ Bai kamata wani ya yanke maka shawara a kan wannan batun ba. Duk da haka, akwai dalilai masu kyau na ƙin fid da rai a aurenka don ba ka jin daɗinsa. Kiristocin da suka jimre a aurensu duk da cewa ba sa jin daɗinsa suna da tamani a gaban Allah. (Karanta 1 Bitrus 2:19, 20.) Ta wajen amfani da Kalmarsa da kuma ruhunsa, Jehobah zai taimaki Kiritoci idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa aurensu.
SUNA A SHIRYE SU TAIMAKA MAKA
12. Yaya dattawa za su ji game da mu idan muka nemi taimakonsu?
12 Idan kana fuskantar matsaloli a aurenka, ka nemi taimako daga wajen Kiristoci da suka manyanta. Dattawa suna kamar makiyaya ne a cikin ikilisiya kuma za su yi farin cikin ba ka shawarar da ke bisa Littafi Mai Tsarki game da aure. (A. M. 20:28; Yaƙ. 5:14, 15) Mutuncinku ba zai zube a gaban dattawa ba idan kuka gaya musu matsaloli masu tsanani da kuke fuskanta a auren kuma kuka nemi taimakonsu. Za su ƙara ƙaunar ku da kuma daraja ku don za su gane cewa kuna son ku faranta wa Allah rai.
13. Wace shawara ce take 1 Korintiyawa 7:10-16?
13 Sa’ad da dattawa suke taimakon ma’aurata da ɗaya cikinsu ba Mashaidi ba ne, suna iya yin amfani da wannan shawara ta Manzo Bulus: “Ga waɗanda sun rigaya sun yi aure ina umurni ba kuwa ni ba ne, Ubangiji ne, kada matan ta rabu da mijinta idan kuwa ta rigaya ta bar shi, ta zauna haka nan ba miji, ko kuwa ta sulhunta da mijinta; mijin kuma kada ka rabu da matatasa. . . . Gama, ke mata, ina kin sani, ko za ki ceci mijinki? kai fa miji, ina ka sani, ko za ka ceci matarka?” (1 Kor. 7:10-16) Abin farin ciki ne sosai sa’ad da abokin aure ya soma bauta wa Jehobah!
14, 15. Mene ne zai iya sa mace ta rabu da mijinta, amma me ya sa za ta yi addu’a a kan batun kuma ta bincika yadda take ji da kyau?
14 Wane yanayi ne zai iya sa Kirista ta “rabu da” mijinta? Wasu sun rabu da mazansu don sun ƙi biyan bukatun iyalin da gangan. Wasu mata sun rabu da mazansu don suna cin zalinsu ko kuma sun hana su bauta wa Jehobah.
15 Ko mace za ta ci gaba da zama da mijinta ko za ta rabu da shi shawara ce da za ta yanke da kanta. Amma, ya kamata ta yi addu’a sosai a kan batun kuma ta bincika yadda take ji da kyau. Alal misali, shin mijin ne ainihi yake hana ta bauta wa Jehobah? Ko kuwa ita ma tana da laifi, wataƙila, ba ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, da halartar taro, da kuma fita wa’azi?
16. Me ya sa bai kamata Kiristoci su yi hanzarin kashe aurensu ba?
16 Daraja dangantakarmu da Allah da kuma nuna godiya don baiwar yin aure da ya tanadar mana zai hana mu yin hanzarin kashe aurenmu. A matsayinmu na bayin Jehobah, ba ma son mu ɓata sunansa. Saboda haka, ba ma son mu ci amanar abokin aurenmu kuma mu rabu da shi don mu auri wani.—Irm. 17:9; Mal. 2:13-16.
17. A wane yanayi ne za a iya ce Allah ya kira Kiristoci cikin salama?
17 ’Yar’uwa da mijinta ba ya bauta wa Jehobah ta yi iya ƙoƙarinta don ta ƙarfafa aurenta. Idan ta yi iya ƙoƙarinta don kada auren ya mutu amma mijinta bai yarda ba kada ta ji cewa tana da laifi. Manzo Bulus ya rubuta: “Amma idan marar bangaskiyan zai rabu, bar shi ya rabu; ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba su cikin bauta in haka nan ne: Amma Allah ya kirawo mu cikin salama.”—1 Kor. 7:15.b
KA DOGARA GA JEHOBAH
18. Wane sakamako mai kyau ne za a iya samu idan mun yi ƙoƙari don kada aurenmu ya mutu, amma hakan bai yiwu ba?
18 Sa’ad da kake fuskantar matsalar aure, ka kasance da gaba gaɗi kuma ka dogara ga Jehobah. (Karanta Zabura 27:14.) Ka yi la’akari da Linda da aka ambata ɗazu. Daga baya sun kashe aurensu duk da cewa ta yi iya ƙoƙarinta don kada auren ya mutu. Shin tana gani cewa ƙoƙarin da ta yi a banza ne? Ta ce, “Sam, ƙoƙarce-ƙoƙarcen da na yi ya ba da shaida mai kyau ga mutane. Ina da lamiri mai kyau. Abin da ya fi ba ni farin cikin shi ne a waɗannan shekarun, na taimaka wa ’yarmu ta kafu a cikin gaskiya. Ta yi girma ta zama Mashaidiya mai ƙwazo.”
19. Wane sakamako ne za a iya samu idan aka yi ƙoƙari don kada aure ya mutu?
19 Wata ’yar’uwa mai suna Marilyn ta yi farin ciki cewa ta dogara ga Jehobah kuma ta yi ƙoƙari sosai don ta ceci aurenta. “Na kusa in rabu da mijina don ya ƙi biyan bukatuna kuma ya sa dangantakata da Jehobah cikin haɗari” in ji ta. “Duk da cewa a dā shi dattijo ne kafin ya fara harkar kasuwanci da ba ta dace ba. Ya daina zuwa taro, kuma muka daina yin magana da juna. Wani hari da ’yan ta’adda suka kawo birninmu ya tsoratar da ni sosai kuma na daina cuɗanya da mutane. Sai na fahimci cewa ni ma ina da laifi. Sai muka soma magana da juna kuma, muka soma nazarinmu na iyali, kuma ya fara halartar taro a kai a kai. Dattawan sun nuna mana alheri kuma sun taimake mu. Ba da daɗewa ba aurenmu ya koma kamar sabo. Da shigewar lokaci, mijina ya sake cancantar samun gata a cikin ikilisiya. Mun koyi darasi amma mun yi farin ciki sosai.”
20, 21. Game da aure, me ya kamata mu ƙudura cewa za mu yi?
20 Ko muna da aure ko ba mu da shi, bari mu riƙa kasancewa da gaba gaɗi da kuma dogara ga Jehobah. Idan muna fuskantar matsaloli a aurenmu, ya kamata mu yi ƙoƙari mu magance su, mu tuna cewa ma’aurata “ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne.” (Mat. 19:6) Kuma mu tuna cewa idan mun jimre a auren da maigida ba Mashaidi ba ne, za mu iya samun farin cikin sa shi ya zama mai bauta wa Jehobah.
21 Ko wane irin yanayi ne muka samu kanmu a ciki, bari mu riƙa yin abubuwa a yadda zai ba da shaida mai kyau ga mutanen da ba sa cikin ikilisiya. Idan muna fuskantar matsaloli masu tsanani a aurenmu kuma muna ganin cewa ba za mu iya ci gaba ba, wajibi ne mu bincika dalilan da suka sa hakan, mu bincika Nassosi sosai kuma mu nemi taimakon dattawa. Abu mafi muhimmanci, mu ƙudura cewa za mu faranta wa Jehobah Allah rai a dukan abubuwa kuma mu nuna godiya sosai don baiwar Allah na aure.
[Hasiya]
a An canja sunaye.
b Ka duba littafin nan“Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 219-221 da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1988, shafuffuka na 26-27 da 15 ga Satumba , 1975, shafi na 575 na Turanci.
[Bayanin da ke shafi na 10]
Kiristocin da ba sa hanzarin kashe aurensu don matsaloli sukan samu sakamako mai kyau
[Bayanin da ke shafi na 12]
A kowane lokaci ka dogara ga Jehobah kuma ka kasance da gaba gaɗi
[Hoto a shafi na 9]
Jehobah yakan albarkaci ma’auratan da suke ƙoƙarin su ƙarfafa aurensu ko da suna fuskantar matsala
[Hoto a shafi na 11]
Ana iya samun ƙarfafa da taimako daga ikilisiyar Kirista