Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Mala’iku da Aljanu Suke Shafan Mu?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Su waye ne mala’iku?
Mala’iku halittu ne da ke zama a sama. Su halittu ne da suka fi ’yan Adam sosai. Allah na gaskiya, wanda shi ma ruhu ne, ya halicci mala’iku kafin ya yi duniya. (Ayuba 38:4, 7; Matta 18:10) Miliyoyin mala’iku masu aminci suna zama tare da Jehobah a sama.—Ka karanta Zabura 103:20, 21; Daniyel 7:9, 10.
2. Shin, mala’iku suna taimakon mutane ne?
Mala’iku sun taimaki wani adali mai suna Lot. Yana zaune ne a wani birnin da Allah ya ƙudura cewa zai halaka domin muguntar mazauna birnin. Mala’iku guda biyu suka ba wa Lot da iyalinsa gargaɗi cewa su bar birnin. Wasu sun yi banza da gargaɗin don sun ɗauka ba gaskiya ba ne. Amma Lot da ’ya’yansa mata guda biyu sun tsira domin sun yi biyayya da wannan gargaɗin da Allah ya yi ta bakin mala’ikun.—Ka karanta Farawa 19:1, 13-17, 26.
Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa mala’iku suna taimaka wa mutane a yau ta wajen ja-gorar waɗanda suke wa’azin Mulkin Allah babu fashi. (Matta 24:14) Wannan bishara ta ƙunshi gargaɗi. Kuma kamar gargaɗi da aka ba wa Lot, wannan ba wasa ba ne. Allah ne yake amfani da mala’iku wajen ba da wannan gargaɗi.—Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 1:1; 14:6, 7.
Allah yana amfani da mala’iku don ya ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar gwaji. Ya taɓa aika mala’ika ya ƙarfafa Yesu.—Ka karanta Luka 22:41-43.
Ba da daɗewa ba Allah zai yi amfani da mala’iku don ya halaka miyagun mutane da suke haddasa wahala. Hakan zai sa ’yan Adam su samu kwanciyar hankali.—Ka karanta 2 Tasalonikawa 1:6-8.
3. Yaya aljanu suke shafan mu?
Kamar yadda mutane da yawa a duniya suka yi wa Allah rashin biyayya, haka ma a sama mala’iku da yawa sun yi wa Allah tawaye. (2 Bitrus 2:4) Ana kiran mala’iku da suka yi rashin biyayya aljanu. Shugabansu shi ne Shaiɗan Iblis. Shaiɗan da aljanunsa suna yaudarar ’yan Adam.—Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Shaiɗan yana yin amfani da kasuwanci da ake ha’inci da gwamnatocin ’yan Adam da kuma addinan ƙarya don ya rinjayi mutane su daina bauta wa Allah. Saboda haka, Shaiɗan ne ya sa mutane suke rashin adalci da rashin imani kuma shi ya sa ake wahala a yau.—Ka karanta 1 Yohanna 5:19.
4. Ta yaya aljanu suke yaudarar mutane?
Shaiɗan yana yaudarar mutane da yawa ta wajen koyar da cewa matattu suna zama ruhohi kuma su yi magana da mutane. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa matattu ba za su iya yin kome ba. (Mai-Wa’azi 9:5) Sau da yawa, aljanu suna yaudarar mutane ta wajen kwaikwayon muryoyin mutane da suka mutu. (Ishaya 8:19) Suna kuma yaudarar mutane ta wajen amfani da bokaye da masu duba da masu sihiri da kuma hisabi. Kalmar Allah ta ce mu guje wa irin waɗannan ayyuka. Saboda haka, ya kamata mu yi watsi da duk wani abin da muke da shi wanda yake da alaƙa da aljanu da kuma sihiri.—Ka karanta Kubawar Shari’a 18:10, 11; Ayyukan Manzanni 19:19.
Idan muna ƙaunar Jehobah, ba ma bukata mu riƙa jin tsoron aljanu. Idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma muka bi umurninsa, za mu yi tsayayya da Iblis kuma mu kusaci Allah. Jehobah ya fi aljanu iko sosai. Mala’ikunsa masu aminci za su ƙarfafa mu a duk lokacin da muke bukatar taimako.—Ka karanta Zabura 34:7; Yaƙub 4:7, 8.
Domin ƙarin bayani, ka duba babi na 10 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah suka wallafa.