Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 pp. 20-21
  • Allah Mai Ƙyamar Rashin Adalci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Mai Ƙyamar Rashin Adalci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Halakar Saduma Da Gwamarata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Yi Tsayayya da Gwaji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Sa Masu Sauraransa Sun Yi Mamaki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 pp. 20-21

Don Matasa

Allah Mai Ƙyamar Rashin Adalci

Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Yayin da kake karanta nassin, ka ji kamar kai ɗan kallo ne da ke ganin yadda abubuwan suke faruwa. Ka yi tunanin yadda abin ya faru. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suka ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.

Shimfiɗar ’yan wasa: Ahab da Jezebel da Naboth da kuma Iliya

Taƙaitawa: Jezebel ta zuga Sarki Ahab ya yi kisa don ya kwace gonar anab na wani.

1 KA YI TUNANIN YANAYIN.—KA KARANTA 1 SARAKUNA 21:1-26.

Yaya za ka kwatanta mutane guda huɗu da ke wannan labarin?

Ahab ․․․․․

Jezebel ․․․․․

Naboth ․․․․․

Iliya ․․․․․

Da wani irin murya ne kake ganin Jezebel da kuma Ahab suka yi magana a ayoyi na 5-7?

․․․․․

Bisa ga abin da ka fahimta, ka kwatanta abin da ya faru a aya ta 13.

․․․․․

Bisa ga abin da aka kwatanta a ayoyi 20-26, yaya kake ganin Iliya da Ahab suka ji sa’ad da suke magana da juna?

․․․․․

2 KA YI BINCIKE SOSAI.

A ayoyi na 7 da kuma 25, wane irin hali ne Jezebel ta nuna?

․․․․․

A aya ta 4, wane irin hali ne Ahab ya nuna?

․․․․․

Su wane ne kuma Ahab ya kashe don ya ƙwace gonar anab na Naboth? (Ka karanta 2 Sarakuna 9:24-26.)

․․․․․

Yaya Jehobah ya ɗauki Ahab? (Ka sake karanta ayoyi 25 da 26, kuma ka karanta 1 Sarakuna 16:30-33, don ƙarin bayani.)

․․․․․

3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .

Yadda Jehobah yake sane da rashin adalci da mutane suke yi.

․․․․․

Yadda Jehobah yake damuwa da waɗanda aka yi musu rashin adalci.

․․․․․

Yadda Jehobah ya nuna cewa shi Allah ne mai adalci. (Ka karanta Kubawar Shari’a 32:4.)

․․․․․

4 DON ƘARIN AMFANI.

Ta yaya waɗansu mutane a yau za su iya nuna hali irin na Jezebel? (Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 2:18-21.)

․․․․․

A waɗanne yanayi na rayuwa ne za ka iya nuna gaba gaɗi irin na Iliya?

․․․․․

Wane tabbaci ne za ka iya samu sa’ad da ka ga ana rashin adalci ko kuma aka yi maka rashin adalci?

․․․․․

5 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?

Ka gwada wannan: Ka mai da kanka mai ba da labari kuma ka ba da wannan labarin. Ka rubuta rahoto game da abin da ya faru. Rahoton ya haɗa da ganawa da aka yi da ’yan wasan da kuma waɗanda suka shaida abin da ya faru.

Ka ƙara koya game da

Littafi Mai Tsarki A www.pr418.com

Za ka iya gurza ko kuma sauƙar da wannan talifin

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba