Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 8/15 pp. 3-7
  • ‘Ina Tare Da Kai’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ina Tare Da Kai’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AN SAMU ‘ILIMI NA GASKE’
  • “MUTANE DA YAWA” SUN KOYI “ILIMI” NA GASKE
  • “ILIMI” NA GASKE YA “ƘARU”
  • SANI NA ALLAH ZAI CIKA DUNIYA
  • An Kafa Mulkin a Sama
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ta Yaya Aka Sake Gano Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 8/15 pp. 3-7

‘Ina Tare Da Kai’

“Mutane da yawa za su kai da kawo a guje, ilimi [na gaske] kuma za ya ƙaru.”​—DAN. 12:4.

MECE CE AMSARKA?

Ta yaya mutane suka samu “ilimi” na gaske a zamaninmu?

Ta yaya “mutane da yawa” suka zo ga sanin Jehobah?

Ta waɗanne hanyoyi ne ilimi na gaske ya “ƙaru”?

1, 2. (a) Ta yaya muka san cewa Yesu yana tare da mu a yanzu kuma zai yi hakan a nan gaba? (b) Kamar yadda littafin Daniyel 12:4 ya nuna, mene ne zai faru sa’ad da wasu suka bincika Nassosi da kyau?

KA YI tunanin cewa kana cikin Aljanna. A kowane wayewar gari, ka tashi kana jin daɗi kuma kana marmarin soma harkokinka na ranar. Ba ka jin ciwo. Ba ka rashin lafiya. Idanunka suna ganin abubuwa sosai, kana jin abubuwa da kunnuwanka raɗau, kana sansana abubuwa da hancinka, kuma kana jin ɗanɗano da harshenka. Kana da ƙarfi sosai da aiki mai ban sha’awa, kana da abokai da yawa kuma ba abin da ke damunka. Abubuwan da za ka mora ke nan sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta bisa duniya. Sarkinmu Yesu Kristi, zai albarkaci talakawansa kuma zai ilimantar da su game da Jehobah.

2 A lokacin, Jehobah zai kasance tare da amintattun bayinsa yayin da suke koya wa mutane game da shi. A kowane lokaci, Jehobah da Ɗansa suna taimaka wa amintattu. Kafin Yesu ya koma sama, ya yi wa bayinsa alkawari cewa zai kasance tare da su. (Karanta Matta 28:19, 20.) Don mu ƙarfafa bangaskiyarmu game da alkawarin Yesu, bari mu tattauna wani annabci da Daniyel ya rubuta a lokacin da yake Babila fiye da shekaru 2,500 da suka shige. Daniyel ya rubuta game da “kwanakin ƙarshe” da muke ciki a yanzu cewa: “Mutane da yawa za su kai da kawo a guje, ilimi [na gaske] kuma za ya ƙaru.” (Dan. 12:4) Yanzu, mun fahimci cewa a cikin wannan ayar, fi’ili na Ibrananci da aka fassara “kai da kawo” yana nufin yin bincike sosai. Annabcin ya nuna cewa waɗanda suka bincika Kalmar Allah sosai za su samu ilimi na gaske game da Allah. Annabcin ya kuma nuna cewa ‘ilimi na gaske zai ƙaru.’ Waɗanda suka samu wannan ilimi na gaske za su amince da shi kuma su koya wa mutane gaskiya. Bugu da ƙari, mutane a ko’ina za su koyi wannan “ilimi” na gaske. Yayin da muke binciken cikar wannan annabcin, za mu fahimci cewa Yesu yana tare da almajiransa a yau kuma tabbas Jehobah zai cika dukan alkawuran da ya yi.

AN SAMU ‘ILIMI NA GASKE’

3. Mene ne ya faru da “ilimi” na gaske bayan mutuwar manzannin?

3 Manzo Bulus ya ambata cewa za a yi ridda bayan mutuwar manzannin kuma hakan zai yaɗu kamar wutar daji. (A. M. 20:28-30; 2 Tas. 2:1-3) Shekaru da yawa bayan haka, aka yi rashin “ilimi” na gaske, har ma a tsakanin waɗanda suke da’awa cewa su Kiristoci ne. Shugabannin Kiristendam suna koyar da ƙarya, wato, “koyarwar aljanu” wanda yake ɓata mutuncin Allah. (1 Tim. 4:1) Saboda haka, yawancin mutane ba su san gaskiya game da Allah ba. A maimakon haka, ana koya musu ƙarya cewa Allah uku cikinɗaya ne da cewa mutum yana da kurwa da ba ta mutuwa kuma cewa za a azabtar da wasu kurwa a cikin wutar jahannama har abada.

4. Ta yaya wani rukunin Kiristoci ya soma neman “ilimi” na gaske wajen shekaru 40 kafin a shiga “kwanaki na ƙarshe”?

4 Amma, wajen shekara 40 kafin a shiga “kwanaki na ƙarshe,” wasu sahihan Kiristoci a jihar Pennsylvania na ƙasar Amirka suka haɗu don su bincika Littafi Mai Tsarki kuma su gano “ilimi” na gaske. (2 Tim. 3:1) Ana ce da su Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Su ba “masu-hikima da masu-fahimi” da Yesu ya ce an ɓoye musu ilimi na gaske ba. (Mat. 11:25) Masu tawali’u ne kuma suna son su yi nufin Allah daga zuciyarsu. Cikin natsuwa da roƙon Allah, suka karanta nassosi, suka tattauna su kuma suka yi bimbini a kan su. Suka bincika ayoyi dabam-dabam na nassi kuma suka yi nazari a kan abubuwan da wasu suka yi bincike. Da shigewar lokaci, waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimci koyarwar gaskiya da mutane da yawa suka yi shekaru da yawa ba su fahimta ba.

5. Me ya sa aka buga jerin warƙar nan mai suna The Old Theology?

5 Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi farin ciki game da abubuwan da suke koya a lokacin, amma ba su yi alfahari saboda haka ba, kuma sun fahimci cewa wannan gaskiyar tana cikin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ba su gaya wa mutane cewa sun gano wata sabuwar koyarwa ba. (1 Kor. 8:1) A maimakon haka, sun buga wata jerin warƙa mai suna The Old Theology. Suna so mutane su fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Warƙa ta farko ta taimaka wa mutane su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki don su guji “al’adun ƙarya na ’yan Adam” kuma su karɓi koyarwar gaskiya na Yesu da manzannin, ko kuma “asalin koyarwar Littafi Mai Tsarki.”—The Old Theology, Na 1, Afrilu 1889, shafi na 32.

6, 7. (a) Mene ne Shaidun Jehobah suka koya fiye da shekara ɗari da ta shige? (b) Waɗanne abubuwa ne ka yi farin cikin koya?

6 Tun fiye da shekaru ɗari da suka shige, Shaidun Jehobah sun koyi abubuwa masu ban sha’awa daga cikin Littafi Mai Tsarki!a Waɗannan abubuwa masu ban sha’awa gaskiya ne kuma koyarwa ne da ke sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana da farin ciki da kuma bege. Suna taimaka mana mu san Jehobah da halayensa masu kyau da kuma nufinsa. Bugu da ƙari, sun sa mun san matsayin Yesu, sun bayyana dalilin zuwansa duniya da mutuwarsa da kuma abin da yake yi yanzu. Waɗannan koyarwa masu ban sha’awa sun bayyana dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta da abin da ya sa muke mutuwa da yadda za mu yi addu’a da kuma abubuwan da za mu yi don mu kasance da farin ciki na gaske.

7 Yanzu za mu iya fahimtar annabce-annabce da aka yi shekaru da yawa da ba a san ma’anarsu ba, amma suna cika a wannan kwanaki na ƙarshe. (Dan. 12:9) Waɗannan sun haɗa da waɗanda suke cikin Linjila da kuma Ru’ya ta Yohanna. Jehobah ya taimaka mana mu san abubuwan da suka faru a cikin sama da ba za mu iya gani ba. Alal misali, yanzu mun san cewa Yesu ya zama Sarki kuma an yi yaƙi a sama, an jefo da Shaiɗan daga sama zuwa duniya. (R. Yoh. 12:7-12) Allah ya taimake mu mu san dalilin da yasa sa abubuwan da muke gani suke faruwa, alal misali, yaƙe-yaƙe da girgizar ƙasa da annoba da ƙarancin abinci da kuma dalilin da ya sa mutane suke aikata miyagun abubuwan da suke sa “miyagun zamanu” da muke ciki suna daɗa muni.—2 Tim. 3:1-5; Luk 21:10, 11.

8. Wane ne ya taimaka mana mu fahimci gaskiya?

8 Yesu ya gaya wa almajiransa: “Idanun da ke duban abin da ku ke duba masu albarka ne: gama ina ce maku, annabawa da sarakuna dayawa suka yi bege su duba abin da ku ke duba, ba su gani ba; su ji abin da ku ke ji, ba su kuwa ji ba.” (Luk 10:23, 24) Hakan ma muke ji a yau. Mun gode wa Jehobah sosai da ya taimaka mana wajen gani da kuma jin abubuwan nan. Kuma mun gode da ya tanadar mana da “mai-taimakon,” wato, ruhu mai tsarki don ya ‘bishe mu cikin dukan gaskiya!’ (Karanta Yohanna 16:7, 13.) Kada mu taɓa manta cewa gaskiyar tana da tamani kuma ya kamata mu riƙa koya wa mutane.

“MUTANE DA YAWA” SUN KOYI “ILIMI” NA GASKE

9. Wace gayyata ce aka buga a cikin Hasumiyar Tsaro ta Afrilu na shekara ta 1881?

9 A watan Afrilu ta 1881, kusan shekara biyu bayan an fara buga mujallar Hasumiyar Tsaro, an wallafa wani talifi inda aka ce ana bukatar masu wa’azi guda 1,000. A cikin talifin an gayyaci waɗanda za su iya ba da lokacinsu don zama majagaba. An gaya musu su shiga wurare dabam-dabam don su nemi Kiristoci masu zuciyar kirki kuma su koya musu gaskiya game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki.

10. Mene ne mutane da yawa suka yi bayan sun karanta cewa ana bukatar masu wa’azi guda 1,000?

10 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun gayyaci wasu su yi wa’azi don sun fahimci cewa wajibi ne Kiristoci su yi wa’azin bishara. A lokacin, ’yan ɗarurruwan mutane ne suke halartar taron Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, saboda haka, mutane da yawa ba su yi na’am da wannan kiran kamar yadda ake zato ba. Amma, mutanen da suka karanta warƙa ko mujallar Hasumiyar Tsaro, sun fahimci cewa sun samu gaskiyar kuma suna so su taimaka wa wasu. Alal misali, a shekara ta 1882 wani mazaunin birnin Landan, a ƙasar Ingila da ya karanta wata mujallar Hasumiyar Tsaro da wata ƙasida ta Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ya rubuta: “Don Allah ku koya mini yadda zan yi wa’azi da kuma abin da zan faɗa don na yi aikin da Allah yake son a yi.”

11, 12. (a) Mene ne muradin majagaba? (b) Ta yaya majagaban suka kafa sababbin ikilisiyoyi?

11 Akwai majagaba guda 300 a shekara ta 1885. Maƙasudinmu ɗaya ne da nasu a lokacin. Suna son su sa mutane su zama almajiran Yesu Kristi. Amma, yadda suka yi wannan aiki ya bambanta da namu a yau. Muna nazari da mutum ɗaya, sai mu gayyaci ɗalibin ya halarci taron ikilisiya. A dā, majagaba suna tara mutane da yawa don su yi nazari da su. Suna rarraba littattafai kuma su gayyaci mutane da suke son saƙonsu su taru don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Ta hakan, majagaba suka kafa sababbin ikilisiyoyi.

12 Alal misali, a shekara ta 1907, majagaba suka zagaya cikin birnin don su gano waɗanda suke da littattafan Millennial Dawn (da kuma aka kira Studies in the Scriptures). Hasumiyar Tsaro ta ce: “Sai majagaban suka gayyace su zuwa taro a gidan ɗaya daga cikin mutanen. A ranar Lahadin, ɗaya daga cikin majagaban ya yini yana ba da jawabi mai jigon nan Divine Plan of the Ages (Abin da Allah Ya Shirya Tun Fil azal) kuma ya gaya musu su riƙa halartar taro a kai a kai.” A shekara ta 1911, ’yan’uwan suka canja tsarin. Masu kula masu ziyara guda hamsin da takwas sun ba da jawabi ga jama’a a dukan ƙasar Amirka da Kanada. Suka rubuta sunaye da adireshin waɗanda suka halarci taron kuma suka shirya su su riƙa yin taro a gidajen mutane kuma su kafa sababbin ikilisiyoyi. Akwai ikilisiyoyi 1,200 a dukan duniya, a shekara ta 1914.

13. Mene ne ya burge ka game da aikin wa’azi?

13 A yau, muna da kusan ikilisiyoyi guda 109,400 a dukan duniya, kuma ’yan’uwa 895,800 ne suke hidima a matsayin majagaba. Kusan mutane miliyan takwas ne yanzu suka amince da “ilimi” na gaske kuma suna amfani da shi a rayuwarsu. (Karanta Ishaya 60:22.)b Wannan ƙaruwa da ban mamaki yake tun da Yesu ya annabta cewa almajiransa za su zama “abin ƙi ga dukan mutane” saboda sunansa. Ya daɗa cewa za a tsananta wa almajiransa, a jefa su cikin kurkuku, har ma a kashe su. (Luk 21:12-17) Ko da yake Shaiɗan da aljanunsa da kuma mutane da yawa suna ƙoƙari su hana aikin wa’azin, amma mutanen Jehobah suna ta samun ci gaba a aikinsu na yin almajirai. A yau, suna yin wa’azi a “dukan al’ummai,” daga ƙasashe da ake zafi sosai zuwa ƙasashen da ake matuƙar sanyi da tsaunuka da hamada da birane da kuma ƙauyuka. (Mat. 24:14) Da ba da taimakon Jehobah ba, da ba su cim ma waɗannan ayyukan ba.

“ILIMI” NA GASKE YA “ƘARU”

14. Ta yaya “ilimi” na gaske ya ƙaru ta wajen littattafanmu?

14 “Ilimi” na gaske ya ƙaru saboda wa’azin bishara da ake yi da kuma littattafai da mujallu da ake bugawa. Bugu da ƙari, ilimin ya ƙaru ta wajen littattafai. A watan Yuli na shekara ta 1879, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka buga mujallar Zion’s Watch Tower [Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona] ta farko. An ba wa wani kamfanin buga littattafai aikin buga kofi 6,000 na mujallar a Turanci kawai. Aka zaɓi Charles Taze Russell mai shekara ashirin da bakwai a lokacin ya zama editan, kuma wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda biyar da suka ƙware suna rubuta wasu talifofi a cikin mujallar. Yanzu, ana buga Hasumiyar Tsaro a harsuna 195. Ita ce mujallar da aka fi rarrabawa a dukan duniya, ana buga kofi guda 42,182,000 a kowace fitowa. Mujalla na biyu da aka fi rarrabawa ita ce Awake!, kuma ana buga kofi guda 41,042,000 a harsuna 84. Bugu da ƙari, ana buga Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafai wajen miliyan 100 a kowace shekara.

15. Ina ne muke samun kuɗaɗen buga littattafanmu?

15 Ana samun kuɗin da ake gudanar da wannan gagarumin aiki ta wajen kyautar da ake ba da da son rai. (Karanta Matta 10:8.) Wannan abu ne da yake ba wa masu aiki a kamfanonin buga littattafai mamaki sosai don sun san yadda kayayyakin buga littattafai suke da bala’in tsada. Wani ɗan’uwa da yake saya wa Bethel kayayyaki ya ce ’yan kasuwa da suke zuwa Bethel suna mamakin abubuwan da muke iya cim ma da kyautar da ake ba da wa da son rai. Kuma, wani abu da yake burge su shi ne cewa waɗanda suke hidima a Bethel matasa ne kuma suna farin ciki.

SANI NA ALLAH ZAI CIKA DUNIYA

16. Me ya sa Jehobah yake sa a yaɗa “ilimi” na gaske?

16 Jehobah ya tanadar da “ilimi” na gaske domin nufinsa ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Jehobah yana son mutane su san gaskiya don su bauta masa kuma su samu albarka. Ta wajen yaɗa “ilimi na gaske,” Jehobah ya tattara shafaffun Kiristoci masu aminci. Kuma yana tattara “taro mai-girma, . . . daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna” waɗanda suke da begen zama a duniya har abada.—R. Yoh. 7:9.

17. Mene ne ƙaruwar masu bauta wa Jehobah yake nufi?

17 A cikin shekaru 130 da suka shige, mutanen da suke bauta wa Jehobah sun ƙaru sosai kuma hakan ya nuna cewa Allah da sarkin da ya naɗa, Yesu Kristi suna tare da bayin Jehobah ta wajen yi musu ja-gora da tanadar musu da kāriya da tsara su da kuma koyar da su. Jehobah ya cika alkawarin da ya yi cewa zai taimaka wa mutane da yawa su zo ga sanin gaskiya a zamaninmu kuma hakan ya ba mu tabbaci cewa zai cika alkawuransa game da nan gaba. A lokacin, “duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.” (Isha. 11:9) Babu shakka, ’yan Adam za su mori rayuwa sosai a lokacin!

[Hasiya]

a Za ka amfana idan ka kalli wannan jerin DBD mai jigo, Jehovah’s Witnesses—Faith in Action, Part 1: Out of Darkness da Jehovah’s Witnesses—Faith in Action, Part 2: Let the Light Shine.

b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2002, shafi na 31, sakin layi na 16.

[Hoto a shafi na 6]

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na farko mutane ne masu tawali’u da suke son su yi nufin Allah

[Hoto a shafi na 7]

Jehobah yana jin daɗin ƙoƙarce-ƙoƙarcen da kake yi wajen yaɗa “ilimi” na gaske

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba