Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kr babi na 2 pp. 13-29
  • An Kafa Mulkin a Sama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Kafa Mulkin a Sama
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Manzona . . . Za Ya kuwa Shirya Tafarki a Gabana”
  • Yin Ibada Cikin Gaskiya
  • “Ku Fito Daga Cikinta, Ya Al’ummata”
  • Yin Taro don Ibada
  • Yin Wa’azi da Ƙwazo
  • An Kafa Mulkin Allah!
  • Lokacin Gwaji
  • Lokacin Farfaɗowa!
  • Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dalla
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Mulkin Allah Yana Sarauta!
kr babi na 2 pp. 13-29

BABI NA 2

An Kafa Mulkin a Sama

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda Allah ya shirya bayinsa kafin a kafa Mulkin

1, 2. Wace aukuwa mafi girma ce ta faru a tarihi, kuma me ya sa mutane ba su ga wannan aukuwar ba?

KA TAƁA yin tunanin yadda rayuwa ta kasance sa’ad da aka yi wani gagarumin canji a tarihi? Mutane da yawa sun taɓa rayuwa a irin wannan lokacin. Amma ka yi la’akari da wannan: Da a ce ka rayu a wannan lokacin, za ka shaida abin da ya kai ga wannan canjin kuwa? Wataƙila a’a. Me ya sa? Domin wasu abubuwa da suke sa a yi juyin mulki ba sa faruwa a gaban jama’a. Yawancin canjin da ake yi a tarihi suna faruwa ne a ɓoye, wato a daƙuna ko gidajen sarauta da jam’iyoyi ko kuma ofisoshin gwamnati. Duk da haka, waɗannan canjin suna shafan rayuwar miliyoyin mutane.

2 Aukuwa mafi girma da ta taɓa faruwa tarihin duniya fa? Wannan aukuwar ta shafi rayuwar miliyoyin mutane. Wannan abin bai faru a duniya ba. Hakika, muna magana ne game da Mulkin Allah da aka kafa a sama, wato gwamnatin Almasihu da aka yi alkawarinta tun da daɗewa, wadda za ta kawo ƙarshen mugun yanayin da duniya take ciki. (Karanta Daniyel 2:34, 35, 44, 45.) Tun da yake ’yan Adam ba su ga lokacin da aka kafa wannan gwamnatin ba, shin hakan yana nufin cewa Jehobah ya hana ’yan Adam sanin abin da ya faru ne? Shin ya shirya amintattun bayinsa ne kafin lokacin? Bari mu bincika.

“Manzona . . . Za Ya kuwa Shirya Tafarki a Gabana”

3-5. (a) Wane ne “mala’ikan alkawari” da aka ambata a littafin Malakai 3:1? (b) Mene ne zai faru kafin zuwan “mala’ikan alkawari” haikali ta alama?

3 Tun dā can, nufin Jehobah shi ne ya shirya mutanensa don Mulkin Almasihu da za a kafa. Alal misali, ka yi la’akari da annabcin da ke littafin Malakai 3:1: “Duba, ina aike manzona, za ya kuwa shirya tafarki a gabana; Ubangiji ma, wanda ku ke biɗarsa, za ya zo a haikalinsa ba labari; mala’ikan alkawari kuma, wanda ku ke murna da shi.”

4 A cikar annabcin nan a zamaninmu, yaushe ne Jehobah, wato “Ubangiji” da aka ambata a annabcin nan, ya zo don ya bincika waɗanda suke yin hidima a haikali na alama a duniya? Annabcin ya ce Jehobah zai zo tare da “mala’ikan alkawari.” Waye ke nan? Babu shakka, Sarki Almasihu ne, wato Yesu Kristi! (Luk 1:68-73) A matsayin sabon Sarki, Yesu zai bincika bayin Allah da ke duniya, kuma ya yi musu gyara.—1 Bit. 4:17.

5 To, wane ne wannan ‘manzon’ da aka ambata da farko a littafin Malakai 3:1? Wannan da aka yi annabcinsa zai kasance kafin bayyanuwar Sarki Almasihu. A shekarun da suka gabaci 1914, shin akwai wanda ya “shirya tafarki” don Sarki Almasihu?

6. Wane ne ‘manzon’ da ya fara zuwa don ya shirya bayin Allah domin abubuwa da za su faru a nan gaba?

6 Za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin a cikin wannan littafin yayin da muke tattauna tarihi mai ƙayatarwa game da mutanen Jehobah a zamaninmu. Tarihin ya nuna cewa a ƙarshen ƙarni na sha tara, wani ƙaramin rukuni na amintattun mutane ya bayyana a matsayin rukunin Kiristoci na gaskiya a tsakanin jabun Kiristoci da yawa. Wannan rukunin shi ne ake kira Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin. Waɗanda suke musu ja-gora su ne Charles Taze Russell da abokan aikinsa. Hakika, kamar yadda aka ambata a annabcin ‘manzon,’ sun koya wa bayin Allah Littafi Mai Tsarki kuma sun shirya su don abubuwan da za su faru a nan gaba. To, bari mu tattauna hanyoyi huɗu da wannan ‘manzon’ ya yi hakan.

Yin Ibada Cikin Gaskiya

7, 8. (a) Su waye ne suka fallasa koyarwar kurwa marar mutuwa a shekara ta 1800 zuwa shekara ta1899? (b) Waɗanne koyarwa ne Ɗan’uwa Russell da abokansa suka fallasa cewa ƙarya ne?

7 Yayin da waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke nazari, sun roƙi Jehobah ya yi musu ja-gora; sun kasance da fahimta guda, kuma suka wallafa gaskiyar Littafi Mai Tsarki da suka gano dalla-dalla. A ƙarnuka da yawa, Kiristendam sun kasance cikin duhun kai sosai game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, domin tushen yawancin koyarwarta daga arna ne. Babban misali shi ne koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa. A tsakanin shekara ta 1800 da 1900, wasu masu nazarin Littafi Mai Tsarki sun bincika wannan koyarwar kuma sun gano cewa ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne. Henry Grew da George Stetson da kuma George Storrs sun yi rubuce-rubuce don bayyana wa mutane cewa wannan koyarwar ƙarya ce kuma sun yi jawabai kai tsaye game da hakan.a Wannan aikin da suka yi ya shafi rayuwar Charles Taze Russell da abokan aikinsa sosai.

8 Wannan ƙaramin rukuni na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun gano daga baya cewa wasu koyarwa da suke da alaƙa da koyarwar kurwa ba ta mutuwa ƙarya ne kuma suna ruɗar da hankalin mutane. Alal misali, koyarwar nan cewa dukan mutane masu adalci za su je sama ko kuma Allah zai azabtar da mugaye a wutar jahannama. Russell da abokan aikinsa sun fallasa waɗannan ƙaryace-ƙaryace kai tsaye a talifofi da littattafai da ƙasidu da warƙoƙi da kuma jawabai da suka wallafa.

9. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta nuna cewa koyarwar Allah-uku-cikin-daya ƙarya ce?

9 Har ila, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fallasa cewa koyarwa ta Allah-uku-cikin-ɗaya da ta yi tasiri ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. A shekara ta 1887, mujallar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta ce: “Nassosi sun yi bayani dalla-dalla game da dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Ubangijinmu Yesu da kuma matsayin kowannensu.” Talifin ya sake bayyana wani abin ban mamaki, wato yadda “koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya da kuma Allah ɗaya cikin uku ya sami karɓa a wajen mutane da yawa. Amma hakan ya nuna cewa ’yan coci sun yi sakaci kuma sun ƙyale magabcin ya yaɗa koyarwar ƙarya.”

10. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa shekara ta 1914 tana da muhimmanci sosai?

10 Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta mai da hankali a kan annabci game da bayyanuwar Kristi, kamar yadda jigonta ta nuna. Amintattun shafaffun Kristi da suka saka hannu a rubuta wannan mujallar sun gane cewa annabcin Daniyel a kan ‘lokatai bakwai’ yana da alaƙa da lokacin da nufin Allah game da Mulkin Almasihu zai cika. Tun daga tsakanin shekara 1870 zuwa 1879, amintattun shafaffun sun nuna cewa shekara ta 1914 ce shekarar da lokatai bakwai za su zo ƙarshe. (Dan. 4:25; Luk 21:24) Ko da yake ’yan’uwanmu a lokacin ba su fahimci cewa wannan shekarar tana da muhimmanci sosai ba, duk da haka, sun yi ta wa’azin abubuwan da suka sani da ƙwazo, kuma aikinsu ya yi tasiri sosai.

11, 12. (a) Wane ne Ɗan’uwa Russell yake yaba wa don abubuwan da ya koyar? (b) Mene ne muhimmancin aikin da Ɗan’uwa Russell da abokansa suka yi kafin shekara ta 1914?

11 Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa masu aminci ba su yi da’awar cewa su ne suka gano gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba. Russell ya yabi waɗanda suka gabace shi. Mafi muhimmanci, ya yabi Jehobah Allah wanda Shi ne yake koyar da mutanensa game da abubuwan da suke bukata su sani a lokacin da ya kamata. Hakika, Jehobah ya albarkaci ƙoƙarin Russell da abokansa a yadda suka tāce koyarwar gaskiya daga na ƙarya. Da shigewar shekaru, bambancin da ke tsakanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da Kiristendam ya daɗa ƙaruwa.

Dan’uwa Charles Taze Russell yana magana da abokan aikinsa

Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki

12 Waɗannan mutane masu aminci sun yi gagarumin aiki wajen ɗaukaka da kuma yaɗa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a shekarun da suka gabaci 1914! Mujallar Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 1 ga Nuwamba, 1917, ta ce: “Miliyoyin mutane a yau sun ’yantu daga tsoro saboda ƙaryace-ƙaryace kamar koyarwar wutar jahannama . . . Koyarwar gaskiya ta fara yaɗuwa tun shekaru arba’in da suka shige kuma za ta ci gaba sai ta cika dukan duniya. Magabtanta za su yi ƙoƙarin hana gaskiyar yaɗuwa, amma duk ƙoƙarinsu zai zama kamar zuba ruwa a kwando.”

13, 14. (a) Ta yaya ‘manzon’ ya taimaka don a shirya wa Sarki Almasihu tafarki? (b) Mene ne za mu iya koya daga ‘yan’uwanmu da suka wanzu fiye da ƙarni guda da ya shige?

13 Ka yi la’akari: Shin bayin Allah za su kasance da shiri ne a farkon bayyanuwar Kristi idan ba su san bambancin da ke tsakanin Kristi da Ubansa, Jehobah ba? A’a. Har ila, ba za su kasance da shiri ba idan suka ɗauka cewa rai marar mutuwa abu ne da kowa yake da shi a maimakon baiwar da Allah yake ba wasu mutane ƙalilan cikin waɗanda suka bi koyarwar Kristi. Ƙari ga haka, ba za su kasance da shiri ba idan suka ɗauka cewa Allah yana azabtar da mutane a wutar jahannama har abada! Babu shakka, ‘manzon’ ya shirya tafarki wa Sarki Almasihu!

14 Mu kuma fa a yau? Wane darasi ne za mu iya koya daga waɗannan ’yan’uwan? Mu ma muna bukatar mu nuna ƙwazo wajen karanta Kalmar Allah da kuma yin nazarinta. (Yoh. 17:3) Yayin da wannan duniyar take ƙara lalacewa saboda rashin sanin Allah, bari mu kasance da ƙwazo wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki don dangantakarmu da Allah ta daɗa danƙo!—Karanta 1 Timotawus 4:15.

“Ku Fito Daga Cikinta, Ya Al’ummata”

15. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimta da sannu-sannu? (Ka duba Ƙarin bayani.)

15 Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin sun koyar da cewa wajibi ne a daina harka da coci-cocin Kiristendom. A shekara ta 1879, mujallar Hasumiyar Tsaro ta yi magana game da “Cocin Babila.” Shin ta yi magana ne a kan shugabancin Paparuma ko kuma cocin Katolika? Ɗarikokin Furotestan sun yi shekaru suna koyar da cewa Babila da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki ita ce cocin Katolika. Amma a hankali, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimta cewa dukan coci-cocin Kiristendam a yau su ne wannan “Babila” da aka yi maganarta. Me ya sa? Domin dukansu suna koyar da ƙaryace-ƙaryacen da aka tattauna a baya.b Da shigewar lokaci, littattafanmu sun soma ba da umurni kai tsaye a kan abin da masu zukatan kirki da ke coci-cocin Babila suke bukatar su yi.

16, 17. (a) Ta yaya littafi na uku na Millennial Dawn da kuma Hasumiyar Tsaro suka karfafa mutane su rabu da addinin ƙarya? (b) Me ya sa ba su ɗauki wannan kashedin da muhimmanci ba? (Ka duba ƙarin bayani.)

16 Alal misali, a shekara ta 1891, Kundi na 3 na Millennial Dawn ya tattauna yadda Allah ya yi watsi da Babila na zamani. Ya ce: “Allah ya yi watsi da dukan coci-cocin Kiristendam.” Ya ƙara da cewa: “Dukan waɗanda ba su amince da koyarwa da ayyukan ƙarya da take yaɗawa ba su fito daga cikinta.”

17 A watan Janairu na shekara ta 1900, Hasumiyar Tsaro ta ba da wani kashedi ga dukan waɗanda har ila sunayensu na rubuce a rajistar coci-cocin Kiristendam, amma suna cewa: “Ai ni ina goyon bayan gaskiya, na daina zuwa coci.” An yi wannan tambayar a cikin talifin: “Shin hakan daidai ne a ce ƙafarka ɗaya tana Babila, ɗaya kuma tana waje? Shin wannan ne irin biyayya . . . da kuma ibadar da Allah ya ce a yi masa? A’a. Duk mutumin da yake coci ya yi alkawari da cocin sa’ad da ya soma tarayya da su, kuma dole ne ya yi biyayya da dukan abin da cocin ya faɗa har sai ya . . . sanar a fili cewa ya daina tarayya da su.” Da shigewar shekaru, wannan kashedin ya yi ƙarfi sosai.c Ya zama wajibi bayin Jehobah su daina duk wata harka da addinin ƙarya.

18. Me ya sa yake da muhimmanci mutane su fito daga Babila Babba?

18 Da ba a ci gaba da yin kashedi a kai a kai cewa a fito daga Babila Babba ba, shin da Kristi, sabon Sarkin da aka naɗa zai sami rukunin bayi shafaffu da suke shirye su yi masa hidima a duniya ne? A’a, domin Kiristocin suka daina harka da Babila su ne kawai suka cancanta su bauta wa Jehobah “cikin ruhu da cikin gaskiya.” (Yoh. 4:24) Shin mu ma mun ƙudura aniyar daina harka da addinin ƙarya a yau, kamar yadda waɗannan bayin Jehobah suka yi? Bari mu ci ga da yin biyayya da wannan umurnin: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:4.

Yin Taro don Ibada

19, 20. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa bayin Allah su yi taro don yin ibada?

19 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koyar da cewa ya dace ’yan’uwa Kiristoci su haɗu su yi ibada tare, idan hakan ya yiwu a inda suke. Barin addinin ƙarya ba shi ne ake bukata kawai daga Kiristoci na gaskiya ba. Zai dace su riƙa yin ibada ta gaskiya. Tun farko, mujallar Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa masu karantata su riƙa taro don yin ibada. Alal misali, a watan Yuli na shekara ta 1880, Ɗan’uwa Russell ya ba da rahoto game da jawaban da ya yi sa’ad da ya yi wata tafiya. Ya ce taron da ya yi a wuraren da ya je sun kasance da ban ƙarfafa sosai. Ƙari ga haka, ya ƙarfafa masu karatu su aiko da rahotanni game da ci gaban da suka samu kuma a wallafa wasu a cikin mujallar Hasumiyar Tsaro. Me ya sa? “Don dukanmu mu san . . . yadda Ubangiji yake muku albarka; ko har ila kuna ci gaba da yin taro da sauran ’yan’uwa da suka amince da koyarwar gaskiya.”

Wani rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a birnin Copenhagen, a ƙasar Denmark a 1909

Ɗan’uwa Charles Russell tare da wani rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a birnin Copenhagen, a ƙasar Denmark a 1909

20 A shekara ta 1882, an wallafa wani talifi a cikin Hasumiyar Tsaro mai jigo “Assembling Together” (Yin Taro). Talifin ya umurci Kiristoci su riƙa yin taro “don su ƙarfafa juna.” Ya ƙara da cewa: “Kasancewa da ilimi ko wata baiwa ba shi ne yake da muhimmanci ba. Bari kowa ya zo da Littafi Mai Tsarki da takarda da fensir da littattafan bincike, . . . da makamantansu. Ku zaɓi batun da kuke so; sai ku roƙi Allah ya ba ku ruhu mai tsarki don ku fahimci batun. Idan kun yi karatu, ku yi tunani a kan abin da kuka karanta kuma ku gwada nassi da nassi, yin hakan zai sa ku fahimci gaskiya.”

21. Wace misali ce ikilisiyar da ke Allegheny, Pennsylvania, ta ƙafa game da halartan taro da kuma ƙarfafa juna?

21 Hedkwatar Ɗaliban Littafi Mai Tsarki tana Allegheny, Pennsylvania, a ƙasar Amirka a lokacin. Sun kafa misali mai kyau na yin taro daidai da umurnin da ke littafin Ibraniyawa 10:24, 25. (Karanta.) Wani ɗan’uwa tsoho mai suna Charles Capen ya tuna yadda yake halartan irin waɗannan taron sa’ad da yake yaro. Ya ce: “Har ila, ban manta da nassin da aka rubuta a bangon majami’ar taro ba. Nassin ya ce, ‘Malaminku ɗaya ne, wato Kristi, ku duka kuwa ’yan’uwa ne.’ Ba na mantawa da wannan nassin da ke nuna cewa babu limamai a cikin ƙungiyar Jehobah.” (Mat. 23:8) Ɗan’uwa Capen ya tuna yadda suke jin daɗin taron, da ƙarfafawar da suke samu da kuma ƙwazon da Ɗan’uwa Russell ya nuna wajen ƙarfafa kowa a cikin ikilisiyar.

22. Mene ne mutane masu aminci suka yi sa’ad da aka ƙarfafa su su riƙa halartan taro, kuma wane darasi ne za mu iya koya?

22 Mutane masu aminci sun bi wannan misalin da kuma shawarar da aka ba su. An kafa ikilisiyoyi a wasu wurare kamar su Ohio da Michigan, kuma daga baya, a dukan nahiyar Amirka ta Arewa da kuma wasu ƙasashe. Ka yi la’akari: Shin kana ganin mutane masu aminci za su yi shiri don bayyanuwar Kristi ne in da ba a koya musu yadda za su bi wannan hurarren umurni na yin taro don ibada ba? Da kyar! Mu kuma fa a yau? Ya kamata mu ƙuduri anniyar halartan taron Kirista babu fashi, kuma mu riƙa amfani da kowane zarafi mu yi ibada tare kuma mu ƙarfafa juna don dukanmu mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.

Yin Wa’azi da Ƙwazo

23. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta bayyana cewa wajibi ne dukan shafaffu su yi wa’azi?

23 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koyar cewa ya kamata dukan shafaffu su yi wa’azi game da gaskiyar Kalmar Allah. A shekara ta 1885, mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce: “Kada mu manta cewa ya kamata dukan shafaffu su yi wa’azi (Isha. 61:1), domin an shafe su ne don yin wa’azi.” Wani talifin Hasumiyar Tsaro ta 1888 ya ce: “Umurninmu a bayyane yake . . . Idan muka ƙi yin wannan aikin kuma muka ba da hujja, hakan zai nuna cewa mu ragwayen bayi ne kuma ba za mu cancanci kasancewa shafaffu ba.”

24, 25. (a) Ban da yin wa’azi mene ne Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa suka ƙarfafa mutane su yi? (b) Ta yaya wani majagaba ya kwatanta aikinsa a zamanin da babu motoci sosai?

24 Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun nuna ƙwazo sosai wajen ƙarfafa mutane su yi wa’azi. Sun kuma soma wallafa wasu warƙoƙi da ake kira Bible Students’ Tracts, waɗanda daga baya aka kira Old Theology Quarterly. Masu karanta Hasumiyar Tsaro sun karɓi waɗannan warƙoƙin don su riƙa rarraba wa mutane kyauta.

Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Ina sa yin wa’azi kan gaba a rayuwata kuwa?’

25 Majagaba ne ake kiran waɗanda suke wa’azi na cikakken lokaci. Ɗan’uwa Charles Capen da aka ambata ɗazun yana cikinsu kuma ya ce: “Na yi amfani da taswirorin da United States Government Geological Survey (Hukumar Duba Yanayi na Ƙasar Amirka) ta tanadar don in san inda ya kamata in yi wa’azi a yankin Pennsylvania. Waɗannan taswirorin sun nuna dukan hanyoyi, kuma hakan ya taimaka mana mu yi wa’azi kuma mu kammala kowace ƙaramar hukuma da kafa. A wasu lokuta bayan na yi tafiya na kwana uku a ƙauyukan ina karɓan odar littattafan Studies in the Scriptures (Nazarin Nassosi), sai in ɗauki hayar karusa don in rarraba littattafan ga waɗanda suka yi oda. Nakan sauka kuma in kwana tare da manoma. Domin a lokacin babu motoci sosai.”

Wani majagaba da doki mai karusa

Wani majagaba. Duba “Chart of the Ages” da aka rubuta a jikin karusar

26. (a) Me ya sa bayin Allah suke bukata su fita wa’azi don su kasance a shirye domin sarautar Kristi? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka dace mu yi kanmu?

26 Yin wa’azi a wannan lokacin ya bukaci gaba gaɗi da kuma ƙwazo. Da a ce ba a koya wa Kiristoci na gaskiya muhimmancin yin wa’azi ba, da sun kasance a shirye don sarautar Kristi ne? A’a! Ballantana ma, wannan wa’azi aiki ne da ke da muhimmanci sosai a lokacin bayyanuwar Kristi. (Mat. 24:14) Bayin Allah suna bukatar su kasance a shirye don su saka wannan aikin cetar da rai abu na farko a rayuwarsu. Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina sa yin wa’azi kan gaba a rayuwata kuwa? Ina yin sadaukarwa don in samu in fita wa’azi sosai kuwa?’

An Kafa Mulkin Allah!

27, 28. Mene ne Yohanna ya gani a wahayi kuma mene ne Shaiɗan da aljannunsa suka yi sa’ad da aka kafa Mulkin?

27 A ƙarshe, shekara mai muhimmanci ta 1914 ta cika. Kamar yadda muka tattauna a farkon wannan babin, babu wanda ya ga abubuwa masu ban al’ajabi da suka faru a sama. Amma, an saukar wa manzo Yohanna wahayin da ya bayyana waɗannan abubuwan a alamance. Ka yi tunanin abin da ya faru: Yohanna ya shaida “wata alama mai-girma” a sama. An kwatanta ƙungiyar Allah da ke sama da ta ƙunshi mala’iku da wata “mace” wadda ta ɗauki ciki kuma ta haifi ɗa namiji. Wannan ɗa na alama ba da daɗewa ba zai “mallaki dukan al’ummai da sanda ta ƙarfe.” Sa’ad da aka haife shi sai aka fizge ‘ɗan, aka kai shi wurin Allah, har ga kursiyinsa.’ Sai aka ji wata babbar murya daga sama ta ce: “Yanzu ceto, da iko, da mulkin Allahnmu ya zo, da sarautar Kristinsa kuma.”—R. Yoh. 12:1, 5, 10.

28 Babu shakka, manzo Yohanna ya ga sa’ad da aka kafa Mulkin Almasihu a wahayi. Lallai hakan abu ne mai ban al’ajabi, amma ba kowa ba ne ya ji daɗin abin da ya faru. Shaiɗan da aljanunsa sun yi yaƙi da mala’iku waɗanda suke ƙarƙashin ja-gorancin Mika’ilu, ko kuma Kristi. Mene ne sakamakon? Ayar ta ce: “Aka jefar da babban maciji, wato tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefar da shi a duniya, aka jefar da mala’ikunsa kuma tare da shi.”—R. Yoh. 12:7, 9.

Bayyanuwar Kristi da ba a iya gani da ido ba

A shekara ta 1914 ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma fahimtar alamar bayyanuwar Kristi da ba a iya gani da ido ba

29, 30. Bayan da Yesu ya soma sarauta, ta yaya yanayi ya canja a (a) duniya? (b) sama?

29 Shekaru da yawa kafin 1914, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ce lokacin shan wuya zai soma ne a wannan shekarar. Amma ba su san cewa abin da suka faɗa zai cika fiye da yadda suke tsammani ba. Kamar yadda wahayin Yohanna ya nuna, Shaiɗan zai soma yin tasiri a al’ummar ’yan Adam sosai. Wahayin ya ce: “Kaiton duniya da teku: Domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (R. Yoh. 12:12) A shekara ta 1914, yaƙin duniya na ɗaya ya ɓarke kuma an soma ganin cikar annabcin bayyanuwar Kristi a matsayin Sarki a faɗin duniya. A wannan lokacin ne “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin suka soma.—2 Tim. 3:1.

30 Amma, an yi farin ciki a sama. An kori Shaiɗan da aljanunsa kwatakwata daga sama. Ru’ya ta Yohanna ta ce: “Domin wannan fa, ku yi farin ciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.” (R. Yoh. 12:12) Tun da an riga an tsabtacce sammai kuma an naɗa Yesu Sarki, hakan ya sa Mulkin Almasihu ya yi shirin ɗaukan mataki a madadin bayin Allah a duniya. Wane mataki ne zai ɗauka? Kamar yadda muka tattauna a farkon wannan babin, abin da Kristi ya soma yi wa bayin Allah a duniya gyara. Wannan shi ne abin da ya soma yi a matsayin “mala’ikan alkawari.” Mene ne hakan yake nufi?

Lokacin Gwaji

31. Mene ne Malachi ya annabta game da lokacin gyara, kuma ta yaya wannan annabcin ya soma cika? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

31 Annabcin Malakai ya nuna cewa gyarar ba za ta kasance da sauƙi ba. Ya ce: ‘Amma wane ne za ya daure da ranar zuwansa? Wane ne kuwa za ya tsaya idan ya bayyana? Gama yana kama da wutar mai-gyaran ƙarfe, kamar sabulun mai-gyaran tufa.’ (Mal. 3:2) Waɗannan kalmomin sun tabbata! Daga shekara ta 1914, bayin Allah a duniya sun fuskanci gwaji da wahala iri-iri masu tsananin gaske. Da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya ɓarke, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun fuskanci tsanantawa sosai kuma an jefa su cikin kurkuku.d

32. Wace matsala ce bayin Allah suka fuskanta a shekara ta 1916?

32 Har ila, an sami matsala a cikin ƙungiyar. Ɗan’uwa Russell ya rasu a shekara ta 1916, yana da shekara 64, kuma rasuwarsa ta gigita bayin Allah da yawa. Mutuwarsa ta bayyana cewa wasu daga cikin mutanen suna girmama shi fiye da yadda ya kamata. Ko da yake Ɗan’uwa Russell ba ya son irin wannan ɗaukakar, amma mutanen tamkar dai suna bauta masa ne a zukatansu. Wasu sun ɗauka cewa mutuwarsa za ta kawo ƙarshen ƙarin hasken da ake samu game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma saboda ɓacin rai, wasu sun yi ƙoƙarin hana ci gaban aikin. Wannan halin ne ya haifar da ’yan ridda da suka raba kan ƙungiyar.

33. Ta yaya abubuwan da ake tsammani za su faru amma ba su faru ba suka gwada bayin Allah?

33 Wani gwajin kuma shi ne wasu abubuwan da ake tsammanin za su faru ba su faru ba. Ko da yake mujallar Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa Lokatan Al’ummai za su cika a shekara ta 1914, ’yan’uwa ba su fahimci abin da zai faru a shekarar ba. (Luk 21:24) Sun yi tsammanin cewa a wannan shekarar ce Kristi zai kai shafaffunsa sama don su yi sarauta tare. Amma hakan bai faru ba. A ƙarshen shekara ta 1917, Hasumiyar Tsaro ta sanar cewa girbin da aka soma shekaru arba’in da suka shige zai ƙare a farkon shekara ta 1918. Amma an ci gaba da yin wa’azi sosai har bayan wannan lokacin. Mujallar ta ce an gama girbin amma ba a gama kala ba. Duk da haka, mutane da yawa sun daina bauta wa Jehobah saboda taƙaici.

34. Wane gwaji ma tsanani ne ya auku a shekara ta 1918, kuma me ya sa Kiristendam suka yi tsammanin cewa bayin Allah ba za su ci gaba da aikinsu ba?

34 Wani gwaji mai tsanani ya auku a shekara ta 1918. Ɗan’uwa Joseph Franklin Rutherford shi ne ya gāji Ɗan’uwa Charles Taze Russell wajen yi wa bayin Allah ja-gora. Kuma an kama shi da kuma wasu ’yan’uwa guda bakwai da suke taimaka masa. An yi musu shari’ar rashin adalci kuma aka yanke musu hukuncin ɗauri na shekaru da yawa a kurkukun gwamnati da ke Atlanta, Georgia, na ƙasar Amirka. A lokacin, kamar dai aikin bayin Allah ya tsaya ne cak. Limaman coci-cocin Kiristendam da yawa sun yi farin ciki. Sun ɗauka cewa tun da an ɗaure “shugabannin,” an rufe hedkwatar da ke Brooklyn, kuma ana yunkurin hana yin wa’azi a Amirka da kuma Turai, ba za a sake ganin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna damun mutane da wa’azinsu ba. (R. Yoh. 11:3, 7-10) Amma hakan ƙarya ne!

Lokacin Farfaɗowa!

35. Me ya sa Yesu ya ƙyale mabiyansa su fuskanci mawuyacin yanayi, kuma wane mataki ne ya ɗauka don ya taimaka musu?

35 Waɗanda suke gāba da bayin Allah ba su san cewa Yesu ne ya ƙyale mabiyansa su fuskanci wannan mawuyacin halin ba. Hakan ya faru ne don Jehobah yana yin aikinsa na ‘mai-gyaran azurfa mai-tsarkake ta.’ (Mal. 3:3) Jehobah da Ɗansa suna da tabbaci cewa wannan gwajin zai gyara bayin Allah masu aminci kuma ya tsarkake su don su cancanci yi wa Sarkin hidima fiye da dā. Daga farkon shekara ta 1919, a bayyane yake cewa ruhun Allah ya yi abin da magabtan bayin Allah suka ɗauka cewa ba zai yiwu ba. Mutanensa masu aminci sun farfaɗo! (R. Yoh. 11:11) A lokacin ne Kristi ya cika wani babban annabci game da kwanaki na ƙarshe. Ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” wato, wani ƙaramin rukunin ’yan’uwa maza shafaffu waɗanda za su riƙa yi wa mutanensa ja-gora ta wurin yi musu tanadin koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan kari.—Mat. 24:45-47.

Bangon Bulletin da The Golden Age na farko

36. Me ya nuna cewa bayin Allah sun soma farfaɗowa a ibadarsu?

36 An sake Ɗan’uwa Rutherford da abokan aikinsa daga kurkuku a ranar 26 ga Maris, 1919. Nan da nan aka shirya wani babban taron da za a yi a watan Satumba na shekarar. Kuma an soma yin shiri don wallafa mujalla ta biyu da za a kira The Golden Age. An tsara wannan mujallar da ake wallafawa tare da Hasumiyar Tsaro don yin wa’azi.e A wannan shekarar ce kuma aka wallafa fitowa ta farko ta Bulletin, wadda yanzu muke kira Hidimarmu ta Mulki. Tun da aka soma wallafa ta, tana tanadar da bayanai game da yadda za mu yi wa’azi. Babu shakka, tun daga shekarar 1919, an fi mai da hankali ga yin wa’azi gida-gida.

37. Ta yaya wasu suka nuna rashin aminci bayan shekara ta 1919?

37 Wa’azin da ake yi ya ci gaba da gyara bayin Kristi, amma masu fahariya da kuma masu taurin kai da ke cikinsu sun ƙi yin wannan aikin. Waɗannan mutanen da suka ƙi yin wannan aikin sun daina tarayya da bayin Allah masu aminci. A ’yan shekaru bayan 1919, wasu mutane marasa aminci sun yi fushi kuma suka soma tsegumi da ɓatanci, har ma suka soma goyon bayan masu tsananta wa amintattun bayin Jehobah.

38. Mene ne nasarar da mabiyan Kristi suka samu ya tabbatar mana?

38 Duk da waɗannan farmakin, mabiyan Kristi da ke duniya sun ci gaba da bunƙasa da kuma ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Dukan nasarorin da suka samu tun daga wannan lokacin ya tabbatar da mu cewa Mulkin Allah yana sarauta! Waɗannan rukunin mutane ajizai sun ci gaba da yin nasara a kan Shaiɗan da kuma wannan muguwar zamanin ne don taimako da kuma albarka da Allah ya tanadar ta hanyar Ɗansa da Mulkinsa!—Karanta Ishaya 54:17.

Ɗan’uwa Rutherford ya ba da wani jawabi mai ƙayatarwa a wani taron gunduma na shekara ta 1919

Ɗan’uwa Rutherford ya ba da wani jawabi mai ƙayatarwa a wani taron gunduma bayan ’yan watanni da sakinsa daga fursuna

39, 40. (a) Ka ambata wasu fassalolin wannan littafin? (b) Ta ya ya za ka amfana daga yin nazarin wannan littafin?

39 A babobi na gaba, za mu tattauna abin da Mulkin Allah ya cim ma a nan duniya tun da aka kafa shi a sama. Kowane sashe na wannan littafin zai tattauna wani muhimmin fanni na aikin da Mulkin yake yi a nan duniya. Kowane babi yana da akwatin bita da zai taimaka wa kowannenmu ya san ko ya gaskata da Mulkin sosai. A babobi na ƙarshe, za mu tattauna abin da zai faru sa’ad da Mulkin ya halaka mugaye kuma ya mai da duniya aljanna. Ta yaya za ka amfana daga yin nazarin wannan littafin?

40 Shaiɗan yana so ka daina gaskatawa da Mulkin Allah. Amma Jehobah yana so ka kasance da bangaskiya sosai don hakan zai kāre ka kuma zai kyautata dangantakarka da shi. (Afis. 6:16) Saboda haka, muna ƙarfafa ka ka yi addu’a sosai a duk lokacin da za ka yi nazarin wannan littafin. Ka riƙa yi wa kanka wannan tambayar, ‘Shin na gaskata da Mulkin Allah kuwa?’ Idan ka gaskata da Mulkin Allah yanzu, za ka kasance da aminci da kuma ƙwazo wajen tallafa wa Mulkin har sai lokacin da kowa ya tabbata cewa Mulkin Allah yana sarauta da gaske!

a Don ƙarin bayani game da Grew, Stetson, da kuma Storrs, ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 45-46.

b Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ga muhimmancin daina tarayya da addinan ƙarya, amma sun yi shekaru suna ɗaukan wasu mutane a matsayin ’yan’uwansu Kiristoci. Waɗannan mutanen ba sa cikinsu ko da yake suna da’awa cewa sun gaskata da fansar Kristi kuma sun keɓe kansu ga Allah.

c Wani abin da ya sa ba su ɗauki wannan kashedin da muhimmanci ba da farko shi ne, an ɗauka cewa ya shafi ƙaramin garken Kristi ne kaɗai wanda ya ƙunshi shafaffu 144,000. A Babi na 5,za mu ga cewa kafin shekara ta 1935, an ɗauka cewa “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, ya ƙunshi membobin coci-cocin Kiristendam; kuma za a ba su ladar zama rukuni na biyu da za su je sama domin sun goyi bayan Kristi a lokacin ƙarshe.

d A watan Satumba ta shekara ta 1920, an wallafa wata mujalla ta musamman mai suna The Golden Age (da yanzu muke kira Awake!) da ta yi bayani dalla-dalla a kan tsanantawa dabam-dabam, har da masu zafi sosai da aka yi wa ’yan’uwanmu a ƙasashe kamar su Kanada da Ingila da Jamus da kuma Amirka. Akasin haka, a shekarun da suka gabaci yaƙin duniya na ɗaya, ba a tsananta wa bayin Allah sosai ba.

e An yi shekaru da yawa ana wallafa Hasumiyar Tsaro don ilimantar da ƙaramin garken kawai.

Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?

  • Waye ne ya taimaka wajen shirya mabiyan Yesu na gaskiya don Mulkin da za a kafa?

  • Ta yaya aka shirya Kiristoci na gaskiya don Mulkin Allah?

  • Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa Mulkin gwamnati ce ta gaske? (Ka duba akwatin nan “Mulkin Allah​—Gwamnati Ce ta Gaske.”)

  • Ta yaya za ka bi misalin mabiyan Kristi masu aminci na ƙarnin da ya wuce yayin da kake goyon bayan Mulkin a yau

MULKIN ALLAH—GWAMNATI CE TA GASKE

Shin Mulkin Allah gwamnati ce ta gaske? Ga kaɗan daga cikin fannonin Mulkin Allah. Ka tambayi kanka, ‘Shin waɗannan fannonin ba su nuna cewa Mulkin Allah gwamnati ce da ta fi kowace gwamnatin ɗan Adam fifiko ba?’

  • Sarki yana zaune a kursiyinsa

    SARKI

    An naɗa Yesu Sarki a shekara ta 1914 kuma shi Sarki ne mai iko da adalci da hikima da kuma tausayi. Ƙari ga haka, yana da tawali’u a gaban Jehobah Allah. (Isha. 9:6, 7; 11:1-3) Akasin shugabannin ’yan Adam ajizai, waɗanda ’yan majalisa da wakilai da kuma rukunoni dabam-dabam sukan hana su yin abin da ya dace, babu wanda zai iya ba Yesu cin hanci ko ya hana shi cim ma burinsa.

  • IKON KAFA DOKOKI DA YIN SHARI’A

    Rayuwar da Yesu ya yi a duniya da misalin da ya kafa ne tushen cikakkiyar shari’a, wato “shari’ar Kristi.”—Gal. 6:2; 1 Bit. 2:21.

    Jehobah ya ba Ɗansa dukan ikon yin shari’a, kuma Yesu yana yin wannan aikin shari’ar yadda ya kamata, fiye da duk wani alƙali a duniya.—Yoh. 5:22.

  • Abokan sarauta

    ABOKAN SARAUTA

    Yesu zai yi mulki da abokan sarauta guda 144,000 kuma za su yi mulkin adalci bisa duniya. Ainihin manufar sarautarsa ita ce ya sulhunta mutane da Allah, saboda haka, abokan sarautarsa za su yi hidima a matsayin firistoci don tabbatar da hakan.—R. Yoh. 14:1; 20:6.

  • Mala’iku da takobansu

    RUNDUNA

    A matsayin Shugaban rundunar mala’iku mafi girma, Yesu yana da rundunar mala’iku masu ƙarfin gaske waɗanda babu irin su. Yesu da rundunarsa za su yi yaƙi don kawar da dukan mugunta.—Zab. 45:1, 3-5; R. Yoh. 19:11, 14-16.

  • MASARAUTA

    Gadon sarautar Yesu yana sama a gefen Ubansa. Sama inda Jehobah yake wuri ne “cike da tsarki da ɗaukaka.” (Isha. 63:15, Littafi Mai Tsarki) Shin hakan gaskiya ne? Hakika! Ba za a iya kwatanta wannan wurin da babban birnin wata ƙasa ko kuma wani ginin gwamnati ba, don abubuwan da ke sama ba sa lalacewa.—Mat. 6:20.

  • Duniya

    YANKI A DUNIYA

    A yau talakawan Yesu suna nan kamar baƙi masu bin doka da ke zaune a kowace ƙasa. Amma Jehobah ya yi musu tanadin ƙungiyarsa wadda za a iya kwatantawa da ƙasar da ake yin nufin Sarkin a ciki. (Isha. 60:2; 66:8) Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Yesu zai mallaki dukan duniya kuma za ta zama yankinsa.—Zab. 72:8.

  • TSARIN AYYUKAN GWAMNATIN

    Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai tanadar da dukan waɗannan abubuwan da Allah ya yi alkawarinsu, har ma da ƙari.—Zab. 72:16; Isha. 2:3; 33:24; 35:6; 65:21.

    • Wata yarinya mai koshin lafiya tana gudu

      ƘOSHIN LAFIYA

    • Wani gida mai kyau

      GIDAJE

    • Wani mutum yana gini

      AIKI

    • Lafiyayyen abinci

      LAFIYAYEN ABINCI

    • Wani mutum yana nazari

      ILIMI

  • TALAKAWA MASU AMINCI

    Littafi Mai Tsarki ya ce “rashin mutane shi ne hallakar hakimi,” ya kuma ce “fahariyar sarki yawan mutane ne.” (Mis. 14:28) Amintattun talakawan da za su kasance a ƙarƙashin Mulkin nan sun wuce miliyan bakwai da dubu ɗari biyar.

    Mutane daga bangarori dabam-dabam

SUN YI SHIRI DON MULKIN DA ZA A KAFA

Ka yi la’akari da wasu abubuwan da suka faru shekaru da yawa kafin shekara ta 1914. Shin za ka iya gano yadda waɗannan abubuwan suka taimaka wa bayin Allah su yi shiri don Mulkin Almasihu da za a kafa?

  1. Wajen 1850

    Henry Grew da George Stetson da kuma George Storrs sun yi bincike kuma sun fallasa koyarwar nan ta ƙarya cewa kurwa ba ta mutuwa

  2. 1868 ko 1869

    Charles Taze Russell ya soma bincike a kan koyarwar coci-cocin Kiristendam kuma ya gano cewa ba su bayyana nassosi da kyau ba. Wa’azin wani ɗan cocin Adventist mai suna Jonas Wendell da Russell ya saurara ne ya sake ƙarfafa “bangaskiyarsa da ta raunana”

  3. 1870

    Ɗan’uwa Russell ya kafa wani rukunin yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma suka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki cikin tsari

    Wai rukunin nazari a shekara ta 1870
  4. 1870-1875

    An daɗa fahimtar gaskiya game da kurwa da fansa da kuma zuwan Kristi

  5. 1876

    Wani talifin da Charles Taze Russell ya rubuta wanda aka wallafa a cikin mujallar nan Bible Examiner, ya bayyana cewa a shekara ta 1914 ne Lokuttan Al’ummai zai ƙare

  6. 1877

    An wallafa mujallar nan The Object and Manner of Our Lord’s Return don a bayyana gaskiya game da bayyanuwar Kristi

  7. 1879

    A wannan shekarar ce aka wallafa mujallar farko ta Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona

    Bangon farko na Zion’s Watch Tower da Herald of Christ’s Presence

    A wannan shekarar ce aka fahimci cewa ƙananan coci-cocin Kiristendom ma sashe ne na Babila Babba

  8. 1880

    Ɗan’uwa Russell ya ziyarci rukunonin nazarin Littafi Mai Tsarki da ke arewa-maso-gabashin Amirka don ya ƙarfafa su

  9. 1881

    An wallafa warƙoƙi masu shafuffuka da yawa (wasu ma fiye da shafuffuka 100) kuma aka ba masu karanta Hasumiyar Tsaro don su rarraba wa mutane kyauta

    Hasumiyar Tsaro ta gayyaci dukan masu karatu su halarci taron Tuna Mutuwar Yesu a yankin Allegheny, a Pennsylvania

    An soma hidimar majagaba

    Talifin da ya ce ana bukatar masu wa’azi 1,000 da kuma wanda ya ce an shafe su su yi wa’azi sun ƙarfafa mutane su yi wa’azi da ƙwazo

    An ƙarfafa Kiristocin da ba sa yin taro a kai a kai su soma yin hakan

  10. 1882

    An wallafa wani talifi da ya ƙaryata koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya

  11. 1885

    Mujallun Hasumiyar Tsaro sun yaɗu zuwa nahiyoyi biyar na duniya

  12. 1886

    An fitar da littafin nan The Divine Plan of the Ages, wanda shi ne kundi na farko na Studies in the Scriptures

    An gayyaci masu karanta Hasumiyar Tsaro zuwa wani babban taro na kwana uku da za a yi bayan taron Tuna Mutuwar Kristi, kuma wannan babban taron ne sanadin soma manyan taron da ake yi duk shekara

  13. 1889

    An gina hedkwatar da ake kira Bible House a yankin Allegheny, Pennsylvania

  14. 1891

    Charles Taze Russell ya soma tafiya ƙasashen waje don ya “yaɗa koyarwar Littafi Mai Tsarki”

  15. 1894

    An tura wasu ’yan’uwa su wakilci Tower Tract Society wajen kai wa ikilisiyoyi ziyara da kuma ƙarfafa su kamar yadda masu kula masu ziyara suke yi a yau

    Masu ziyara a shekara ta 1890
  16. 1895

    Hasumiyar Tsaro ta ce wasu ’yan’uwa suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ake kira “Dawn Circles” tare a matsayin rukuni sai ya ƙarfafa ’yan’uwa a ko’ina su riƙa yin hakan”

  17. 1896

    Charles Taze Russell ya wallafa wata ƙasida mai suna What Say the Scriptures About Hell?

    Watch Tower Society sun biya wata maɗaba’a ta wallafa musu Littafi Mai Tsarki, fassarar Joseph B. Rotherham’sNew Testament

  18. 1900

    An buɗe ofishin reshe na farko a birnin Landan, a ƙasar Ingila

    Wa’azi ya kai ƙasashe 28

  19. 1903

    An soma rarraba warƙoƙi gida-gida kyauta a ranar Lahadi. Kafin wannan lokacin, ana rarraba su a hanyoyin da ke kusa da coci-coci ne kawai

    An soma wallafa wa’azin Ɗan’uwa Russell a cikin jaridu a kai a kai

  20. 1909

    An ƙaurar da Hedkwatar Watch Tower Society zuwa yankin Brooklyn a birnin New York

    ’Yan’uwa uku suna tattaunawa
  21. 1910

    Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma amfani da sunan nan International Bible Students Association

  22. 1911-1912

    A wani tafiyar da suka yi mai nisan mil 35,000, Charles Taze Russell da abokan aikinsa shida sun yi yawon zagawa suna ziyartar wurare a faɗin duniya don su bincika “matsayi da kuma yiwuwar yaɗuwar Kiristanci” a ƙasashe da yawa kamar su Caina da Indiya da Japan da kuma Filifin

  23. 1914

    An nuna wannan fim mai suna “Photo-Drama of Creation” a karo na farko a birnin New York, a ranar 11 ga Janairu, kuma a watan Fabrairu na shekarar, an nuna shi a wasu birane biyar. A ƙarshen wannan shekarar, mutane kusan 9,000,000 a nahiyar Amirka ta arewa da Turai da Ostareliya da kuma New Zealand sun kalli fim ɗin a hanyoyi dabam-dabam

    Wani mai kunna fim din “Photo-Drama”

    A watan Oktoba, Charles Taze Russell ya yi wata sanarwa ga iyalin Bethel, cewa: “Lokuttan Al’ummai ya ƙare; kuma zamanin sarakunansu ya wuce.” Wata ’yar’uwa da take wurin ta ce ya daɗa da cewa: “Saboda haka, ba mu san abin da zai faru da mu a nan gaba ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba