Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 8/15 pp. 20-24
  • Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA KASHE WUTAR YIN MAGANA DA GARAJE
  • KA GUJI ZARGE, WATO, TSORO DA MATSI
  • KA GUJE WA TARKON DA KE RUGURGUJE ABU, WATO, YAWAN JIN LAIFI
  • MU BA JAHILAI BA NE GA TARKUNAN SHAIƊAN
  • Za Ka Iya Kuɓuta Daga Tarkon Shaiɗan!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • “Ku Yi Tsayayya Da Iblis”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 8/15 pp. 20-24

Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!

‘Ka kuɓuce wa tarkon Iblis.’​—2 TIM. 2:26, Littafi Mai Tsarki.

MECE CE AMSARKA?

Me ya kamata ka yi idan kana yawan kushe mutane?

Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Bilatus da Bitrus game da jin tsoro da kuma faɗawa cikin matsi?

Ta yaya za mu guji yawan jin laifi?

1, 2. Waɗanne tarkuna da Shaiɗan yake amfani da su ne za mu tattauna a wannan talifin?

SHAIƊAN yana ƙoƙari sosai don ya rinjayi bayin Jehobah. Amma, ba kowanne lokaci ba ne yake halaka bayin Jehobah kamar yadda maharbi yake kashe kamunsa ba. Ainihin abin da yake so sa’ad da ya kama mutum cikin tarkonsa shi ne ya yi amfani da mutumin yadda ya ga dama.—Karanta 2 Timotawus 2:24-26.

2 Idan maharbi yana son ya kama dabba, zai iya yin amfani da tarkuna iri-iri. Zai iya sa dabbar ta fito daga inda ta ɓoye don ya kama ta da zarge. Ko kuma zai iya ɓoye tarko sosai yadda dabbar ba za ta iya sani ba. Shaiɗan yana yin amfani da abubuwa da ke kamar tarko don ya kama bayin Allah. Idan ba ma son ya kama mu, dole ne mu kasance a faɗake kuma mu mai da hankali ga alamun da suke nuna cewa mun kusan faɗa cikin wani tarkon da Shaiɗan ya ɗana. Wannan talifin zai tattauna yadda za mu iya kāre kanmu daga tarkuna guda uku da Shaiɗan ya yi amfani da su wajen kama wasu bayin Allah. Waɗannan tarkunan su ne, (1) yin magana da garaje, (2) tsoro da matsi da kuma (3) yawan jin laifi. A talifi na gaba, za a tattauna ƙarin tarkuna biyu da Shaiɗan yake amfani da su.

KA KASHE WUTAR YIN MAGANA DA GARAJE

3, 4. Wace matsala ce yin magana da garaje zai iya jawowa? Ka ba da misali.

3 Idan maharbi yana son ya kama wata dabba da ke a ɓoye cikin daji, zai iya cinna wa wurin wuta. Kuma sai ya kama dabbar idan tana neman gudu don kada wutar ta ƙone ta. Hakazalika, a alamance, Shaiɗan zai so ya cinna wa ikilisiyar Kirista wuta don ’yan’uwa su watse. Kuma idan ya yi nasara, sai ya kama duk wanda ya nemi ya gudu. Ta yaya za mu iya sa Shaiɗan ya yi nasara ba tare da saninmu ba?

4 Wani almajirin Yesu mai suna Yaƙub ya kamanta harshe da wuta. (Karanta Yaƙub 3:6-8.) Idan muna yin magana da garaje za mu iya cinna wa ikilisiya wuta a alamance. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ka yi la’akari da wannan misalin: An yi sanarwa a taron ikilisiya cewa an naɗa wata ’yar’uwa a matsayin majagaba na kullum. Bayan an tashi taron, sai wasu ’yan’uwa mata biyu suka soma taɗi game da sanarwar da aka yi. Ɗaya cikinsu ta nuna cewa tana farin ciki sosai don sanarwar da aka yi. Amma, ɗayan ta soma kushe ’yar’uwar cewa tana neman suna ne a cikin ikilisiya. Wace ce za ka so ta zama abokiyarka a cikin waɗannan ’yan’uwa mata biyun? Ba shi da wuya a san wadda za ta cinna wa ikilisiya wuta a alamance ta yadda take magana.

5. Idan muna son mu kashe wutar yin magana da garaje, me ya kamata mu yi?

5 Ta yaya za mu iya kashe wutar yin magana da garaje? Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Mat. 12:34) Wannan ayar ta nuna cewa abu na farko da za mu yi shi ne mu bincika zuciyarmu. Zai dace mu kawar da tunani marar kyau da zai sa mu riƙa yin maganganu marasa kyau game da mutane. Alal misali, idan mun samu labari cewa wani ɗan’uwa yana aiki tuƙuru a cikin ikilisiya, muna yin tunani cewa yana yin hakan ne don ya faranta wa Jehobah rai ne, ko kuwa muna gani cewa yana neman suna ne? Idan muna yawan sūkar ’yan’uwanmu, ya kamata mu tuna cewa Shaiɗan ma ya yi shakkar amintaccen bawan Jehobah mai suna Ayuba. (Ayu. 1:9-11) Maimakon sūkar ’yan’uwanmu, ya kamata mu yi tunani a kan dalilin da ya sa muke yin hakan. Shin muna da ƙwaƙƙwarar dalilin na yin hakan? Ko kuwa rashin ƙauna da ya zama gama gari a wannan kwanaki na ƙarshe ne ya mamaye mu.—2 Tim. 3:1-4.

6, 7. (a) Waɗanne dalilai ne za su iya sa mu riƙa kushe mutane? (b) Mene ne ya kamata mu yi idan mutane suka yi mana baƙar magana?

6 Ka yi la’akari da wasu dalilai da za su iya sa mu riƙa kushe mutane. Dalili na ɗaya shi ne, wataƙila za mu so abubuwan da muke yi su riƙa burge mutane sosai. Saboda haka, idan muna kushe wasu, za mu nuna cewa mun fi sauran mutane adalci. Ko kuma muna neman hujjar ƙin yin abin da ya kamata mu yi. Ko da muna kushe mutane domin muna da fahariya, ko kuma don ba mu yarda da kanmu ba, hakan zai kawo sakamako marar kyau.

7 Wataƙila muna yin tunani cewa muna da ƙwaƙƙwarar dalili na kushe mutane. Mai yiwuwa, ya taɓa mana baƙar magana. Ko da hakan ya ɓata mana rai, bai dace mu yi ramako ba. Yin hakan zai daɗa sa abin ya yi muni. Abin da Shaiɗan yake son mu yi ke nan, amma Allah ba ya son haka. (2 Tim. 2:26) Ya kamata mu yi koyi da Yesu. Sa’ad da aka zarge shi, “ba ya mayar da zagi ba.” Maimakon haka, ya ‘dogara ga mai shari’ar adalci.’ (1 Bit. 2:21-23) Yesu ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai daidaita yanayin a hanyar da kuma a lokacin da ta dace. Ya kamata mu ma mu dogara ga Allah. Idan mun yi maganar da ke ƙarfafa mutane, muna sa ikilisiya ta kasance da “ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.”—Karanta Afisawa 4:1-3.

KA GUJI ZARGE, WATO, TSORO DA MATSI

8, 9. Me ya sa Bilatus ya ce a kashe Yesu?

8 Idan tarko ya kama dabba, ba za ta iya yawo kuma ba. Hakazalika, idan mutum ya ƙyale tsoro da matsi su shawo kansa, ba zai iya sakewa sosai ba. (Karanta Misalai 29:25.) Bari mu tattauna misalan maza biyu da suka ƙyale matsi da tsoron mutane su shawo kansu. Kuma za mu ga yadda za mu iya koyi darasi daga misalinsu.

9 Bilatus Babunti, Gwamnan ƙasar Roma ya san cewa Yesu bai da wani laifi, saboda haka, ba ya son ya hukunta shi. Bilatus ya ma ce Yesu bai yi wani abu “wanda ya isa mutuwa” ba. Amma duk da haka, Bilatus ya ce a kashe shi. Me ya sa ya ɗauki wannan matakin? Domin mutanen sun matsa masa. (Luk 23:15, 21-25) Mutanen sun ta da muryarsu suna cewa, “idan ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne.” (Yoh. 19:12) Wataƙila Bilatus ya ji tsoro cewa idan ya goyi bayan Yesu zai rasa muƙaminsa ko kuma za a kashe shi. Ya ƙyale matsin ya shawo kansa kuma ya yi nufin Shaiɗan.

10. Me ya sa Bitrus ya musunci Yesu?

10 Manzo Bitrus abokin Yesu na kud da kud ne. Ya ma yi shela cewa Yesu ne Almasihu. (Mat. 16:16) Akwai wani lokacin da Yesu ya faɗi abin da ya sa almajiransa suka watse. Amma, Bitrus bai rabu da bin Yesu ba, ya kasance da aminci. (Yoh. 6:66-69) Kuma sa’ad da maƙiya suka zo kama Yesu, Bitrus ya kāre shi da takobinsa. (Yoh. 18:10, 11) Daga baya, Bitrus ya ƙyale tsoro ya shawo kansa, har ma ya musunci Yesu. Jin tsoron mutum yana kama da tarko, kuma wannan tarkon ya kama Bitrus na ɗan lokaci. A wannan lokacin, bai kasance da gaba gaɗin yin abin da ya dace ba.—Mat. 26:74, 75.

11. Waɗanne gwaje-gwaje ya kamata mu yi tsayayya da su?

11 Tun da yake mu Kiristoci ne, ya kamata mu guji yin abin da zai sa mu ɓata wa Allah rai. Shugaban aikinmu ko kuma wasu, za su iya matsa mana don mu yi rashin gaskiya ko kuma mu yi lalata. Za a iya matsa wa Kiristoci da suke zuwa makaranta su yi maguɗi a jarabawa, ko su kalli hotunan batsa, ko su sha taba ko kuma su yi lalata. Tun da yake Jehobah ba ya farin ciki idan mun ƙyale matsi ko tsoro ya shawo kanmu, mene ne za mu iya yi don mu guji faɗawa cikin wannan tarkon?

12. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Bilatus da kuma Bitrus?

12 Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga misalan Bilatus da kuma Bitrus. Bilatus bai san Yesu sosai ba. Amma duk da haka, ya san cewa Yesu bai yi wani laifi ba kuma ya bambanta da sauran mutane. Bilatus bai da tawali’u kuma ba ya ƙaunar Allah na gaskiya. Kuma hakan ya sa Iblis ya samu sauƙin kama shi cikin tarkonsa. Bitrus ya san Allah sosai kuma yana ƙaunarsa. Amma, akwai lokacin da bai nuna filako ba, ya ji tsoron mutum kuma ya ƙyale matsi ya shawo kansa. Dab da lokacin da aka kama Yesu, Bitrus ya cika baki ya ce: “Ko duka za su yi tuntuɓe, ban da ni.” (Mar. 14:29) Da ya kamata Bitrus ya dogara ga Jehobah kamar yadda wani marubucin zabura ya kasance a shirye sosai don ya yi tsayayya da gwaji. Marubucin zaburar ya ce: “Ubangiji yana wajena; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum za ya yi mani?” (Zab. 118:6) A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya kai Bitrus da Yaƙub da Yohanna lambun Jathsaimani. Yesu ya gaya musu su yi tsaro, amma Bitrus da sauran manzannin suka yi barci. Sa’ad da Yesu ya dawo ya same su suna barci, sai ya ce musu: “Ku yi tsaro ku yi addu’a, domin kada ku shiga cikin jaraba.” (Mar. 14:38) Amma, Bitrus ya sake yin barci kuma daga baya tsoron mutum da matsi ya shawo kansa.

13. Ta yaya za mu iya yin tsayayya da matsin yin abin da bai dace ba?

13 Misalan Bilatus da Bitrus za su iya koya mana wani darasi mai muhimmanci: Muna bukatar kasancewa da cikakken sanin Allah da tawali’u da filako da ƙaunar Allah da kuma tsoronsa don kada tsoro mutum ko matsi ya shawo kanmu. Idan muna da imani da ke bisa cikakken sani, za mu samu gaba gaɗin yin magana game da imaninmu. Hakan zai taimaka mana kada matsi da tsoron mutum su shawo kanmu. Bai kamata mu taɓa yin tunani cewa ba za mu iya faɗa wa matsi da tsoro ba. Maimakon haka, ya kamata mu nuna tawali’u kuma mu amince cewa muna bukatar taimakon Allah don mu yi tsayayya da matsi. Ya kamata mu yi addu’a don Jehobah ya ba mu ruhunsa. Kuma ya kamata ƙaunar da muke masa ta motsa mu mu tsarkake sunansa kuma mu bi ƙa’idojinsa. Bugu da ƙari, ya kamata mu yi shiri kafin mu fuskanci gwaji. Alal misali, muna bukatar mu yi addu’a da yaranmu kuma mu shirya su don su san matakin da za su ɗauka sa’ad da tsaransu sun matsa musu su yi abin da bai dace ba.—2 Kor. 13:7.a

KA GUJE WA TARKON DA KE RUGURGUJE ABU, WATO, YAWAN JIN LAIFI

14. Wane tunani ne Shaiɗan zai so mu yi game da zunubanmu na dā?

14 A wasu lokatai, ana ɗana tarko da babbar gungume ko dutse a hanyar da dabba take wucewa. Idan dabbar ta ture igiyar da aka ɗana tarkon da shi sai gungumen ya faɗo ya danna ta. Za a iya kwatanta irin wannan tarkon da yawan jin laifi. Sa’ad da muke tunani a kan laifuffukan da muka yi a dā, mukan “ƙuƙuje ƙwarai.” (Karanta Zabura 38:3-5, 8.) Shaiɗan yana son mu ji cewa zunubinmu ya yi yawa ainun kuma Jehobah ba zai yafe mana ba kuma ba za mu iya bin ƙa’idojinsa ba.

15, 16. Ta yaya za mu guji yawan jin laifi da ke kamar tarko?

15 Ta yaya za ka iya guje wa yawan jin laifi? Idan ka yi zunubi mai tsanani, ka ɗauki mataki yanzu don ka daidaita dangantakarka da Jehobah. Ka je wajen dattawa don su taimaka maka. (Yaƙ. 5:14-16) Ka yi iya ƙoƙarinka don ka yi gyarar da ake bukata. (2 Kor. 7:11) Idan an yi maka horo, kada ka karaya. Horo alama ne cewa Jehobah yana ƙaunarmu. (Ibran. 12:6) Ka ƙuduri aniya cewa ba za ka sake yin zunubin ba, kuma ka yi iya ƙoƙarinka don ka guji abin da zai sa ka sake yin zunubin. Bayan ka tuba kuma ka soma yin abin da ya dace, ya kamata ka kasance da imani cewa Allah zai iya yafe zunubanka ta hadayar fansa ta Yesu Kristi.—1 Yoh. 4:9, 14.

16 Wasu mutane sun ci gaba da jin cewa Allah bai yafe kurakuransu ba duk da cewa sun riga sun tuba. Idan kai ma kana jin hakan, ka tuna cewa Jehobah ya gafarci Bitrus da sauran almajiran ko da yake sun watse sun bar Yesu sa’ad da ake son a kashe shi. Wani mutumin da ya yi lalata kuma aka yi masa yankan zumunci a ikilisiyar Korinti, ya tuba daga baya ya yi kuma Jehobah ya gafarta masa. (1 Kor. 5:1-5; 2 Kor. 2:6-8) Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mutanen da suka tuba bayan sun yi zunubi mai tsanani, kuma Allah ya gafarce su.—2 Laba. 33:2, 10-13; 1 Kor. 6:9-11.

17. Yaya hadayar fansa ta Yesu za ta iya taimaka maka?

17 Jehobah zai gafarta maka dukan kurakuranka idan ka tuba da gaske kuma ka gaskata cewa zai yi maka jin ƙai. Kada ka taɓa yin tunani cewa hadayar fansa ta Yesu ba ta isa ta sa Jehobah ya yafe zunubanka ba. Tunanin da Shaiɗan yake son ka yi ke nan. Amma, za a iya gafarta zunuban waɗanda suka tuba. (Mis. 24:16) Yin imani da hadayar fansa ta Yesu za ta taimaka maka ka daina yawan jin laifi kuma ka samu gaba gaɗin bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka da ranka da kuma azancinka.—Mat. 22:37.

MU BA JAHILAI BA NE GA TARKUNAN SHAIƊAN

18. Ta yaya za mu guji tarkunan Shaiɗan?

18 Shaiɗan bai damu da irin tarkon da ya kama mu ba. Amma abin da yake so dai shi ne ya ga cewa mun faɗa cikin tarkonsa. Za mu iya gujewa tarkunan Shaiɗan, tun da yake mun san dabarunsa. (2 Kor. 2:10, 11) Idan mun yi addu’a ga Allah don ya ba mu hikima mu jimre da gwaje-gwaje, ba za mu faɗa cikin tarkunan Shaiɗan ba. Yaƙub ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙ. 1:5) Ya kamata mu yi ayyukan da suka jitu da addu’o’inmu ta wajen yin nazari da kanmu a kai a kai kuma ta yin amfani da darussan da muka koya. Littattafan da bawan nan mai-aminci, mai-hikima yake wallafawa suna taimaka mana mu san tarkunan Shaiɗan kuma mu guje su.

19, 20. Me ya sa ya kamata mu tsani mugunta?

19 Yin addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana mu ƙaunaci nagarta. Amma, yana da muhimmanci mu tsani abin da bai da kyau. (Zab. 97:10) Yin tunani a kan sakamako yin abu marar kyau zai taimaka mana mu guje su. (Yaƙ. 1:14, 15) Muna bukatar mu tsani mugunta kuma mu yi ƙaunar nagarta. Idan mun yi hakan, ba za mu yi sha’awar abubuwan da Shaiɗan ke amfani da su don ya kama mutane ba, domin za mu tsane su.

20 Muna godiya sosai don Allah ya taimaka mana don kada mu faɗa cikin tarkunan Shaiɗan! Jehobah yana yin amfani da ruhunsa da Littafi Mai Tsarki da kuma ƙungiyarsa don ya “cece mu daga mugun.” (Mat. 6:13) A talifi na gaba, za mu koyi yadda za mu guji faɗawa cikin wasu tarkuna biyu da Shaiɗan yake amfani da su don ya kama bayin Jehobah.

[Hasiya]

a Iyaye suna bukatar su tattauna batun nan da yaransu “Peer-Pressure Planner” a littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 2, shafuffuka na 132-133. Za su iya tattauna wannan littafin a lokacin Bauta ta Iyali da yamma.

[Hoto a shafi na 21]

Za mu iya cinna wa ikilisiya wuta a alamance idan muna yin magana da garaje

[Hoto a shafi na 24]

Za ka iya kawar da yawan jin laifi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba