Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 p. 12
  • ‘Al’ummai Za Su Sakankance Ni Ne Jehobah’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Al’ummai Za Su Sakankance Ni Ne Jehobah’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Mene ne Sunan Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 p. 12

Ka Kusaci Allah

‘Al’ummai Za Su Sakankance Ni Ne Jehobah’

A CE wani ya yi laifi kuma ya sa wasu mutane cikin wahala, sai aka ce kai ne ka yi laifin. Mene ne za ka yi? Babu shakka, za ka so ka wanke kanka daga wannan zargin da ake yi maka. Shin ka san cewa Jehobah yana fuskantar irin wannan yanayin? A yau, mutane da yawa suna ɗora wa Allah laifi cewa shi yake sa rashin adalci da wahala da muke fama da su a duniya. Shin, Jehobah zai ɗau mataki ne don ya kawo ƙarshen wannan zargin da ake masa? Shakka babu. Ka yi la’akari da abin da ya faɗa a littafin Ezekiyel.—Ka karanta Ezekiyel 39:7.

Jehobah ya ce: “Ba kuwa zan bari a sāke tozartadda sunana mai-tsarki ba.” A duk lokacin da mutane suka ɗora wa Allah laifin rashin adalci, suna ɓata masa suna. A wace hanya ke nan? A cikin Littafi Mai Tsarki, ana iya ba mutum suna bisa ga halinsa. Wani littafin bincike ya ce sunan Allah yana nufin “abin da aka sani game da shi, wato, abin da ya bayyana game da kansa; yana kuma nufin yadda Allah yake da girma da ɗaukaka.” Sunan Jehobah yana bayyana halinsa. Yaya Jehobah yake ji game da rashin adalci? Ya ƙi jinin rashin adalci. Yana jin tausayin waɗanda ake musu rashin adalci.a (Fitowa 22:22-24) Mutane suna ‘ɓata sunan’ Allah a duk lokacin da suka ɗora masa laifin duk wata mummunar aukuwa.—Zabura 74:10.

Ka lura cewa Jehobah ya yi amfani da wannan kalamin “mai tsarki” sau biyu. (Aya ta 7) A cikin Littafi Mai Tsarki, an sha ambata sunan Jehobah tare da kalamin nan “mai tsarki” da kuma “tsarki.” Sunan Jehobah mai tsarki ne domin Allah Jehobah mai tsarki ne, wato, ba ya da alaƙa ko kaɗan da duk wani abin da ke da aibi ko kuma mara tsabta. Saboda haka, waɗanda suke zargin Jehobah da miyagun ayyukan da ke faruwa suna mugun ɓata sunansa “mai tsarki.”

Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don ya tsarkake sunansa. Wannan shi ne nufinsa kuma shi ne ainihin jigon Littafi Mai Tsarki. An sha ambata wannan jigon a cikin littafin Ezekiyel da wannan kalamin: “Al’ummai kuma za su sakankance ni ne Ubangiji.” (Ezekiyel 36:23; 37:28; 38:23; 39:7) Ka lura cewa ba al’ummai ne za su yanke shawara da kansu cewa za su san ko shi ne Jehobah ko a’a ba. Amma, ‘za su kuwa sakankance’ hakan. Wato, Jehobah ne zai ɗau matakin da zai sa al’ummai su amince cewa shi ne Jehobah, Mai Ikon Mallaka wanda sunansa yana nufin tsarki ko tsabta, ko sun ƙi ko sun so.

Sau da yawa ana ambata alkawarin nan: ‘Al’ummai za su sakankance ni ne Jehobah.’ Wannan albishiri ne ga waɗanda suke son su ga ƙarshen rashin adalci da shan wahala. Ba da daɗewa ba, Jehobah zai cika wannan alkawari kuma zai wanke kansa daga zargin da aka yi masa. Jehobah zai kawar da mugunta da waɗanda suke haddasa ta amma zai ceci waɗanda suka ɗaukaka sunan da kuma abin da sunan yake nufi. (Misalai 18:10) Sanin hakan ya kamata ya motsa ka ka koya yadda za ka kusace Jehobah, Allah mai tsarki wanda yake “ƙaunar abin da ke daidai,” ko ba haka ba?—Zabura 37:9-11, 28.

[Hasiya]

a Ka duba talifin nan “Ka Kusaci Allah Mai Son Adalci,” a cikin Hasumiyar Tsaro na Janairu-Maris 2009.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba