Yadda Za A Kawo Ƙarshen Wannan Duniyar
“Ba cikin duhu ku ke ba, da ranan nan za ta tarshe ku kamar ɓarawo.”—1 TAS. 5:4.
MECE CE AMSARKA?
Waɗanne al’amura marasa ganuwa ne aka ambata a nassosi na gaba?
1 Tasalonikawa 5:3
Ru’ya ta Yohanna 17:16
Daniyel 2:44
1. Mene ne zai taimaka mana mu yi tsaro kuma mu jimre da gwaje-gwaje?
ABUBUWAN da za su tayar da hankulan mutane za su faru nan ba da daɗewa ba. Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa hakan gaskiya ne. Saboda haka, ya kamata mu yi tsaro. Mene ne zai taimaka mana mu yi hakan? Manzo Bulus ya aririce mu mu ‘lura da al’amura marasa-ganuwa.’ Muna bukatar mu tuna cewa Jehobah zai albarkace mu da rai madawwami a cikin sama ko a duniya. Bulus ya rubuta waɗannan kalmomin ne don ya ƙarfafa Kiristoci da ke zamaninsa su mai da hankali ga ladar da za su samu don kasancewa da aminci ga Allah. Yin hakan zai kuma taimaka musu su jimre da gwaje-gwaje da kuma tsanantawa.—2 Kor. 4:8, 9, 16-18; 5:7.
2. (a) Me ya kamata mu yi don mu kasance da bege sosai? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?
2 Kalaman Bulus suna ɗauke da ƙa’idoji masu muhimmanci. Idan muna son mu kasance da bege sosai, muna bukatar mu mai da hankali ga abubuwan da suke ganuwa. Amma mafi muhimmanci, wajibi ne mu mai da hankali ga abubuwan da ba mu gani ba tukun. (Ibran. 11:1; 12:1, 2) Za mu tattauna abubuwa guda goma da za su faru a nan gaba da suka shafi begenmu na yin rayuwa har abada.a
ME ZAI FARU DAB DA ƘARSHEN DUNIYAR NAN?
3. (a) Wane abu da zai faru a nan gaba ne yake cikin littafin 1 Tasalonikawa 5:2, 3? (b) Mene ne ’yan siyasa za su yi kuma wataƙila su waye ne za su goyi bayan su?
3 A cikin wasiƙar Manzo Bulus ga Tasalonikawa, ya rubuta game da wani abu da zai faru a nan gaba. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:2, 3.) Ya ambata “Ranar Ubangiji” a cikin wasiƙarsa. Ranar nan za ta soma sa’ad da aka halaka addinin ƙarya kuma za a kammala ta a yaƙin Armageddon. Amma, kafin ranar Jehobah ta soma, shugabannin duniyar nan za su riƙa cewa “Kwanciyar rai da lafiya.” Wataƙila za a yi hakan ne sau ɗaya ko kuma sau da yawa. Al’ummai za su yi tunani cewa sun kusan magance wasu cikin manya-manyan matsalolinsu. Limaman addinai kuma fa? Su ma na duniyar nan ne. Wataƙila su ma za su kasance tare da shugabannin duniyar nan sa’ad da suke cewa “Kwanciyar rai da lafiya.” (R. Yoh. 17:1, 2) Ta yin hakan, limaman addinai za su yi koyi da annabawan ƙarya na Yahuda ta dā waɗanda suke cewa “Lafiya, lafiya.” Amma Jehobah ya ce musu “ba kuwa lafiya.”—Irm. 6:14; 23:16, 17.
4. Wane abu ne muka sani da yawancin mutane ba su sani ba?
4 Ko ma waye ne ya ce “Kwanciyar rai da lafiya” hakan zai nuna cewa ranar Jehobah na dab da somawa. Shi ya sa Bulus ya ce: “’Yan’uwa, ba cikin duhu ku ke ba, da ranan nan za ta tarshe ku kamar ɓarawo: gama ku duka ’ya’yan haske ne.” (1 Tas. 5:4, 5) Mutane da yawa ba su fahimci ma’anar abubuwan da ke faruwa a yau ba, amma mu mun san ma’anarsu. Ta yaya wannan annabci game da “Kwanciyar rai da lafiya” zai cika? Muna bukatar mu jira mu ga abin da zai faru. Bari mu ƙuduri aniya cewa za mu “yi zamanmu ba barci ba maye.”—1 Tas. 5:6; Zaf. 3:8.
‘SARAUNIYAR’ DA BA TA SAN CEWA ZA A HALAKA TA BA
5. (a) Yaya “ƙunci mai-girma” zai soma? (b) Wace ce “sarauniya” da ta yi zato cewa babu abin da zai same ta?
5 Wane abu ne kuma zai faru a nan gaba? Bulus ya ce: ‘Bayan suna cikin faɗin, kwanciyar rai da lafiya, sai halaka farat ta auko musu.’ Abin da za a fara halaka shi ne addinan ƙarya a duniyar nan, wato, “Babila Babba” ko “uwar karuwai” wadda ita ce daular addinan ƙarya. (R. Yoh. 17:5, 6, 15) Harin da za a kai wa dukan addinan ƙarya har da Kiristendam shi ne somawar “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:21; 2 Tas. 2:8) Mutane da yawa za su yi mamaki sa’ad da hakan ya faru. Me ya sa? Domin har lokacin da za a halaka karuwar, za ta yi zato cewa ita “Sarauniya” ce wadda ba za ta “ga kewa ba daɗai.” Amma za ta gane cewa ta yi kuskure. Za a halaka ta nan da nan kamar a “rana ɗaya.”—R. Yoh. 18:7, 8.
6. Wane ne zai halaka addinin ƙarya?
6 Littafi Mai Tsarki ya ce wadda za ta kai wa karuwar hari “bisa” ce mai “ƙafo goma.” Idan mun yi nazarin littafin Ru’ya ta Yohanna, za mu fahimci cewa wannan bisa Majalisar Ɗinkin Duniya ce. ‘Ƙafo goman’ suna wakiltar dukan gwamnatocin da suke goyon bayan bisa mai ‘launi ja wur.’b (R. Yoh. 17:3, 5, 11, 12) Yaya yawan halakar za ta kasance? Ƙasashe masu goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya za su ƙwace dukan dukiyar karuwar, su sanar wa jama’a tsananin muguntarta da lalatar ta, su cinye ta su kuma “ƙoƙone ta sarai da wuta.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:16.
7. Ta yaya bisar za ta soma kai wa karuwar hari?
7 Annabcin Littafi Mai Tsarki ya kuma bayyana yadda wannan halakar za ta soma. Jehobah zai sa shugabanni “su yi nufinsa,” wato, su halaka karuwar. (R. Yoh. 17:17) Addini na jawo yaƙe-yaƙe da kuma matsaloli da yawa a duniya. Saboda haka, al’ummai za su zata cewa za su amfana idan suka halaka karuwar. Kuma sa’ad da shugabanni suka kai wa karuwar hari, za su yi zato cewa suna yin abin da suka nufa ne. Amma, Allah zai yi amfani da su don halaka dukan addinan ƙarya. Hakan yana nufin cewa sashe ɗaya na duniyar Shaiɗan, zai kai wa wani sashe hari kuma Shaiɗan ba zai iya hana su ba.—Mat. 12:25, 26.
ZA A KAI WA BAYIN ALLAH FARMAKI
8. Mene ne hari na ‘Gog na ƙasar Magog’ yake nufi?
8 Bayan an halaka addinan ƙarya, bayin Allah za su ci gaba da “zaman lafiya” kuma za su yi zamansu “ba garu.” (Ezek. 38:11, 14) Mene ne zai faru da waɗannan mutanen da suka ci gaba da bauta wa Jehobah kuma ake gani kamar ba su da kāriya? Kamar dai “jama’a mai-girma” za su kai musu hari. Kalmar Allah ta bayyana cewa wannan harin daga “Gog, na ƙasar Magog” ne. (Karanta Ezekiyel 38:2, 15, 16.) Yaya ya kamata mu ji game da wannan harin?
9. (a) Mene ne ya fi muhimmanci ga Kirista? (b) Mene ne ya kamata mu yi yanzu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?
9 Mun san cewa za a kai wa bayin Allah hari, amma hakan ba ya sa mu fargaba. Abin da ya fi muhimmanci a gare mu ba samun ceto ba ne, amma tsarkake sunan Allah ne da kuma nuna cewa shi ne ya fi dacewa ya zama Maɗaukakin Sarki. Hakika, fiye da sau sittin Jehobah ya ce: “Za ku sani ni ne Ubangiji.” (Ezek. 6:7) Muna ɗokin ganin yadda wannan sashe mai muhimmanci na annabcin Ezekiyel zai cika. Kuma muna da tabbaci cewa Jehobah “ya san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” (2 Bit. 2:9) Duk da haka, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu samu damar kasancewa da aminci ga Jehobah ko yaya irin tsananin da za mu fuskanta. Me ya kamata mu yi? Ya kamata mu yi addu’a da nazarin Kalmar Allah da bimbini da kuma yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah. Idan mun yi hakan, begenmu na samun rai madawwami zai zama kamar “anka.”—Ibran. 6:19; Zab. 25:21.
AL’UMMAI ZA SU SAN KO WANE NE JEHOBAH
10, 11. Ta yaya za a soma yaƙin Armageddon, kuma mene ne zai faru a lokacin?
10 Wane abu da zai tayar da hankulan mutane ne zai faru sa’ad da aka kai wa bayin Jehobah hari? Jehobah zai yi amfani da Yesu da kuma rundunar da ke sama don taimaka wa bayinsa. (R. Yoh. 19:11-16) Wannan ne “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” wato, Armageddon.—R. Yoh. 16:14, 16.
11 Sa’ad da Jehobah yake magana game da wannan yaƙin ta bakin Ezekiyel, ya ce: “Zan kira dukan duwatsuna su kawo takobi a kansa [Gog], in ji Ubangiji Yahweh: takobin kowane mutum yana gāba da ɗan’uwansa.” Waɗanda suke tare da Shaiɗan za su ruɗe su kuma firgita, sai su soma kashe juna. Jehobah ya ce: ‘Zan zuba masa [Gog] daga sama wuta, da ƙibiritu; a kansa da dukan tattarmukan yaƙinsa da danguna masu-yawa da ke tare da shi.’ (Ezek. 38:21, 22) Mene ne zai zama sakamakon hakan?
12. Mene ne al’ummai za su sani ko sun ƙi ko sun so?
12 Al’ummai za su san cewa Jehobah ne ya ba da umurni a halaka su. Kuma kamar Masarawa da suka bi Isra’ilawa a Jar Teku, masu goyon bayan Shaiɗan ma za su ce: “Ubangiji yana wajensu.” (Fit. 14:25) Dole ne al’ummai su san Jehobah. (Karanta Ezekiyel 38:23.) A wane lokaci ne waɗannan abubuwan za su soma?
GWAMNATIN ’YAN ADAM BA ZA TA SAKE SARAUTA BISA DUNIYA BA
13. Mene ne muka sani game da sashe na biyar na sifar da Daniyel ya bayyana?
13 Wani annabci da ke littafin Daniyel ya taimaka mana mu fahimci lokacin da muke yanzu. Daniyel ya bayyana wata sifa mai kama da mutum da aka ƙera gaɓoɓin jikinta da ƙarafa dabam-dabam. (Dan. 2:28, 31-33) Tana wakiltar mulkokin duniya da suka shafi mutanen Allah a zamanin dā da kuma yau. Waɗannan mulkokin duniya su ne Babila da Midiya-da-Farisa da Hellas da kuma Roma. Kuma mulkin duniya na ƙarshe yana sarauta a zamaninmu. Mun koya a cikin annabcin Daniyel cewa ƙafafu da sawayen sifar suna wakiltar wannan mulkin duniya na ƙarshe. A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Biritaniya ta ƙulla yarjejeniya ta musamman da ƙasar Amirka. Sashe na biyar na wannan sifar tana wakiltar mulkin Biritaniya da Amirka. Ƙafafun shi ne sashe na ƙarshe na sifar. Hakan ya nuna cewa babu mulkin da zai yi sarauta bayan Biritaniya da Amirka. Ƙafafu da sawayen sifar na baƙin ƙarfe ne da kuma yumɓu. Hakan ya nuna cewa ba su da ƙarfi sosai kuma.
14. Wane mulkin duniya ne zai riƙa sarauta sa’ad da za a soma yaƙin Armageddon?
14 A wannan annabcin, an kwatanta Mulkin Allah da wani babban dutse da aka yanko daga kan tsauni a shekara ta 1914. Tsaunin yana wakiltar ikon Jehobah na yin sarauta. Nan ba da daɗewa ba, dutsen zai bugi ƙafar sifar. Za a rugurguje sifar da ƙafafunta a Armageddon. (Karanta Daniyel 2:44, 45.) Biritaniya da Amirka ne za su riƙa sarauta sa’ad da za a soma yaƙin Armageddon. Muna ɗokin ganin lokacin da wannan annabcin zai cika!c Amma, mene ne Jehobah zai yi wa Shaiɗan?
MENE NE ZAI FARU DA BABBAN MAGABCIN ALLAH?
15. Mene ne zai faru da Shaiɗan da aljanunsa bayan Armageddon?
15 Da farko, Shaiɗan zai ga cewa an halaka ƙungiyarsa da ke duniya baki ɗaya. Bayan haka, sai abin ya juye a kan Shaiɗan. Manzo Yohanna ya bayyana abin da zai faru. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 20:1-3.) Yesu Kristi wanda shi ne ‘mala’ika mai riƙe da maƙullin rami marar-matuƙa’ zai jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar-matuƙa har tsawon shekara dubu. (Luk 8:30, 31; 1 Yoh. 3:8) Wannan ne farkon ƙuje kan macijin.d—Far. 3:15.
16. Mene ne zai faru da Shaiɗan sa’ad da yake cikin “rami marar-matuƙa”?
16 “Rami marar-matuƙa” da za a jefa Shaiɗan da aljanunsa ciki, wuri ne da babu wanda zai iya isa sai dai Jehobah da kuma mala’ikan da ya naɗa wanda ke “riƙe da maƙullin rami marar-matuƙa.” Za a jefa Shaiɗan a wurin don kada ya “ƙara ruɗin al’ummai.” Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan yana kamar “zaki mai-ruri.” Amma sa’ad da aka jefa shi cikin wannan ramin, ba zai iya ko uffan ba.—1 Bit. 5:8.
ABUBUWAN DA ZA SU FARU KAFIN LOKACIN SALAMA
17, 18. (a) Waɗanne al’amura marasa ganuwa ne muka tattauna? (b) Me zai faru bayan waɗannan abubuwan sun auku?
17 Abubuwan da za su tayar da hankulan mutane za su faru nan ba da daɗewa ba. Muna ɗokin ganin yadda faɗin “kwanciyar rai da lafiya” zai faru. Bayan haka, za mu ga yadda za a halaka Babila Babba da harin da Gog na ƙasar Magog zai kai wa bayin Allah da kuma yaƙin Armageddon. Za a kuma jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar-matuƙa. Bayan haka, za a cire dukan mugunta. Rayuwarmu za ta canja sosai a lokacin sarautar Yesu na Shekara Dubu. Kuma za mu more “yalwar salama.”—Zab. 37:10, 11.
18 Mun tattauna al’amura guda biyar “marasa ganuwa” a wannan talifin. A talifi na gaba, za mu tattauna wasu al’amura marasa ganuwa da ya kamata mu “lura da” su.
[Hasiya]
a Za a tattauna waɗannan abubuwa goma a wannan talifin da kuma na gaba.
b Ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax at Hand! shafuffuka na 251-258 na Turanci.
c Kalmomin nan ‘za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki’ da ke littafin Daniyel 2:44 yana nufin mulkokin da gaɓoɓin sifar suke wakilta. Amma dai, wani annabci na Littafi Mai Tsarki da ya yi magana game da lokacin kuma ya ce ‘sarakunan dukan duniya’ za su yi jerin gwano don su yaƙi Jehobah a “babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (R. Yoh. 16:14; 19:19-21) Hakan ya nuna cewa ba mulkokin da sifar take wakilta kaɗai za a halaka ba. Armageddon zai halaka dukan mulkokin da ke duniyar nan.
d Lokaci na ƙarshe da za a ƙuje kan macijin shi ne bayan shekara dubu na sarautar Yesu. A lokacin, za a jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin “ƙorama ta wuta da ƙibiritu.”—R. Yoh. 20:7-10; Mat. 25:41.
[Akwati/Hotona a shafi na 4, 5]
ABUBUWA BIYAR DA ZA SU FARU:
1 Za a yi shelar “Kwanciyar rai da lafiya”
2 Al’ummai za su kai wa “Babila Babba” hari kuma su halaka ta
3 Za a kai wa bayin Allah farmaki
4 Za a yi yaƙin Armageddon
5 Za a jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar-matuƙa