Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/15 pp. 3-6
  • Sun Ba da Kansu da Yardan Rai—A Ƙasar Brazil

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Ba da Kansu da Yardan Rai—A Ƙasar Brazil
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “NA YI MAMAKI ƘWARAI”
  • YA SAKE BINCIKA HIDIMARSA
  • GWANI MAWAƘI KO MAI HIDIMA?
  • “BA NI DA WANI ZAƁI”
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Ƙasar Ecuador
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/15 pp. 3-6

Sun Ba da Kansu da Yardan Rai​—A Ƙasar Brazil

WATA ’yar’uwa ’yar shekara talatin mai suna Rúbia (1) ta ziyarci Sandra (2) shekarun baya. Sandra tana hidimar majagaba a wata ikilisiya da ba masu shela da yawa da ke kudancin Brazil. Sa’ad da Rúbia ta ziyarce ta, wani abu ya faru da ya burge ta sosai, kuma hakan ya sa ta canja maƙasudinta. Mene ne ya faru? Bari Rúbia da kanta ta gaya mana.

“NA YI MAMAKI ƘWARAI”

“Sandra da Rúbia sun je yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata. Sa’ad da suke nazarin, matar ta gaya wa Sandra: “’Yammata uku da muke aiki tare suna son su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma na gaya musu cewa ba ki da lokacin yin nazari da su yanzu. Na san kina da mutane da yawa da kike nazari da su a wannan shekarar.’ Na yi mamaki ƙwarai cewa mutane suna ma jira a yi nazari da su! Yana da wuya a samu wanda za a yi nazari da shi a yankinmu. Nan take, na yi sha’awar taimaka wa mutane da suke garin da Sandra take hidimar majagaba. Ba da daɗewa ba, sai na ƙaura zuwa garin.”

Wane sakamako ne Rúbia ta samu? Ta ce: “Na soma nazari da mutane goma sha biyar cikin wata biyu. Kuma ba da daɗewa ba, mutane suka soma jira na yi nazari da su kamar yadda suke wa Sandra!”

YA SAKE BINCIKA HIDIMARSA

Wani ɗan’uwa matashi mai suna Diego (3) ya ziyarci wasu ma’aurata da suke hidimar majagaba a garin Prudentópolis da ke kudancin Brazil. Wannan ziyarar ta sa ya yi tunani game da hidimarsa. Sai ya ce: “Ina yin sa’o’i kaɗan kawai a wa’azi a ikilisiyarmu. Amma sa’ad da na ziyarci waɗannan majagaba kuma na ji labarinsu, sai na ga cewa suna farin ciki sosai a hidimarsu fiye da yadda nake yi. Sai ni ma na so rayuwata ta kasance da ma’ana kamar su.” Diego ya soma hidimar majagaba bayan ya koma.

Kai matashi ne kamar Diego? Kana ji ba ka farin ciki sosai a hidimarka ko da yake kana wa’azi da kuma halarta taro? Idan haka ne, kana ganin za ka iya yin canje-canje a rayuwarka don ka yi farin cikin yin hidima a inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai? Hakika, ba shi da sauƙi ka bar rayuwar jin daɗi. Duk da haka, matasa da yawa sun yi hakan. Sun canja maƙasudinsu da sha’awoyinsu don su daɗa ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Ka yi la’akari da misalin Bruno.

GWANI MAWAƘI KO MAI HIDIMA?

Wani mai suna Bruno (4) wanda ɗan shekara ashirin da takwas ne yanzu, ya je babban makarantar mawaƙa. Yana so ya zama gwani mawaƙi. Ya ƙware sosai da har an gaya masa ya ja-goranci rukunin ƙwararrun mawaƙa. Kamar dai zai yi nasara sosai a aikinsa. Amma Bruno ya ce: “Ina ganin da akwai abin da ba na yi a rayuwata. Ko da yake na keɓe rayuwata ga Jehobah, na damu sosai cewa ba na iya ƙoƙarina a hidimata a gare shi. Na gaya wa Jehobah yadda nake ji sa’ad nake addu’a, na kuma yi magana da ’yan’uwa da suka manyanta a cikin ikilisiya. Sai na tsai da shawara na daɗa ƙwazo a hidimata, na bar makarantar kuma na ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shelar Mulki sosai.” Mene ne sakamakon shawararsa?

Bruno ya ƙaura zuwa garin Guapiara. Wannan garin yana da nisan mil 160 daga birnin São Paulo kuma mutane dubu bakwai ne ke garin. Wannan canji ne na musamman. Ya ce: “Na kama haya a wani ƙaramin gida da babu firiji da talabijin ko kuma Intane. Duk da haka, akwai wasu abubuwa a cikin gidan da ba ni da su a dā, kamar su lambu da itatuwa!” Sa’ad da Bruno yake hidima a wata ikilisiya, sau ɗaya a mako sai ya cika jakarsa da abinci da ruwa da littattafai ya je wani ƙauye wa’azi a kan babur ɗinsa. Ba a taɓa yi wa mutane da yawa a wannan yankin wa’azi ba. Bruno ya ce: “Na yi nazari da mutane goma sha takwas. Ganin yadda waɗannan mutane suka yi canje-canje a rayuwarsu ya sa ni farin ciki sosai!” Sai ya ce: “A yanzu na samu gamsuwa don saka al’amura na Mulki a kan gaba a rayuwata. Da ban yi farin ciki ba da a ce na biɗi abin duniya.” Yaya Bruno yake samun kuɗin biyan bukatunsa a garin Guapiara? Ya ce: “Ta wajen koya wa mutane yadda ake kaɗa garaya.” Har ila shi gwani ne.

“BA NI DA WANI ZAƁI”

Yanayin wata matashiya mai suna Mariana (5) ɗaya ne da Bruno. Ita lauya ce, amma ba ta samun gamsuwa duk da cewa tana samun kuɗi sosai a aikinta. Ta ce: “Na ji kamar ina ‘harbin iska ne kawai.’” (M. Wa 1:17, Littafi Mai Tsarki) ’Yan’uwa da yawa sun ƙarfafa ta ta soma hidimar majagaba. Mariana tare da ƙawayenta Bianca (6) da Caroline (7) da Juliana (8) suka ƙaura zuwa wata ikilisiya da ke garin Barra do Bugres. Wannan wani gari ne da ke kusa da ƙasar Bolivia da ke da nisa sosai daga garinsu. Mene ne sakamakon?

Mariana ta ce: “Na yi niyyar zama a garin wata uku. Amma na soma nazari da mutane goma sha biyar a ƙarshen wata uku! Waɗannan ɗalibai suna bukatar taimako sosai don su samu ci gaba a ƙungiyar Jehobah. Saboda haka, ba ni da wani zaɓi, dole ne na ci gaba da zama a garin.” Kuma abin da dukan ƙawaye huɗun suka yi ke nan. Mariana tana ganin ta fi jin daɗin rayuwarta sosai yanzu. Ta ce: “Ina farin ciki sosai da yake Jehobah yana amfani da ni don taimaka wa mutane su kyautata rayuwarsu. Albarka ce a gare ni cewa ina yin amfani da lokacina da kuzarina don yin abin da yake amfanar mutane.” Caroline ta faɗa yadda dukan ’yan’uwa mata huɗun suke ji game da yadda suke ƙwazo sosai a hidimarsu ga Jehobah. Ta ce: “Ina jin na yi abin da ya kamata, sa’ad da na kwanta daddare bayan na dawo daga yin hidima. Na mai da hankali ga taimaka wa mutane da nake nazari da su. Ina farin ciki sosai ganin suna samun ci gaba. Na ga cewa waɗannan kalaman gaskiya ne: ‘Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne.’”—Zab. 34:8.

Jehobah yana farin ciki sosai sa’ad da matasa suka ƙaura zuwa wurare masu nisa don su yi wa’azi. ‘Suna bada kansu da yardan rai.’ (Zab. 110:3; Mis. 27:11) Jehobah yana musu albarka domin sun ba da kansu.—Mis 10:22.

[’Yan rubutu na ba da bayani a shafi na 5]

Ba Mu Yi Rashin Kome Ba

[’Yan rubutu na ba da bayani a shafi na 5]

Sa’ad da João Paulo da matarsa Noemi suka ce za su ƙaura zuwa inda ake bukatar masu wa’azi sosai, wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiyarsu sun sa su sanyin gwiwa. Wasu sun ce masu: “Ba za ku iya biyan bukatunku ba a wannan ƙauyen. Me ya sa za ku ƙaura bayan akwai aiki da yawa da za ku yi a wannan ikilisiyar?” João Paulo ya ce: “Yana da sauƙi mutum ya yi sanyin gwiwa da yake a ganinsu shawara ce mai kyau suka bayar.” Amma yanzu João Paulo da Noemi suna farin ciki saboda shawarar da suka yanke shekaru da suka shige na ƙaura zuwa inda ake bukatar masu wa’azi sosai. João Paulo ya ce: “Ba mu yi rashin kome ba tun da muka ƙaura zuwa nan. Kuma mun sami albarka fiye da dā.” Noemi ta ce: “Abin da muka yi kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu.”

Biyan bukatun rayuwa a ƙauye yana da wuya. Ta yaya waɗanda suka ƙaura zuwa ƙauyuka suke biyan bukatunsu? Ta yin amfani da iyawarsu wajen yin abubuwa dabam-dabam. Wasu suna koyar da Turanci ko wani yare a makarantu da koyar da yara a gidajensu. Wasu kuma suna ɗinki da fantin gida da kuma duk wani aikin da zai ba su lokacin yin wa’azi sosai. Yaya waɗannan suke ji game da salon rayuwarsu? Suna jin cewa albarkar da suke samu ya fi ƙalubalen da suke fuskanta.

[Akwati/​Hoto a shafi na 6]

Kewar Gida

Tiago ya ce: “Na soma sanyin gwiwa ba da daɗewa ba bayan na ƙaura. Masu shela kaɗan ne a garin kuma babu wurin shaƙatawa. Sai na soma kewar gida. Na san ina bukatar na yi wani abu don na daina jin hakan. Na tsai da shawara na yi abokantaka da ’yan’uwan da ke ikilisiyar kuma hakan ya taimake ni. Yanzu na samu abokai kuma ina farin ciki sosai.”

[Hoto a shafi na 3]

Noemi da João Paulo, a garin Ascurra, Santa Catarina

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba