Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Ƙasar Ecuador
WANI ɗan’uwa matashi a ƙasar Italiya mai suna Bruno yana fuskantar wata matsala da ke damunsa sosai. Bai daɗe da sauƙe karatu daga makarantar sakandare ba, kuma ya ci jarabawarsa. Amma, danginsa da kuma malamansa suna matsa masa ya je jami’a. Bruno bai daɗe sosai da keɓe kansa ga Jehobah ba, kuma ya masa alkawari cewa zai saka hidimarsa farko a rayuwarsa. Wane zaɓi ne Bruno ya yi? Ya bayyana: “Na yi addu’a ga Jehobah, kuma na gaya masa cewa zan cika alkawarin da na yi cewa zan saka hidimarsa farko a rayuwa ta. Na kuma roƙe shi cewa ina son na more hidimarsa kuma yi ayyuka dabam-dabam.”
’Yan shekaru bayan haka, Bruno ya je ƙasar Ecuador, a Amirka ta Kudu. Ya ce: “Jehobah ya ba ni fiye da abin da na roƙe shi.” Sa’ad da ya isa ƙasar Ecuador, ya haɗu da wasu matasa da suka ƙaura zuwa ƙasar don su yi ƙarin ayyuka a hidimar Jehobah.
MATASA DA SUKA DOGARA GA JEHOBAH
Jehobah yana gayyatarmu mu bauta masa da dukan zuciyarmu kuma zai yi mana albarka. Ya ce: “Ku gwada ni haka nan yanzu, . . . ko ba zan buɗe maku sakatan sama ba, in zuba maku da albarka.” (Mal. 3:10) Da yake suna ƙaunar Jehobah sosai, sai suka gwada shi ta wajen ba da lokacinsu da kuzarinsu da kuma dukiyarsu don su goyi bayan wa’azin da ake yi a ƙasarsu inda ake bukatar masu wa’azin Mulki sosai.
Sa’ad da suka isa ƙasar, sun ga cewa “girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.” (Mat. 9:37) Alal misali, Jaqueline daga ƙasar Jamus ta rubuta wannan wasiƙar ga ofishin reshen da ke ƙasar Ecuador: “Ya fi shekara biyu da nake hidima a ƙasar Ecuador, amma ina da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 13, huɗu cikinsu suna halartar taro a kai a kai. Wannan ba abin mamaki ba ne?” Wata mai suna Chantal daga ƙasar Kanada ta ce: “A shekara ta 2008, na ƙaura zuwa wani yanki a ƙasar Ecuador inda akwai ikilisiya guda kawai. Amma, yanzu akwai ikilisiyoyi guda uku da kuma majagaba fiye da 30 a yankin. Ganin sababbin ɗalibai na Littafi Mai Tsarki suna samun ci gaba abu mai sa farin ciki ne sosai.” Ta ci gaba da cewa: “Bai daɗe ba da na ƙaura zuwa wani birni da ke Tudun Andes mai tsawon kafa 9,000. Fiye da mutane 75,000 ne suke zama a wannan birnin, amma akwai ikilisiya guda kawai. Wuri ne da mutane suke sauraron wa’azinmu. Ina jin daɗin wa’azi na sosai.”
BA ABU MAI SAUƘI BA NE
Gaskiya ne cewa yin hidima a wata ƙasa ba ta da sauƙi. Wasu matasa suna fuskantar matsaloli kafin su ƙaura. Wata mai suna Kayla daga ƙasar Amirka ta ce: “Wasu a ikilisiyarmu sun ce kada na ƙaura, kuma hakan ya sa ni sanyin gwiwa. Ba su fahimci dalilin da ya sa nake son na ƙaura zuwa wata ƙasa ba don na yi hidimar majagaba. Hakan ya sa ni tunani ko na yi zaɓi mai kyau.” Amma duk da haka, Kayla ta tsai da shawara cewa za ta ƙaura. Ta bayyana: “Na yi addu’a sau da yawa ga Jehobah kuma na tattauna da ’yan’uwa maza da mata da suka manyanta. Yin haka ya taimaka mini na ga cewa Jehobah yana wa waɗanda suka ba da kansu da yardar rai albarka.”
Yana wa wasu wuya sosai su koyi wani harshe. Wata mai suna Siobhan daga ƙasar Ireland ta tuna abin da ya faru: “Yana mini wuya sosai na furta ra’ayina. Na koyi yin haƙuri da koyon yaren sosai da kuma yi wa kaina dariya duk sa’ad da na yi kuskure.” Wata mai suna Anna daga ƙasar Estoniya ta ce: “Sabawa da zafi da kura da kuma rashin wanka da ruwan zafi bai kai koyon yaren Sfanisanci wuya ba. A wasu lokatai, ina ji kamar na share shi kawai. Na koyi mai da hankali ga yadda nake samun ci gaba, ba ga kuskuren da nake yi ba.”
Yin kewar gida ma wata babbar matsala ce. Wani mai suna Jonathan daga ƙasar Amirka ya ce: “Jim kaɗan bayan na isa ƙasar, na yi sanyin gwiwa domin na baro abokaina da iyalina. Amma, yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin wa’azi sun taimaka mini na jimre da wannan matsalar. Ba da daɗewa ba, na samu sakamako masu kyau a wa’azin da nake yi kuma sababbin abokai na da samu sun taimaka mini na sake yin farin ciki.”
Zama a wata ƙasa matsala ce. Wataƙila ba zai yi daidai da wanda ka saba ba. Beau daga ƙasar Kanada ya ce: “Sa’ad da nake gida, muna yawan samun wutar lantarki da ruwan fanfo, amma yanzu da ƙyar muke samunsu.” A wasu ƙasashe, mutane da yawa ba su da ilimi kuma motocinsu ba su da kyau sosai. Wasu kuma suna da talakawa da yawa. Mene ne ya taimaki wata mai suna Ines daga ƙasar Ostriya ta jimre da yanayin? Ta mai da hankali ga halaye masu kyau na mutanen. Ta ce: “Suna da halin karɓan baƙi da sauƙin kai da taimako da kuma tawali’u. Kuma suna son su koya game da Allah.”
‘ALBARKA MAI YAWAN GASKE’
Ko da yake waɗannan matasan da suke hidima a ƙasar Ecuador sun yi sadaukarwa, amma Jehobah ya ba su dukan abin da suke bukata. Ya albarkace su ‘gaba da dukan abin da suke tsammani.’ (Afis. 3:20) Sun san cewa ya ba su “albarka mai yawan gaske.” (Mal. 3:10, Littafi Mai Tsarki) Kalamai na gaba sun nuna yadda suke ji game da hidimar da suke yi:
Bruno: “Na soma hidimata a ƙasar Ecuador a wani yankin Amazon. Daga baya, na taimaka wajen gina ofishin reshe da ke ƙasar Ecuador. Yanzu, ina hidima a Bethel. Sa’ad da nake ƙasar Italiya, na zaɓi na saka hidimar Jehobah farko a rayuwata, kuma yanzu ina more rayuwa ta sosai a hidimomi dabam-dabam.”
Beau: “Dangantakata da Jehobah ta daɗa ƙarfi sosai domin a nan ƙasar Ecuador, ina yin amfani da dukan lokaci na a hidimarsa. Ina yin tafiya zuwa wurare masu kyau, kuma hakan abin da nake sha’awa ne sosai.”
Anna: “Ban san cewa a matsayita na ’yar’uwa da ba ta yi aure ba zan iya more irin rayuwar masu wa’azi a ƙasashen waje. Amma yanzu na san cewa hakan zai yiwu. Ina godiya sosai ga Jehobah don albarkarsa. Ina almajirantarwa da gina Majami’un Mulki da kuma samun sababbin abokai. Ina bala’in farin ciki.”
Elke: “Sa’ad da nake Ostriya, ina addu’a ga Jehobah cewa ya ba ni ɗalibin Littafi Mai Tsarki guda kawai. Amma a nan, ina da ɗalibai 15. Ɗalibaina na Littafi Mai Tsarki suna farin ciki sosai don koyo game da Jehobah. Kuma hakan ma, yana sa ni farin ciki.”
Joel: “Bauta wa Jehobah a wata ƙasa abu mai kyau ne sosai. Na koyi yin dogara a gare shi sosai, kuma ina ganin yadda yake albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarce na! A shekarata ta farko a ƙasar Amirka, rukunin da nake hidima ya samu ƙaruwa daga masu shela 6 zuwa 21. Kuma mutane 110 sun halarci taron Tuna da mutuwar Yesu.”
KAI MA ZA KA IYA BA DA KANKA?
’Yan’uwa maza da mata, za ku iya yin hidima a inda ake da bukata sosai? Babu shakka, za ka bukaci yin shiri sosai kafin ka tsai da irin wannan shawarar. Amma, abu na musamman da zai motsa ka ka yi hakan shi ne ƙaunarka ga Jehobah da kuma maƙwabtanka. Idan kana da wannan ƙaunar kuma za ka iya ƙaura, ka yi addu’a ga Jehobah sosai game da yin hidima a wata ƙasa. Ƙari ga hakan, ka tattauna da iyayenka da kuma dattawa game da muradinka. Kai ma za ka iya tsai da shawara cewa kana son ka bauta wa Jehobah a wannan hanyar mai gamsarwa da kuma daɗi sosai.
[Bayanin da ke shafi na 3]
“Na yi addu’a sau da yawa ga Jehobah kuma na tattauna da ’yan’uwa maza da mata da suka manyanta. Yin haka ya taimaka mini na ga cewa Jehobah yana wa waɗanda suka ba da kansu da yardar rai albarka.”—Kayla daga ƙasar Amirka
[Akwati/Hoto a shafi na 6]
Yadda za ka yi shiri don yin hidima a wata ƙasa
• Ka riƙa yin nazari a kai a kai
• Ka yi bitar Hidimarmu Ta Mulki ta Nuwamba 2011, shafuffuka na 4-6
• Ka tattauna da mutanen da suka yi hidima a wata ƙasa
• Ka yi bincike game da al’ada da kuma tarihin ƙasar
• Ka koyi yaren ƙasar
[Akwati/Hoto a shafi na 6]
Wasu da suka yi hidima a wata ƙasa sun kula da bukatansu ta wajen . . .
• yin aiki na ’yan watanni a ƙasarsu duk shekara
• ba da hayar gidansu ko wajen sana’arsu
• yin aiki ta Intane
[Hotona a shafi na 4, 5]
1 Jaqueline daga ƙasar Jamus
2 Bruno daga ƙasar Italiya
3 Beau daga ƙasar Kanada
4 Siobhan daga ƙasar Ireland
5 Joel daga ƙasar Amirka
6 Jonathan daga ƙasar Amirka
7 Anna daga ƙasar Estoniya
8 Elke daga ƙasar Ostriya
9 Chantal daga ƙasar Kanada
10 Ines daga ƙasar Ostriya