Ka Amfana Daga Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana?
“Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, . . . yana gafarta laifi da saɓo da zunubi.”—FIT. 34:6, 7.
MECE CE AMSARKA?
Sa’ad da Dauda da Manasseh suka yi zunubi, ta yaya Jehobah ya bi da su, kuma me ya sa?
Me ya sa Jehobah bai gafarta wa al’ummar Isra’ilawa ba?
Mene ne ya kamata mu yi don Jehobah ya gafarta mana?
1, 2. (a) Jehobah wane irin Allah ne ga Isra’ilawa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
A ZAMANIN Nehemiya, wasu Lawiyawa sun faɗi a addu’arsu cewa al’ummar Isra’ila sun “ƙi biyayya” ga dokokin Jehobah sau da sau. Amma, Jehobah ya ci gaba da gafarta musu. Shi “Allah ne mai-son aikin gafara, mai-alheri ne, cike da tausai, mai-jinkirin fushi, mayalwaci da jinƙai.” Jehobah ya ci gaba da nuna wa mutanen da aka kai bauta a zamanin Nehemiya jin ƙai.—Neh. 9:16, 17.
2 Ya kamata kowanenmu ya yi wa kansa wannan tambayar, ‘Ta yaya zan iya amfana daga yadda Jehobah yake gafartawa?’ Yadda Jehobah ya gafarta wa Sarki Dauda da Manasseh zai taimaka mana mu samu amsar wannan tambayar.
DAUDA YA YI ZUNUBAI MASU TSANANI
3-5. Waɗanne zunubai masu tsanani ne Dauda ya yi?
3 Dauda ya yi zunubai masu tsanani, duk da cewa shi bawan Allah ne. Zunubai biyu da ya yi sun shafi wasu ma’aurata Uriah da Bath-sheba. Wannan zunubin ya jawo wa Dauda da Uriah da kuma Bath-sheba mummunar sakamako. Amma, yadda Jehobah ya yi wa Dauda gyara ya koya mana darasi game da yadda Jehobah yake gafartawa. Bari mu tattauna abin da ya faru.
4 Dauda ya aiki rundunar Isra’ila su kewaye birnin Rabbah. Birnin yana da nisan mil 50 daga Urushalima, a hayin Kogin Urdun. Sa’ad da rundunar suka tafi, sai Dauda ya hau kan soron gidansa kuma ya hango Bath-sheba tana wanka. A lokacin, mijinta ba ya gida. Abin da Dauda ya gani ya ta da sha’awarsa sosai har ya ce a kawo masa Bath-sheba, kuma ya yi zina da ita.—2 Sam. 11:1-4.
5 Sa’ad da Dauda ya ji cewa Bath-sheba ta yi ciki, sai ya ce Uriah ya dawo Urushalima. Yana son Uriah ya sadu da matarsa domin ya yi zato cewa shi ya sa ta juna biyu. Amma, Uriah ya ma ƙi ya shiga cikin gidansa. Bayan haka, sai Dauda ya aika wa kwamandarsa wasiƙa cewa ya sanya Uriah a gaban dāga, kuma ya gaya wa rundunar cewa su gudu su bar shi. Ƙulle-ƙullen Dauda ya yi nasara, kuma aka kashe Uriah. (2 Sam. 11:12-17) Dauda ya ninka zunubin da ya yi. Ya yi zina da kuma kisan kai.
DAUDA YA TUBA
6. Mene ne Jehobah ya yi bayan Dauda ya yi zunubi, kuma mene ne hakan ya koya mana game da Jehobah?
6 Hakika, Jehobah ya ga kome da ya faru. (Mis. 15:3) Ko da yake Dauda ya auri Bath-sheba bayan Uriah ya rasu, Jehobah “bai ji daɗin mugun abin da Dauda ya yi ba.” (2 Sam. 11:27) Mene ne Jehobah ya yi? Ya tura annabinsa Nathan wurin Dauda. Tun da Jehobah Allah ne mai gafartawa, ya so ya yi wa Dauda jin ƙai. Amma, Jehobah yana son ya san ko Dauda ya tuba. Abu mai ban sha’awa ne sosai cewa Jehobah yana son ya ga ko Dauda ya tuba da gaske. Bai tilasta wa Dauda ya yi ikirarin laifinsa ba, amma ya dai tura Nathan wurinsa don ya bayyana masa tsananin zunubin da ya yi. (Karanta 2 Sama’ila 12:1-4.) Yadda Jehobah ya bi da batun yana da kyau sosai.
7. Mene ne Dauda ya yi sa’ad da ya ji labarin Nathan?
7 Nathan ya soma tattaunawarsa da wani kwatanci. Kwatancin ya sa Dauda fushi sosai, kuma yana son a hukunta mawadacin da Nathan ya ambata. Sai ya ce wa Nathan: “Na rantse da ran Ubangiji, mutumin da ya yi wannan ya isa mutuwa.” Dauda ya kuma ce ya kamata a saka wa mutumin da aka ƙwace tunkiyarsa. Amma, sai Nathan ya ce wa Dauda: “Kai ne mutumin nan.” Maganar ta birkitar da Dauda. Sai Nathan ya gaya wa Dauda cewa, “takobi ba za ya rabu da gidanka ba daɗai” kuma bala’i zai auko wa iyalinsa. Za a kuma ci mutuncinsa a gaban mutane. Hakan ya sa hankalin Dauda ya dawo jikinsa, sai ya ce: “Na yi wa Ubangiji zunubi.”—2 Sam. 12:5-14.
DAUDA YA ROƘI JEHOBAH YA GAFARCE SHI
8, 9. Yaya Dauda ya bayyana yadda yake ji a cikin Zabura ta 51, kuma mene ne hakan ya koya mana game da Jehobah?
8 Abin da Dauda ya rubuta a Zabura ta 51 ya nuna cewa ya tuba sosai. A wannan zaburar, Dauda ya roƙi Jehobah kuma ya ce ya taimaka masa. Ya kuma tuba daga zunubansa. Abin da ya fi muhimmanci ga Dauda shi ne dangantakarsa da Jehobah. Ya yi ikirarin laifinsa ya ce: “Kai kaɗai na yi maka zunubi.” Sai ya roƙe Jehobah, ya ce: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina. . . . Ka mayas mani da farinciki na cetonka: Ka tokare ni da ruhu na yardan rai.” (Zab. 51:1-4, 7-12) Sa’ad da kake magana da Jehobah, kana gaya masa dukan abin da ke damunka kuwa?
9 Jehobah bai cire sakamakon laifuffukan Dauda ba. Sun ci gaba da la’anta shi muddar ransa. Amma, Jehobah ya bincika zuciyar Dauda, kuma ya ga cewa yana da “karyayyar zuciya mai- tuba.” A sakamako, Jehobah ya gafarce shi. (Karanta Zabura 32:5; Zab. 51:17) Jehobah Maɗaukaki ya san ainihin dalilin da ya sa muke zunubi. Saboda haka, Jehobah bai ce alƙalai ’yan Adam su hukunta Dauda da Bath-sheba ba, kamar yadda aka ambata a cikin doka. (Lev. 20:10) Jehobah ya shar’anta Dauda da Bath-sheba da kansa kuma ya yi musu jin ƙai. Allah ya ma sa ɗansu Sulemanu ya zama sarkin ƙasar Isra’ila.—1 Laba. 22:9, 10.
10. (a) Me ya sa Jehobah ya gafarta wa Dauda? (b) Me ya kamata mutum ya yi don Jehobah ya gafarta masa?
10 Wataƙila dalilin da ya sa Jehobah ya gafarta wa Dauda shi ne don ya yi wa Saul jin ƙai. (1 Sam. 24:4-7) Yesu ya bayyana cewa Jehobah yana bi da mu daidai yadda muke bi da mutane. Ya ce: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku. Gama da irin shari’a da ku ke shar’antawa, da shi za a shar’anta muku: da mudun nan da ku ke aunawa kuma da shi za a auna muku.” (Mat. 7:1, 2) Muna samun wartsakewa don mun san cewa Jehobah zai gafarta zunubanmu, ko da mun yi zina ne ko kuma kisan kai. Amma, zai gafarta mana idan muna a shirye mu gafarta kurakuren mutane, kuma muna ikirarin laifuffukanmu, kuma muka canja ra’ayinmu. Idan mai zunubi ya tuba, Jehobah zai sa ya samu “wartsakewa.”—Karanta Ayyukan Manzanni 3:19.
MANASSEH YA YI ZUNUBI MAI TSANANI, AMMA YA TUBA
11. Waɗanne miyagun ayyuka ne Sarki Manasseh ya yi?
11 Ka yi la’akari da wani misali da ya nuna cewa Jehobah yana a shirye ya gafarta zunubi mai tsanani. Manasseh ya soma sarauta shekara 360 bayan zamanin Dauda, kuma ya yi sarauta na tsawon shekara 55. Manasseh ya ɓata wa Jehobah rai sosai domin ya yi zunubai masu tsanani a lokacin sarautarsa. Alal misali, Manasseh ya gina bagadai don Baal, ya bauta wa “dukan rundunar sama,” ya miƙa ’ya’yansa hadaya ta ƙonawa kuma ya ƙarfafa mutane su yi sihiri. Hakika, Manasseh “ya yi aikin mugunta da yawa a ganin Ubangiji.”—2 Laba. 33:1-6.
12. Ta yaya Manasseh ya komo ga Jehobah?
12 Daga baya, Babiloniyawa suka kama Manasseh zuwa ƙasarsu, kuma suka saka shi cikin kurkuku. Wataƙila ya tuna da abin da Musa ya ce wa Isra’ilawa: “Sa’anda kana cikin ƙunci, dukan waɗannan al’amura kuma sun auko maka, cikin kwanaki na ƙarshe za ka juya wurin Ubangiji Allahnka, ka kuma saurara ga muryatasa.” (K. Sha 4:30) Manasseh ya komo wurin Jehobah. Ta yaya? “Ya ƙasƙantar da kansa da gaske . . . ya kuwa yi addu’a” ga Allah (kamar yadda aka nuna a shafi na 21). (2 Laba. 33:12, 13) Littafi Mai Tsarki bai faɗa dalla-dalla abin da Manasseh ya ce a addu’arsa ba, amma wataƙila yana da nasaba da wadda Sarki Dauda ya yi da aka rubuta a Zabura ta 51. Ko yaya dai, mun san cewa Manasseh ya tuba da dukan zuciyarsa.
13. Me ya sa Jehobah ya gafarta wa Manasseh?
13 Shin Jehobah ya saurari addu’ar Manasseh kuwa? Jehobah “ya kula da roƙonsa, ya amsa addu’arsa.” Manasseh ya san cewa ya yi zunubi mai tsanani, kuma ya tuba da gaske kamar Dauda. Shi ya sa Jehobah ya gafarta masa, kuma ya ƙyale shi ya sake zama sarki a Urushalima. A sakamakon haka, Manasseh ya san cewa “Ubangiji shi ne Allah.” (2 Laba. 33:13) Wannan misalin ya nuna mana cewa Jehobah mai jin ƙai ne, kuma yana gafarta wa waɗanda suka tuba da dukan zuciyarsu.
A KOYAUSHE NE JEHOBAH YAKE GAFARTAWA?
14. Mene ne yake sa Jehobah ya gafarta wa mai zunubi?
14 Yawancin bayin Jehobah ba su taɓa yin zunubin da ya kai na Dauda da kuma Manasseh tsanani ba. Amma za mu iya koyan darassi daga labarinsu. Jehobah yana a shirye ya gafarta wa duk mutumin da ya yi zunubi, kome tsananinsa idan ya tuba da dukan zuciyarsa.
15. Yaya muka san cewa ba a koyaushe ba ne Jehobah yake gafartawa?
15 A koyaushe ne Jehobah yake gafartawa? A’a. Ra’ayin Dauda da Manasseh ya bambanta da na Isra’ilawa da Yahudawa masu taurin kai. Sa’ad da Dauda ya yi zunubi, Jehobah ya aiki Nathan ya gaya masa abin da ya yi don ya ga ko zai tuba. Dauda ya tuba da dukan zuciyarsa. Sa’ad da Manasseh ma ya ankara cewa ya yi kuskure, ya tuba da dukan zuciyarsa. Amma sau da yawa, Isra’ilawa da Yahudawa sun ƙi tuba. Shi ya sa Jehobah bai gafarta musu ba, amma sau da sau, ya tura annabawa su gaya musu yadda zunubinsu yake ɓata masa rai. (Karanta Nehemiya 9:30.) Har bayan Isra’ilawa sun dawo daga bauta a ƙasar Babila, Jehobah ya ci gaba da aika annabawa kamar, Ezra da Malakai. Mutanen sun yi farin ciki sa’ad da suka yi nufin Jehobah.—Neh. 12:43-47.
16. (a) Mene ne Jehobah ya yi wa Isra’ilawa domin sun ƙi tuba daga zunubansu? (b) Wane zarafi ne Jehobah ya ba wani da shi Ba’isra’ile ne?
16 A yau, Jehobah ba ya son mu yi hadaya ta dabba kamar yadda Isra’ilawa suke yi a dā. Maimakon haka, ya aiko da Ɗansa Yesu zuwa duniya ya mutu domin mu. (1 Yoh. 4:9, 10) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya bayyana ra’ayin Jehobah game da Urushalima. Ya ce: “Ya Urushalima, Urushalima, wanda ki ke kisan annabawa, kina jejjefe waɗanda an aiko a gareki! so nawa ina so in tattara ’ya’yanki, kamar yadda kaza ta kan tattara ’yan tsākinta ƙarƙashin fikafikanta, amma ba ku yarda ba! Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Mat. 23:37, 38) Jehobah ya sauya al’ummar Isra’ila da ba ta tuba ba da “Isra’ila na Allah.” (Mat. 21:43; Gal. 6:16) Amma, zai yiwu a gafarta wa wani da shi Ba’isra’ile ne? Ƙwarai kuwa. Jehobah yana a shirya ya gafarta musu idan suna da imani ga Allah da kuma hadayar Yesu Kristi. A lokacin da Jehobah zai ta da matattu, zai gafarta wa wasu da suka rasu amma ba su tuba ba.—Yoh. 5:28, 29; A. M. 24:15.
TA YAYA ZA MU AMFANA?
17, 18. Me ya kamata mu yi don Jehobah ya gafarta mana?
17 Mene ne ya kamata mu yi tun da Jehobah yana a shirye ya gafarta mana? Ya kamata mu tuba kamar Dauda da Manasseh. Zai dace mu yi ikirarin zunubinmu, mu tuba, mu roƙe Jehobah ya gafarta mana kuma mu ce ya taimaka mana mu yasar da mugun sha’awa. (Zab. 51:10) Idan kuma mun yi zunubi mai tsanani, zai dace mu gaya wa dattawa abin da muka yi don su taimaka mana. (Yaƙ. 5:14, 15) Abin ƙarfafa ne sosai sanin cewa kome tsananin zunubinmu, Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi.” Kuma Jehobah bai canja ba.—Fit. 34:6, 7.
18 Jehobah ya yi wa Isra’ilawan da suka tuba alkawari cewa zai gafarta musu baki ɗaya. Ya ce ko da zunubansu “ja wur” ne, za su zama fari fat kamar “ƙanƙara.” (Karanta Ishaya 1:18.) Amma, wane amfani za mu samu domin Jehobah yana gafartawa? Jehobah zai gafarta mana baki ɗaya, idan muka tuba kuma muna matuƙar godiya don yana gafarta mana.
19. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
19 Tun da Jehobah yana gafarta mana, ta yaya za mu iya yin koyi da shi? Ta yaya za mu iya gafarta wa mutanen da suka yi zunubi kuma suka tuba da dukan zuciyarsu? Talifi na gaba zai taimaka mana mu bincika zuciyarmu, don mu yi koyi da Jehobah wanda ‘nagari ne, mai-hanzarin gafartawa’ kuma.—Zab. 86:5.
[Hoto a shafi na 24]
Jehobah ya gafarta wa Manasseh, kuma ya ƙyale shi ya ci gaba da sarauta domin ya tuba