Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 p. 10
  • “Ya Roƙi Ubangiji Allahnsa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ya Roƙi Ubangiji Allahnsa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Amfana Daga Yadda Jehobah Yake Gafarta Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mene ne Tuban Gaske Yake Nufi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Josiah Ya Zaɓi Ya Yi Abin da Ya Dace
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 p. 10

Ka Kusaci Allah

“Ya Roƙi Ubangiji Allahnsa”

“NA YI tunanin cewa ba ni da wata daraja,” in ji wani mutumin da ya bijire daga bin mizanan Allah da ya koya sa’ad da yake ƙarami. Sa’ad da ya soma ɗaukan matakai don ya canja halayensa, ya yi fargabar cewa Allah ba zai taɓa gafarta masa ba. Amma wannan mai zunubin da ya tuba ya samu ƙarfafawa daga labarin Manassa da ke cikin Littafi Mai Tsarki, a 2 Labarbaru 33:1-17. Idan ka taɓa tunanin cewa ba ka da wata daraja saboda zunubanka na dā, wataƙila labarin Manassa zai iya ƙarfafa ka.

An yi rainon Manassa ne cikin iyalin da ke bauta wa Allah na gaskiya. Mahaifinsa, Hezekiya, yana ɗaya daga cikin fitattun sarakunan Yahuda. An haifi Manassa ne wajen shekaru uku bayan Allah ya ƙara tsawon rayuwar mahaifinsa ta hanyar mu’ujiza. (2 Sarakuna 20:1-11) Babu shakka Hezekiya ya ɗauki wannan ɗa a matsayin kyauta daga Allah saboda rahamarsa, kuma ya koya masa ya ƙaunaci bauta ta gaskiya. Amma ba a kowane lokaci ba ne yara suke bin sawun iyayensu da ke bauta wa Allah na gaskiya ba. Abin da Manassa ya yi ke nan.

Manassa bai wuce ɗan shekara 12 ba sa’ad da mahaifinsa ya rasu. Abin baƙin ciki, Manassa “ya aika mugunta a gaban Ubangiji.” (Ayoyi 1, 2) Masu ba da shawara da ba su damu da bauta ta gaskiya ne suka ruɗi wannan sarki matashi? Littafi Mai Tsarki bai ambata ba. Abin da ya gaya mana shi ne cewa Manassa ya dulmuya cikin bautar gumaka da zalunci sosai. Ya gina bagadai ga allolin ƙarya, ya yi hadaya da ’ya’yansa, ya yi sihiri, kuma ya ajiye gunki a cikin haikalin Jehobah a Urushalima. Manassa mai taurin kai ya ƙi bin gargaɗin da Jehobah ya yi masa a kai a kai, duk da cewa mu’ujizar da Allah ya yi na ƙara tsawon ran Hezekiya ne ya kai ga haihuwarsa.—Ayoyi 3-10.

A ƙarshe, Jehobah ya yarda a yi gaba da Manassa cikin sarka zuwa Babila. A can inda yake zaman bauta, Manassa ya samu damar yin tunani a kan tafarkinsa. Ya lura cewa gumakansa marasa ƙarfi da rai sun ƙasa kāre shi ne? Ko kuwa ya sake yin tunani ne a kan abubuwan da mahaifinsa da ke bauta wa Allah na gaskiya ya koya masa sa’ad da yake ɗan ƙarami? Ko ma mene ne, Manassa ya canja halinsa. Labarin ya ce: “Ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa da gaske . . . Ya kuwa yi addu’a gareshi.” (Ayoyi 12, 13) Amma zai yiwu Allah ya gafarta wa mutumin da ya aikata irin waɗannan mugayen zunuban?

Tuba na gaske da Manassa ya yi ya motsa Jehobah. Allah ya amsa roƙonsa na neman jin ƙai kuma ‘ya komo da shi cikin Urushalima bisa mulkinsa.’ (Aya 13) Don ya tabbatar da tubansa, Manassa ya yi iya ƙoƙarinsa ya daidaita mugayen ayyukansa, ya kawar da bautar gumaka daga daularsa kuma ya umurci mutanensa “su bauta ma Ubangiji.”—Ayoyi 15-17.

Idan kana jin cewa ba ka cancanci samun gafartawar Allah ba saboda zunuban da ka yi a dā, bari misalin Manassa ya ƙarfafa ka. Wannan labarin sashe ne na hurarriyar Kalmar Allah. (Romawa 15:4) Hakika, Jehobah yana son mu san cewa shi “mai hanzarin gafartawa” ne. (Zabura 86:5) Abin da ya fi muhimmanci a gabansa shi ne yanayin zuciyar mai zunubin ba zunubin ba. Mai zunubin da ya yi addu’a cike da nadama, ya daina zunubin da yake yi, kuma ya ƙudurta yin adalci zai iya samun jin ƙan Jehobah, kamar Manassa.—Ishaya 1:18; 55:6, 7.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba