Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 12/15 pp. 9-13
  • Kai Wakili Ne Mai Riƙon Amana!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kai Wakili Ne Mai Riƙon Amana!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AIKIN WAKILAI
  • MU NA ALLAH NE
  • ABIN DA JEHOBAH YAKE SON MU YI
  • AMFANIN KASANCEWA DA AMINCI
  • YA DACE MU GWADA KANMU DA WANI?
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Wakili Mai Aminci Da Hukumarsa Ta Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kai ‘Wakili Na Alherin Allah’ Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Yi Biyayya Ga Kristi Da Kuma Amintaccen Bawansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 12/15 pp. 9-13

Kai Wakili Ne Mai Riƙon Amana!

“Ku kuwa ba na kanku ba ne.”—1 KOR. 6:19.

MECE CE AMSARKA?

Mene ne aikin wakilai na dā?

Mene ne Allah yake son dukan wakilansa su yi?

Da yake mu wakilai ne, yaya ya kamata mu ɗauki bautarmu ga Allah?

1. Mene ne ra’ayin mutane game da bayi?

SHEKARU 2,500 da suka shige, wani marubuci Bahelleni ya ce: “Ba wanda yake son ya zama bawa.” Yawancin mutane a yau za su yarda da waɗannan kalaman. Domin ana tilasta wa bawa ya yi aikin da ba zai amfane shi ba, kuma ana wulaƙanta shi.

2, 3. (a) Wane hakki ne bayin Kristi da suke aiki da yardar rai suke da shi? (b) Wace tambaya game da wakili ne za mu amsa?

2 Duk da haka, Yesu ya nuna cewa almajiransa za su ƙaskantar da kansu kamar bayi. Amma, hakan ba ya nufin cewa Kiristoci za su yi bauta na wulaƙanci ko azaba ba. Za a daraja da kuma amince da su. Ka yi la’akari da abin da Yesu ya ce kafin ya rasu game da wani “bawa.” Ya ce zai ɗanka wa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” hakki.—Mat. 24:45-47.

3 Ka lura cewa a littafin Luka, an kira wannan bawan “wakili.” (Karanta Luka 12:42-44.) Yawancin Kiristoci masu aminci a yau ba sa cikin wannan “wakili mai-aminci.” Duk da haka Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan bayin Allah wakilai ne. Wane aiki ne Allah ya ba mu? Yaya ya kamata mu ɗauki waɗannan wakilan? Domin mu amsa waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna aikin da wakilai suke yi a zamanin dā.

AIKIN WAKILAI

4, 5. Waɗanne aikace-aikace ne wakilai na dā suke yi? Ka ba da misalai.

4 A zamanin dā, wakili bawa ne da ubangidansa ya amince da shi, kuma ya sanya shi ya kula da gidansa ko kuma sana’arsa. Har ila, wakili yana kula da mallaka da kuɗi da kuma sauran bayin ubangidansa. Wani misali shi ne Eliezer, wanda Ibrahim ya sanya shi bisa mallakarsa. Wataƙila shi ne Ibrahim ya aika ya nema wa ɗansa Ishaƙu mata a ƙasar Mesopotamiya. Babu shakka wannan gagarumin aiki ne.—Far. 13:2; 15:2; 24:2-4.

5 Yusufu tattaɓa-kunnen Ibrahim ya kula da gidan Fotifar. (Far. 39:1, 2) Da shigewar lokaci, Yusufu ya samu wani da ya zama ‘wakilin gidansa.’ Wannan wakilin ne ya marabci ’yan’uwan Yusufu guda goma kuma ya biya bukatunsu. Yusufu ya sa shi ya gwada ’yan’uwansa da ƙoƙo na azurfa. Hakan ya nuna cewa iyayengiji sun amince da wakilansu sosai.—Far. 43:19-25; 44:1-12.

6. Waɗanne ayyuka ne dattawa suke yi?

6 Bayan kusan shekaru 1,800, manzo Bulus ya rubuta cewa dattawa ‘wakilan Allah ne.’ (Tit. 1:7) Dattawa suna kula da kuma ja-gorar ikilisiyoyi domin su ne makiyaya da ke kiwon “garken Allah.” (1 Bit. 5:1, 2) Hakika, dattawa suna da hakki dabam-dabam a cikin ƙungiyar Jehobah. Alal misali, yawanci suna hidima ne a cikin ikilisiya guda. Masu kula masu ziyara suna hidima a ikilisiyoyi da yawa. Waɗanda suke Kwamitin da ke kula da ofishin reshe kuma suna kula da dukan ikilisiyoyi da ke cikin ƙasar. Duk da haka, ana bukatar dukan dattawa su yi aikin su daidai wa daida. Dukansu za su ba da “lissafin aikinsu” ga Allah.—Ibran. 13:17.

7. Ta yaya muka san cewa dukan Kiristoci wakilai ne?

7 Yaya muka san cewa Kiristoci masu aminci da yawa wakilai ne ko da yake su ba dattawa ba? Manzo Bitrus ya ce a wasiƙar da ya rubuta wa dukan Kiristoci: “Yayinda kowa ya karɓi baiko, kuna yi ma junanku hidima da shi, kamar nagargarun wakilai na alherin Allah iri iri masu-yawa.” (1 Bit. 1:1; 4:10) Allah ya yi mana alheri ta wajen ba dukanmu basira da iyawa da abubuwan mallaka da kuma baiwa iri-iri domin mu taimaka wa ’yan’uwa. Saboda haka, dukan wanda yake bauta wa Allah wakili ne. Allah ya amince da kuma daraja mu, kuma yana son mu yi amfani da dukan baiwar da ya ba mu.

MU NA ALLAH NE

8. Wace ƙa’ida guda mai muhimmanci ce bai kamata mu manta ba?

8 Bari mu bincika abubuwa uku da ya kamata dukan Kiristoci wakilai su yi la’akari da su. Na ɗaya: Dukanmu na Allah ne kuma wajibi ne mu faranta masa rai. Bulus ya ce: “Ku kuwa ba na kanku ba ne; gama aka saye ku da tamani,” wato, ta hanyar hadayar fansa ta Kristi. (1 Kor. 6:19, 20) Domin mu na Jehobah ne, wajibi ne mu yi biyayya ga dokokinsa. Dokokinsa kuwa ba su da wuya ainun. (Rom. 14:8; 1 Yoh. 5:3) Mu bayin Kristi ne. Muna da ’yanci kamar wakilai na zamanin dā, amma ’yancinmu yana da iyaka. Mu bayin Allah da kuma Yesu ne. Saboda haka, ko da wane hakki ne muke da shi a ƙungiyar Allah, wajibi ne mu bi umurni da aka ba mu.

9. Ta yaya Yesu ya bayyana abin da ubangida yake son bawansa ya yi?

9 Yesu ya taimaka mana mu fahimci abin da ubangida yake son bawansa ya yi. Ya gaya wa almajiransa cewa akwai wani bawa da ya dawo gida bayan ya gama aikinsa. Shin, ubangidansa ya ce masa ne “Ka zo yanzu ka zauna wurin abinci?” A’a. Amma ya ce masa: “Ka yi shirin abin da zan ci, ka yi ɗamara, ka yi mani hidima, har in ci in sha tukuna; kāna daga baya kai za ka ci ka sha?” Wane darasi ne Yesu ya koya wa almajiransa ta wannan misalin? Yesu ya ce: “Hakanan ku kuma, sa’anda kun yi dukan abin da aka umurce ku, sai ku ce, Mu bayi marasa-amfani ne; mun yi abin da ya wajaba garemu.”—Luk 17:7-10.

10. Me ya nuna cewa Jehobah bai rena ƙoƙari da muke yi don mu bauta masa ba?

10 Hakika, Jehobah yana daraja duk wani ƙoƙari da muke yi don mu bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” (Ibran. 6:10) Jehobah ba zai taɓa ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. Ƙari ga haka, dukan abin da ya ce mu yi zai amfane mu kuma ba zai yi wuya ainun ba. Amma, misalin da Yesu ya bayar ya nuna cewa bawa zai biya bukatar ubangidansa kafin tasa. Hakazalika, mun zaɓa mu yi nufin Allah kafin namu, shi ya sa muka keɓe kanmu gare shi. Ko ba haka ba?

ABIN DA JEHOBAH YAKE SON MU YI

11, 12. Wane hali ne ya kamata mu nuna a matsayin wakilai? Kuma mene ne za mu guje wa?

11 Na biyu, muna bukatar mu tuna cewa ƙa’idoji ɗaya muke bi domin dukanmu wakilai ne. Ko da yake kalilan cikinmu suna da hakki a cikin ƙungiyar Allah, amma abu ɗaya ne Allah yake bukatar dukanmu mu yi. Alal misali, a matsayinmu na almajiran Yesu da kuma Shaidun Jehobah, wajibi ne mu yi ƙaunar juna. Yesu ya ce mutane za su san cewa mu almajiransa ne idan muna ƙaunar juna. (Yoh. 13:35) Hakan ba ya nufin cewa za mu ƙaunaci ’yan’uwanmu Kiristoci ne kawai. Amma, za mu ƙoƙarta mu ƙaunaci waɗanda ba Kiristoci ba ne. Ya kamata dukanmu mu yi haka, kuma ba abu mai wuya ba ne.

12 Allah yana bukatar mu yi abin da ya ce halal ne, kuma mu guji abin da ya haramta. Bulus ya ce: “Masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza, da ɓarayi, da masu-ƙyashi, da masu-maye, da masu-alfasha, da masu-ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.” (1 Kor. 6:9, 10) Ba shi da sauƙi mu yi abin da Allah yake so. Amma za mu amfana sosai, idan muka yi ƙoƙari. Alal misali, za mu samu lafiyar jiki da dangantaka mai kyau da mutane da kuma Jehobah.—Karanta Ishaya 48:17, 18.

13, 14. Wane aiki ne aka ba dukan Kiristoci, kuma yaya ya kamata mu ɗauki aikin?

13 Ka kuma tuna cewa wakili yana da aiki da yake yi. Mu ma haka. Allah ya ba mu kyauta mai tamani, wato, koyarwa ta gaskiya game da shi. Kuma yana son mu koya wa mutane wannan gaskiyar. (Mat. 28:19, 20) Bulus ya ce: ‘Mu fa, sai a yi lissafinmu hakanan, ma’aikatan Kristi ne, wakilai na asiran Allah kuma.’ (1 Kor. 4:1) A matsayin wakili, Bulus ya san cewa yana da hakkin kula da ‘asirai’ ko gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ya koya wa wasu. Wannan shi ne abin da Ubangijinsa, watau, Yesu Kristi yake son ya yi.—1 Kor. 9:16.

14 Muna ƙaunar mutane sa’ad da muka koya musu gaskiya. Da yake yanayinmu ya bambanta, ba za mu iya cim ma abu ɗaya ba a wa’azi. Jehobah ya sa da hakan. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu yi iya ƙoƙarinmu. Ta hakan, za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma mutane sosai.

AMFANIN KASANCEWA DA AMINCI

15-17. (a) Me ya sa wakili zai zama mai aminci? (b) Ta yaya Yesu ya nuna sakamakon rashin aminci?

15 Abu na uku da muke bukatar mu tuna shi ne cewa, wajibi ne mu nuna amincinmu ta wajen yin biyayya. Duk halaye masu kyau da kuma iyawar da wakili yake da su duk banza ne idan ba ya biyayya ga ubangidansa, kuma ba ya aiki tuƙuru. Dole ne wakili ya kasance da aminci idan yana son ya yi aikinsa da kyau, kuma ya faranta ran ubangidansa. Ka tuna cewa Bulus ya ce: “Abin da a ke nema ga wakilai, [shi ne] a iske mutum da aminci.”—1 Kor. 4:2.

16 Babu shakka, Allah zai sāka mana idan muka kasance da aminci. Amma idan mun yi rashin aminci, zai daina amince da mu. Mun san hakan domin misalin talinti da Yesu ya bayar. A wannan misalin, ubangidan ya yaba wa bayi masu kirki da suka yi “ciniki” da kuɗin da ya ba su, kuma ya sāka musu. Amma ya kira bawan da ya yi rashin aminci ‘mugu,’ da “mai-ƙiwuya” da kuma “bawan banza.” Ubangidan ya ƙwace talinti daga wajen bawan, kuma ya jefa shi waje.—Karanta Matta 25:14-18, 23, 26, 28-30.

17 Akwai lokaci kuma da Yesu ya nuna sakamakon rashin aminci. Ya ce: “Akwai wani mai arziki wanda yake da wakili; shi wannan fa aka kai ƙarassa gareshi, wai yana ɓarnatadda dukiyarsa. Ya kirawo shi, ya ce masa, menene wannan da ni ke jin labarinka? Sai ka ba ni lissafin wakilcinka, gama ba shi yiwuwa ka ƙara zama wakili.” (Luk 16:1, 2) Ubangidan ya sallami bawan domin ya ɓarnatar da dukiyarsa. Wannan misali ne mai kyau a gare mu. Ya kamata mu ci gaba da kasancewa da aminci ta wajen yin duk abin da Allah ya ce.

YA DACE MU GWADA KANMU DA WANI?

18. Me ya sa bai dace mu gwada kanmu da wasu ba?

18 Ya kamata kowa ya tambayi kansa, ‘wane irin wakili ne ni?’ Amma wauta ce mu gwada kanmu da wani. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa: “Bari kowane mutum shi auna nasa aiki, sa’annan za ya sami fahariyarsa bisa ga zancen kansa kaɗai, ba ga zancen wani ba.” (Gal. 6:4) Maimakon mu riƙa damuwa ainun da abin da wasu suke yi, ya fi kyau mu mai da hankali ga abin da mu kanmu za mu iya yi. Hakan zai sa ba za mu yi fahariya ba, kuma ba za mu yi sanyin gwiwa ba. Yana da kyau mu sani kuma cewa yanayinmu yakan canja. Wataƙila domin tsufa ko rashin lafiya ko kuma wasu hakki, ba za mu iya yin abubuwa da muke yi a dā ba. A wata sassa kuma, wataƙila yanzu ne muka sami damar yin waɗannan abubuwan fiye da dā. Idan haka ne, me zai hana mu ƙara ƙwazo a hidimarmu?

19. Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba idan ba mu sami wani gata ba?

19 Wani abu kuma shi ne, bai kamata mu gwada kanmu da waɗanda suke da gatar da muke son mu samu ba. Alal misali, wani ɗan’uwa zai iya son ya zama dattijo ko kuma ya riƙa ba da jawabai a manyan taro da taron gunduma. Ko da yake yana da kyau mu yi ta ƙoƙari don mu ƙware, amma ba zai dace ba mu yi sanyin gwiwa idan ba a ba mu gatan nan da nan ba. Wataƙila akwai dalilai da suka sa gatan ya ɗan makara, amma ba mu sani ba. Ka tuna cewa da farko Musa yana ganin ya ƙware ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa ƙasar alkawari, amma sai da ya jira har shekaru arba’in kafin ya yi hakan. A wannan lokacin, Musa ya koyi halaye da suka taimaka masa ya ja-goranci wannan al’umma mai taurin kai da kuma tawaye.—A. M. 7:22-25, 30-34.

20. Wane darasi ne misalin Jonathan ya koya mana?

20 A wani lokaci, akwai gatan da ba za mu taɓa samu ba. Abin da ya faru da Jonathan ke nan. Shi ɗan Saul ne kuma ya kamata ya zama sarkin Isra’ila. Amma Allah ya zaɓi Dauda, wanda Jonathan ya girme shi sosai ya zama sarki. Mene ne Jonathan ya yi? Ya amince da zaɓi da Allah ya yi, har ya ma taimaka wa Dauda a bakin ransa. Jonathan ya ce wa Dauda: “Za ka zama sarki kuma bisa Isra’ila, ni kuma zan zama na biyunka.” (1 Sam. 23:17) Ka fahimci darassin da misalin Jonathan ya koya mana? Ya yi na’am da yanayinsa, kuma bai soma kishin Dauda kamar yadda ubansa Saul ya yi ba. Maimakon mu yi kishin gata da wasu suke da shi, ya fi kyau mu yi ƙoƙari sosai wajen yin aikin da aka ba mu da kyau. Muna da tabbaci cewa a sabuwar duniya, Jehobah zai biya dukan muradinmu masu kyau.

21. Yaya ya kamata mu ɗauki bautarmu ga Allah?

21 Mu riƙa tuna cewa mu wakilan Allah ne, ba bayi da ake wulaƙanta da kuma tilasta musu ba. Akasin haka, Jehobah ya amince da mu kuma ya ba mu aiki mai muhimmanci, watau wa’azin bishara a wannan kwanaki na ƙarshe. Wannan aiki ne da ba za a sake yi ba. Kuma ya ba mu ’yancin zaɓan yadda za mu cika hakkinmu. Saboda haka, bari mu ci gaba da zama wakilai masu riƙon amana. Kuma kada mu manta cewa babban gata ne mu bauta wa Jehobah, wanda shi ne mafi girma a dukan sararin sama.

[Hotona a shafi na 12]

Ya kamata mu yi ƙoƙari sosai wajen yin duk aikin da aka ba mu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba