Kada Ka Ƙyale Kome Ya Nisanta Ka Daga Jehobah
“Ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa.”—JOSH. 24:15.
1-3. (a) Me ya sa Joshua misali ne mai kyau a gare mu? (b) Me ya kamata mu tuna duk sa’ad da muke son mu yi zaɓi?
KALMAR nan “zaɓa” tana da muhimmanci sosai. Wanda yake da zaɓi yana da ɗan ’yanci a kan abubuwan da zai yi a rayuwarsa. Alal misali, a ce mutum yana kan tafiya sai ya isa mararraba. Wacce cikin hanyoyin ne zai bi? Idan ya san inda za shi, ba zai yi masa wuya ba ya bi hanyar da ta dace kuma da ta fi kusa.
2 Littafi Mai Tsarki ya ba da misalin mutane da yawa da suka tsai da shawarwari masu muhimmanci. Alal misali, Kayinu ya sami ’yanci ya zaɓa ko zai aikata bisa fushinsa ko a’a. (Far. 4:6, 7) Joshua ya sami damar ya zaɓa ko zai bauta wa Allah na gaskiya ko kuma allolin ƙarya. (Josh. 24:15) Abin da ya fi ma Joshua muhimmanci shi ne ya kusaci Jehobah. Kuma ya yi zaɓin da zai taimaka masa ya cim ma wannan. Akasin haka, Kayinu ba ya son ya kusaci Jehobah shi ya sa ya yi zaɓin da zai nisanta shi daga Jehobah.
3 A wani lokaci, wajibi ne mu tsai da shawara mai muhimmanci kamar mutumin da yake mararraba. Idan hakan ya faru, ka tuna cewa burinka shi ne ka girmama Jehobah kuma ka guji yin duk wani abin da zai nisanta ka da shi. (Karanta Ibraniyawa 3:12.) A wannan talifin da kuma na gaba, za mu tattauna yadda za mu tsai da shawara mai kyau a fannoni guda bakwai na rayuwa domin kada su nisanta mu daga Jehobah.
AIKI
4. Me ya sa yin aiki yake da muhimmanci?
4 Wajibi ne Kiristoci su yi aiki tuƙuru don su biya bukatunsu da na iyalansu. Littafi Mai Tsarki ya ce duk wanda ba ya son ya tanada wa iyalinsa ba ya fi marar bangaskiya mugunta. (2 Tas. 3:10; 1 Tim. 5:8) Hakan ya nuna cewa yin aiki yana da muhimmanci sosai. Amma idan ba ka yi hattara ba, zaɓin da ka yi game da aiki zai iya nisanta ka daga Jehobah. Ta yaya hakan zai faru?
5. Mene ne ya kamata mu tuna kafin mu yi na’am da aikin da aka ba mu?
5 A ce kana neman aiki, kuma samun aiki a inda kake zama ba cin tuwo ba ne fa? Kana iya yin na’am da kowane irin aikin da aka ba ka. Amma, idan aikin ya saɓa wa ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki kuma fa? Ko kuwa, idan aikin zai sa ka riƙa fasa taro da wa’azi kuma ba za ka riƙa kasancewa da iyalinka ba fa? Shin za ka ce irin wannan aikin ya fi babu, kuma ka yi na’am da shi? Ka tuna cewa zaɓin da ka yi zai iya sa ka kasance kusa da Jehobah ko kuma ya nisanta ka da shi. (Ibran. 2:1) Idan kana neman aiki ko kuma kana son ka canja wanda kake yi, mene ne zai taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau?
6, 7. (a) Waɗanne dalilai biyu ne suka sa mutane suke neman aiki? (b) Wanne cikinsu zai sa ka kasance kusa da Jehobah, kuma me ya sa?
6 Ka tuna cewa zaɓin da ka yi zai nuna abin da kake son ka yi da rayuwarka. Ka tambayi kanka ‘Me ya sa nake son na yi wannan aikin?’ Idan ka nemi aikin da zai sa ka biya bukatunka da na iyalinka, kuma ka ci gaba da bauta wa Jehobah, zai albarkace ka. (Mat. 6:33) Jehobah zai taimaka maka idan ka rasa aikinka ko kuma kana fuskantar matsalar kuɗi. (Isha. 59:1) Ya san “yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba.”—2 Bit. 2:9.
7 Idan kana son ka sami aiki don ka yi arziki ne kuma fa? Wataƙila za ka yi nasara. Amma, ka tuna cewa mutum zai iya fuskantar haɗari idan neman arziki ne ainihin dalilin da ya sa yake son ya yi wannan aikin. (Karanta 1 Timotawus 6:9, 10.) Za ka iya nisanta kanka daga Jehobah, idan yin aiki da kuma neman arziki ne suka fi muhimmanci a rayuwarka.
8, 9. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata iyaye su yi wa kansu game da aikin da suke yi? Me ya sa?
8 Idan kai mahaifi ne, ka tuna cewa yaranka za su yi koyi da zaɓin da kake yi. A ganinsu, mene ne ya fi muhimmanci a gareka? Aikinka ne ko kuma dangantakarka da Jehobah? Idan sun ga cewa kana ƙoƙarin ka yi suna ko arziki, kana ganin ba za su yi koyi da hakan ba idan suka yi girma? Ko kuwa zaɓin da ka yi zai sa su daina daraja ka? Wata ’yar’uwa matashiya ta ce: “Abin da nake tunawa, shi ne cewa mahaifina ya shagala sosai a aikinsa. Da farko, na ɗauka yana yin hakan ne don ya kula da mu sosai. Amma yanzu, ba abin da ya sa yake aiki tuƙuru ke nan ba. Yana aiki ba hutu kuma ya sayi abubuwa masu tsada, har da waɗanda ba ma bukata. Saboda haka, mutane sun fi saninmu da iyali mai arziki, maimakon wadda ke taimaka wa mutane su bauta wa Jehobah. Zan fi yin farin ciki idan mahaifina ya yi ƙoƙari ya taimaka mana mu kusaci Jehobah, maimakon tara arziki.”
9 Iyaye, kada ku ƙyale aikinku ya nisanta ku daga Jehobah. Ku kafa wa ’ya’yanku misali mai kyau. Ku tabbatar musu cewa dangantaka mai kyau da Jehobah ta fi yin arziki ko tara kayan mallaka.—Mat. 5:3.
10. Mene ne ya kamata matashi ya yi tunani a kai kafin ya zaɓa aikin da zai yi?
10 Idan kai matashi ne kuma kana tunanin aikin da za ka yi, mene ne zai taimake ka ka yi zaɓi mai kyau? Ka tuna da abin da muka tattauna ɗazu. Zaɓin da ka yi zai nuna abin da kake son ka yi da rayuwarka. Sana’ar da kake son ka koya ko aikin da kake son ka yi zai ƙyale ka ka bauta wa Jehobah sosai ko kuwa zai nisanta ka da shi? (2 Tim. 4:10) Kana son ka zama kamar mutane da suke farin ciki ne kawai sa’ad da suka ci riɓa mai yawa? Ko kuwa za ka dogara ga Jehobah kamar Dauda wanda ya ce: “Dā yaro na ke, yanzu kuwa na tsufa: Amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” (Zab. 37:25) Wannan yana kamar zaɓan hanyar da za ka bi. Ka tuna cewa ɗaya za ta nisanta ka daga Jehobah, ɗaya kuma za ta sa ka yi rayuwa a hanyar da ta fi kyau. (Karanta Misalai 10:22; Malakai 3:10.) Wacce za ka zaɓa?a
NISHAƊI
11. Mene ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da nishaɗi, amma mene ne ya kamata mu tuna?
11 Littafi Mai Tsarki bai haramta nishaɗi ba kuma ba ya ɗaukansa a matsayin ɓata lokaci. Bulus ya rubuta wa Timotawus cewa “wasa jiki tana da amfaninta kaɗan.” (1 Tim. 4:8) Har ila, Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin dariya da “lokacin rawa,” kuma ya ƙarfafa mu mu riƙa hutawa daidai wa daida. (M. Wa. 3:4; 4:6) Amma idan ba ka yi hattara ba, nishaɗi zai iya nisanta ka daga Jehobah. Ta yaya hakan zai faru? Matsalar kashi biyu ne, watau irin nishaɗin da kuma yawan lokacin da muke amfani da shi.
12. Mene ne za ka yi la’akari da shi kafin ka zaɓi nishaɗin da za ka yi?
12 Da farko, ka yi la’akari da irin nishaɗin. Ka tabbata cewa za ka iya samun nishaɗi mai kyau. Amma abin takaici ne cewa duniya tana cike da ire-iren nishaɗi da suka ƙunshi abubuwan da Jehobah ya tsana, kamar su nuna ƙarfi da sihiri da kuma lalata. Saboda haka, kana bukatar ka mai da hankali sosai a kan irin nishaɗin da kake son ka zaɓa. Ta yaya nishaɗin ya shafe ka? Shin yana sa ka zama mai nuna ƙarfi ko mai yin gasa ko kuma mai ƙishin ƙasa? (Mis. 3:31) Nishaɗin yana sa ka kashe kuɗi ainun ne? Zai sa wasu tuntuɓe? (Rom. 14:21) Waɗanne irin abokai ne kake yin nishaɗin da su? (Mis. 13:20) Nishaɗin yana motsa ka ka aikata abin da ba shi da kyau ne?—Yaƙ. 1:14, 15.
13, 14. Me ya sa ya kamata ka mai da hankali ga yawan lokacin da kake yin nishaɗi da shi?
13 Ka yi la’akari kuma da yawan lokacin da nishaɗin zai ci. Ka tambayi kanka, ‘Ina ɓata lokaci da yawa a wajen nishaɗin har ya hana ni zuwa taro ko wa’azi?’ Idan ka ɓata lokaci sosai wajen yin nishaɗin, ba za ka wartsake yadda ya kamata ba. Hakika waɗanda suka fi more nishaɗi su ne waɗanda suke yinsa daidai wa daida. Me ya sa? Domin sun san cewa sun fara cim ma “mafifitan al’amura,” shi ya sa ba sa yin da-na-sani bayan sun yi nishaɗi.—Karanta Filibiyawa 1:10, 11.
14 Ko da yake kana iya jin cewa ɓata lokaci sosai wajen yin nishaɗi yana kayatarwa, amma yin hakan zai nisanta ka daga Jehobah. Wata ’yar’uwa ’yar shekara 20 mai suna Kim ta shiga irin wannan matsalar, kuma ta ce: “Ina halartar liyafa kowace ranar Jumma’a da Asabar da kuma Lahadi. Amma yanzu na fahimci cewa akwai abubuwa da yawa da suka fi muhimmanci da ya kamata na yi. Alal misali, tun da ni majagaba ce yanzu, ba yadda zan riƙa zuwa liyafa har ƙarfe ɗaya ko biyu don ina bukatar na farka ƙarfe shida na safe. Na san cewa ba dukan liyafa ba ne suke da lahani, amma suna iya janye hankalina. Dole ne in daina ɓata lokaci sosai a wajen liyafa.”
15. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su zaɓi nishaɗi mai kyau?
15 Iyaye suna bukatar su tanada wa iyalansu dukan abubuwan da suke bukata. Waɗannan sun haɗa da taimaka wa iyalin ta kasance kusa da Jehobah kuma ta riƙa farin ciki kuma tana ƙaunar juna sosai. Iyaye, kada ku riƙa jin cewa dukan nishaɗi ba su da kyau. Kuma kada ku nuna halin ko oho. (1 Kor. 5:6) Amma idan kuka yi ƙoƙari sosai, za ku zaɓi nishaɗin da zai sa iyalin ta wartsake sosai.b Kuma nishaɗin da kuka zaɓa ba za ta nisanta ku daga Jehobah ba.
DANGANTAKAR IYALI
16, 17. Wane abin baƙin ciki ne ya sami iyaye da yawa? Ta yaya muka san cewa Jehobah ya san yadda suke ji?
16 Iyaye suna ƙaunar ’ya’yansu sosai, shi ya sa Jehobah ya ce yana ƙaunar mutanensa kamar hakan. (Isha. 49:15) Saboda haka, ba laifi ba ne iyaye su yi baƙin ciki sosai sa’ad da wani ɗansu ya daina bauta wa Jehobah. Wata ’yar’uwa da aka yi wa ’yarta yankan zumunci ta ce: “Na yi baƙin ciki ƙwarai. Kuma ina ta mamakin abin da ya sa ta daina bauta wa Jehobah. Sai na soma jin kamar laifi na ne.”
17 Jehobah ya fahimci yadda kuke ji. Shi kansa ma ya yi baƙin ciki sa’ad da ɗansa Adamu ya yi tawaye. Kuma rashin biyayyar da mutane suka yi kafin Rigyawa ta zamanin Nuhu “ya ɓata masa zuciya kwarai.” (Far. 6:5, 6) Zai yi wa wasu wuya su fahimci yadda iyaye suke ji domin ba su taɓa kasancewa a cikin wannan yanayin ba. Duk da haka, iyaye za su wuce gona da iri idan suka ƙyale horon da aka yi wa ɗansu ya nisanta su daga Jehobah. To, mene ne zai taimaka wa iyaye su jimre idan ɗansu ya bar Jehobah?
18. Me ya sa bai dace iyaye su ɗora wa kansu laifi ba sa’ad da ɗansu ya daina bauta wa Jehobah?
18 Kada ku ɗora wa kanku laifin abin da ya faru. Duk wanda ya riga ya keɓe kansa ga Jehobah yana da hakkin yanke wa kansa shawarar ko zai ci gaba da bauta masa ko a’a. Kuma ‘zai ɗauki kayan kansa.’ (Gal. 6:5) Tabbas, Jehobah zai ga laifin mai zunubin ne ba ku ba. (Ezek. 18:20) Ƙari ga haka, kada ku ɗora wa wani laifi. Ku daraja tsarin da Jehobah ya kafa na horar da mai laifi. Ku yi tsayayya da Iblis maimakon ganin laifin dattawa da suke ƙoƙarin kāre ikilisiya.—1 Bit. 5:8, 9.
19, 20. (a) Mene ne zai taimaka wa iyaye su jimre sa’ad da aka yi wa ɗansu yankan zumunci? (b) Wane bege ne waɗannan iyayen suke da shi?
19 Za ku nisanta kanku daga Jehobah idan kuka zaɓa ku riƙa fushi da shi domin ya yi wa ɗanku horo. Ku sa sauran yaranku su ga cewa kuna ƙaunar Jehobah fiye da kome, har ma da iyalinku. Saboda haka, za ku iya jimre da yanayin idan kuka yi ƙoƙarin ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Kada ku daina yin tarayya da ’yan’uwanku Kiristoci. (Mis. 18:1) Ku gaya wa Jehobah dukan yadda kuke ji. (Zab. 62:7, 8) Kada ku soma neman hujja na yin cuɗanya da wanda aka yi masa yankan zumunci. Alal misali, ta wajen kiransu a waya ko aika musu i-mail ko saƙon ta waya. (1 Kor. 5:11) Ku duƙufa a hidimar Jehobah. (1 Kor. 15:58) ’Yar’uwar da aka ambata ɗazu ta ce: “Na san cewa ina bukatar in duƙufa a hidimar Jehobah kuma in ƙarfafa dangantakata da shi saboda in taimaka wa ’yata duk sa’ad da ta soma bauta wa Jehobah.”
20 Littafi Mai Tsarki ya ce ƙauna “tana kafa bege ga abu duka.” (1 Kor. 13:4, 7) Ba laifi ba ne ka kasance da begen cewa ɗanka zai sake dawowa ya bauta wa Jehobah. Kowace shekara, waɗanda aka yi musu yankan zumunci sukan tuba kuma su dawo ƙungiyar Jehobah. Allah ba zai ci gaba da yin fushi da su ba. Amma zai yafe musu domin shi “mai-hanzarin gafartawa” ne.—Zab. 86:5.
KA YI ZAƁI MAI KYAU
21, 22. Waɗanne irin zaɓi ne ka ƙudura za ka riƙa yi?
21 Jehobah ya ba mu ’yancin yin zaɓi. (Karanta Kubawar Shari’a 30:19, 20.) Amma ya kamata mu yi amfani da wannan ’yancin da kyau. Kowane Kirista ya tambayi kansa, ‘zaɓin da nake yi suna ƙyale ni na bi hanyar da ta dace kuwa? Shin na ƙyale aiki ko nishaɗi ko kuma dangatakar iyali ta nisanta ni daga Jehobah?’
22 Jehobah ba zai daina ƙaunar mutanensa ba. Abin da kawai zai iya nisanta mu daga Jehobah shi ne zaɓi marar kyau. (Rom. 8:38, 39) Amma fa, bai kamata mu ƙyale hakan ya faru ba. Ka tabbata cewa ba ka bar kome ya nisanta ka daga Jehobah ba. A talifi na gaba, za mu tattauna fannoni huɗu na rayuwa da kake bukatar ka yi ƙoƙari don kada su nisanta ka daga Jehobah.
a Don ƙarin bayani game da zaɓan aiki, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2007, shafi na 24-25.
b Don ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2011, shafi na 10-14.