Nishaɗin Da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?
“Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—AFIS. 5:10.
1, 2. (a) Ta yaya Kalmar Allah ta nuna cewa Jehobah yana son mu more rayuwa? (b) Ɗaukan nishaɗi a matsayin “kyautar Allah” zai sa mu yi mene ne?
LITTAFI MAI TSARKI ya nuna sarai cewa Jehobah yana son mu more rayuwarmu. Alal misali, Zabura 104:14, 15 ta ce Jehobah yana “fito da abinci daga ƙasa: ruwan anab wanda yana sa zuciyar mutum ta wartsake, da mai domin a sa fuskatasa ta yi sheƙi, da abinci kuma mai-ƙarfafa zuciyar mutum.” Hakika, Jehobah ne yake sa shuke-shuke su yi girma domin mu samu hatsi da māi da kuma ruwan anab. Ko da yake ba dole ba ne a sha ruwan anab don a more rayuwa, yana iya ‘sa zuciya ta wartsake.’ (M. Wa. 9:7; 10:19) Hakika, Jehobah yana son mu yi farin ciki, mu cika zuciyarmu da “farinciki.”—A. M. 14:16, 17.
2 Saboda haka, bai kamata mu ga laifi ne mu yi amfani da lokacinmu don “duba tsuntsaye na sama” da kuma “lura da furanni na jeji” ba. Irin waɗannan ayyukan za su iya ba mu ƙarfi kuma su sa rayuwarmu ta yi daɗi. (Mat. 6:26, 28; Zab. 8:3, 4) Yin rayuwa mai farin ciki da kuma isashen lafiya “kyautar Allah” ce. (M. Wa. 3:12, 13) Ɗaukan lokacin da muke yin nishaɗi a matsayin ɗaya daga cikin kyauta da Allah ya ba mu zai motsa mu mu yi amfani da shi a hanyar da za ta faranta wa Allah rai.
Nishaɗi Iri-Iri da Kasawarsu
3. Me ya sa mutane suke da zaɓi dabam-dabam game da nishaɗinsu?
3 Waɗanda suke da ra’ayin da ya dace game da nishaɗi sun san cewa suna da ’yancin yin zaɓi. Me ya sa? Don ba da amsa, bari mu gwada nishaɗi da abinci. Mutane a wurare dabam-dabam na duniya suna son cin abinci iri-iri. Hakika, abincin da wasu suke alfahari da shi yana zama abin ƙyama ga wasu a wasu ƙasashe. Hakan nan ma, Kiristoci da suke zama a ɓangarorin duniya dabam-dabam suna jin daɗin nishaɗi iri-iri. Har ma Kiristoci da suke zama a yanki ɗaya suna iya zaɓan yin abubuwa dabam-dabam, abin da wani yake gani cewa nishaɗi ne kamar, karanta littafi mai kyau da tuƙa keke za su iya zama abin ƙyama ga wasu. Duk da haka, mun san cewa mutane suna da ’yancin zaɓan irin abinci da za su ci, da irin nishaɗin da za su yi.—Rom. 14:2-4.
4. Me ya sa za mu kafa iyaka a kan irin nishaɗin da za mu zaɓa? Ka ba da misali.
4 Ko da muna da ’yancin zaɓan nishaɗin da muke so, bai kamata mu saka hannu a dukan nishaɗi ba. Ka yi la’akari kuma da misalin abinci. Ko da yake muna iya son cin abinci dabam-dabam, ba za mu zaɓa mu ci ruɓaɓɓen abinci ba. Irin wannan abinci yana iya sa mu rashin lafiya. Haka ma, ko da yake za mu so mu yi nishaɗi dabam-dabam masu kyau, ba za mu yi nishaɗi da zai sa rayuwarmu cikin haɗari ba ko yin lalata. Yin irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma za su sa lafiyarmu ta zahiri da ta ruhaniya cikin haɗari. Don mu tabbata cewa mun kafa iyaka ga nishaɗin da muka zaɓa, muna bukatar mu yi tunani sosai game da nishaɗin da za mu so mu yi da zai amfane mu da kuma faranta wa Jehobah rai. (Afis. 5:10) Ta yaya za mu iya yin hakan?
5. Ta yaya za mu san ko nishaɗinmu yana faranta wa Jehobah rai?
5 Don nishaɗi ya amfane mu kuma ya faranta wa Jehobah rai, dole ne ya yi daidai da mizanai da ke cikin Kalmar Allah. (Zab. 86:11) Don ka tsai da shawarwari game da nishaɗi, kana iya rubuta tsari mai sauƙi. Tsarin ya ƙunshi fannoni uku na nishaɗi: Irin nishaɗin da lokacin da za a yi nishaɗin da kuma abokan da za a yi nishaɗin tare da su. Bari mu tattauna su ɗaya bayan ɗaya.
Wane Irin Nishaɗi Ne?
6. Wane nishaɗi ne muke bukatar mu ƙi, kuma me ya sa?
6 Kafin ka zaɓi wani nishaɗi, kana bukatar ka fara tambayar kanka: Wane irin nishaɗi ne? Yana da kyau ka tuna cewa da akwai nishaɗi iri biyu. Na farko ya ƙunshi abubuwa da ba za mu taɓa yi ba, na biyu kuma abubuwa ne da muna iya tsai da shawara mu yi. Nishaɗi da yawa a cikin wannan muguwar duniya sun ƙunshi ayyuka da sun saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ko kuma waɗanda suka taka dokokin Allah. (1 Yoh. 5:19) Ya kamata Kiristoci na gaskiya su ƙi irin wannan nishaɗin. Wannan ya haɗa da nishaɗin da ke nuna zalunci da sihiri da luwaɗi da batsa ko mugunta ko kuma ke ɗaukaka wasu ayyukan lalata. (1 Kor. 6:9, 10; karanta Ru’ya ta Yohanna 21:8.) Ko a ina ne muke da zama, muna son mu nuna wa Jehobah cewa muna “ƙyamar abin da ke mugu” ta wajen ƙin yin irin wannan nishaɗin.—Rom. 12:9; 1 Yoh. 1:5, 6.
7, 8. Mene ne zai iya taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau game da wasu irin nishaɗi? Ka ba da misali.
7 Irin nishaɗi na biyu ya ƙunshi ayyuka da ba su shafi abubuwa da Kalmar Allah ta hana kai tsaye ba. Saboda haka, kafin mu tsai da shawarwari game da irin wannan nishaɗi, ya kamata mu tabbata cewa ba su saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. (Mis. 4:10, 11) Da haka muna bukatar mu tsai da shawara da za ta taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau. (Gal. 6:5; 1 Tim. 1:19) Ta yaya za mu iya yin hakan? Ka yi tunanin wannan: Kafin mu ci abin da ba mu taɓa ci ba, za mu so mu san abubuwan da aka dafa abincin da su. Hakazalika, kafin mu zaɓa nishaɗi, muna bukatar mu bincika ainihin abubuwan da ya ƙunsa.—Afis. 5:17.
8 Alal misali, wataƙila kana son wasanni, kuma hakan daidai ne. Wasanni yana da daɗi. Amma a wasu wasanni, gasar tana iya kasance da mugunta ko kuma saka rayuwar mutumin cikin haɗari da sa raunuka na zahiri. A wasu wasanni, mutane suna biki a hanyar mugunta kuma su yi tunani cewa ƙasarsu ta fi na wasu kyau. Mene ne ya kamata ka yi idan kana son wasannin da ake waɗannan abubuwan? Bayan ka yi tunani game da abin da waɗannan wasanni suka ƙunsa, wataƙila za ka tsai da shawara cewa irin wannan nishaɗin bai jitu da yadda Jehobah yake tunani ko saƙon salama da ƙauna da muke wa mutane wa’azin su ba. (Isha. 61:1; Gal. 5:19-21) Amma idan ka tabbata cewa nishaɗin ya yi daidai da ƙa’idodin Jehobah, yana iya kasance da amfani a gare ka kuma ya ba ka ƙarfi.—Gal. 5:22, 23; karanta Filibiyawa 4:8.
A Wane Lokaci ne Zan Yi Nishaɗin?
9. Mene ne amsarka ga wannan tambayar, ‘A wane lokaci ne zan yi nishaɗi’ ta nuna?
9 Tambaya ta biyu da za ka yi wa kanka ita ce, ‘A wane lokaci ne zan yi nishaɗin? Yaya yawan lokacin da zan yi amfani da shi wajen yin nishaɗin?’ Amsar da muka ba da ga wannan tambayar mene ne? ta bayyana abubuwa da yawa game da halinmu, wato, abin da muka ga ya dace da abin da bai dace ba a gabanmu. Amma, amsa ga wannan tambayar a wane lokaci ne zan yi nishaɗin? yana nuna abubuwa da suka fi muhimmanci da kuma abubuwan da ba su da muhimmanci a gare mu. Yaya za mu san yadda nishaɗi yake da muhimmanci a rayuwarmu?
10, 11. Ta yaya kalamin Yesu da ke Matta 6:33 za su taimaka mana wajen tsai da shawara game da yawan lokaci da za mu yi nishaɗi?
10 Yesu Kristi ya gaya wa mabiyansa: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.” (Mar. 12:30) Muna nuna cewa abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu shi ne mu ƙaunaci Jehobah ta wajen yin biyayya ga abin da Yesu ya ce: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.” (Mat. 6:33) Ta yaya wannan furuci zai taimaka mana mu san yadda nishaɗi yake da muhimmanci a rayuwarmu da kuma yawan lokaci da za mu yi shi?
11 Ka lura cewa Yesu ya gargaɗe mu mu ‘fara biɗan mulkin.’ Bai gaya mana mu ci gaba ‘biɗan mulkin kaɗai’ ba. Babu shakka, Yesu ya san cewa za mu bukaci mu biɗi abubuwa da yawa a rayuwa har da Mulkin. Muna bukatar wajen kwana da abinci da tufafi da ilimi da aiki da kuma nishaɗi da sauransu. Amma, ayyuka na Mulki ne za su kasance na farko a cikin dukan abubuwa da muke biɗa. (1 Kor. 7:29-31) Sanin wannan gaskiya ta musamman ya kamata ya motsa mu mu biɗa sauran abubuwa, har da nishaɗi a hanyar da za ta taimaka mana mu yi aikin da ya fi muhimmanci, wato, al’amura na Mulki. Idan muka yi hakan, nishaɗi zai iya amfane mu.
12. Ta yaya za mu iya yin amfani da ƙa’idar da ke Luka 14:28 sa’ad da muke nishaɗi?
12 Saboda haka, kafin mu yi nishaɗi ya kamata mu yi lissafin kuɗin da za mu kashe da lokacin da za mu ɓatar tun da wuri. (Luk 14:28) Muna bukatar mu san yawan lokaci da za mu yi wani nishaɗi. Sai kuma mu tsai da yawan lokaci da ya dace mu yi nishaɗin. Ba zai dace ba mu yi wani nishaɗi da zai sa mu mance da wasu ayyuka masu muhimmanci kamar yin nazarin Littafi Mai Tsarki da bauta ta iyali da halartar tarurrukan Kirista ko kuma yin wa’azin bishara ba. (Mar. 8:36) Amma idan nishaɗi zai ba mu ƙarfi don mu ci gaba a hidimarmu ga Allah, muna iya tsai da shawara cewa yin amfani da lokacinmu don wannan zai amfane mu.
Su Waye ne Abokaina?
13. Me ya sa za mu yi tunani sosai game da waɗanda za mu yi cuɗanya da su a nishaɗi?
13 Tambaya ta uku da za ka yi wa kanka, ita ce: ‘Su waye ne nake cuɗanya da su sa’ad da nake nishaɗi?’ Amsar wannan tambaya tana da muhimmanci domin mutanen da muke cuɗanya da su za su iya shafan nishaɗin da muka zaɓa. Kamar yadda kake jin daɗin cin abinci tare da abokan kirki, sau da yawa nishaɗi ya fi daɗi sa’ad da ka yi hakan da abokan kirki. Mutane da yawa a cikinmu, musamman matasa suna jin daɗin nishaɗi da suka yi tare da wasu. Amma, don mu tabbata cewa wani nishaɗi zai amfane mu, yana da kyau mu tsai da shawara tun da wuri a kan irin mutanen da za mu zaɓa a matsayin abokanmu da kuma irin waɗanda za mu guji.—2 Laba. 19:2; karanta Misalai 13:20; Yaƙ. 4:4.
14, 15. (a) Wane misali ne Yesu ya kafa wajen zaɓan abokai da suka dace? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu game da abokanmu?
14 Bin misalin Yesu zai taimaka mana mu samu abokan kirki. Yesu yana ƙaunar mutane tun daga lokacin halitta. (Mis. 8:31) Sa’ad da yake duniya, ya nuna ƙauna kuma ya daraja kowa. (Mat. 15:29-37) Amma Yesu ya san cewa da akwai bambanci tsakanin kasancewa mai fara’a da kuma zama aboki na kud da kud. Ko da yake Yesu yana da fara’a ga dukan mutane, yana abokantaka da waɗanda suka cika ainihin abubuwa da ake bukata. Da yake yi wa manzanninsa 11 masu aminci magana, Yesu ya ce: ‘Ku ne abokaina idan kun yi abin da na umurce ku.’ (Yoh. 15:14; ka kuma duba Yoh. 13:27, 30.) Yesu ya zaɓa waɗanda suka bi shi da kuma bauta wa Jehobah kaɗai a matsayin abokansa na kud da kud.
15 Saboda haka, kafin ka zaɓi wani ya zama abokinka na kud da kud, zai dace ka tuna da abin da Yesu ya ce. Ka yi wa kanka waɗannan tambayoyi: ‘Shin wannan mutum yana nuna ta kalamansa da ayyukansa cewa yana biyayya ga umurnin Jehobah da kuma Yesu? Shin yana ƙaunar abin da yake da kyau kuma ya ƙi mugunta? Shin zai ƙarfafa ni na fara biɗan Mulkin a rayuwata kuma na zama bawa mai aminci ga Jehobah?’ Idan amsarka e ce ga waɗannan tambayoyi, ka san cewa kana da aboki nagari wanda za ka iya more nishaɗi tare da shi.—Karanta Zabura 119:63; 2 Kor. 6:14; 2 Tim. 2:22.
Shin Nishaɗin da Nake Yi Ya Ci Gwajin?
16. Mene ne ya kamata mu tambayi kanmu game da nishaɗinmu?
16 Mun ɗan tattauna fannoni uku na nishaɗi, wato, irin nishaɗi da za a yi da yawan lokaci da za a yi shi da kuma abokan da za mu yi nishaɗin tare da su. Don nishaɗi ya amfane mu, dole ne ya jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, kafin mu yi wani nishaɗi, muna bukatar mu gwada shi. Idan ya zo ga irin nishaɗi da za mu yi, muna bukatar mu san: ‘Mene ne ya ƙunsa? Mai kyau ne ko kuma ya ƙunshi mugunta ko lalata?’ (Mis. 4:20-27) Idan ya zo ga yawan lokaci da za mu yi nishaɗi, muna bukatar mu san: ‘Yawan wane lokaci ne zan yi wannan nishaɗi? Yawan lokacin ya dace ne ko bai dace ba?’ (1 Tim. 4:8) Idan ya zo batun abokai, muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Su waye zan yi wannan nishaɗin tare da su? Shin abokan nagari ne ko kuma mugun tarayya ne.—M. Wa. 9:18; 1 Kor. 15:33.
17, 18. (a) Ta yaya za mu gwada kanmu mu ga ko nishaɗinmu ya yi daidai da mizanan Littafi Mai Tsarki? (b) Mene ne ka ƙuduri aniya ka yi idan ya zo ga batun zaɓan nishaɗi?
17 Nishaɗin da za mu yi bai ci gwaji ba, idan bai jitu da mizanai da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. A wani ɓangare kuma, idan mun tabbata cewa ayyukanmu na hutu sun jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki a dukan fannoni ukun, nishaɗinmu zai ɗaukaka Jehobah kuma ya amfane mu.—Zab. 119:33-35.
18 Saboda haka, idan ya zo ga batun nishaɗi, bari mu yi iyakar ƙoƙarinmu don mu yi abin da ya dace a lokacin da ya dace kuma da mutanen da suka dace. Hakika, ya kamata mu so yin biyayya ga abin da Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.”—1 Kor. 10:31.
Za Ka Iya Bayyanawa?
Game da batun nishaɗi, ta yaya za ka yi amfani da ƙa’idodin da suke . . .
• Filibiyawa 4:8?
• Matta 6:33?
• Misalai 13:20?
[Hotunan da ke shafi na 9]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
✔Irin Nishaɗin
[Hotunan da ke shafi na 10]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
✔Lokacin Nishaɗin
[Hotunan da ke shafi na 12]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
✔Irin Abokan
[Hoto a shafi na 10]
Ta yaya za mu bi misalin Yesu wajen zaɓan abokanmu da kuma nishaɗinmu?