Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 3/1 pp. 19-23
  • Nishaɗi Mai Kyau Da Ke Kawo Wartsakewa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nishaɗi Mai Kyau Da Ke Kawo Wartsakewa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zaɓan Nishaɗi Mai Kyau
  • Biyan Bukatunmu na Nishaɗi a Hanyoyi Masu Kyau
  • Wasu Tunasarwa da Kuma Gargaɗi
  • Nishaɗin Da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Kana Kaunata Fiye da Wadannan?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kada Ka Ƙyale Kome Ya Nisanta Ka Daga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 3/1 pp. 19-23

Nishaɗi Mai Kyau Da Ke Kawo Wartsakewa

“Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.”—1 KORINTHIYAWA 10:31.

1, 2. Me ya sa ya kamata a ɗauki ayyuka mai kyau “kyautar Allah,” kuma wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba da?

KOWANENMU na son ya yi ayyukan da za su sa shi farin ciki. Allahnmu Jehobah mai farin ciki yana son mu more rayuwarmu, saboda haka ya yi mana tanadin abubuwa masu yawa don mu cim ma haka. (1 Timothawus 1:11; 6:17) Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Na sani babu abin da ya fi masu, kamar su yi murna. . . . Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.”—Mai-Wa’azi 3:12, 13.

2 Sa’ad da mutum ya yi tunani bisa ayyuka masu kyau da ya cim ma, hakan na kawo wartsakewa, musamman na tarayya mai kyau da iyalinsa ko abokai. Ya kamata a ɗauki irin wannan murnar “kyautar Allah.” Hakika, ko da yake Mahalicci yana yi mana tanadi mai yawa, hakan bai ba mu damar yin nishaɗin da zai wuce gona da iri ba. Littafi Mai Tsarki ya haramta maye, zarin ci, da kuma lalata, kuma ya yi gargaɗi cewa waɗanda suke aikata waɗannan abubuwa “ba za su gaji mulkin Allah ba.”—1 Korinthiyawa 6:9, 10; Misalai 23:20, 21; 1 Bitrus 4:1-4.

3. Menene zai taimaka mana mu kasance a faɗake kuma riƙa tuna babbar ranar Jehobah?

3 A wannan mugun zamanin, fiye da dā, Kiristoci suna fuskantar ƙalubalen zama a duniyar da ta lalace ba tare da sun tallafa wa ayyukanta ba. (Yohanna 17:15, 16) Kamar yadda aka annabta, mutanen wannan zamanin sun zama “ma-fiya son annishuwa da Allah,” har ya kai ga “ba su farga ba” da alamun da suke nuna cewa “ƙunci mai-girma” na nan tafe. (2 Timothawus 3:4, 5; Matta 24:21, 37-39) Yesu ya gargaɗi mabiyansa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko.” (Luka 21:34, 35) Mu bayin Allah mun ƙudurta cewa za mu bi gargaɗin Yesu. Ba kamar waɗanda suke cikin wannan duniya marar ibada ba, mu muna ƙoƙarin kasancewa a faɗake a ruhaniya da kuma saka babbar ranar Jehobah a zuciyarmu.—Zephaniah 3:8; Luka 21:36.

4. (a) Me ya sa yake da wuya a sami nishaɗi mai kyau? (b) Wane gargaɗi da ke cikin Afisawa 5:15, 16 ne ya kamata mu yi amfani da shi?

4 Guje wa ayyuka marasa kyau na wannan duniyar ba shi da sauƙi, domin Iblis ya mai da su abin sha’awa da kuma sauƙin samu. Hakan yana da wuya, musamman ma sa’ad da muka biɗi nishaɗi. Yawancin abin da duniya ke bayarwa an yi su ne domin “sha’awoyi na jiki.” (1 Bitrus 2:11) Akwai nishaɗi mai lahani a ko’ina, amma kuma zai iya shiga cikin gida ta hanyar littattafai, Talabijin, Intane, da bidiyo. Saboda haka, Kalmar Allah ta ba da gargaɗi mai kyau ga Kiristoci: “Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi, tun da shi ke miyagun kwanaki ne.” (Afisawa 5:15, 16) Idan muka bi wannan gargaɗin sau da kafa za mu guje wa nishaɗi mai lahani, ba zai ɓata mana lokaci ba, kuma ba zai lalata dangantakarmu da Jehobah ba, wanda hakan zai kai mu ga halaka!—Yaƙub 1:14, 15.

5. Daga menene muke samun wartsakewa mafi kyau?

5 Tun da yake Kiristoci suna aiki tuƙuru, sukan ji cewa suna bukatar lokaci na morar nishaɗi. Hakika, Mai-Wa’azi 3:4 ta ce akwai “lokacin dariya” da kuma “lokacin rawa.” Saboda haka, Littafi Mai Tsarki bai ɗauki nishaɗi a matsayin ɓata lokaci ba. Amma, ya kamata nishaɗi ya sa mu wartsake, ba ya yi wa ruhaniyarmu lahani ba ko kuwa ya shafi ayyukanmu na ruhaniya. Kiristoci ƙwararru sun sani cewa ana samun farin ciki ta wajen yin kyauta. Sun saka yin nufin Jehobah abu na farko a rayuwarsu, kuma suna shaida tabbataccen ‘hutu a rayuwarsu’ domin sun ɗauki karkiya mai sauƙi na Yesu.—Matta 11:29, 30; Ayukan Manzanni 20:35.

Zaɓan Nishaɗi Mai Kyau

6, 7. Menene zai taimake ka ka san nishaɗin da ke da kyau da wanda ba shi da kyau?

6 Ta yaya za mu tabbata cewa ga irin nishaɗin da ya dace da Kirista? Iyaye suna ba da ja-gora ga yaransu, kuma dattawa suna ba da taimako yadda ya kamata. Hakika, ba dole ba ne sai wasu sun gaya mana irin littafi, siliman, wasa, rawa, ko kuwa waƙa ba shi da kyau. Bulus ya ce “isassun mutane . . . suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14; 1 Korinthiyawa 14:20) Littafi Mai Tsarki ya bayar da mizanan da za su yi mana ja-gora. Lamirinka, wanda Kalmar Allah ta koyar, zai taimake ka idan ka saurare shi.—1 Timothawus 1:19.

7 Yesu ya ce “bisa ga yaya ana sansance da itace.” (Matta 12:33) Idan nishaɗin da ake biɗa yana sa a yi sha’awar mugunta, lalata, ko sihiri, ya kamata a guje shi. Ba a amince da nishaɗin da zai sa rai ko lafiyar mutum cikin haɗari ba, da zai kawo talauci, kashe gwiwa, ko kuwa wanda zai sa wasu su yi tuntuɓe. Manzo Bulus ya yi mana gargaɗi cewa idan muka raunana lamirin ’yan’uwanmu, to mun yi zunubi. Bulus ya rubuta: “Sa’anda ku ke yi ma yan-uwa zunubi, kuna kuwa rotsa lamirinsu da shi ke rarrauna, Kristi ku ke yi ma zunubi. Ni fa, idan abinci za ya sa ɗan-uwana shi yi tuntuɓe, ba ni cin nama har abada, domin kada in sa ɗan-uwana shi yi tuntuɓe.”—1 Korinthiyawa 8:12, 13.

8. Waɗanne haɗarurruka ne ke tattare da kallon wasannin bidiyo?

8 Kantuna suna cike da wasannin bidiyo. Wataƙila wasu suna iya ba da farin ciki ba tare da lahani ba, amma irin waɗannan wasanni suna ci gaba da gabatar da abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya haramta. Hakika, kallon wasan da ake naƙasa ko kuma aka kashe mutane, ko wanda ake mugun lalata a ciki, ba nishaɗi ba ne marar lahani! Jehobah ba ya son “mai-son zalunci.” (Zabura 11:5; Misalai 3:31; Kolossiyawa 3:5, 6) Idan wasan da kake yi yana ɗaukaka haɗama ko kuwa zafin hali a cikin zuciyarka, idan yana shafan sosuwar zuciyarka, ko ɓata lokacinka mai tamani, ya kamata ka mai da hankali ga lahani na ruhaniya da hakan zai iya jawowa kuma ka yi gyara tun da wuri.—Matta 18:8, 9.

Biyan Bukatunmu na Nishaɗi a Hanyoyi Masu Kyau

9, 10. Menene mutane masu fahimi suke yi domin su cika bukatunsu na nishaɗi?

9 A wasu lokatai, Kiristoci suna yin tambaya: “Wane nishaɗi ne ke da kyau? Yawancin abubuwan da duniya take gabatarwa ba sa jituwa da mizanan Littafi Mai Tsarki.” Ka tabbata cewa za a iya samun nishaɗi mai kyau, amma hakan na bukatar ƙoƙari. Hakan na bukatar tunani da kuma shiri, musamman ga iyaye. Yawanci sun ga cewa nishaɗi cikin iyali da kuma ikilisiya yana kawo albarka. Cin abinci tare, a hankali sa’ad da ake tattauna abubuwan da suka faru a ranar ko wani batu na Littafi Mai Tsarki yana da kyau da kuma ban ƙarfafa. Ana iya shirya yawon shan iska, wasannin da suka dace, da kuma zuwa wurare masu ban sha’awa. Irin waɗannan ayyuka na nishaɗi suna kawo farin ciki da kuma wartsakewa.

10 Wani dattijo da matarsa da suka yi renon ’ya’yansu uku sun ba da rahoto: “Tun ’ya’yanmu suna ƙanana, suke saka hannu wajen zaɓan inda za mu je hutu. A wasu lokatai, muna ƙyale yaranmu su gayyaci abokan kirki, kuma hakan na sa hutun ya ƙara armashi. Mun ga wasu aukuwa na musamman a rayuwar ’ya’yanmu. Lokaci lokaci, muna gayyatar iyalai da abokai da suke cikin ikilisiya zuwa gidanmu. Muna dafa abinci mu ci tare kuma mu yi wasanni. Muna zuwa inda duwatsu suke, mu kuma yi amfani da irin wannan lokacin mu koyi game da halittar Jehobah.”

11, 12. (a) Menene za ka iya yi domin ka saka wasu cikin shirinka na nishaɗi? (b) Wace irin tarayya ce ta kasance abin da wasu ba za su mance ta ba?

11 Kai ko iyalinka kuna gayyatar wasu sa’ad da kuke shirin yin nishaɗi? Mutane kamar gwauraye, marasa aure, iyalan iyaye gwauraye, wataƙila suna bukatar ƙarfafa. (Luka 14:12-14) Kana iya haɗa da sababbi ’yan kalilan, amma a mai da hankali kada wasu su koyi muguwar tarayya. (2 Timothawus 2:20, 21) Idan yana da wuya naƙasassu su fita waje, ana iya shirya a kai abinci gidansu a ci tare da su.—Ibraniyawa 13:1, 2.

12 A taron da waɗanda aka gayyata suka ji daɗin abinci, suka ji yadda wasu suka zama Kiristoci, kuma suka koyi abin da ya taimaka musu su riƙe amincinsu ga Allah, ya zama abin da yawancinsu ba za su taɓa manta ba. Ana iya tada batutuwa na Littafi Mai Tsarki don duk mutanen da aka gayyata su tattauna, har da yara ma. Irin waɗannan tattaunawar za su iya zama taɗi na ƙarfafa juna, kuma hakan ba zai sa wani ya ji kunya ko kuwa ya ji bai isa ba.

13. Ta yaya ne Yesu da kuma Bulus suka kafa misali wajen nuna halin karɓan baƙi da kuma halartar liyafa?

13 Yesu ya kafa misali mai kyau wajen nuna halin karɓan baƙi da kuma halartar liyafa. Yana amfani da irin waɗannan lokatai ya idar da albarkatu na ruhaniya. (Luka 5:27-39; 10:42; 19:1-10; 24:28-32) Almajiransa na farko sun yi koyi da misalinsa. (Ayukan Manzanni 2:46, 47) Manzo Bulus ya rubuta: “Ina marmarin ganinku, domin in ba ku wani baiko mai-ruhaniya, zuwa kafuwarku; watau, ni da ku mu sami ƙarfafawa a wurinku, kowannenmu ta wurin bangaskiyar junanmu, taku da tawa kuma.” (Romawa 1:11, 12) Hakazalika, ya kamata taronmu a kowane lokaci ya zama na ƙarfafa juna.—Romawa 12:13; 15:1, 2.

Wasu Tunasarwa da Kuma Gargaɗi

14. Me ya sa ba abin hikima ba ce a yi babban liyafa?

14 Yin babban liyafa ba zai dace ba, domin kula da irin wannan taron zai yi wuya. A lokacin da ba zai shafi tsarin ayyuka na ruhaniya ba, iyalai marar yawa suna iya yin wasa da ba na gasa ba. Sa’ad da wasu dattawa, bayi masu hidima, ko kuwa wasu ƙwararru suke wajen liyafar, sukan kasance da tasiri mai kyau kuma liyafar za ta zama mai wartsakarwa.

15. Me ya sa yin liyafa ya haɗa da kula sosai?

15 A taron liyafa, ya kamata waɗanda suka yi shirin su kula da abubuwan da suke faruwa sosai. Sa’ad da kake ƙaunar nuna karɓan baki, kana ganin cewa ba za ka yi baƙin ciki ba, idan ka ji cewa domin wani ɗan sakaci da ka yi, wani cikin waɗanda ka gayyata ya yi tuntuɓe domin abin da ya faru a gidanka? Ka yi la’akari da mizanin da aka tattauna a Kubawar Shari’a 22:8. An umurci Ba’isra’ile wanda ya gina sabon gida ya ɗaura rawani a saman gidan inda ake marabtar baƙi. Me ya sa? “Domin kada ka ja ma gidanka alhakin jini, idan wani ya faɗo daga can.” Hakazalika, abubuwan da ka yi, ba tare da yin hanin da bai dace ba don kāre baƙinka a taron liyafar, ya kamata ya zama wanda zai kāre su a zahiri da kuma a ruhaniya.

16. Me ya kamata a yi idan aka raba giya a wurin liyafa?

16 Idan za a ba da giya a wajen liyafa, ya kamata a mai da hankali sosai. Yawancin Kiristocin da suka gayyaci baƙi sun yanke shawarar cewa, za su raba giya ne kawai idan za su iya kula da abin da aka ba baƙinsu ko kuwa abin da za su sha. Kada a ƙyale kowane abu da zai iya sa wani tuntuɓe ko kuwa wanda zai sa wani ya yi maye. (Afisawa 5:18, 19) Domin wasu dalilai, wasu baƙi suna iya ƙin shan giya. A wurare da yawa, doka ta ƙayyade shekarun da mutum zai kai kafin ya sha giya, kuma ya kamata Kiristoci su yi biyayya ga dokokin Kaisar ko da dokar ba ta ba da sukuni ba.—Romawa 13:5.

17. (a) Idan za a saka waƙa a wurin liyafa, me ya sa yana da muhimmanci wanda ya gayyaci baƙi ya yi zaɓi sosai? (b) Idan za a yi rawa a wurin liyafa, ta yaya za a nuna filako?

17 Wanda ya gayyaci baƙi ya kamata ya tabbata cewa duk kiɗa, rawa, da kuma nishaɗi sun jitu da mizanan Kirista. Waƙoƙin da mutane suke so ya bambanta, kuma akwai waƙoƙi kala-kala. Amma, yawancin waƙoƙi a yau suna ɗaukaka ruhun tawaye, lalata, da mugunta. Ana bukatar a yi zaɓi. Waƙa mai kyau ba dole ba ne ta kasance marar kara, kuma bai kamata ta kasance mai tada marmarin jima’i ko kuwa lalata ba, ko kuma wadda aka yi ta da kara sosai. Ka mai da hankali kada ka ba wanda bai fahimci bukatar rage sautin rediyo ba zaɓen waƙa, da kuma kula da muryar sauti. Rawar da ta haɗa da hali marar kyau, gwatso da girgiza nono wadda ke iya tayar da sha’awa, ba ta dace da Kirista ba.—1 Timothawus 2:8-10.

18. Ta yaya ne iyaye za su iya kāre ’ya’yansu ta wajen kula da liyafar da za su?

18 Ya kamata iyaye Kiristoci su bincika abubuwan da aka shirya a liyafar da aka gayyaci ’ya’yansu, kuma hikima ce sau da yawa su je tare da su. Abin baƙin ciki, wasu iyaye sun ƙyale ’ya’yansu su halarci liyafar da babu mai kula da shi, kuma yawancin waɗanda suka halarta sun faɗa cikin lalata ko wasu halaye marasa kyau. (Afisawa 6:1-4) Ko da matasa suna cikin shekarunsu na goma sha kuma za a iya amincewa da su, duk da haka, ana bukatar a taimaka musu su “guje ma sha’awoyin ƙuruciya.”—2 Timothawus 2:22.

19. Wace gaskiya ce za ta taimaka mana mu mai da hankali a kan abin da za mu ‘fara biɗa’?

19 Yin nishaɗi mai kyau kuma mai wartsakewa jifa jifa na sa rayuwa ta kasance da daɗi. Jehobah bai hana mu yin nishaɗi ba, amma mun sani cewa irin waɗannan ayyukan ba sa taimaka mana mu ajiye wa kanmu dukiya na ruhaniya a sama. (Matta 6:19-21) Yesu ya taimaka wa almajiransa su fahimci cewa ‘fara biɗan mulki, da adalcin Allah’ su ne abu mafi muhimmanci a rayuwa, ba abin da za mu ci, sha, ko sanya ba, waɗanda sune “al’ummai suna ta biɗa.”—Matta 6:31-34.

20. Waɗanne abubuwa masu kyau ne bayin Jehobah masu aminci za su iya sa rai daga wurin Mai Tanadi Mai Girma?

20 Hakika, ko muna ‘ci fa, ko muna sha, ko kuwa iyakar abin da mu ke yi,’ muna iya yin “duka domin a girmama Allah,” muna gode wa Mai Tanadi Mai Girma domin abubuwa masu kyau da muke mora daidai kima. (1 Korinthiyawa 10:31) A Aljannarsa ta duniya da ta yi kusa, za a sami lokaci marar iyaka na morar karimcin Jehobah sosai, tare da zumunta mai kyau na duka mutanen da suka cika farillansa na aminci.—Zabura 145:16; Ishaya 25:6; 2 Korinthiyawa 7:1.

Ka Tuna?

• Me ya sa yake da wuya a yau Kiristoci su sami nishaɗi mai kyau?

• Waɗanne irin nishaɗi ne suka kasance masu kyau ga iyalan Kiristoci?

• Sa’ad da ake moran nishaɗi mai kyau, waɗanne tunasarwa da kuma gargaɗi ne ya kamata a riƙa tunawa?

[Hoto a shafi na 20]

Ka zaɓi nishaɗin da ke ba da sakamako mai kyau

[Hotuna a shafi na 21]

Waɗanne irin nishaɗi ne Kiristoci suka ƙi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba