Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 1/15 pp. 22-26
  • Bauta Ba Tare da Yin Da-na-sani Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bauta Ba Tare da Yin Da-na-sani Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KURAKUREN DA BULUS YA YI
  • KANA YIN DA-NA-SANI?
  • KA TUNA DA NAN GABA
  • KADA KA YI DA-NA-SANI A HIDIMARKA
  • YADDA ZA KA GUJI YIN DA-NA-SANI
  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Yesu Ya Zabi Shawulu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 1/15 pp. 22-26

Ka Bauta wa Jehobah ba Tare da Yin Da-na-sani Ba

‘Ka manta da abubuwan da ke baya, kana kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba.’—FILIB. 3:13.

KA YI LA’AKARI DA WAƊANNAN MUHIMMAN TAMBAYOYIN:

  • Mene ne ya taimaka wa manzo Bulus ya sha kan yin nadama game da kurakuran da ya yi?

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi don mu samu kwanciyar rai?

  • Mene ne zai taimaka mana mu bauta wa Jehobah ba tare da yin nadama ba?

1-3. (a) Mene ne da-na-sani yake nufi, kuma yaya yin hakan zai iya shafanmu? (b) Wane misali ne Bulus ya kafa mana?

A YAWANCIN lokaci, mutane suna yin amfani da kalmar nan: “Da-na-sani” don nuna nadama. Da-na-sani yana nufin nuna baƙin ciki ko yin fushi don mun yi ko kuma ba mu yi wani abu ba. Dukanmu muna iya yin nadama. Amma, wasu sukan yi hakan sau da sau kuma sukan yi baƙin ciki sosai. Shin akwai abin da ke sa ka yin nadama?

2 Wasu mutane sun taɓa yin kuskure ko kuma aikata laifi mai tsanani a rayuwarsu. Wasu kuma suna ji kamar sun yi zaɓin da bai dace ba. Wasu sun shawo kan waɗannan matsalolin. Amma har ila, akwai waɗanda suke yin da-na-sani. (Zab. 51:3) Kai kuma fa? Kana son ka ci gaba da bauta wa Allah ba tare da yin da-na-sani ba domin kurakuran da ka taɓa yi? Shin akwai mutumin da za mu iya yin koyi da shi? Hakika, za mu iya yin koyi da manzo Bulus.

3 Bulus ya yi kurakurai masu tsanani da kuma zaɓi masu kyau a rayuwarsa. Kuma ya yi nadama sosai domin kurakuran da ya yi, amma daga baya, ya koyi cewa yana bukatar ya yi ƙoƙari sosai a hidimarsa ga Allah. Bari mu ga darussan da za mu koya daga misalinsa.

KURAKUREN DA BULUS YA YI

4. Me ya sa Bulus ya yi da-na-sani?

4 Sa’ad da Bulus yake saurayi da kuma Ba-farisi, ya yi abubuwan da suka sa shi yin nadama daga baya. Alal misali, ya tsananta wa almajiran Yesu sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce nan da nan bayan masu hamayya suka kashe Istifanus, sai Shawulu “ya ɓarnatar da ikklisiya, yana shiga kowane gida, yana jawo maza da mata, yana jefa su a kurkuku.” (A. M. 8:3) Wani masani mai suna Albert Barnes ya ce kalmar nan “ɓarnatar da” ta nuna cewa Shawulu ya kai wa ikilisiyar Kirista hari da hasala sosai kamar “dabbar daji.” Shawulu Ba-yahude ne mai ƙwazo sosai, kuma ya gaskata cewa nufin Allah ne ya halaka ikilisiyar Kirista baki ɗaya. Saboda haka, ya tsananta wa Kiristoci sosai kuma yana barazanar cewa zai karkashe dukan “mata da maza.”—A. M. 9:1, 2; 22:4.a

5. Me ya sa Shawulu ya daina tsananta wa mabiyan Yesu kuma ya soma wa’azi game da shi?

5 Shawulu yana kan hanya zuwa Dimaska ke nan don ya fid da Kiristoci daga gidajensu, kuma ya kai su Urushalima don majalisar Yahudawa ta hukunta su. Amma, bai cim ma burinsa ba domin yana gāba da Yesu shugaban ikilisiyar Kirista. (Afis. 5:23) Sai Yesu ya bayyana a gabansa, kuma haske daga sama ya makantar da shi. Bayan hakan, Yesu ya tura Shawulu ya je Dimaska don a gaya masa abin da yake bukatar ya yi. Mun san sauran labarin.—A. M. 9:3-22.

6, 7. Me ya nuna cewa Bulus ya san kurakurai masu tsanani da ya yi a dā?

6 Bulus ya fahimci cewa ya yi kuskure. Sai nan da nan ya daina tsananta wa almajiran Kristi, kuma ya soma wa’azi game da shi da ƙwazo sosai. Duk da haka, Bulus bai yi saurin mantawa da abubuwan da ya yi a dā ba. Ya ce: “Gama kun ji labarin irin rayuwan da na yi cikin addinin Yahudawa a dā, tsananta ikilisiyar Allah da na yi gaba da misali, niyyan in lalatar da ita.” (Gal. 1:13) Daga baya, ya ambata rayuwarsa ta dā a wasiƙun da ya rubuta wa Korintiyawa da Filibiyawa da kuma Timotawus. (Karanta 1 Korintiyawa 15:9; Filib. 3:6; 1 Tim. 1:13) Bulus bai buga ƙirji game da rayuwarsa ta dā ba, kuma bai yi da’awar cewa bai taɓa aikata waɗannan abubuwan ba. Ya san cewa ya yi kurakurai masu tsanani.—A. M. 26:9-11.

7 Wani manazarin Littafi Mai Tsarki mai suna Frederic W. Farrar ya rubuta cewa za mu iya sanin irin baƙin cikin da Bulus ya yi, idan muka yi tunanin yawan tsanantawar da ya yi wa Kiristoci. Ban da haka ma, wasu sun yi ta sūkarsa. Sa’ad da Bulus ya ziyarci ikilisiyoyi, wataƙila wasu ’yan’uwa da ba su taɓa ganinsa ba sun ce masa: ‘Wato, kai ne Bulus, wanda ke tsananta mana a dā ko?’—A. M. 9:21.

8. Yaya Bulus ya ji game da jin ƙai da ƙaunar da Jehobah da kuma Yesu suka nuna masa? Wane darasi ne hakan ya koya mana?

8 Duk da haka, Bulus ya fahimci cewa Allah ya yi masa alheri ta wajen ba shi gatan zama manzo. Ya ambata alherin Allah sau casa’in a cikin wasiƙunsa guda 14, kuma ya ambata hakan fiye da kowane marubucin Littafi Mai Tsarki. (Karanta 1 Korintiyawa 15:10.) Bulus ya yi godiya sosai domin jin ƙai da Allah ya nuna masa kuma ya so ya nuna hakan. Saboda haka, ya yi aiki tuƙuru fiye da sauran manzanni. Mene ne za mu iya koya daga misalinsa? Jehobah yana a shirye ya gafarta mana idan muka yi imani da hadayar fansa ta Yesu, kuma muka yi ikirarin zunubanmu ko da masu tsanani ne. Saboda haka, ka tuna da misalin Bulus idan kana ji kamar zunubanka sun yi tsanani sosai, da har hadayar fansa ta Kristi ba ta isa ta sa a gafarta maka ba. (Karanta 1 Timotawus 1:15, 16.) Ko da yake Bulus ya tsananta wa Kiristoci sosai, ya rubuta cewa: ‘Ɗan Allah . . . ya ƙaunace ni, ya ba da kansa kuma domina.’ (Gal. 2:20; A. M. 9:5) Hakika, Bulus ya koyi cewa yana bukatar ya yi hidimarsa da kyau, domin kada ya sake yin da-na-sani a nan gaba. Kai ma ka koyi wannan darasin kuwa?

KANA YIN DA-NA-SANI?

9, 10. (a) Me ya sa wasu Shaidu suke yin da-na-sani? (b) Me ya sa bai dace mu ci gaba da damuwa game da kurakuranmu na dā ba?

9 Shin akwai abubuwan da ka yi da ke sa ka yin da-na-sani? Kana ji kamar ka ɓata lokaci da kuma kuzarinka wajen yin abubuwan da ba su da muhimmanci? Ka taɓa aikata abin da ya jawo wa wasu lahani ne? Ko kuwa wataƙila kana jin cewa da so samu ne, da ba ka ɗauki matakin da ka ɗauka ba a dā. Mene ne za ka iya yi game da yadda kake ji?

10 Wasu mutane suna damuwa kullum game da kurakuransu. Irin wannan damuwar tana sa su alhini sosai. Amma, shin damuwa tana iya magance matsalar kuwa? Ko kaɗan! Yin hakan yana kama ne da yin ƙoƙarin cika ruwa a kwando. Za ka ɓata lokaci da kuma kuzarinka, amma kwandon ba zai taɓa cika ba. Maimakon ka riƙa damuwa, ka yi ƙoƙarin magance matsalar. Ka nemi gafara a wajen wanda ka yi wa laifi kuma ka yi ƙoƙarin kyautata dangantakarku. Ka yi tunanin yadda za ka hana hakan sake faruwa a nan gaba. Amma, ka san cewa akwai wasu kurakurai da sakamakonsu ba sa ƙarewa. Duk da haka, yin alhini ba zai taimaka maka ba. Maimakon haka, sai dai ya daɗa raunana ka kuma ba za ka iya bauta wa Allah da ƙwazo ba.

11. (a) Mene ne ya kamata mu yi don Jehobah ya nuna mana jin ƙai kuma ya ƙaunace mu? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi don mu daina alhini game da laifuffukanmu na dā?

11 Wasu mutane suna jin cewa ba su cancanci jin ƙan Allah ba, domin laifuffukan da suka yi a dā suna da tsanani sosai. Suna ganin cewa suna yawan yin laifuffuka ko laifuffukansu suna cika tsanani. Amma gaskiyar ita ce, za su iya tuba su yi canji kuma su nemi gafara. (A. M. 3:19) Jehobah zai nuna musu jin ƙai kuma ya ƙaunace su, kamar yadda ya yi wa mutane da yawa. Jehobah zai gafarta wa duk wanda yake da tawali’u da gaskiya kuma bai yi tuban mage ba. Alal misali, Allah ya gafarta wa Ayuba wanda ya ce: “Na tuba cikin ƙura da toka.” (Ayu. 42:6) Wajibi ne mu bi abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar don mu daina alhini game da kurakuranmu kuma mu samu kwanciyar rai. Ya ce: “Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: Amma dukan wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.” (Mis. 28:13; Yaƙ. 5:14-16) Muna bukatar mu yi ikirarin zunubanmu ga Allah, mu nemi gafara kuma mu ɗauki matakan da suka nuna cewa mun tuba da gaske. (2 Kor. 7:10, 11) Idan muka yi hakan, Jehobah wanda ke “gafara a yalwace” zai nuna mana jin ƙai.—Isha. 55:7.

12. (a) Idan lamirinmu yana damunmu, ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Dauda? (b) A wace hanya ce Jehobah ya tuba, kuma ta yaya sanin hakan zai iya taimaka mana? (Ka duba akwati.)

12 Addu’a hanya ce mai kyau da Allah zai iya taimaka mana. Dauda ya raira waƙar da ta nuna cewa ya gaskata cewa Jehobah ya amsa addu’arsa. (Karanta Zabura 32:1-5.) Kafin Dauda ya yi ikirarin zunubansa, lamirinsa ya yi ta damunsa. Hakan ya sa shi alhini da ciwo da kuma baƙin ciki. Amma, ya sami kwanciyar hankali sa’ad da ya yi ikirari ga Allah. Jehobah ya saurari Dauda kuma ya ƙarfafa shi. Ya kuma taimaka masa ya ci gaba da yin nufinsa. Hakazalika, idan ka yi addu’a da dukan zuciyarka kuma ka yi ƙoƙarin yin gyara, ka tabbata cewa Jehobah zai saurare ka kuma zai gafarta maka.—Zab. 86:5.

KA TUNA DA NAN GABA

13, 14. (a) Mene ne ya kamata ya fi muhimmanci a gare mu yanzu? (b) Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu yi la’akari da abin da muke yi da rayuwarmu yanzu?

13 Babu shakka, za mu iya koyon darussa daga abubuwan da suka faru a dā. Amma, bai kamata su riƙa damunmu ba. Saboda haka, ya kamata mu manta da dā, kuma mu mai da hankali ga yanzu da kuma nan gaba. Ka tambayi kanka: ‘Akwai abin da nake yi ko kuma ba na yi yanzu da zai sa in yi da-na-sani a nan gaba? Ina yin iya ƙoƙarina kuwa a bautar Jehobah don kada in yi nadama nan gaba?’

14 Ƙunci mai girma ya yi kusa fiye da dā. Kuma ba ma son mu soma da-na-sani sa’ad da ya auko, muna cewa, ‘Me ya sa ban daɗa ƙwazo sosai a hidimar Allah ba? Me ya sa ban yi hidimar majagaba ba sa’ad da na sami damar yin hakan? Me ya hana ni zama bawa mai hidima? Shin na yi ƙoƙari sosai wajen canja halayena? Shin iri na ne Jehobah yake so a sabuwar duniyarsa?’ Maimakon mu riƙa alhini game da waɗannan tambayoyin, ya kamata su taimaka mana mu daɗa ƙwazo sosai a hidimarmu ga Jehobah. Idan ba haka ba, za mu ci gaba da yin rayuwar da za ta sa mu yin da-na-sani a nan gaba.—2 Tim. 2:15.

KADA KA YI DA-NA-SANI A HIDIMARKA

15, 16. (a) Waɗanne sadaukarwa ne wasu suka yi don su bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinsu? (b) Me ya sa bai kamata mu yi da-na-sani ba don mun sadaukar da wasu abubuwa saboda hidimar Jehobah?

15 Shin ka sadaukar da abubuwa da yawa domin ka yi hidima ta cikakken lokaci? Wataƙila ka yi murabus da wani aiki ko kuma kasuwanci mai kawo riɓa sosai don ka ƙara ƙwazo a bautarka ga Jehobah. Ko kuma, wataƙila ka yanke shawara ka zama marar aure ko marar ’ya’ya don ka yi hidima a Bethel ko ka zama ɗaya cikin masu yin gine-gine a ƙasashe dabam dabam ko mai kula da da’ira ko kuma mai wa’azi a ƙasashen waje. Ya kamata ka yi nadama ne yanzu da ka daɗe kana yin wannan hidimar? Ko ya kamata ka ji cewa sadaukarwar da ka yi ba ta dace ba ko kuma ka yi hanzarin yinsu? Ko kaɗan!

16 Ka tsai da wannan shawarar domin kana ƙaunar Jehobah, kuma kana son ka taimaka wa mutane su bauta masa. Kada ka yi tunanin cewa da rayuwarka ta fi hakan ma’ana, da a ce ka biɗi wani abu dabam. Za ka yi farin ciki sosai idan ka san cewa zaɓin da ka yi na bauta wa Jehobah kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu. Jehobah ba zai taɓa mantawa da dukan sadaukarwar da ka yi ba. A nan gaba kuma, zai albarkace ka da abubuwan da suka ɗara na yanzu.—Zab. 145:16; 1 Tim. 6:19.

YADDA ZA KA GUJI YIN DA-NA-SANI

17, 18. (a) Mene ne Bulus ya yi don ya guji yin da-na-sani? (b) Ta yaya za ka bi misalin Bulus?

17 Mene ya taimaka wa Bulus ya bauta wa Jehobah ba tare da yin da-na-sani ba? Ya ce: “Ina manta da abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba.” (Karanta Filibiyawa 3:13, 14.) Bulus bai ci gaba da yin tunani a kan abubuwan da ya yi sa’ad da yake addinin Yahudawa ba. Maimakon haka, ya yi amfani da dukan kuzarinsa don yin hidimar da za ta sa ya sami rai na har abada.

18 Dukanmu za mu iya amfana daga kalaman Bulus. Bai kamata mu riƙa yin alhini game da abubuwan da suka faru a dā ba, domin ba za mu iya canja su ba. Amma, ya fi kyau mu mai da hankali ga abin da za mu iya yi yanzu don mu sami albarka a nan gaba. Ko da yake ba za mu iya daina tunani a kan waɗannan kurakuran ba, amma kada mu ƙyale su su riƙa damunmu. Za mu iya daina damuwa game da dā, mu bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinmu a yanzu, kuma mu yi tunani a kan albarkar da za mu more a nan gaba.

a Littafi Mai Tsarki ya ambata sau da sau cewa Shawulu ya tsananta wa mata. Hakan ya nuna cewa a ƙarni na farko, mata sun taka rawar a zo a gani a aikin wa’azi kamar yadda suke yi a yau.—Zab. 68:11.

A WACE HANYA CE JEHOBAH YA TUBA?

Littafi Mai Tsarki ya ambata sau da yawa cewa Jehobah ya “tuba.” (Yun. 3:10; Far. 6:6, 7; Alƙa. 2:18; 1 Sam. 15:11) Hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana kuskure, domin dukan ayyukansa kamiltattu ne. (Lit. Lis. 23:19; K. Sha 32:4) Maimakon haka, yana nufin cewa Jehobah yana canja ra’ayinsa domin wani yanayi ya canza. Alal misali, a zamanin dā, Jehobah ya hukunta wasu mutane domin muguntarsu. Amma, daga baya ya nuna musu jin ƙai kuma ya gafarta musu domin sun yi canje-canje, kuma sun soma yin nagarta.—Irm. 18:7-10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba