Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/1 p. 5
  • Musa—Mutumi Ne Mai Tawali’u

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Musa—Mutumi Ne Mai Tawali’u
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/1 p. 5

Musa Mutumi Ne Mai Tawali’u

MENE NE TAWALI’U?

Tawali’u yana nufin rashin girman kai ko fahariya, wato, sauƙin kai ke nan. Mutumi mai tawali’u ba ya ɗauka cewa wasu suna ƙasa da shi ba. Mutum mai tawali’u zai amince cewa yana da kasawa kuma akwai wasu abubuwan da ba zai iya yi ba.

TA YAYA MUSA YA NUNA TAWALI’U?

Musa bai yi fahariya ba sa’ad da ya sami matsayi. A yawancin lokaci, ana iya gane mai fahariya ko kuma mai tawali’u nan da nan idan ya sami mukami. Wani marubuci mai suna Robert G. Ingersoll ya ce: “Yawancin mutane suna iya jure wahala. Amma idan kana son ka san ainihin mai tawali’u, sai ka ba shi iko.” A wannan fannin, Musa ya kafa mana misali mai kyau. Ta yaya?

Jehobah ya ba Musa matsayi mai girma sa’ad da ya umurce shi ya ja-goranci Isra’ilawa. Amma hakan bai sa Musa fahariya ba. Alal misali, ka lura da yadda Musa ya nuna cewa yana da kasawa sa’ad da aka zo wurinsa ya yanke shari’a a kan batun gādo. (Littafin Lissafi 27:1-11) Wannan batun mai muhimmanci ne sosai, domin matakin da za a dauka zai kafa gurbi na yadda ya kamata a riƙa yanke shari’a a irin waɗannan batutuwa.

Mene ne Musa ya yi? Ya ɗauka cewa da yake shi ne shugaban Isra’ilawa, zai iya yanke shawarar da ta dace da kansa? Shin, zai yanke shawara ne kawai bisa iyawarsa ko ƙwarewarsa ko kuma ilimi da yake da shi game da Jehobah?

Da a ce Musa mai fahariya ne da ya yi hakan. Amma bai yi hakan ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Musa kuwa ya kawo da’awarsu a gaban Ubangiji.” (Littafin Lissafi 27:5) Ka yi la’akari da hakan! Duk da cewa ya yi shekaru 40 yana shugabancin Isra’ilawa, Musa ya dogara ga Jehobah, ba ga kansa ba. Abin da Musa ya yi a nan ya nuna cewa shi mai tawali’u ne da gaske.

Musa bai yi tunani cewa shi kaɗai ne ya kamata ya zama shugaba ba. Ya yi farin ciki sa’ad da Jehobah ya naɗa wasu daga cikin Isra’ilawa su zama annabawa. (Littafin Lissafi 11:24-29) Sa’ad da surukinsa ya ba shi shawara cewa ya zaɓi wasu mazaje da za su iya taimaka masa da aikinsa, Musa ya karɓi shawarar. (Fitowa 18:13-24) Kuma ko da yake yana da ƙarfinsa a lokacin da ya kusan mutuwa, Musa ya gaya wa Jehobah ya naɗa wani da zai gāje shi. Sa’ad da Jehobah ya zaɓi Joshua, Musa ya goyi bayan wannan matashi da dukan zuciyarsa, kuma ya umurce dukan Isra’ilawa su bi ja-gorar Joshua don su shiga Ƙasar Alkawari. (Littafin Lissafi 27:15-18; Kubawar Shari’a 31:3-6; 34:7) Hakika, yi wa Isra’ilawa ja-gora wajen bauta babban gata ne ga Musa. Duk da haka, bai ɗauki matsayinsa da muhimmanci fiye da taimakon mutane ba.

WAƊANNE DARUSSA NE ZA MU KOYA?

Bai kamata mu bar iko ko matsayi ko iyawa da muke da shi ya sa mu fahariya ba. Idan muna son mu yi wa Jehobah hidima a hanya da yake so, ya kamata mu tuna cewa nuna tawali’u ya fi gwaninta muhimmanci. (1 Sama’ila 15:17) Idan muna da tawali’u da gaske, za mu ƙoƙarta mu bi wannan shawara mai kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.”—Misalai 3:5, 6.

Misalin Musa ya kuma koya mana cewa bai kamata mu ɗauki matsayinmu ko ikonmu da muhimmanci fiye da yadda ya kamata ba.

Shin za mu amfana ne idan mun yi koyi da tawali’un da Musa ya nuna? Hakika! Idan mun kasance da tawali’u, mutane za su so zama tare da mu. Mafi muhimmanci kuma, Jehobah Allah wanda ke nuna wannan halin zai ƙaunace mu. (Zabura 18:35) “Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana ba da alheri ga masu-tawali’u.” (1 Bitrus 5:5) Wannan babban dalili ne na bin misalin Musa wajen nuna tawali’u, ko ba haka ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba