Kada Ka Ƙyale Kome Ya Hana Ka Samun Girma
“Mai-tawali’u za ya sami girma.”—MIS. 29:23.
1, 2. (a) Mene ne kalmar nan “girma” take nufi a Ibrananci? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?
ME KAKE tunawa sa’ad da ka ji kalmar nan “girma”? Kana tuna kyaun halittun Allah? A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “girma” a Ibrananci tana nufin abu mai nauyi. A ƙarni na farko, ana amfani da azurfa da zinariya don ƙera tsabar kuɗi. Nauyin wannan tsabar kuɗin ce ke nuna darajarta. Shi ya sa kalmar nan “girma” take nufin abu mai amfani ko kuma wanda ke burgewa sosai.
2 Mutane suna daraja waɗanda suke da iko ko kuma sanannu. Amma, littafin Misalai 22:4 ya gaya mana abin da zai sa Allah ya daraja mutum: “Ladar tawali’u da tsoron Ubangiji dukiya ne, da girma, da rai.” Almajiri Yaƙub ya ce: “Ku ƙasƙanta a gaban Ubangiji, shi kuwa za ya ɗaukaka ku.” (Yaƙ. 4:10) Wace girma ce Allah yake ba ’yan Adam? Mene ne zai iya hana mu samun wannan girmar? Kuma ta yaya za mu taimaka wa waɗansu su same ta?
3-5. Ta yaya Jehobah yake girmama mu?
3 Wani marubucin zabura ya gaskata cewa Jehobah zai girmama shi. (Karanta Zabura 73:23, 24.) Ta yaya Jehobah yake girmama mutane? Yana yin hakan ta wajen amincewa da kuma yi wa bayinsa masu biyayya albarka a hanyoyi masu yawa. Alal misali, yana taimaka musu su fahimci nufinsa. (1 Kor. 2:7) Kuma yana ba su gata su zama abokansa.—Yaƙ. 4:8.
4 Jehobah yana kuma girmama bayinsa da gatan yin wa’azin bishara. (2 Kor. 4:1, 7) Jehobah zai daraja mu idan muka more wannan gatan ta wajen yaba masa da kuma taimaka wa mutane. Kuma Jehobah ya yi mana alkawari cewa: “Waɗanda su ke girmamana, ni kuma zan girmama su.” (1 Sam. 2:30) Jehobah yana girmama waɗanda suka yi wannan aikin ta wajen ba su suna mai kyau, wato za su samu tagomashi a gabansa. ’Yan’uwa a cikin ikilisiya ma za su yaba musu.—Mis. 11:16; 22:1.
5 A nan gaba, mene ne zai faru da waɗanda suka yi biyayya ga Jehobah? Ya yi alkawari cewa: “[Jehobah] za ya ɗaukake ka ka gaji ƙasan: lokacinda an datse miyagu, ka gani.” (Zab. 37:34) Suna da begen yin rayuwa har abada. Babu girmar da ta kai wannan.—Zab. 37:29.
‘BA NA KARƁAR GIRMA DAGA MUTANE’
6, 7. Me ya sa mutane da yawa suka ƙi gaskata da Yesu?
6 Mene ne zai iya hana mu samun girmar da Jehobah yake bayarwa? Wani abin da zai sa hakan ya faru shi ne, idan muna bin ra’ayin waɗanda ba su da dangantaka mai kyau da Jehobah. Abin da ya faru da wasu masu sarauta ke nan a zamanin Yesu. Manzo Yohanna ya ce game da su: “Har cikin hakimai mutane dayawa suka bada gaskiya gareshi; amma saboda Farisawa ba su shaida shi ba, domin kada a fitarda su daga cikin majami’a: gama suka fi son girma wurin mutane da girman Allah.” (Yoh. 12:42, 43) Da waɗannan sarakunan sun amfani kansu da a ce ba su saurari koyarwar Farisawa ba.
7 Yesu ya bayyana sarai, abin da zai sa mutane da yawa ba su gaskata cewa shi ne Almasihu ba. (Karanta Yohanna 5:39-44.) Isra’ilawa sun daɗe sosai suna jiran Almasihu. Sa’ad da Yesu ya soma koyarwa, wataƙila wasu mutane sun tuna da annabcin da Daniyel ya yi cewa Almasihun ya kusan zuwa. Watanni da suka gabata, mutane da yawa sun ma ɗauka cewa Yohanna mai Baftisma ne Almasihu. (Luk 3:15) Amma, sa’ad da Almasihun ya zo, malaman addinai ba su gaskata da shi ba. Me ya sa? Yesu ya bayyana dalilin a tambayar da ya yi: “Ƙaƙa za ku iya bada gaskiya, ku da ku ke karɓan daraja daga wurin junanku, daraja kuwa wadda tana fitowa daga wurin Allah makaɗaici ba ku neme ta ba?”
8, 9. Ta yaya misalin haske, ya nuna cewa neman girma daga mutane zai iya hana Jehobah girmama mu?
8 Idan muka kwatanta girma da haske, za mu fahimci yadda karɓan girma daga mutane zai hana Jehobah girmama mu. Sararin sama yana cike da haske. Za ka iya tuna daren da ka fita waje kuma ka kalli dubban taurari da ke sarari? Babu shakka, ‘daraja ta taurari’ ta sa ka mamaki sosai. (1 Kor. 15:40, 41) Amma, idan mutum yana zama a birni mai cike da hasken wutar lantarki, da kyar zai iya ganin taurari. Me ya sa? Ba domin haske daga gidaje da kuma tituna sun fi taurari haske ko kyau ba, amma domin sun fi kusa da mu. Shi ya sa yake hana mu ganin kyaun taurari. Idan muna son mu gan hasken taurari, wajibi ne mu je inda babu wutar lantarki.
9 Hakanan ma samun girma daga mutane, zai iya hana mu daraja girmar da Jehobah yake bayarwa. Mutane da yawa suna ƙin bishara domin suna tsoron yadda dangi ko kuma abokansu za su ɗauke su. Amma, shin hakan zai iya faruwa da bayin Jehobah kuwa? Ƙwarai kuwa. Alal misali, a ce wani matashi ya fita wa’azi a inda aka waye shi sosai, amma ba a matsayin Mashaidi ba. Zai ƙyale tsoro ya hana shi wa’azi ne? Ko kuma a ce wani yana son ya daɗa ƙwazo a hidimarsa ga Jehobah, amma wasu suna masa ba’a domin maƙasudansa. Shin zai saurare waɗannan da ba su ɗauki hidimarsu ga Jehobah da muhimmanci ba? Ko kuwa, a ce wani Kirista ya yi zunubi mai tsanani. Shin zai ɓoye zunubinsa ne domin ba ya son ya rasa gatansa a cikin ikilisiya, ko kuma domin yana tsoron ɓata wa dangi ko abokansa rai? Idan yana son ya kyautata dangantakarsa da Jehobah, zai “kira dattiɓan ikilisiya” don su taimaka masa.—Karanta Yaƙub 5:14-16.
10. (a) Me zai iya faruwa idan muna damuwa ainun game da yadda wasu suke ɗaukanmu? (b) Wane tabbaci ne muke da shi idan muka zama masu tawali’u?
10 Wataƙila kana ƙoƙari ka manyanta a matsayin Kirista, amma wani ɗan’uwa yana yawan yi maka gyara. Za ka iya amfana daga shawararsa idan ka kasance da tawali’u, ka ƙi neman hujja da kuma tunanin cewa za a ɓata maka suna. Ko kuwa, a ce kai da ’yan’uwa kuna wani aiki tare. Za ka riƙa damuwa cewa za a yaba wa wani dabam, bayan kai ne ka fi yin aikin? Idan kana cikin irin wannan yanayin, ka tuna cewa “mai-tawali’u za ya sami girma.”—Mis. 29:23.
11. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da aka yaba mana, kuma me ya sa?
11 Ya kamata dattawa da kuma ’yan’uwa maza da suke burin samun gata a cikin ikilisiya, su yi hattara don kada su soma neman daraja daga mutane. (1 Tim. 3:1; 1 Tas. 2:6) Mene ne ya kamata ɗan’uwa ya yi sa’ad da aka yaba masa don abin da ya cim ma? Hakika, ba zai gina wa kansa umudi ba kamar Sarki Saul. (1 Sam. 15:12) Amma, shin ya nuna cewa Jehobah ne ya taimaka masa ya cim ma abin da ya yi, kuma shi ne zai iya sa ya yi nasara a nan gaba? (1 Bit. 4:11) Yadda muke ji sa’ad da aka yaba mana zai nuna ko wace irin girma ce muke so.—Mis. 27:21.
KUNA SON KU AIKATA SHA’AWOYI “NA UBANKU”
12. Me ya sa wasu Yahudawa suka ƙi saurarar Yesu?
12 Wani abin da zai iya hana Jehobah girmama mu shi ne sha’awoyi marasa kyau. Waɗannan sha’awoyin suna iya hana mu saurarar gaskiya. (Karanta Yohanna 8:43-47.) Yesu ya gaya wa wasu Yahudawa cewa ba su saurari saƙonsa ba domin suna da nufin su yi ‘ƙyashe ƙyashe na ubansu’ Shaiɗan.
13, 14. (a) Mene ne masu bincike suka ce game da ƙwaƙwalwa da kuma muryarmu? (b) Mene ne ke sa mu zaɓi wanda za mu saurara?
13 A wasu lokatai, muna jin abin da muke son mu ji ne kaɗai. (2 Bit. 3:5) Mukan yi kunnen uwar shegu ga wasu ƙara, domin yadda Jehobah ya halicce ƙwaƙwalwarmu. Ka ɗan dakata, ka yi tunani a kan ire-iren ƙarar da za ka iya ji yanzu. Wataƙila, ba za ka iya tuna da wasunsu ba. Me ya sa? Domin ko da yake ƙwaƙwalwarka ce take sa ka saurari ire-iren ƙara, tana taimaka maka ka fi mai da hankali ga iri guda. Amma, masu bincike sun ce ba zai yiwu mu saurari mutane biyu a lokaci ɗaya ba. Hakan yana nufin cewa idan mutane biyu suna magana da kai, dole ne ka zaɓi wanda za ka saurare shi. Kuma wanda ka fi so ne za ka zaɓa. Yahudawa sun fi son su aikata nufin ubansu Iblis, shi ya sa ba su saurari Yesu ba.
14 A alamance, Littafi Mai Tsarki ya ce “hikima” da kuma ‘rashin wayo’ suna son mu saurare su. (Mis. 9:1-5, 13-17) Amma, muna da zaɓi. Za mu zaɓi hikima ne ko kuwa rashin wayo? Zaɓin ya dangana ga wanda muke son mu faranta masa rai. Idan mu tumakin Yesu ne, za mu ji muryarsa kuma za mu bi gurbinsa. (Yoh. 10:16, 27) Yesu ya ce tumakinsa suna bin “gaskiya.” (Yoh. 18:37) Kuma “ba su san muryar baƙi ba.” (Yoh. 10:5) Jehobah yana girmama irin waɗannan masu tawali’u.—Mis. 3:13, 16; 8:1, 18.
‘WANNAN KUWA DARAJARKU CE’
15. Me ya sa Bulus ya ce tsananin da yake sha daraja ce ga Afisawa?
15 Idan muka dage a yin nufin Jehobah, za mu ƙarfafa ’yan’uwa kuma hakan zai sa ya girmama su. Bulus ya rubuta wa ikilisiyar da ke Afisa: “Ina roƙo kada ku yi suwa saboda tsananin da na ke sha dominku; wannan kuwa darajarku ne.” (Afis. 3:13) Me ya sa Bulus ya ce tsananin da ya sha daraja ce ga Afisawa? Domin Bulus ya ci gaba da yi wa ’yan’uwansa hidima duk da tsanantawa, kuma hakan ya nuna musu cewa ya kamata bauta wa Jehobah ta fi muhimmanci ga Kirista. Da a ce Bulus bai jimre da tsanantawa ba, da ’yan’uwa sun soma ganin cewa dangantakarsu da Jehobah da hidimarsu da kuma begensu ba su da wani muhimmanci. Ta wajen jimirinsa, ya nuna musu cewa zama mabiyin Kristi kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu.
16. Mene ne ya faru da Bulus a Listra?
16 Ka yi tunanin yadda misalin ƙwazo da kuma jimirin Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwa. Ayyukan Manzanni 14:19, 20 ya ce: “Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya: sa’anda suka rinjayi taro, suka jejjefe Bulus, suka janye shi bayan birni [Listra], tsammani su ke yi ya mutu. Amma sa’anda masu-bi suka kewaye shi, ya tashi, ya shiga cikin birni; washegari ya fita tare da Barnaba, suka tafi Darba.” Yaya kake ganin Bulus ya ji sa’ad da ya yi tafiyar mil 60 a kafa bayan dūkan-kawo-wuƙa da aka yi masa?
17, 18. (a) Ta yaya Timotawus ya san da wahalar da Bulus ya sha? (b) Ta yaya jimrewar da Bulus ya yi ya taimaki Timotawus?
17 Ina Timotawus yake sa’ad da aka jejjefi Bulus? Wataƙila yana wajen. Amma littafin Ayyukan Manzanni bai gaya mana ba. Duk da haka, Timotawus ya san abin da ya faru. Bulus ya gaya masa a wasiƙarsa ta biyu cewa: “Ka bi koyarwata, da tasarrufina . . . irin al’amuran da suka same ni cikin Antakiya [an kore shi daga birnin], da Ikoniya [an kusan jejjefe shi], da Listra [an jejjefe shi], irin tsanani da na jimre: daga cikinsu duka fa Ubangiji ya cece ni.”—2 Tim. 3:10, 11; A. M. 13:50; 14:5, 19.
18 Timotawus ya san cewa Bulus ya jimre da dukan waɗannan wahalolin. Babu shakka, ya koyi darasi daga misalin Bulus. Sa’ad da Bulus ya ziyarci Listra, ya sami labarin cewa Timotawus yana kafa misali mai kyau a cikin ikilisiya, kuma “’yan’uwa da ke cikin Listra da Ikoniya suna shaidarsa.” (A. M. 16:1, 2) Daga baya Timotawus ya ƙware, kuma ya samu ƙarin gata.—Filib. 2:19, 20; 1 Tim. 1:3.
19. Ta yaya yadda muke jimrewa zai shafi ’yan’uwa?
19 Idan muka ci gaba da bauta wa Jehobah, misalinmu zai taimaka wa ’yan’uwa musamman ma matasa su zama bayin Allah masu tamani sosai. Matasa suna yin koyi da yadda muke yi wa mutane wa’azi, amma sun fi amfana daga yadda muke bi da matsaloli a rayuwa. Bulus ya ce ya ‘daure da dukan abu’ don ya taimaka wa mutane su sami rai na har abada.—2 Tim. 2:10.
20. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da neman girma daga Allah?
20 Muna da dalilai masu kyau na ci gaba da biɗan girma “wadda tana fitowa daga wurin Allah.” (Yoh. 5:44; 7:18) Jehobah yana ba da “rai na har abada” ga waɗanda ke biɗan girma. (Karanta Romawa 2:6, 7.) Ban da haka ma, za mu taimaka wa ’yan’uwa su riƙe imaninsu idan muka ci gaba da jimrewa. Saboda haka, kada ka ƙyale kome ya hana ka samun girma daga Allah.