Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 9/1 pp. 9-14
  • Kiristoci Ku Nuna Ɗaukakar Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kiristoci Ku Nuna Ɗaukakar Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zarafin da ba a Yi Amfani da Shi Ba
  • Abin da Ya Sa Bishara Take a Rufe
  • “Ganin Wannan da Ba Ya Ganuwa”
  • Za Ka Nuna Ɗaukakar Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kana Nuna Ɗaukakar Jehobah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Kada Ka Ƙyale Kome Ya Hana Ka Samun Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 9/1 pp. 9-14

Kiristoci Ku Nuna Ɗaukakar Jehobah

“Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.”—MATIYU 13:16.

1. Wace tambaya ce take faɗowa a zuciyarmu game da abubuwan da Isra’ilawa suka yi wa Musa a Dutsen Sinai?

ISRA’ILAWAN da suka taru a ƙarƙashin Dutsen Sinai suna da kyakkyawan dalili na kusantar Jehobah. Ballantana ma, ya cece su daga hannun Masarawa da ƙarfinsa. Ya kula da bukatunsu, ya ba su abinci da ruwa a cikin jeji. Bayan haka, ya sa su ci nasara bisa rundunar yaƙin Amalekawan da suka kai musu hari. (Fitowa 14:26-31; 16:2–17:13) Sa’ad da suka taru a jeji a gaban Dutsen Sinai, mutanen sun ji tsoron tsawa da walƙiyoyi har suka yi rawan jiki. Bayan haka, sun ga Musa yana sauƙowa daga kan Dutsen Sinai, kuma fuskarsa tana nuna ɗaukakar Jehobah. Duk da haka, maimakon su nuna godiya, sai suka ja da baya. Sun ji ‘tsoro su kusaci [Musa].’ (Fitowa 19:10-19; 34:30) Me ya sa suka ji tsoron ganin ɗaukakar Jehobah, wanda ya yi musu abubuwa masu yawa?

2. Me ya sa Isra’ilawa suka ji tsoron ganin ɗaukakar Allah da Musa ya nuna?

2 Wataƙila, Isra’ilawa sun ji tsoro ne domin abin da ya faru a dā. Sa’ad da suka yi wa Jehobah rashin biyayya ta wajen yin gunkin ɗan maraƙi, ya yi musu horo. (Fitowa 32:4, 35) Sun yi koyi da horon da Jehobah ya yi musu kuma sun nuna godiya kuwa? Yawancinsu sun ƙi yin haka. Kusan ƙarshen rayuwarsa, Musa ya tuna wa Isra’ilawa batun gunkin ɗan maraƙin da kuma rashin biyayyar da suka yi. Ya gaya wa mutanen: “Sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba. Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.”—Maimaitawar Shari’a 9:15-24.

3. Menene Musa ya yi game da lulluɓe fuskarsa da yake yi?

3 Yi la’akari da abin da Musa ya yi game da tsoron da Isra’ilawa suka ji. Labarin ya ce: “Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. Amma duk lokacin da ya je [cikin mazauni a] gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama’ar Isra’ila abin da aka umarce shi. Jama’ar Isra’ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa’an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.” (Fitowa 34:33-35) Me ya sa Musa ke lulluɓe fuskarsa a wasu lokatai? Menene za mu koya daga wannan? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su iya taimaka mana mu auna dangantakarmu da Jehobah.

Zarafin da ba a Yi Amfani da Shi Ba

4. Wane ma’ana ne manzo Bulus ya bayyana game da lulluɓin da Musa ya yi?

4 Manzo Bulus ya bayyana cewa Musa yana lulluɓe fuskarsa ne domin yanayin zuciya da hankalin Isra’ilawan. Bulus ya rubuta: “Isra’ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta . . . hankalinsu ya dushe.” (2 Korantiyawa 3:7, 14) Wannan yanayi ne mai sa baƙin ciki! Isra’ilawan zaɓaɓɓun mutanen Jehobah ne, kuma yana so su kusance shi. (Fitowa 19:4-6) Duk da haka, ba sa son su duba hasken ɗaukakar Jehobah. Sun bauɗe wa Jehobah maimakon su mai da hankalinsu da zuciyarsu ga Jehobah a cikin bauta ta ƙauna.

5, 6. (a) Ta yaya Yahudawa na ƙarni na farko suka yi kama da Isra’ilawa na zamanin Musa? (b) Wane bambanci ke akwai tsakanin waɗanda suka saurari Yesu da waɗanda suka ƙi sauraronsa?

5 Mun ga makamancin wannan a ƙarni na farko A.Z. A lokacin da Bulus ya zama Kirista, an sauya Dokar alkawari da sabuwar alkawari, da Yesu Kristi, Musa Babba ya ƙafa. Yesu ya nuna kamiltaccen ɗaukakar Jehobah ta wurin ayyuka da kalamai. Bulus ya rubuta game da Yesu da aka ta da daga matattu: “Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa.” (Ibraniyawa 1:3) Yahudawa sun sami dama mafi kyau! Za su iya saurarar kalamai na rai madawwami daga Ɗan Allah! Abin baƙin ciki, yawancin waɗanda Yesu ya yi wa wa’azi ba su saurare shi ba. Game da su, Yesu ya yi ƙaulin annabcin Jehobah ta bakin Ishaya: “Zuciyar jama’an nan ta yi kanta, sun toshe kunnuwansu, sun kuma runtse idanunsu, wai don kada su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su kuma fahimta a zuciyarsu, har su juyo gare ni in warkar da su.’ ”—Matiyu 13:15; Ishaya 6:9, 10.

6 Da bambanci tsakanin Yahudawa da almajiran Yesu, wanda Yesu ya ce game da su: “Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.” (Matiyu 13:16) Kiristoci na gaskiya suna ɗokin sani da kuma bauta wa Jehobah. Suna son yin nufinsa, kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. Shafaffun Kiristoci suna haskaka ɗaukakar Jehobah a hidimarsu ta sabuwar alkawari, kuma waɗansu tumaki suna yin haka.—2 Korantiyawa 3:6, 18.

Abin da Ya Sa Bishara Take a Rufe

7. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa yawancin mutane sun ƙi bishara?

7 Kamar yadda muka gani, a zamanin Yesu da Musa, yawancin Isra’ilawa sun yi watsi da dama mafi muhimmanci da suka samu. Haka yake a zamaninmu. Yawancin mutane sun ƙi bisharar da muke wa’azinta. Wannan ba abin mamaki ba ne a gare mu. Bulus ya rubuta: “Ko da bishararmu a rufe take, ai, ga waɗanda suke hanyar halaka kaɗai take a rufe. Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu.” (2 Korantiyawa 4:3, 4) Ƙari ga ƙoƙarin da Shaiɗan yake yi na rufe bisharar, yawancin mutane sun rufe fuskarsu domin ba sa son su gani.

8. A wace hanya ce jahilci ya makantar da yawancin mutane, kuma ta yaya za mu iya kauce wa hakan?

8 Idanu na alama na yawancin mutane sun makance domin jahilci. Littafi Mai Tsarki ya ce game da al’ummai, “duhun zuciya gare su, bare suke ga rai wanda Allah ke bayarwa, sabili da jahilcin da ke gare su.” (Afisawa 4:18) Kafin ya zama Kirista, Bulus, wanda mutum ne da ya san Doka sosai, jahilci ya makantar da shi har ya tsananta wa ikilisiyar Allah. (1 Korantiyawa 15:9) Duk da haka, Jehobah ya bayyana masa gaskiya. Bulus ya yi bayani: “An yi mini jinƙai musamman don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yā nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.” (1 Timoti 1:16) Kamar Bulus, yawancin mutanen da suke hamayya da gaskiyar Allah a dā, suna bauta masa a yanzu. Wannan shi ne kyakkyawan dalilin da ya sa za mu ci gaba da yin wa’azi har ga waɗanda suke yi mana hamayya. Amma, idan muka yi nazarin Kalmar Allah a kai a kai kuma muka fahimce ta, za mu sami kāriya daga aikatawa cikin jahilci wanda hakan na iya kai wa ga ɓata wa Jehobah rai.

9, 10. (a) Ta yaya ne Yahudawa na ƙarni na farko suka kasance da tsattsauran ra’ayi kuma suka nuna cewa ba sa son koyi? (b) Akwai makamancin haka a Kiristendom a yau kuwa? Ka yi bayani.

9 Yawancin mutane ba su fahimci batutuwa na ruhaniya ba, domin ba sa son a koya musu kuma suna da tsattsauran ra’ayi. Yawancin Yahudawa sun ƙi Yesu da koyarwarsa domin sun liƙe wa Dokar Musa. Amma akwai waɗanda suka bambanta. Alal misali, bayan an ta da Yesu daga matattu, “firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na’am da bangaskiyan.” (Ayyukan Manzanni 6:7) Duk da haka, game da yawancin Yahudawa, Bulus ya rubuta: “Har ya zuwa yau, duk lokacin da ake karatun littattafan Musa, sai mayafin nan yakan rufe zukatansu.” (2 Korantiyawa 3:15) Bulus ya san abin da Yesu ya taɓa gaya wa shugaban addinai na Yahudawa: “Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne ke shaidata.” (Yahaya 5:39) Ya kamata Nassosin da suke duba wa ya taimaka musu su fahimci cewa Yesu shi ne Almasihu. Amma, Yahudawan suna da nasu ra’ayin, har ma ayyukan mu’ujiza da Ɗan Allah ya yi bai motsa su ga ba da gaskiya ba.

10 Haka yake game da Kiristendom a yau. Kamar Yahudawa na ƙarni na farko, “suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba.” (Romawa 10:2) Ko da yake wasu suna nazarin Littafi Mai Tsarki, ba sa son su gaskata abin da ya ce. Sun ƙi su yarda cewa Jehobah yana koya wa mutanensa ta wurin amintaccen bawansa mai hikima na shafaffun Kiristoci. (Matiyu 24:45) Mun fahimci cewa Jehobah yana koya wa mutanensa kuma fahimtar hurarriyar gaskiya tana ƙara ci gaba. (Karin Magana 4:18) Ta wajen ƙyale Jehobah ya koyar da mu, muna samun albarkacin saninsa da kuma manufarsa.

11. Yaya gaskata abin da mutum yake son ya gaskata yake rufe gaskiya?

11 Wasu kuma sun makance ne domin sun gaskata abin da suke son su gaskata. An annabta cewa wasu za su yi wa mutanen Allah ba’a da kuma saƙon da suke sanarwa game da bayyanuwar Yesu. Manzo Bitrus ya rubuta: “Da gangan suke goce wa maganan nan,” cewa Allah ya kawo rigyawa a zamanin Nuhu. (2 Bitrus 3:3-6) Hakazalika, yawancin mutane masu da’awar cewa su Kiristoci ne, sun yarda cewa Jehobah yana nuna jinƙai, alheri, yana gafartawa; duk da haka, sun yi watsi da cewa ba ya ’yantarwa daga horo. (Fitowa 34:6, 7) Kiristoci na gaskiya suna mai da hankali domin su fahimci ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ke koyarwa.

12. Ta yaya ne al’ada ta makantar da mutane?

12 Al’ada ta makantar da yawancin masu zuwa coci. Ga shugabannin addinai na zamaninsa, Yesu ya ce: “Saboda al’adunku kun banzanta maganar Allah.” (Matiyu 15:6) Yahudawa sun mai da bauta ta gaskiya da himma sa’ad da suka dawo daga zaman bauta a Babila, duk da haka, firistocin sun zama masu fariya da adalcin kai. Idodi na addini sun zama abin yi kawai, wanda hakan ba ya ɗaukaka Allah. (Malakai 1:6-8) A zamanin Yesu, malaman attaura da Farisawa sun daɗa al’adu masu yawa ga Dokar Musa. Yesu ya fallasa su kuma ya kira su munafukai domin sun kasa fahimtar mizanai masu aminci da aka kafa Dokar a kansu. (Matiyu 23:23, 24) Dole ne Kiristoci na gaskiya su kula kada al’adun addinai na mutane su janye su daga tsarkakkiyar bauta.

“Ganin Wannan da Ba Ya Ganuwa”

13. A waɗanne hanyoyi biyu ne Musa ya ga ɗaukakar Allah?

13 Musa ya yi roƙo cewa yana son ganin ɗaukakar Allah a kan dutse, kuma ya ga ƙyalli na ɗaukakar Jehobah. Sa’ad da ya shiga cikin mazauni, bai lulluɓe fuskarsa ba. Musa mutum ne mai cikakken bangaskiya wanda ke son yin nufin Allah. Ko da yake ya sami albarkacin ganin wasu ɗaukakar Jehobah a wahayi, a azanci, ya ga Allah da idanun bangaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce Musa ya “jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa.” (Ibraniyawa 11:27; Fitowa 34:5-7) Kuma ya nuna ɗaukakar Allah ba kawai ta ƙyallin da ke fita daga fuskarsa ba na ɗan lokaci, amma ta wurin ƙoƙarinsa na taimaka wa Isra’ilawa su sani kuma su bauta wa Jehobah.

14. Ta yaya ne Yesu ya ga ɗaukakar Allah, kuma menene yake son yi?

14 A sama, Yesu ya ga ɗaukakar Allah kai tsaye na shekaru aru-aru, har ma kafin a halicci sararin samaniya. (Karin Magana 8:22, 30) A wannan lokacin, Jehobah da Yesu sun ƙulla zurfafan ƙauna da dangantaka mai kyau da juna. Jehobah Allah ya nuna ƙauna ta gaskiya ga wannan ɗan fari na dukan halitta. (Karin Magana 8:30) Yesu ma zai yi haka ta wajen nuna zurfafan ƙaunarsa ga Mai Ba da Rai. (Yahaya 14:31; 17:24) Ƙaunar da ke tsakanin Uban da Ɗansa kamiltacciya ce. Kamar Musa, Yesu yana son nuna ɗaukakar Jehobah a abubuwan da yake koyarwa.

15. A wace hanya ce Kiristoci suke tunani game da ɗaukakar Allah?

15 Kamar Musa da Yesu, Shaidun Allah na zamani da ke duniya suna ɗokin yin tunani a kan ɗaukakar Jehobah. Ba su ƙi wannan bisharar ta ɗaukaka ba. Manzo Bulus ya rubuta: “Da zarar mutum ya juyo ga Ubangiji [domin yin nufinsa], akan yaye masa mayafin.” (2 Korantiyawa 3:16) Muna nazarin Nassosi domin muna so mu yi nufin Allah. Muna yaba wa ɗaukakar da Ɗan Jehobah kuma shafaffen Sarki, Yesu Kristi yake nunawa, kuma muna yin koyi da misalinsa. Kamar Musa da Yesu, an albarkace mu da hidima, na koya wa wasu game da Allah mai ɗaukaka da muke bauta wa.

16. Ta yaya muke amfana don sanin gaskiya?

16 Yesu ya yi addu’a: “Na gode maka ya Uba, . . . domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.” (Matiyu 11:25) Jehobah yana ba masu tawali’u da kuma sahihai fahimi game da manufofinsa da mutuntakarsa. (1 Korantiyawa 1:26-28) Muna ƙarƙashin kāriyarsa, kuma yana koyar da mu domin mu amfane kanmu, wato, mu more rayuwarmu sosai. Bari mu yi amfani da kowane dama domin mu kusanci Jehobah, kuma mu nuna godiya ga tanadinsa domin saninsa sosai.

17. Ta yaya muka san halayen Jehobah sosai?

17 Bulus ya rubuta wa shafaffun Kiristoci: “Mu dukanmu kuma fuska ba lulluɓi muke nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa.” (2 Korantiyawa 3:18) Ko begenmu na sama ne ko duniya, idan muka san Jehobah sosai, halayensa, da mutuntakarsa kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki, ƙaunarmu a gare shi za ta ƙaru. Idan cikin godiya muka yi tunani game da rayuwa, hidima, da koyarwar Yesu Kristi, za mu nuna halayen Jehobah sosai. Abin farin ciki ne sanin cewa muna sa ana yabon ga Allahnmu, wanda muke nuna ɗaukakarsa!

Ka Tuna?

• Me ya sa Isra’ilawa suka ji tsoron ganin ɗaukakar Allah da Musa ya nuna?

• A waɗanne hanyoyi ne bishara take a “rufe” a ƙarni na farko? da kuma a zamaninmu?

• Ta yaya ne muke nuna ɗaukakar Allah?

[Hoto a shafi na 9]

Isra’ilawa sun kasa kallon fuskar Musa

[Hotuna a shafi na 11]

Kamar Bulus, yawancin mutanen da dā suke yi wa gaskiyar Allah hamayya, suna bauta masa yanzu

[Hotuna a shafi na 13]

Bayin Jehobah suna son nuna ɗaukakar Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba