Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/1 pp. 4-5
  • Yesu Ya Koya Mana Yadda Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Koya Mana Yadda Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Waɗanne Irin Halaye Ne Yesu Yake da Su?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • ‘Ɗan Yana A Shirye ya Bayyana Uban’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yadda Yesu Ya Ɗaukaka Adalcin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/1 pp. 4-5

Yesu Ya Koya Mana Yadda Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana

YESU ya yi rayuwa mai ma’ana kuwa da gaske? Iyayensa ba masu arziki ba ne kuma a duk rayuwarsa bai mallaki abubuwa da yawa ba. Bai kasance da gidan kansa ba don Littafi Mai Tsarki ya ce ba ya da “wurin da za ya sa kansa.” (Luka 9:57, 58) Ban da haka ma, an ƙi shi, an tsegunta shi kuma a ƙarshe magabtansa suka kashe shi.

Wataƙila za ka ce, ‘Ai wannan ba rayuwa mai ma’ana ba ce!’ Amma akwai wasu abubuwa game da rayuwar Yesu da ya kamata mu bincika. Bari mu tattauna abubuwa huɗu daga cikinsu.

1. RAYUWAR YESU TA KASANCE DA MANUFA, WATO, YIN NUFIN ALLAH.

“Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.”—Yohanna 4:34.

Ta kalamansa da kuma ayyukansa, Yesu ya nuna cewa burinsa shi ne ya yi nufin Jehobah, Ubansa na sama.a Yin nufin Allah ya sa Yesu farin ciki sosai. Yesu ya kwatanta yin nufin Allah da abinci, kamar yadda aka nuna a ayar da aka yi ƙaulinta a baya. Bari mu bincika abin da ya sa Yesu ya yi wannan maganar.

Yesu ya yi wannan magana da rana ne. (Yohanna 4:6) Babu shakka, Yesu ya soma takawa zuwa Samariya tun da safe kuma Samariya birni ne mai tuddai sosai. Saboda haka, ya ji yunwa sosai. Shi ya sa almajiransa suka gaya masa: ‘Rabbi, ka ci abinci.’ (Yohanna 4:31) Amsar da Yesu ya bayar ta nuna cewa ya sami gamsuwa da kuma ƙarfafa a yin nufin Allah. Wannan ya nuna cewa rayuwarsa ta kasance da ma’ana, ko ba haka ba?

2. YESU YA ƘAUNACI UBANSA SOSAI.

“Ina ƙaunar Uba.”—Yohanna 14:31.

Yesu ya kasance da dangantaka mai kyau da Ubansa na sama. Yadda Yesu ya ƙaunaci Ubansa ya sa ya sanar wa mutane sunan Ubansa da nufinsa da kuma halayensa. Ta furucinsa, ayyukansa da kuma halinsa, Yesu ya nuna cewa ra’ayinsa ya zo ɗaya da na Ubansa sosai, kuma saboda haka a duk lokacin da muka karanta wani abu game da Yesu, kamar dai muna koyan wani abu game da Ubansa ne. Shi ya sa a lokacin da Filibus ya gaya wa Yesu: “Ka nuna mana Uban,” sai Yesu ya ce masa: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”—Yohanna 14:8, 9.

Yesu ya ƙaunaci Ubansa sosai har ya yarda ya mutu domin yana son ya yi masa biyayya. (Filibiyawa 2:7, 8; 1 Yohanna 5:3) Yadda Yesu ya ƙaunaci Ubansa kamar yadda aka kwatanta a baya ne ya sa rayuwarsa ta kasance da ma’ana.

3. YESU YA ƘAUNACI MUTANE.

“Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya ba da ransa domin abokansa.”—Yohanna 15:13.

Da yake mu ajizai ne, ba mu da begen yin rayuwa har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Domin wannan fa, kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Babu ɗan Adam da zai iya kāre kansa daga sakamakon zunubi, wato, mutuwa.—Romawa 6:23.

Muna godiya ga Jehobah domin tanadin da ya yi na magance sakamakon zunubi. Ya bar Yesu, Ɗansa marar aibi, ya sha wahala kuma ya mutu domin ya fanshi ’yan Adam daga zunubi da mutuwa. Yadda Yesu ya ƙaunaci Ubansa da kuma ’yan Adam ne ya sa ya ba da ransa don ya ’yantar da mu. (Romawa 5:6-8) Irin wannan ƙauna ta sa rayuwarsa ta kasance da ma’ana.b

4. YESU YA SAN CEWA UBANSA YA AMINCE DA SHI KUMA YANA ƘAUNARSA.

“Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.”—Matta 3:17.

Jehobah ya yi wannan magana daga sama sa’ad da ake yi wa Yesu baftisma. Ta hakan, Jehobah ya bayyana a fili cewa yana ƙaunar Yesu kuma ya amince da shi. Shi ya sa Yesu ya ce: “Uba yana ƙaunata.” (Yohanna 10:17) Da yake ya san cewa Ubansa yana ƙaunarsa kuma ya amince da shi, Yesu ya sami gaba gaɗin jimre hamayya da kuma zargi. Haka ma, Yesu bai ji tsoro ba sa’ad da za a kashe shi domin ya san cewa Ubansa yana ƙaunarsa. (Yohanna 10:18) Babu shakka, sanin cewa Ubansa yana ƙaunarsa kuma ya amince da shi ya sa rayuwar Yesu ta kasance da ma’ana sosai.

Hakika, Yesu ya yi rayuwa mai ma’ana. A gaskiya, za mu iya koyan yadda za mu yi rayuwa mai ma’ana daga misalinsa. Talifin da ke gaba zai tattauna wasu shawarwari masu kyau da Yesu ya ba wa mabiyansa a kan yadda za su yi rayuwa mai ma’ana.

a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.

b Don ƙarin bayani game da yadda mutuwar Yesu take da amfani, ka duba babi na 5 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba