Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/1 pp. 6-7
  • Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana ta Bin Misalin Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana ta Bin Misalin Yesu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YIN TUNANIN GABA
  • Za A Iya Yin Rayuwa Mai Ma’ana Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yesu Ya Koya Mana Yadda Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yadda Zantattukan Yesu Ke Kawo Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Na Sami Albarka Sosai don Na Jimre da Tsanantawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/1 pp. 6-7

Za Mu Yi Rayuwa Mai Ma’ana ta Bin Misalin Yesu

Ka ‘yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi tafiya.’—1 Yohanna 2:6.

KAMAR yadda muka tattauna a talifi na baya, Yesu ya yi rayuwa mai ma’ana. Saboda haka, idan muna son mu yi rayuwa mai ma’ana, zai dace mu bi misalin Yesu da kuma shawararsa.

Jehobah ne da kansa ya gaya mana mu yi hakan kamar yadda Nassin da aka yi ƙaulinsa a baya ya faɗa. Yin tafiya kamar yadda Yesu ya yi yana nufin yin rayuwa da ta jitu da misalinsa da kuma koyarwarsa. Hakan zai sa Allah ya amince da mu kuma za mu yi rayuwa mai ma’ana.

Koyarwar Yesu sun haɗa da ƙa’idodin da za su taimaka mana mu yi irin rayuwar da ya yi. Za mu sami irin waɗannan ƙa’idodi da yawa a cikin wasu furucin da Yesu ya yi. Bari mu bincika kaɗan daga cikin ƙa’idodin nan kuma mu ga yadda za mu yi amfani da su a rayuwarmu.

ƘA’IDA: “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu.”—Matta 5:3, Littafi Mai Tsarki.

YADDA WANNAN ƘA’IDAR TAKE INGANTA RAYUWA:

Yesu ya nuna cewa an halicci ’yan Adam a hanyar da za su yi marmarin koyan abubuwa game da Allah. Muna marmarin samun amsoshi ga tambayoyi kamar su: Me ya sa aka halicce mu? Me ya sa ake shan wahala sosai a duniya? Allah ya damu da mu kuwa da gaske? Mutane za su ci gaba da rayuwa ne bayan sun mutu? Muna bukatar mu san amsoshin waɗannan tambayoyin idan muna son mu yi rayuwa mai ma’ana. Yesu ya san cewa za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyi daga wuri ɗaya ne kawai, wato, daga cikin Kalmar Allah. Sa’ad da Yesu yake addu’a ga Ubansa, ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Shin, Kalmar Allah za ta iya taimaka mana mu san Allah kuma mu yi farin ciki da gaske?

LABARI:

Esa mawaƙi ne da ke ja-gorar wani sanannen rukunin mawaƙa kuma yana gab da zama tauraro. Duk da haka, Esa bai yi farin ciki sosai ba. Ya ce: “Duk da cewa ina jin daɗin kasancewa da rukuninmu, na yi ɗokin yin rayuwa mai ma’ana sosai.” Amma wata rana, Esa ya haɗu da wani Mashaidin Jehobah. Esa ya ce: “Na yi masa tambayoyi da yawa. Yadda ya ba da amsoshi masu kyau daga Littafi Mai Tsarki ya burge ni sai na yarda ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.” Abin da Esa ya koya daga Littafi Mai Tsarki ya ratsa zuciyarsa kuma hakan ya motsa shi ya keɓe kansa don yin nufin Jehobah. Esa ya ce: “A dā, nakan shiga damuwa sosai, amma yanzu, rayuwata ta kasance da ma’ana.”

ƘA’IDA: “Masu-albarka ne masu-jinƙai.”—Matta 5:7.

YADDA WANNAN ƘA’IDAR TAKE INGANTA RAYUWA:

Jin ƙai ya ƙunshi jin tausayin mutane da kuma yi musu alheri. Yesu ya nuna jin ƙai ga mutanen da suke shan wahala. Tausayi ya motsa Yesu ya ɗauki matakai don ya taimaka wa mutanen da suke shan wahala. (Matta 14:14; 20:30-34) Idan muka yi koyi da Yesu a nuna jin ƙai, za mu yi rayuwa mai ma’ana, domin waɗanda suke nuna jin ƙai ga mutane suna farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Za mu iya nuna wa wasu jin ƙai ta wajen yin furuci da ayyuka masu kyau kuma hakan zai sa su ɗan ji sauƙi. Shin, nuna jin ƙai yana inganta rayuwarmu kuwa da gaske?

LABARI:

Maria da maigidanta, Carlos wasu ne da suka nuna jin ƙai. Mahaifiyar Maria ta rasu kuma a cikin ’yan shekaru da suka shige, mahaifinta ya yi rashin lafiya mai tsanani har ba ya iya tashi daga kan gado. Maria da Carlos sun kai shi gidansu kuma suna kula da shi da kyau. Sau da yawa ba sa barci da dare, kuma duk lokacin da ciwon sukari da yake da shi ya tashi, suna kai shi asibiti ko da da dare ne. Sun yarda cewa sukan gaji sosai a wasu lokatai. Amma kamar yadda Yesu ya faɗa, suna farin ciki domin sun san cewa suna kula da mahaifin Maria yadda ya kamata.

ƘA’IDA: “Masu-albarka ne masu-sada zumunta [“son zaman lafiya,” NW].”—Matta 5:9.

YADDA WANNAN ƘA’IDAR TAKE INGANTA RAYUWA:

Ta yaya zaman lafiya da mutane zai sa mu yi rayuwa mai ma’ana? Zaman lafiya da mutane zai sa mu more dangantaka mai kyau da waɗanda muke sha’ani da su. Zai dace mu bi shawarar nan na Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” (Romawa 12:18) “Dukan mutane” sun haɗa da mambobin iyalinmu da kuma mutanen da addininmu ba ɗaya da su ba. Shin, zaman lafiya da “dukan mutane” zai sa mu yi rayuwa mai ma’ana kuwa?

LABARI:

Ka yi la’akari da labarin wata mata mai suna Nair. Ta fuskanci matsaloli da yawa da suka sa bai yi mata sauƙi ta yi zaman lafiya da mutane ba, musamman ma da iyalinta. Tun daga lokacin da maigidanta ya bar ta shekaru 15 da suka shige, ta yi rainon yaranta ita kaɗai. Ɗaya cikin ’ya’yanta maza yana shaye-shaye kuma a wasu lokatai yakan bugu har ya yi wa mahaifiyarsa Nair da kuma ƙanwarsa barazana. Nair ta gaskata cewa abin da ta koya daga Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ta ta yi zaman lafiya da mutane, har ma a mawuyacin yanayi. Tana ƙoƙartawa ta guji yin gardama da kuma faɗa da mutane. Tana tausaya wa mutane kuma ta yi musu alheri. (Afisawa 4:31, 32) Ta tabbata cewa zaman lafiya da mutane ya sa ta jin daɗin zumunci da iyalinta da kuma sauran mutane.

YIN TUNANIN GABA

Idan muka bi misalin Yesu, za mu yi farin ciki kuma mu kasance da wadar zuci. Don mu yi rayuwa mai ma’ana, muna bukata mu san abin da zai faru nan gaba. Ta yaya rayuwa za ta kasance da ma’ana idan iyakacin abubuwan da ta ƙunsa su ne tsufa da rashin lafiya da kuma mutuwa? Hakika, waɗannan abubuwan ne muke fama da su a duniya.

Amma akwai albishiri! Jehobah zai albarkaci waɗanda suka yi ƙoƙari su ‘yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi tafiya.’ Jehobah ya yi alkawari cewa ba da daɗewa ba zai kawo sabuwar duniya, inda ’yan Adam masu aminci za su yi rayuwa kamar yadda Jehobah ya nufa, wato, yin rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya. Kalmarsa ta ce: “Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

Maria, mai shekara 84 da aka ambata a talifi na farko tana ɗokin ganin cikar waɗannan kalmomin. Kai fa? Za ka so ka ƙara koyan yadda za ka sami “hakikanin rai,” wato, irin rayuwa da za a yi a ƙarƙashin Mulkin Allah? (1 Timotawus 6:19) Idan kana so, ka tuntuɓi Shaidun Jehobah a yankinku ko kuma ka rubuta wasiƙa zuwa ga mawallafan wannan mujallar.a

a Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa ya taimaka wa mutane da yawa su san abubuwa da dama daga Littafi Mai Tsarki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba