KA KUSACI ALLAH
Ka Ci Gaba da ‘Roƙo, Za A Ba Ka’
“Ubangiji, ka koya mana yin addu’a.” (Luka 11:1) Ɗaya daga cikin almajiran Yesu ne ya yi wannan roƙon. Yayin da Yesu yake ba da amsa, ya ba da misalai biyu da suka koya mana yadda za mu yi addu’a kuma Allah ya ji. Idan ka taɓa shakka ko Allah yana jin addu’arka, za ka so ka san amsar da Yesu ya bayar.—Ka karanta Luka 11:5-13.
A misali na farko, ya mai da hankali ga wanda yake addu’ar. (Luka 11:5-8) Labarin ya yi magana ne game da wani mutum da ya yi baƙo da dare kuma ba shi da abinci da zai ba wa baƙon. Ga wannan mutumin, wannan batu ne mai muhimmanci. Sai ya tashi ya je gidan wani abokinsa don ya ari abinci duk da cewa dare ya yi sosai. Da farko abokin bai so ya tashi ba domin iyalinsa suna barci. Amma wannan mutumin ya cire kunya kuma ya nace da roƙon har sai da abokin ya tashi ya ba shi abin da yake bukata.a
Mene ne wannan misalin yake koya mana game da addu’a? Yesu yana koya mana cewa muna bukata mu riƙa nacewa, wato, mu ci gaba da roƙo da nema da kuma ƙwanƙwasawa. (Luka 11:9, 10) Me ya sa? Shin, Yesu yana nufin cewa Allah ba ya son jin addu’o’inmu ne? A’a. Abin da Yesu yake nufi shi ne, Allah ba kamar aboki da yake jinkiri ba, amma Allah yana marmarin jin roƙe-roƙen da aka yi cikin bangaskiya da suka jitu da nufinsa. Idan muka nace cikin addu’a, muna nuna wa Allah cewa muna da bangaskiya. Ta wajen roƙo a kai a kai, muna nuna wa Allah cewa muna bukatar abin da muke roƙa kuma mun tabbata cewa zai ba mu idan abin da muka roƙa daidai ne da nufinsa.—Markus 11:24; 1 Yohanna 5:14.
Misali na biyu ya mai da hankali ga Jehobah “Mai-jin addu’a.” (Zabura 65:2) Yesu ya yi wannan tambayar: “Wanene daga cikinku da shi ke uba, ɗansa za ya roƙi . . . kifi, ya ba shi kuma maciji maimakon kifi? Ko kuwa idan ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama?” Abin da Yesu yake nufi a nan shi ne, ba mahaifin da zai ba wa ’ya’yansa abin da zai cutar da su. Bayan haka, Yesu ya bayyana misalin: ’Yan Adam ajizai sukan ba da “kyautai masu-kyau” ga ’ya’yansu “balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki,” wato kyauta mafi tamani ga ’ya’yansa da ke duniya waɗanda suka roƙe shi.b—Luka 11:11-13; Matta 7:11.
Allah yana ɗokin amsa addu’o’in da mutane suka yi da bangaskiya kuma bisa ga nufinsa
Mene ne wannan misalin yake koya mana game da Jehobah “Mai-jin addu’a”? Yesu yana son mu ɗauki Jehobah a matsayin Uba wanda yake marmarin biyan bukatun ’ya’yansa. Saboda haka, masu bauta wa Jehobah za su iya bayyana abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya ba tare da wata tantama ba. Kuma sanin cewa Allah yana son su amfana sosai zai sa su amince da amsar da ya bayar ga roƙonsu, ko da amsar ba ita ce suke zato ba.c
Karatun Littafi Mai Tsarki na Yuni
a Misalin da Yesu ya bayar yana kwatanta wata al’ada ta Yahudawa ne. Karɓan baƙi farilla ce a wajen Yahudawa. Iyalai sukan yi gurasar da za ta ishe su a rana guda kawai, saboda haka, sun saba aran gurasa idan nasu ya ƙare. Ƙari ga haka, idan iyalin matalauta ne, sukan kwana a ƙasa a cikin ɗaki guda.
b Yesu ya yi amfani da kalmar nan “balle” wajen nuna cewa Allah ya fi ’yan Adam.
c Don ƙarin bayani game da yadda za ka yi addu’a kuma Allah ya ji, ka duba babi na 17 a wannan littafin, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.