Jehobah Yana “Bada Ruhu Mai-tsarki Ga Waɗanda Su Ke Roƙonsa”
“Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?”—LUKA 11:13.
1. Yaushe ne musamman muke bukatar taimakon ruhu mai tsarki?
‘BA ZAN iya jimre wannan ba. Sai da taimakon ruhu mai tsarki zan iya jimre da wannan gwaji!’ Ka taɓa furta irin waɗannan kalmomin? Kiristoci da yawa sun furta haka. Wataƙila ka furta irin waɗannan kalmomi sa’ad da ka fahimci cewa ka kamu da mugun cuta. Ko kuwa lokacin da abokiya ko abokin aurenka ta ko ya mutu. Ko kuwa dā kai mai fara’a ne amma yanzu matsala ta sa ka zama mai baƙin ciki. A lokacin da kake baƙin ciki, sai ka ga ka jimre saboda ruhun Jehobah ne yake ba ka “mafificin iko.”—2 Korinthiyawa 4:7-9; Zabura 40:1, 2.
2. (a) Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci na gaskiya suke fuskanta? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Dole ne Kiristoci na gaskiya su fuskanci matsi da hamayya daga cikin wannan duniya marar ibada. (1 Yohanna 5:19) Bugu da ƙari, Shaiɗan ne da kansa yake kai wa masu bin Kristi hari, shi ne yake yaƙi da “waɗanda ke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Shi ya sa muke bukatar taimakon ruhun Allah yanzu fiye da dā. Menene za mu iya yi don mu ci gaba da samun taimakon ruhu mai tsarki? Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah zai ba mu ƙarfin da muke bukata a lokacin da muke fuskantar gwaji? Za mu samu amsar waɗannan tambayoyi daga kwatanci biyu da Yesu ya yi.
Ka Nace da Yin Addu’a
3, 4. Wane kwatanci ne Yesu ya ba da, kuma ta yaya ne ya shafi yin addu’a?
3 Ɗaya daga cikin almajiran Yesu ya ce: “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a.” (Luka 11:1) Yesu ya ba almajiransa amsar ta wajen kwatanci biyu. Na farko game da wani mutum da ya yi baƙo, na biyu kuma game da wani uba da ya saurari ɗansa. Bari mu tattauna waɗannan kwatanci biyu.
4 Yesu ya ce: “Wanene daga cikinku idan yana da aboki, ya kuwa tafi wurinsa da tsakiyar dare, ya ce masa, Aboki, ka ranta mani dunƙulen gurasa uku; gama wani abokina ya zo wurina daga tafiya, ba ni da abin da zan sa gabansa: shi kuwa daga ciki ya amsa, ya ce, Kada ka dame ni; ƙofa tana ƙuble yanzu, ’ya’yana kuma suna tare da ni cikin shimfiɗa; ban iya tashi in ba ka ba? Ina ce maku, Ko ba za ya tashi ya ba shi ba domin abokinsa ne, saboda naciyassa za ya tashi ya ba shi gwalgwadon abin da ya ke bukata.” Sannan Yesu ya bayyana yadda wannan kwatancin ya shafi yin addu’a, ya ce: “Kuma ina ce muku, Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku. Gama kowane mai-roƙo yana karɓa; mai-nema kuma yana samu; wanda ya ke ƙwanƙwasawa kuma, za a buɗe masa.”—Luka 11:5-10.
5. Menene kwatancin mutumin nan mai naci ya koya mana game da yadda ya kamata mu riƙa yin addu’a?
5 Wannan kwatanci na mutumin da ya riƙa nacewa yana nuna mana yadda ya kamata mu yi a lokacin da muke addu’a. Ka lura cewa Yesu ya ce mutumin ya yi nasarar samun abin da yake bukata “saboda naciyassa.” (Luka 11:8) Wannan furcin ‘naciya’ ya bayyana so ɗaya ne kawai a cikin Littafi Mai Tsarki. An fassara shi daga kalmar Helenanci da take nufin “rashin kunya.” Sau da yawa rashin kunya yana nufin mugun hali. Duk da haka, sa’ad da aka yi amfani da rashin kunya ko kuwa nacewa ta hanya mai kyau, zai iya zama halin da ake yabawa. Haka yake da mai masauki a wannan kwatanci. Bai ji kunyar nacewa a roƙon abin da yake bukata ba. Tun da Yesu ya ba mu misali da wannan mai masauki, dole ne mu nace a addu’o’inmu. Jehobah yana son ‘mu roƙa, mu nema, mu ƙwanƙwasa.’ Saboda zai ‘ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.’
6. A zamanin Yesu, yaya ne mutane suka ɗauki halin karɓan baƙi?
6 Yesu ya nuna mana yadda za mu riƙa nacewa a yin addu’a da kuma abin da ya sa ya kamata mu yi addu’a. Domin mu fahimci wannan darassi sosai, bari mu tattauna yadda waɗanda suka saurari kwatancin Yesu game da mai masaukin da ya nace, suka ɗauki halin karɓan baƙi. Labarai na cikin Nassosi sun nuna cewa a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kula da baƙi al’ada ce mai muhimmanci, musamman a wurin bayin Allah. (Farawa 18:2-5; Ibraniyawa 13:2) Abin kunya ne idan mutum ba shi da halin karɓan baƙi. (Luka 7:36-38, 44-46) Da haka, bari mu ƙara yin la’akari da labarin Yesu.
7. Me ya sa mai masauki na kwatancin Yesu bai ji kunyar ta da abokinsa ba?
7 A cikin kwatancin, mai masaukin ya yi baƙo a tsakar dare. Yana son ya ba wa baƙonsa abinci amma ‘ba shi da abin da zai sa gabansa.’ A gare shi wannan matsala ce! Dole ne ya nemi gurasa ko ta yaya. Sai ya tafi gidan abokinsa ya tashe shi ba tare da jin kunya ba. Mai masauki ya ce: “Aboki, ka ranta mani dunƙulen gurasa uku.” Ya nace da roƙonsa sai da ya sami abin da yake bukata. Sa’annan ne zai zama mai masaukin kirki.
Ka Yi Roƙo Sosai Idan Kana Bukatar Abu
8. Menene zai motsa mu mu nace da yin addu’a don mu sami ruhu mai tsarki?
8 Menene wannan kwatancin ya nuna game da dalilin da ya sa muke nacewa da yin addu’a? Mutumin ya ci gaba da roƙon gurasa saboda ya san cewa idan ya samu gurasar zai zama mai masaukin kirki. (Ishaya 58:5-7) Rashin gurasa zai hana shi zama mai masaukin kirki. Haka nan ma, mun fahimci cewa kasancewa da ruhun Allah zai taimake mu mu yi hidimarmu na Kiristoci na gaskiya, shi ya sa muke ci gaba da roƙon Allah ya ba mu wannan ruhu. (Zechariah 4:6) Idan ba haka ba, ba za mu yi nasara ba. (Matta 26:41) Ka fahimci darassi mai muhimmanci da za mu iya koya daga wannan kwatanci? Idan muka fahimci cewa ruhun Allah abu ne da muke bukata sosai, zai sa mu nace a roƙonsa.
9, 10. (a) Ka kwatanta dalilin da ya sa muke bukatar nacewa idan za mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa mai tsarki. (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu, kuma me ya sa?
9 Don mu yi amfani da wannan darassin a rayuwarmu, a ce wani daga cikin iyalinku ya soma rashin lafiya a tsakar dare. Idan ciwon ba mai tsanani ba ne, za ka tashi likita don neman taimako? A’a. Amma, idan yana da ciwon zuciya, ba za ka ji kunyar kiran likita ba. Me ya sa? Saboda kana cikin yanayi na gaggawa. Ka fahimci cewa kana bukatar taimakon gwani. Idan ba ka nemi taimako ba mai rashin lafiyar zai iya mutuwa. Haka nan ma, a alamance Kiristoci na gaskiya suna cikin lokaci na gaggawa yanzu. Hakika, Shaiɗan yana yawo kamar “zaki mai-ruri,” yana ƙoƙari ya cinye mu. (1 Bitrus 5:8) Idan muna son mu riƙe ruhaniyarmu, muna bukatar taimakon ruhun Allah. Rashin neman taimako daga wurin Allah zai kawo mana lahani a rayuwa. Saboda haka, mu nace da roƙon ruhu mai tsarki daga wurin Allah. (Afisawa 3:14-16) Ta yin haka ne kawai za mu ci gaba da samun ƙarfin da muke bukata don mu “jimre har matuƙa.”—Matta 10:22; 24:13.
10 Yana da muhimmanci sosai mu tambayi kanmu, ‘Ina nacewa kuwa da yin addu’a?’ Ka tuna, idan muka fahimci cewa muna bukatar taimako daga wurin Allah, za mu nace da addu’o’inmu na neman ruhu mai tsarki.
Menene Yake Motsa Mu Mu Yi Addu’a da Tabbaci?
11. Ta yaya ne Yesu ya yi amfani da kwatancin uba da ɗansa don ya nanata muhimmancin addu’a?
11 Kwatancin da Yesu ya yi game da yadda wani mai masauki ya nace ya nanata halin wanda yake addu’a wato mai bi. Kwatanci na biyu kuma ya nanata halin wanda yake jin addu’a wato Jehobah Allah. Yesu ya yi tambaya: “Wanene daga cikinku da shi ke uba, ɗansa za ya roƙi dunƙulen gurasa, shi kuwa ya ba shi dutse? ko kuwa kifi, ya ba shi kuma maciji maimakon kifi? Ko kuwa idan ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama?” Yesu ya ba da bayani, yana cewa: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?”—Luka 11:11-13.
12. Ta yaya ne kwatancin uba da yake saurarar roƙon ɗansa yake nanata yadda Jehobah yake amsa addu’o’inmu?
12 A misalin da Yesu ya yi game da uba da ya ba wa ɗansa abin da ya roƙa, Yesu ya nuna ra’ayin Jehobah game da waɗanda suke addu’a a gare shi. (Luka 10:22) Da farko, ka lura da bambancin waɗannan kwatancin biyu. Ba kamar mutumi na kwatanci na farko wanda yake jinkiri wurin ba da taimako ba, Jehobah yana kama da uba mai kula, wanda yake son ya amsa roƙon ɗansa. (Zabura 50:15) Yesu ya nuna yadda Jehobah yake son ta taimaka mana, ta wurin kwatanta haka da uba na ’yan adam da kuma Ubanmu na samaniya. Ya ce idan har uba na ɗan adam ‘da yake mugu’ saboda zunubin da ya gada, yana ba wa ɗansa kyauta mai kyau, mai zai hana Ubanmu na samaniya, mai kirki ya ba da ruhu mai tsarki ga iyalinsa masu bauta masa?—Yaƙub 1:17.
13. Wane tabbaci ne muke da shi idan muka yi addu’a ga Jehobah?
13 Menene muka koya? Muna da tabbaci cewa idan muka roƙi ruhu mai tsarki daga wurin Ubanmu na samaniya zai ba mu. (1 Yohanna 5:14) Idan muka nace da yin addu’a, Jehobah ba zai taɓa cewa ba: “Kada ka dame ni; ƙofa tana ƙuble yanzu.” (Luka 11:7) Maimakon haka, Yesu ya ce: “Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku.” (Luka 11:9, 10) Hakika, Jehobah zai “amsa mana lokacin da muna kira.”—Zabura 20:9; 145:18.
14. (a) Wane tunani ne da bai dace ba yake damun waɗanda suke fuskantar gwaji? (b) Idan muna fuskantar gwaji, me ya sa ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah da tabbaci?
14 Kwatancin Yesu na uba mai kula ya nanata cewa alherin Jehobah ya fi wanda iyaye suke nunawa. Saboda haka, kada kowannenmu ya ji kamar gwajin da muke fuskanta yana nuna cewa Allah yana fushi da mu ne. Amma, babban magabcinmu Shaiɗan ne yake son mu yi tunanin haka. (Ayuba 4:1, 7, 8; Yohanna 8:44) Babu inda aka nuna haka a cikin Nassosi. Jehobah ba ya gwada mu “da mugunta.” (Yaƙub 1:13) Ba ya gwada mu da gwaji mai tsanani. Ubanmu na samaniya yana ‘bada alheri ga waɗanda su ke roƙonsa.’ (Matta 7:11; Luka 11:13) Hakika, idan muka fahimci alherin Jehobah da yadda yake son ya taimake mu, hakan zai motsa mu mu yi addu’a da tabbaci. Idan muka yi haka, za mu furta kalmomi irin na mai zabura wanda ya rubuta: “Amma hakika Allah yā ji; Yā kasa kunne ga muryar addu’ata.”—Zabura 10:17; 66:19.
Yadda Ruhu Mai Tsarki Yake Taimakonmu
15. (a) Wane alkawari ne Yesu ya yi game da ruhu mai tsarki? (b) Ta wace hanya ɗaya ce ruhu mai tsarki yake taimakon mu?
15 Kafin mutuwarsa, Yesu ya maimaita tabbacin da ya yi a kwatancinsa. Sa’ad da yake magana game da ruhu mai tsarki, ya ce wa manzaninsa: “Ni ma in roƙi Uban, shi kuma za ya ba ku wani Mai-taimako, domin shi zauna tare da ku har abada.” (Yohanna 14:16) Da haka, Yesu ya yi alkawari cewa mai taimako ko ruhu mai tsarki, zai kasance da mabiyansa a nan gaba, har zamaninmu. A wace hanya ce ta musamman muke samun wannan taimako a yau? Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu jimre wa gwaji dabam dabam. Ta yaya ne ruhu mai tsarki yake taimakon mu? Manzo Bulus da ya fuskanci gwaji, ya kwatanta yadda ruhun Allah ya taimake shi a cikin wasiƙar da ya yi wa Kiristocin da ke Koranti. Bari mu ɗan tattauna abin da ya rubuta.
16. Ta yaya ne yanayin mu ya yi kama da na Bulus?
16 Da farko, Bulus ya ce wa ’yan’uwansa mabiyi yana fama da ‘masuki cikin jikinsa,’ wato wani irin gwaji. Sa’annan ya ce: “Na yi roƙo ga Ubangiji so uku saboda wannan, a raba ni da shi.” (2 Korinthiyawa 12:7, 8) Ko da yake Bulus ya roƙi Allah ya cire masa ciwon, amma ya ci gaba. A yau wataƙila kana fuskantar irin wannan yanayi. Kamar Bulus, wataƙila ka nace da yin addu’a da kuma tabbaci, kana roƙon Jehobah ya cire maka gwajin. Duk da roƙon da ka yi, matsalar ta ci gaba da damun ka. Wannan yana nufin cewa Jehobah ba ya amsa addu’arka kuma ruhunsa ba ya taimakonka ne? A’a! (Zabura 10:1, 17) Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya ce.
17. Ta yaya ne Jehobah ya amsa addu’ar Bulus?
17 Ta wurin amsa addu’o’in Bulus, Allah ya ce masa: “Alherina ya ishe ka: gama cikin kumamanci ikona ya ke cika.” Bulus ya ce: “Na gwammace fa in yi fahariya cikin kumamancina, wannan kuwa da farinciki mai-yawa, domin ƙarfin Kristi shi inuwantarda ni.” (2 Korinthiyawa 12:9; Zabura 147:5) Duk da haka, Bulus ya fahimci cewa ta wurin Yesu ya samu kāriyar Allah. A yau, Jehobah yana amsa addu’o’inmu ta wannan hanya. Yana kāre mabiyansa sosai.
18. Me ya sa muke iya jimre wa gwaji?
18 Hakika, bukka ba ta hana ruwa ko kuwa ta hana iska hurawa, amma tana tanadin kāriya daga waɗannan abubuwa. Hakazalika, kāriya daga “ƙarfin Kristi” ba ta hana gwaji ya shafe mu ko kuwa wahala ta same mu. Duk da haka, yana ba da kāriya ta ruhaniya daga mugayen abubuwa na duniyan nan da kuma hari daga mai mulkinsa, Shaiɗan. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 15, 16) Saboda haka, idan kana fuskantar gwaji da ya ‘ƙi ya rabu da kai,’ ka tabbata cewa Jehobah yana ganin ƙoƙarinka kuma ya amsa “muryar kukanka.” (Ishaya 30:19; 2 Korinthiyawa 1:3, 4) Bulus ya rubuta: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1 Korinthiyawa 10:13.
19. Menene ka ƙudurta za ka yi, kuma me ya sa?
19 Hakika, an kwatanta “kwanaki na ƙarshe” na wannan duniya marar ibada da “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1) Amma, mabiyan Allah za su iya bi da wannan miyagun zamani. Me ya sa? Saboda taimako da kuma kāriyar ruhu mai tsarki na Allah, wanda Jehobah yake ba da wa da son rai ga waɗanda suke nacewa a roƙonsa da tabbaci. Bari mu ƙudurta mu ci gaba da yin addu’a muna roƙon Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki a kowace rana.—Zabura 34:6; 1 Yohanna 5:14, 15.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene ya kamata mu yi don mu sami ruhu mai tsarki na Allah?
• Me ya sa ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai amsa addu’armu na neman ruhu mai tsarki?
• Ta yaya ne ruhu mai tsarki yake taimakon mu mu jimre?
[Hoto a shafi na 13]
Me za mu iya koya daga kwatancin da Yesu ya yi game da maƙwabci mai nacewa?
[Hoto a shafi na 14]
Kana nacewa a yin addu’a don ka sami ruhu mai tsarki?
[Hoto a shafi na 15]
Menene muka koya game da Jehobah daga kwatancin uba mai kulawa?