AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Me ya sa ’yan Adam sun kasa samar da zaman lafiya a duniya?
Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai na musamman guda biyu. Na farko, ba a halicce ’yan Adam su ja-goranci kansu ba duk da cewa sun cim ma abubuwa masu ban al’ajabi. Na biyu, ’yan Adam sun kasa cim ma burinsu na tabbatar da zaman lafiya don “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” Shi ya sa ƙoƙarce-ƙoƙarcen ’yan Adam ya ci tura.—Ka karanta Irmiya 10:23; 1 Yohanna 5:19.
Ƙari ga haka, son kai da dogon buri ma sun sa samun zaman lafiya a duniya ya yi wuya. Gwamnatin da za ta iya tabbatar da zaman lafiya a duniya ita ce wadda za ta yi mulki a dukan duniya kuma ta koya wa mutane nagarta da ƙaunar juna.—Ka karanta Ishaya 32:17; 48:18, 22.
Wane ne zai samar da zaman lafiya a duniya?
Allah Maɗaukakin Sarki ya yi alkawari cewa zai kafa wata gwamnati da za ta mulki dukan mutane. Gwamnatin za ta sauya gwamnatocin ’yan Adam. (Daniyel 2:44) Ɗan Allah, wato Yesu, zai yi sarauta a matsayin Sarkin Salama. Zai kawar da mugunta daga dukan duniya kuma zai koya wa mutane yadda za su yi zaman lafiya da juna.—Ka karanta Ishaya 9:6, 7; 11:4, 9.
A yanzu haka, a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu, miliyoyin mutane a faɗin duniya suna amfani da Kalmar Allah wajen koya wa mutane yadda za su yi zaman lafiya da juna. Nan ba da daɗewa ba, zaman lafiya zai tabbata a dukan duniya.—Ka karanta Ishaya 2:3, 4; 54:13.