Salama a Duniya—Me Ya Sa Ta Yi Wuya?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ƙoƙarin da mutane suke yi don su kawo salama a duniya ya kasa kuma zai ci gaba da kasawa don dalilai da yawa:
- “Hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irmiya 10:23) Ba a halicci ’yan Adam da ikon yin sarauta ba, saboda haka ba za su iya samun salama na dindindin ba. 
- “Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi. Numfashinsa ya kan fita, ya kan koma turɓayarsa kuma; a cikin wannan rana shawarwarinsa su kan lalace.” (Zabura 146:3, 4,) Shugabannan gwamnati, har waɗanda suke da nufin yin abubuwa masu kyau ba su iya magance abubuwan da ke jawo yaƙi ba. 
- “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama . . . masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura.” (2 Timothawus 3:1–4) Muna zama a “kwanaki na ƙarshe” na wannan muguwar duniya, lokaci da abubuwan da ke faruwa suke hana samun salama. 
- “Kaiton duniya da teku: Domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) An ɗaure magabcin Allah, Iblis, a duniya kuma yana sa mutane su bi mugun halinsa. Muddin shi ne “mai-mulkin wannan duniya,” ba za mu taɓa samun salama ba.—Yohanna 12:31. 
- “[Mulkin Allah] za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su [da suke adawa da Allah], shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Daniel 2:44) Babu wata gwamnatin mutum, sai Mulkin Allah ne kawai zai iya cika burinmu na samun salama a duniya dindindin.—Zabura 145:16.