Ka Daraja Halayen Jehobah Sosai
“Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.”—AFIS. 5:1.
1. (a) Waɗanne halayen Jehobah ne Kirista zai iya yin bincike a kai? (b) Ta yaya yin nazari a kan halayen Allah zai taimaka mana?
SA’AD DA kake tunani game da Jehobah, waɗanne halayensa ne kake tunawa? Za ka tuna da ƙauna da adalci da hikima da kuma ikonsa. Duk da haka, mun san cewa Jehobah yana da halaye masu kyau da yawa. Hakika, cikin shekaru da yawa, mun tattauna halaye fiye da 40 na Jehobah a cikin littattafanmu. Idan ka yi nazarin kowanne cikin waɗannan halayen da kanka ko kuma tare da iyalinka, babu shakka, za ka koya abubuwa da yawa game da Jehobah. Kuma za ka ƙara daraja halayensa. Hakan zai sa ka so yin koyi da Jehobah kuma ka ƙulla abokantaka na kud da kud da shi.—Josh. 23:8; Zab. 73:28.
2. (a) Ka kwatanta yadda nazari game da halayen Jehobah zai iya taimaka mana mu daraja su sosai. (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?
2 Ta yaya za mu koya daraja abu sosai? Ga wani misali da zai bayyana hakan. A ce kana son ka ci abincin da ba ka taɓa ci ba. Sai ka ji ƙamshin abincin kuma ka ɗanɗana shi. Sa’ad da ka ɗanɗana shi, sai ka lura cewa abincin yana da daɗi sosai. Daga baya, sai ka dafa abincin da kanka. Hakazalika, idan muka koyi halayen Jehobah, muka yi bimbini a kan yadda yake nuna su kuma muka nuna su a rayuwarmu, za mu ƙara daraja halayen sosai. (Afis. 5:1) A wannan talifin da kuma biyu da ke gaba, za mu tattauna wasu cikin halayen Jehobah. Sa’ad da muka tattauna kowane hali, za mu amsa waɗannan tambayoyin: Mene ne wannan halin yake nufi? Ta yaya Jehobah yake nuna shi? Kuma, ta yaya za mu nuna wannan halin kamar Jehobah?
JEHOBAH YANA DA SAUƘIN HALI
3, 4. (a) Wane irin mutum ne yake da sauƙin hali? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai sauƙin hali ne?
3 Wane irin mutum ne yake da sauƙin hali? Mutumin da ke da alheri, kuma a kowane lokaci yana a shirye ya tattauna kuma ya saurari wasu. Za ka iya sanin mutumin da ke da sauƙin hali, ta kalamansa da fara’arsa da yadda yake saurara da kuma taimaka wa mutane.
4 Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana da sauƙin hali? Duk da cewa shi ne Mahalicci da kuma Maɗaukakin sarki, ya tabbatar mana cewa yana a shirye kuma yana ɗokin ji da kuma amsa addu’armu. (Karanta Zabura 145:18; Ishaya 30:18, 19.) Za mu iya yin magana da Jehobah a kowane lokaci kuma a ko’ina. Ba ya gajiya da jin mu, kuma ba ya fushi da mu don muna magana da shi. (Zab. 65:2; Yaƙ. 1:5) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehobah a hanyoyin da suka nuna cewa yana so mu kusace shi, kuma mu yi magana da shi. Alal misali, Dauda ya ce ‘idanun Ubangiji suna fuskantar’ mu kuma ‘hannunsa na dama’ yana riƙe da mu. (Zab. 34:15; 63:8) Annabi Ishaya ya kwatanta Jehobah da makiyayi. Ya ce: “Za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya ɗauke su a cikin ƙirjinsa.” (Isha. 40:11) Jehobah yana son mu kasance kusa da shi kamar yadda ’yar tunkiya ke manne wa ƙirjin makiyayi mai kula sosai. Sanin hakan yana ƙarfafa mu kuma yana sa mu ƙaunace shi sosai. Ta yaya za mu iya yin koyi da Jehobah?
HALI NE MAI MUHIMMANCI SOSAI
5. Me ya sa yake da muhimmanci dattawa su kasance da sauƙin hali?
5 A kwanan nan, an tambayi wasu ’yan’uwa daga ƙasashe dabam-dabam ko wane hali na dattijo ne suka fi so. Sai yawanci suka ce sun fi son dattijo da yake da sauƙin hali. Ko da yake kowane Kirista yana bukatar ya kasance da wannan halin, amma ya kamata dattawa su zama kan gaba a yin hakan. (Isha. 32:1, 2) Me ya sa? Wata ’yar’uwa ta ce: “Idan dattijo bai da sauƙin hali, ba za a amfana daga sauran halayensa masu kyau ba.” Babu shakka, hakan gaskiya ne. Ta yaya za ka iya kasance da sauƙin hali?
6. Mene ne za ka yi don ka zama mai sauƙin hali?
6 Idan kana nuna cewa ka damu da mutane kuma kana son ka taimaka musu, hakan zai sa su kusace ka. Kuma idan dattijo ya yi hakan, ’yan’uwa maza da mata da kuma yara za su saki jiki kuma su kusace shi. (Mar. 10:13-16) Carlos ɗan shekara 12 ya ce: “Ina lura da yadda dattawa suke yin fara’a kuma suke murmushi a Majami’ar Mulki, kuma ina sha’awar hakan.” Dattijo yana iya furta cewa yana da sauƙin hali, amma gani ya kori ji. (1 Yoh. 3:18) Ta yaya dattijo zai nuna wannan halin?
7. Me ya sa mutane ba sa jinkirin yin magana da mu sa’ad da muka saka bajon taron gunduma, kuma mene ne hakan ya koya mana?
7 Alal misali, wani ɗan’uwa ya halarci taron gunduma a wata ƙasa a kwana kwanan nan. Ya saka bajonsa sa’ad da yake dawowa a jirgin sama. Wani ma’aikacin jirgin ya ga abin da aka rubuta a bajon, wato ‘Bari Mulkin Allah Ya Zo!’ Sai ya ce wa ɗan’uwan: “Ƙwarai kuwa, za mu tattauna anjima.” Daga baya, sun tattauna sosai kuma mutumin ya karɓi mujallunmu. Wataƙila hakan ya taɓa faruwa da kai. Me ya sa mutane ba sa jinkirin yin magana da mu sa’ad da muka saka bajon taron gunduma? Domin sa’ad da muka saka bajo, kamar dai muna cewa: “Ka kusace ni, kuma ka yi mini tambaya game da inda za ni.” Bajon yana nuna wa mutane cewa muna a shirye mu tattauna game da imaninmu. Hakazalika, ya kamata dattawa su nuna cewa suna so mutane su kusace su, kuma su saki jiki da su. A waɗanne hanyoyi ne za su nuna hakan?
8. Yaya dattawa suke nuna cewa suna kula da ’yan’uwa, kuma yaya ’yan’uwa suke ji game da hakan?
8 A yawancin ƙasashe, muna nuna cewa muna kula da ’yan’uwanmu ta wajen yin murmushi da shan hannu da kuma gai da su da kyau. Wane ne ya kamata ya kasance kan gaba a yin hakan? Ka yi la’akari da misalin Yesu. Matta ya ce sa’ad da Yesu da almajiransa suka taru, sai “Yesu kuwa ya zo wurinsu, ya yi zance da su.” (Mat. 28:18) Haka nan ma, dattawa suna ƙoƙartawa wajen zuwa wurin ’yan’uwa don su tattauna da su. Yaya ’yan’uwa suke ji game da hakan? Wata majagaba mai shekara 88 ta ce: “Yadda dattawa suke murmushi da ni da kuma ƙarfafa ni duk sa’ad da na shigo Majami’ar Mulki yana sa in kusace su.” Wata ’yar’uwa kuma ta ce: “Yadda dattijo yake murmushi sa’ad da yake marabta na a taro yana ƙarfafa ni sosai.”
KA KEƁE LOKACI DON TATTAUNAWA DA ’YAN’UWA
9, 10. (a) Wane misali ne mai kyau Jehobah ya kafa mana? (b) Ta yaya dattawa za su yi koyi da misalin Jehobah?
9 Idan muna son mutane su kusace mu, wajibi ne mu keɓe lokaci don su tattauna da mu. Jehobah ya kafa mana misali mai kyau a wannan batun. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (A. M. 17:27) Hanya ɗaya da dattawa za su iya yin koyi da Jehobah ita ce ta wajen tattaunawa da ’yan’uwa yara da manya, kafin lokacin taro da kuma bayan hakan. Wani ɗan’uwa majagaba ya ce: “Sa’ad da dattijo ya tambaye ni ko ina nan lafiya, kuma ya tsaya ya saurari amsata, nakan ji cewa yana ƙauna ta.” Wata ’yar’uwa da take bauta wa Jehobah kusan shekara 50 ta ce: “Dattawa da suke keɓe lokaci don su tattauna da ni bayan taro, suna sa in ji cewa suna daraja ni.”
10 Hakika, dattawa suna da ayyuka da yawa, amma a wurin taro, ya kamata su tabbata cewa sun keɓe lokaci don tattauna da ’yan’uwa.
JEHOBAH BA YA SON ƘAI
11, 12. (a) Mene ne rashin son kai ya ƙunsa? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ba mai tara ba ne?
11 Wani hali mai kyau na Jehobah shi ne rashin son kai. Mene ne rashin son kai? Yana nufin a bi da mutane yadda ya kamata. Rashin son kai yana da fannoni biyu, wato hali da kuma ayyuka. Me ya sa ake bukatarsu? Domin idan mutum ba ya son kai, zai riƙa bi da kowa daidai wa daida. A cikin Nassosin Helenanci, furucin nan “ba mai-tara ba” yana nufin mutumin da ba “ya kallon fuska,” wato bai fi son wani ba. (A. M. 10:34) Saboda haka, mutumin da ba ya son kai yana mai da hankali ga halin mutum, maimakon siffa ko kuma yanayinsa.
12 Jehobah ne ya kafa misali mafi kyau na rashin son kai. Kalmarsa ta ce shi “ba mai-tara ba ne,” kuma ba ya nuna son kai ga kowa. (Karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35; Kubawar Shari’a 10:17.) Bari mu tattauna wani misali da ya nuna hakan.
13, 14. (a) Wace matsala ce ’ya’ya mata biyar na Zelophehad suka shiga? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ba ya son kai?
13 Akwai wata matsala da ta taso a Isra’ila jim kaɗan kafin su shiga Ƙasar Alkawari. Wani mutum mai suna Zelophehad daga ƙabilar Manassa yana da ’ya’ya biyar mata. Sun san cewa iyalinsu za su gaji fegin da aka keɓe wa mahaifinsu, kamar yadda Isra’ilawa suka saba yi. (Lit. Lis. 26:52-55) Amma, kafin a ba mahaifinsu rabonsa na fegin, sai ya rasu. Bisa ga al’ada, ’ya’ya maza ne kawai suke gādan fegi. Amma, mahaifinsu ba shi da ’ya’ya maza. (Lit. Lis. 26:33) Shin danginsu ne za a ba fegin? Mene ne ’yammatan nan za su yi?
14 Sun je wurin Musa kuma suka ce: “Don me sunan ubanmu za shi mutu cikin danginsa, domin ba shi da ɗa?” Sai suka roƙe shi: “Ka ba mu gādo a cikin ’yan’uwan ubanmu.” Shin Musa ya amsa cewa, ‘Abin da doka ta ce ke nan, ba zan iya taimaka muku ba’? A’a, amma “ya kawo da’awarsu a gaban Ubangiji.” (Lit. Lis. 27:2-5) Mene ne Jehobah ya yi? Ya gaya wa Musa: “’Ya’ya mata na Zelophehad sun yi magana daidai: hakika za ka ba su rabo na gādo cikin ’yan’uwan ubansu; ka sa gādon ubansu kuma ya zama nasu.” Jehobah bai tsaya a nan ba, amma ya gaya wa Musa ya saka wannan cikin Doka: “Idan mutum ya mutu, ba shi kuwa da ɗa, sai a bada gādonsa ga ɗiyarsa.” (Lit. Lis. 27:6-8; Josh. 17:1-6) Tun daga lokacin, dukan mata Isra’ilawa da suke cikin irin wannan yanayin suna samun gādo.
15. (a) Ta yaya Jehobah yake bi da bayinsa, har da waɗanda ba su da mai taimako? (b) Waɗanne labarai cikin Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa Jehobah ba ya son kai?
15 Hakika, wannan rashin son kai ne! Waɗannan ’yan’uwa mata biyar ba su da wanda zai taimaka musu, amma Jehobah ya bi da su cikin alheri da daraja, yadda ya bi da sauran Isra’ilawa. (Zab. 68:5) Wannan ɗaya ne kawai cikin labarai da yawa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa sa’ad da Jehobah yake bi da bayinsa, ba ya nuna son kai.—1 Sam. 16:1-13; A. M. 10:30-35, 44-48.
ZA MU IYA YIN KOYI DA JEHOBAH
16. Ta yaya za mu zama masu rashin son kai kamar Jehobah?
16 Ta yaya za mu zama masu rashin son kai kamar Jehobah? Ka tuna cewa rashin son kai yana da fannoni biyu. Sai idan mu masu rashin son kai ne za mu bi da mutane hakan. Wataƙila kana ji cewa ba ka son kai. Amma, a wasu lokatai yana da wuya mu san ainihin yadda muke ɗaukan mutane. Ta yaya za ka san cewa ba ka son kai? Sa’ad da Yesu yake son ya san yadda mutane suke ɗaukansa, ya tambayi aminansa cewa: “Wa mutane ke cewa Ɗan Mutum yake?” (Mat. 16:13, 14) Ka bi misalin Yesu, wataƙila za ka zaɓi abokin da ka san zai gaya maka gaskiya kuma ka tambaye shi, ‘Kana ganin ina bi da mutane cikin adalci? Shin mutane suna ganin ba na son kai?’ Alal misali, yana iya gaya maka cewa, a wasu lokatai kana daraja mutane daga wasu ƙabilai fiye da wasu ko kuma ka fi yin fara’a da masu kuɗi ko kuma masu ilimi sosai. Idan haka ne, ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka yi gyara, don ka bi misalinsa a yadda kake bi da mutane da rashin son kai.—Mat. 7:7; Kol. 3:10, 11.
17. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa mu ba masu son kai ba ne?
17 A cikin ikilisiya, za mu iya yin koyi da Jehobah ta wajen bi da kowa cikin daraja da alheri. Alal misali, sa’ad da kake gayyatar ’yan’uwa zuwa gidanka, ka gayyaci mutane daga al’adu dabam-dabam. Kana iya haɗa da waɗanda ka fi su kuɗi ko gwauraye ko kuma matasa da iyayensu ba Shaidu ba. (Karanta Galatiyawa 2:10; Yaƙub 1:27.) Sa’ad da muke wa’azi, ya kamata mu yi wa mutane dabam-dabam magana har da mutane daga wasu ƙasashe. Muna farin ciki cewa ƙungiyar Jehobah ta wallafa littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki cikin kusan harsuna 600. Hakan tabbaci ne cewa mu ba masu son kai ba ne.
18. Ta yaya za ka nuna cewa kana son yadda Jehobah yake da sauƙin hali da kuma rashin son kai?
18 Yayin da muke ƙara tunani game da yadda Jehobah yake da sauƙin hali kuma ba ya son kai, hakan zai sa mu ƙara daraja waɗannan halayen. Saboda haka, ya kamata mu yi koyi da Jehobah kuma mu nuna waɗannan halayen a yadda muke bi da ’yan’uwanmu da waɗanda muke haɗuwa da su sa’ad da muke wa’azi.