’Ya’yan Zelofehad suna roƙo a ba su gādon babansu
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Yi Koyi da Halin Rashin Son Kai na Jehobah
’Ya’ya mata biyar na Zelofehad sun roƙa a ba su gādon babansu (L.Ƙi 27:1-4; w13 6/15 10 sakin layi na 14; ka duba hoton da ke shafin farko)
Jehobah ya nuna rashin son kai a shawarar da ya yanke (L.Ƙi 27:5-7; w13 6/15 11 sakin layi na 15)
Mu ma dole ne mu nuna halin rashin son kai (L.Ƙi 27:8-11; w13 6/15 11 sakin layi na 16)
Idan muka nuna wa ’yan’uwanmu ƙauna kuma muka yi wa dukan mutane wa’azi, muna yin koyi da halin rashin son kai na Jehobah.