Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/15 pp. 9-14
  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU YANA KULA DA SU
  • MANZO YA ‘SHIRYA TAFARKI’
  • LOKACIN BINCIKE DA KUMA TSARKAKEWA
  • MENE NE YA FARU A LOKACIN KAKA?
  • YADDA MUKA AMFANA
  • “Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Kwatancin Alkama da Zawan
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • ‘Bari Mulkinka Ya Zo’
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • An Fallasa Maƙiyin Imani
    Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/15 pp. 9-14

‘Ga Shi, Ina Tare Da Ku Kullayaumi’

“Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—MAT. 28:20.

KA AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Me ya sa za mu ce tun daga ƙarni na farko har zuwa yau, ba a taɓa rasa shafaffun Kiristoci a duniya ba?

  • Wane bincike ne Yesu ya yi a shekara ta 1914?

  • Waɗanne abubuwa a cikin almarar Yesu game da alkama da kuma ciyayi ne za su faru a nan gaba?

1. (a) Ka taƙaita almarar alkama da kuma ciyayi. (b) Ta yaya Yesu ya bayyana almarar?

A WANI kwatancin da Yesu ya yi game da Mulkin Allah, ya ambata cewa wani manomi ya yi noman alkama, sai magabcinsa ya shuka zawan, wato ciyayi a gonar. Ciyayin sun girma sun rufe alkamar, amma mai gonar ya ce wa bayinsa su ƙyale “duka biyu su yi girma tare har kaka.” Sa’ad da kaka ta kai, sai aka nome ciyayin kuma aka tattara alkamar. Yesu ya bayyana wannan almarar. (Karanta Matta 13:24-30, 37-43.) Mene ne wannan almarar take nufi? (Ka duba akwatin nan “Alkamar da Ciyayin.”)

2. (a) Mene ne abubuwan da suke faruwa a gonar suke wakilta? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Abubuwa da suke faruwa a wannan gonar suna kwatanta lokaci da kuma yadda Yesu zai zaɓi Kiristoci shafaffu da za su yi sarauta tare da shi a Mulkinsa. Kuma su ne ke wakiltar alkamar da aka ambata a cikin almarar. An soma zaɓansu a ranar Fentakos ta shekara ta 33 a zamanin Yesu. Za a kammala tattara shafaffun sa’ad da dukansu da ke da rai a ƙarshen wannan zamanin suka tafi sama. (Mat. 24:31; R. Yoh. 7:1-4) Kamar yadda mutum yake iya ganin dukan gari sa’ad da ya hau kan dutse mai tsawo, hakan ma wannan almarar tana nuna mana dalla-dalla abubuwan da za su faru a cikin shekaru 2,000. Waɗanne abubuwa da suka shafi Mulkin ne suke faruwa? Yesu ya ambata lokacin da aka shuka alkamar da lokacin da za ta yi girma da kuma lokacin da za a girbe ta a almarar. A wannan talifin, za mu mai da hankali ga lokacin girbi.a

YESU YANA KULA DA SU

3. (a) Mene ne ya faru a ƙarni na biyu? (b) Wace tambaya ce aka yi a Matta 13:28, kuma wane ne ya yi tambayar? (Ka duba ƙarin bayani.)

3 Sa’ad da aka shiga ƙarni na biyu, sai ciyayin, wato jabun Kiristoci suka “bayyana.” (Mat. 13:26) A ƙarni na huɗu, waɗannan jabun Kiristoci sun fi shafaffun Kiristoci yawa. Ka tuna cewa a almarar, bayin sun tambayi ubangijinsu ko yana so su tuge ciyayin.b (Mat. 13:28) Mene ne ubangijin ya gaya musu?

4. (a) Mene ne amsar Yesu ta nuna? (b) A wane lokaci ne shafaffun Kiristoci suka bayyana?

4 Yesu ya ce game da ciyayin da kuma alkamar: “Bar su duka biyu su yi girma tare har kaka.” Wannan umurnin ya nuna cewa tun daga ƙarni na farko har zuwa yanzu, Kiristoci shafaffu ba su taɓa daina wanzuwa a duniya ba. Me ya sa muka ce hakan? Domin Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: ‘Ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.’ (Mat. 28:20) Saboda haka, Yesu zai ci gaba da kula da shafaffun Kiristoci har zuwa ƙarshen zamanin nan. Amma, me ya sa ba mu san waɗanda suke cikin shafaffun ba ƙarnuka da yawa da suka shige? Domin Kiristoci masu kamar ciyayi sun shawo kansu. Duk da haka, shafaffun Kiristoci sun bayyana shekaru da yawa kafin lokacin girbi. Ta yaya aka gano su?

MANZO YA ‘SHIRYA TAFARKI’

5. Ta yaya annabcin Malakai ya cika a ƙarni na farko?

5 Shekaru da yawa kafin Yesu ya ba da almarar alkama da kuma ciyayi, Jehobah ya sa annabi Malakai ya faɗi abubuwan da Yesu ya ambata a almararsa. (Karanta Malakai 3:1-4.) Yohanna mai baftisma ne manzo da ya ‘shirya tafarki.’ (Mat. 11:10, 11) Sa’ad da Yesu ya zo a shekara ta 29, lokacin hukunta al’ummar Isra’ila ya kusa. Yesu ne manzo na biyu. Ya tsarkake haikalin da ke Urushalima sau biyu, wato a lokacin da ya soma hidimarsa da kuma sa’ad da ya kusan kammala ta. (Mat. 21:12, 13; Yoh. 2:14-17) Saboda haka, tsarkake haikali da Yesu ya yi ya ɗauki lokaci.

6. (a) A wace hanya ce kuma annabcin Malakai ya cika? (b) A wane lokaci ne Yesu ya yi bincike a yadda ake bauta wa Jehobah? (Ka duba ƙarin bayani.)

6 A wace hanya ce kuma annabcin Malakai ya cika? Kafin shekara ta 1914, Ɗan’uwa Charles Taze Russell da kuma abokansa sun yi irin aikin da Yohanna mai baftisma ya yi. Sun sake yin bincike don su gano koyarwa ta gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koyar da ainihin ma’anar fansa da koyarwar wutar jahannama, kuma sun yi shelar ƙarshen Lokutan Al’ummai. Duk da haka, akwai addinai da yawa da suke da’awar su Kiristoci ne. Hakan ya sa aka yi wata tambaya mai muhimmanci: Wanne ne cikin waɗannan rukuni biyu yake wakiltar alkamar? Don a amsa wannan tambayar, Yesu ya soma bincike a yadda ake bauta wa Jehobah a shekara ta 1914. Wannan bincike da kuma tsarkakewa sun soma daga shekara ta 1914 zuwa somawar shekara ta 1919.c

LOKACIN BINCIKE DA KUMA TSARKAKEWA

7. Mene ne Yesu ya gano sa’ad da ya soma bincike a shekara ta 1914?

7 Mene ne Yesu ya gano sa’ad da ya soma bincikensa? Ya gano ƙaramin rukunin da ake kira Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suka yi shekaru fiye da talatin suna yin amfani da dukan ƙarfinsu da kuma arzikinsu wajen yaɗa bishara.d Hakika, Yesu da mala’iku sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka gano wannan ƙaramin rukuni da yake da bangaskiya sosai, duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da Shaiɗan ya yi don ya halaka shi. Duk da haka, ana bukatar a “tsarkake ’ya’yan Levi,” wato shafaffun. (Mal. 3:2, 3; 1 Bit. 4:17) Me ya sa?

8. Waɗanne abubuwa ne suka faru bayan shekara ta 1914?

8 A ƙarshen shekara ta 1914, wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi sanyin gwiwa sosai don ba su je sama ba. A tsakanin shekara ta 1915 zuwa 1916, an tsananta wa Ɗaliban kuma hakan ya sa suka daina wa’azi da ƙwazo. Kuma bayan mutuwar Ɗan’uwa Russell a watan Oktoba na shekara ta 1916, sai wasu cikin ’yan’uwa suka soma hamayya da juna. Sa’ad da aka zaɓi Ɗan’uwa Rutherford a matsayin wanda zai ja-goranci ƙungiyar, sai ’yan’uwa huɗu cikin darektoci bakwai a lokacin suka ƙi amincewa da hakan. Sun ƙoƙarta su jawo jayayya tsakanin ’yan’uwa, amma hakan bai yiwu ba. Sun bar Bethel a watan Agusta na shekara ta 1917, kuma hakan ya tsarkake ƙungiyar. Wasu ’yan’uwa kuma sun daina bauta wa Jehobah domin tsoron mutum. Duk da haka, yawanci sun amince da tsarkakewar da Yesu ya yi kuma sun yi gyara. Shi ya sa Yesu ya amince da su a matsayin alkama ko kuma Kiristoci na gaskiya, kuma ya ƙi da dukan jabun Kiristoci da suka haɗa da dukan mabiyan cocin Kiristendom. (Mal. 3:5; 2 Tim. 2:19) Mene ne kuma ya faru? Bari mu sake bincika almarar Yesu game da alkama da kuma ciyayi.

MENE NE YA FARU A LOKACIN KAKA?

9, 10. (a) Mene ne za mu tattauna game da kaka? (b) Mene ne aka soma yi a kakar?

9 Yesu ya ce: “Kaka kuma matuƙar zamani ce.” (Mat. 13:39) Kakar ta soma a shekara ta 1914 ne. Yanzu za mu bincika abubuwa guda biyar da Yesu ya ce za su faru a wannan lokacin.

10 Na farko shi ne tattara ciyayin. Yesu ya ce: “Lokacin kaka kuma in ce wa masu-girbi, ku tattara zawan [ciyayi] tukuna, a ɗaure su cikin kaya.” Bayan shekara ta 1914, sai mala’ikun suka soma ware jabun Kiristoci daga cikin “’ya’yan mulki,” wato Kiristoci shafaffu.—Mat. 13:30, 38, 41.

11. Wane aiki ne ya bambanta Kiristoci na gaskiya daga jabun Kiristoci?

11 Yayin da ake ci gaba da yin aikin tattarawa, ana ƙara ganin bambanci da ke tsakanin Kiristoci na gaskiya da kuma na ƙarya. (R. Yoh. 18:1, 4) A shekara ta 1919, sai aka ga tabbaci cewa Babila Babba ta faɗi. Mene ne ya fi bambanta Kiristoci na gaskiya da na ƙarya? Kiristoci na gaskiya suna wa’azi. Waɗanda suke ja-gora a ƙungiyar Jehobah a lokacin suka nanata cewa yana da muhimmanci kowa ya riƙa zuwa wa’azi. Alal misali, a cikin wata warƙa mai jigo To Whom the Work Is Entrusted, (Wanda Aka Ba Aikin) da aka wallafa a shekara ta 1919, an umurci dukan Kiristoci shafaffu su yi wa’azi gida-gida. Warƙar ta ce: “Wannan jan aiki ne, amma na Ubangiji ne kuma da taimakonsa za mu yi shi. Gata ne ka saka hannu a aikin.” Wane sakamako ne aka samu? An faɗi a Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1922 cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun daɗa ƙwazo a wa’azi. Kafin a sani, yin wa’azi gida-gida ya zama aikin da aka fi sanin Kiristoci na gaskiya da shi. Hakan ma yake a yau.

12. A wane lokaci ne aka tattara shafaffu, kuma yaya aka yi hakan?

12 Na biyu shi ne tattara alkama. Yesu ya umurci mala’ikunsa cewa: “Ku tattara alkama, ku kai rumbuna.” (Matt. 13:30) An soma tattara shafaffun Kiristoci cikin ikilisiya tun daga shekara ta 1919. Amma, za a kammala wannan tattarawar sa’ad da shafaffu da suke da rai a lokacin da za a halaka wannan duniyar suka tafi sama.—Dan. 7:18, 22, 27.

13. Mene ne Ru’ya ta Yohanna 18:7 ya ce game da halin Kiristendom da kuma Babila Babba a yau?

13 Na uku shi ne kuka da cizon haƙora. Mene ne zai faru bayan mala’iku sun ɗaure ciyayin? Yesu ya ce: “Can za a yi kuka da cizon haƙora.” (Matt. 13:42) Shin hakan ya soma faruwa? A’a. A yau, Kiristendom wanda sashe ne na karuwar tana ce game da kanta: “Sarauniya ne ke zaune, ba gwauruwa nike ba, ba kuwa zan ga kewa ba daɗai.” (R. Yoh. 18:7) Hakika, Kiristendom tana ji kamar ita ‘sarauniya’ ce don tana yin tasiri a kan manyan shugabannin siyasa. Mabiyan addinin Kiristendom da ke wakiltar ciyayi suna fahariya ne a yau, ba kuka ba. Amma, kiɗa za ta canja ba da daɗewa ba.

14. (a) A wane lokaci ne jabun Kiristoci za su yi “cizon haƙora,” kuma me ya sa? (b) Wace nasaba ce ke tsakanin bayanin da ke littafin Matta 13:42 da kuma Zabura 112:10? (Ka duba ƙarin bayani.)

14 A lokacin ƙunci mai girma, za a halaka dukan addinan ƙarya. Dukan mabiyansu za su nemi maɓuya, amma ba za su samu ba. (Luk 23:30; R. Yoh. 6:15-17) Da yake ba su sami maɓuya ba, za su yi ta kuka da kuma “cizon haƙora” domin yawan baƙin ciki. Kamar yadda Yesu ya annabta, “za su yi baƙinciki” sosai.e—Mat. 24:30; R. Yoh. 1:7.

15. Mene ne za a yi da ciyayin, kuma a wane lokaci?

15 Na huɗu, za a jefa ciyayin cikin wuta. Su wane ne za su yi hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce mala’iku za su “jefa su cikin wuta mai ruruwa.” (Mat. 13:42) Hakan yana nufin cewa za a halaka su baki ɗaya. Saboda haka, za a halaka mabiyan dukan addinan ƙarya a sashe na ƙarshe na ƙunci mai girma, wato yaƙin Armageddon.—Mal. 4:1.

16, 17. (a) Mene ne zai faru a ƙarshe kamar yadda Yesu ya ambata a almararsa? (b) Me ya sa muka ce a nan gaba ne hakan zai faru?

16 Na biyar, za su haskaka. Su wane ne za su haskaka? Yesu ya kammala annabcinsa da cewa: “Sa’annan masu-adalci za su haskaka kamar rana a cikin mulkin Ubansu.” (Mat. 13:43) A wane lokaci ne hakan zai faru, kuma a ina? Wannan annabcin zai cika a nan gaba, kuma a sama.f Ka yi la’akari da dalilai biyu da suka sa muka ce hakan.

17 Na farko shi ne lokacin. Yesu ya ce: ‘Sa’an nan masu-adalci za su haskaka.’ Wace sa’a ce Yesu yake nufi a furucinsa? Yana nufin lokacin da za a jefa ciyayin ‘cikin wuta.’ Hakan zai faru a nan gaba a yaƙin Armageddon. A wannan lokacin ne shafaffun Kiristoci za su “haskaka.” Na biyu shi ne inda za su haskaka. Yesu ya ce masu adalci za su haskaka ‘a cikin mulkin.’ Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin cewa dukan shafaffu da suke duniya bayan sashe na farko na ƙunci mai girma sun riga sun karɓi hatimi na ƙarshe, kuma za su tafi sama, kamar yadda Yesu ya ambata a annabcinsa game da hatimi na ƙarshe. (Mat. 24:31) A sama ne za su haskaka ‘a cikin mulkin Ubansu.’ Jim kaɗan bayan yaƙin Armageddon, za su yi farin ciki tare da Yesu, domin su ne amarya a “auren Ɗan rago.”—R. Yoh. 19:6-9.

YADDA MUKA AMFANA

18, 19. Ta yaya ka amfana daga fahimtar almarar Yesu game da alkama da kuma ciyayi?

18 Ta yaya za mu amfana daga wannan almarar? Ka yi la’akari da hanyoyi uku. Ta ɗaya ita ce, ta sa mun fahimci wani dalili mai muhimmanci da ya sa Jehobah ya ƙyale wahala. Ya ƙyale “tukwane na fushi” su shirya “tukwane na jinƙai,” wato shafaffun Kiristoci.g (Rom. 9:22-24) Hanya ta biyu ita ce, ta sa mun kasance da gaba gaɗi. Yayin da ƙarshen wannan duniyar take kusatowa, magabtanmu za su yi gāba da mu fiye da dā, ‘amma ba za su yi nasara da mu ba.’ (Karanta Irmiya 1:19.) Kamar yadda Jehobah ya kāre shafaffu shekaru da yawa da suka shige, haka nan ma zai kasance tare da mu “kullayaumi,” ta wajen Yesu da kuma mala’iku.—Mat. 28:20.

19 Na uku, almarar Yesu ta taimaka mana mu san waɗanda suke wakiltar alkamar. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin sanin waɗanda suke wakiltar alkamar zai taimaka mana mu sami amsar wata tambaya da Yesu ya yi sa’ad da yake annabci game da kwanaki na ƙarshe. Ya ce: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima?” (Mat. 24:45) Za a amsa wannan tambayar a talifofi biyu na gaba.

a Sakin layi na 2: Don ka tuna da ma’anar sauran abubuwan da aka ambata a wannan almarar, muna ƙarfafa ka ka karanta talifin nan “Masu-adalci Za Su Haskaka Kamar Rana,” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2010.

b Sakin layi na 3: Waɗannan bayin suna wakiltar mala’iku, da yake manzannin Yesu sun mutu kuma sauran shafaffun da suke duniya ne suke wakiltar alkamar. Daga baya, an ambata a almarar cewa mala’iku ne suke yanka ciyayin.—Mat. 13:39.

c Sakin layi na 6: A dā, mun ɗauka cewa Yesu ya yi binciken a shekara ta 1918 ne, amma wannan sabon bayanin ya sauya shi.

d Sakin layi na 7: Daga shekara ta 1910 zuwa 1914, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun rarraba littattafai kusan 4,000,000 da kuma warƙoƙi fiye da 200,000,000.

e Sakin layi na 14: Wannan sabon bayani ne a kan littafin Matta 13:42. A dā, mun wallafa a littattafanmu cewa jabun Kiristoci sun yi shekaru suna “kuka da cizon haƙora,” domin suna baƙin ciki cewa “’ya’yan mulkin” sun fallasa su a matsayin “’ya’yan mugun.” (Mat. 13:38) Amma, ya kamata a lura cewa wannan kuka da cizon haƙora yana da nasaba da halaka.—Zab. 112:10.

f Sakin layi na 16: Littafin Daniyel 12:3 ya ce “waɗanda ke da hikima [shafaffun Kiristoci] kuma za su haskaka kamar walƙiyar sararin sama.” Sa’ad da suke duniya, suna haskakawa ta wajen yin wa’azi. Amma, littafin Matta 13:43 yana nufin lokacin da za su haskaka sosai a Mulkin sama. A dā, mun ɗauka cewa waɗannan nassosin suna nufin abu ɗaya, wato aikin wa’azi.

g Sakin layi na 18: Ka duba littafin nan Ka Kusaci Jehovah, shafuffuka na 288-289.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba