DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 12-13
Kwatancin Alkama da Zawan
Yesu ya yi amfani da kwatancin alkama da zawan wajen kwatanta yadda zai zaɓi shafaffun Kiristoci da suke kama da alkama daga cikin mutane da kuma lokacin da zai yi hakan. An soma hakan a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu.
‘Wani mutum ya shuka iri mai-kyau cikin gonarsa’
Mai shukin: Yesu Kristi
Iri mai kyau da aka shuka: An shafe almajiran Yesu da ruhu mai tsarki
Gonar: Mutane
“Lokacin da mutane suna barci, maƙiyinsa ya zo, ya shuka zawan”
Maƙiyi: Shaiɗan
Da mutane suka yi barci: A lokacin da manzanni suka mutu
“Bar su duka biyu su yi girma tare har kaka”
Alkama: Shafaffun Kiristoci
Zawan: Kiristoci na ƙarya
‘Ku tattara zawan tukuna . . . ; kafin ku tattara alkama’
Bayi ko masu girbi: Mala’iku
Zawan da aka tattara: An ware Kiristoci na ƙarya daga shafaffun Kiristoci
Tattara su zuwa rumbu: An tattara shafaffun Kiristoci zuwa cikin ikilisiya
Idan aka soma girbin, ta yaya za a bambanta Kiristoci na gaskiya daga Kiristoci na ƙarya?
Wane darasi na koya daga wannan kwatancin?