Abin Da Muka Koya Daga Yesu
Yadda Mala’iku Suke Taimaka Mana
Yesu yana zaune ne a duniyar ruhu tare da Ubansa “tun duniya ba ta zama ba.” (Yohanna 17:5) Saboda haka, ya cancanta sosai ya amsa tambayoyin da ke gaba.
Mala’iku sun damu da mu kuwa?
▪ Daga Yesu, mun koyi cewa mala’iku sun damu da mutane sosai. Ya ce: “Akwai murna a wurin mala’ikun Allah a kan mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba.”—Luka 15:10.
Yesu ya bayyana cewa mala’iku suna da hakkin taimaka wa bayin Allah su ƙarfafa dangantakarsu da shi. Shi ya sa, sa’ad da Yesu ya gargaɗi almajiransa game da sa wasu yin tuntuɓe, ya ce: “Ku yi hankali kada ku rena wani a cikin waɗannan ƙanƙanana; gama ina ce maku, cikin sama kullum mala’ikunsu suna duban fuskar Ubana wanda ke cikin sama.” (Matta 18:10) Ba wai Yesu yana nufin cewa kowane mabiyansa yana da mala’ikan da aka ce ya tsare shi ba. Yesu ya nuna ne cewa mala’ikun da suke aiki kafaɗa da kafaɗa da Allah sun damu ƙwarai da gaske da duk wani da ke cikin ikilisiyar Kirista.
Ta yaya Iblis zai iya yi mana illa?
▪ Yesu ya gargaɗi mabiyansa cewa Shaiɗan yana ƙoƙarin hana mutane su koyi gaskiya game da Allah. “Kadan wani ya ji zancen mulkin, ba ya kuwa gāne ba,” in ji Yesu, “mugun ya kan zo, ya fizge abin da aka shuka a zuciyarsa.”—Matta 13:19.
Yesu ya fallasa hanya guda da Shaiɗan yake ruɗar da mutane sa’ad da ya gabatar da wani kwatanci game da wani mutumin da ya shuka alkama a gonarsa. Mutumin yana wakiltan Yesu, kuma alkamar tana wakiltan Kiristoci na gaskiya da za su yi sarauta tare da Yesu a sama. Amma, Yesu ya ce wani maƙiyi ya zo ya “shuka zawan kuma a tsakanin alkama.” Zawan yana nufin Kiristoci na ƙarya. ‘Maƙiyin da ya shuka su kuma Shaiɗan ne.’ (Matta 13:25, 39) Kamar yadda zawan zai fito da ruwan alkama, waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne suna iya bayyana kamar masu bauta ta gaskiya. Addinan da suke gabatar da koyarwan ƙarya suna yaudarar mutane su yi rashin biyayya ga Allah. Shaiɗan yana amfani da addinin ƙarya ya hana mutane yin abota da Jehobah.
Ta yaya za mu iya hana Shaiɗan ya yi mana illa?
▪ Yesu ya kira Shaiɗan “sarkin duniya.” (Yohanna 14:30) A cikin wata addu’a da ya yi ga Allah, Yesu ya bayyana yadda za mu iya samun kāriya daga Shaiɗan. Game da almajiransa, Yesu ya yi addu’a ga Uba na sama: “Ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. Ka tsarkake su cikin gaskiya: maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:15-17) Sanin Kalmar Allah zai iya kāre mu daga tasirin wannan duniyar da Shaiɗan yake sarauta.
Ta yaya mala’iku suke taimaka mana a yau?
▪ “Cikin matuƙar zamani,” in ji Yesu, “malaiku za su fito, su rarraba miyagu daga cikin masu adalci.” (Matta 13:49) A yanzu muna zaune ne a “cikin matuƙar zamani,” kuma miliyoyi suna yin na’am ga bisharar Mulkin Allah.—Matta 24:3, 14.
Amma ba dukan waɗanda suka soma yin nazarin Kalmar Allah ba ne suke samun amincewarsa. Mala’iku suna yi wa aikin bayin Jehobah ja-gora, kuma ana raba mutanen da suke ƙaunar Allah da gaske daga waɗanda ba sa son su yi amfani da abin da suka koya. Sa’ad da yake kwatanta waɗanda suka samu amincewar Allah, Yesu ya ce: “Su ne waɗanda sun ji magana cikin zuciya mai-gaskiya mai-kyau, daga baya su kan riƙe ta, da haƙuri kuma suna bada amfani.”—Luka 8:15.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 10 na wannan littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah suka wallafa.
[Hoton da ke shafi na 24]
Mala’iku suna taimakawa wajen tattara mutane masu gaskiya zuwa cikin ikilisiyar Kirista