Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/15 pp. 15-19
  • Yesu Yana Ciyar da Jama’a ta Hannun Mutane Ƙalilan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Yana Ciyar da Jama’a ta Hannun Mutane Ƙalilan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU YA ZAƁI MUTANE ƘALILAN
  • YA SOMA CIYAR DA SU DAGA RANAR FENTAKOS
  • SA’AD DA CIYAYIN SUKA FI ALKAMAR YAWA
  • WANE NE ZAI CIYAR DA MUTANE A LOKACIN KAKA?
  • Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Kalila
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • ‘Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yesu Ya Ciyar da Dubban Mutane
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • ‘Bari Mulkinka Ya Zo’
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/15 pp. 15-19

Yesu Yana Ciyar Da Jama’a Ta Hannun Mutane Ƙalilan

“[Yesu] ya kakkarya, ya ba da dunƙulen nan ga almajiransa, almajiran kuwa suka ba taron.”—MAT. 14:19.

MECE CE AMSARKA?

  • A wace hanya ce Yesu ya ciyar da jama’a?

  • Yaya Yesu ya yi amfani da manzanni da kuma dattawa da ke Urushalima?

  • A wane lokaci ne Kristi ya kafa tsari na koyar da kalmar Allah?

1-3. Ta yaya Yesu ya ciyar da jama’a a kusa da ƙauyen Baitsaida? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)

KA YI la’akari da abin da ya faru kafin ranar Fentakos ta shekara ta 32 a zamanin Yesu. (Karanta Matta 14:14-21.) Mazaje dubu biyar tare da mata da yara sun bi Yesu da almajiransa zuwa kusa da ƙauyen Baitsaida da ke arewancin gaɓar Tekun Galili.

2 Sa’ad da Yesu ya ga mutanen sai ya ji tausayinsu, ya warkar da marasa lafiya kuma ya koya musu abubuwa da yawa game da Mulkin Allah. Sa’ad da rana ta soma faɗuwa, sai almajiran Yesu suka gaya masa ya sallame mutanen su shiga cikin ƙauyukan da ke kusa don su sayi abinci. Amma, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku ba su abinci.” Babu shakka, sun yi mamaki domin gurasa biyar da kifaye biyu kaɗai ne suke da shi.

3 Yesu ya ji tausayinsu kuma ya ciyar da su. Wannan mu’ujizar ce kaɗai dukan marubutan Linjila huɗu suka ambata. (Mar. 6:35-44; Luk 9:10-17; Yoh. 6:1-13) Yesu ya sa almajiransa su gaya wa mutanen su zauna hamsin-hamsin da ɗari-ɗari a kan ciyawa. Bayan Yesu ya yi addu’a, sai ya gutsuttsura gurasan kuma ya rarraba kifin. Maimakon Yesu ya ba mutanen abincin da kansa, sai ya miƙa wa almajiran su kuma suka raba wa “taron” kuma kowa ya ci ya ƙoshi. Hakika, Yesu ya ciyar da dubbai ta hannun mutane ƙalilan, wato almajiransa.a

4. (a) Yesu ya fi damuwa da yin tanadin wane irin abinci, kuma me ya sa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?

4 Yesu ya fi damuwa da yadda zai koya wa mabiyansa game da Allah. Ya san cewa koya musu Kalmar Allah za ta sa su samu rai madawwami. (Yoh. 6:26, 27; 17:3) Yesu ya ji tausayin taron shi ya sa ya ciyar da su kuma ya yi sa’o’i da yawa yana koyar da mabiyansa. (Mar. 6:34) Amma ya san cewa ba zai daɗe a duniya ba domin zai koma sama. (Mat. 16:21; Yoh. 14:12) Ta yaya Yesu zai ciyar da mabiyansa da ke duniya daga sama? Zai bi tsarin da ya kafa, wato ciyar da jama’a ta hannun mutane ƙalilan. Su waye ne ƙalilan? A wannan talifin, za mu ga yadda Yesu ya ciyar da mabiyansa shafaffu da yawa a ƙarni na farko ta hannun mutane ƙalilan. A talifi na gaba, za mu tattauna wannan tambayar da ke da muhimmanci ga kowannenmu: Ta yaya za mu san mutane ƙalilan da Kristi yake amfani da su wajen ciyar da mu a yau?

YESU YA ZAƁI MUTANE ƘALILAN

5, 6. (a) Mene ne Yesu ya yi don ya tabbata cewa an ciyar da mabiyansa bayan mutuwarsa? (b) Ta yaya Yesu ya shirya mabiyansa don wani aiki mai muhimmanci?

5 Maigidan kirki yana shirya yadda za a kula da iyalinsa idan ya mutu. Hakazalika, Yesu wanda zai zama Shugaban ikilisiyar Kirista ya yi shirye-shirye don a ci gaba da kula da mabiyansa bayan mutuwarsa. (Afis. 1:22) Alal misali, kusan shekara biyu kafin Yesu ya mutu, ya tsai da shawara mai muhimmanci. Ya zaɓi mutane ƙalila na farko da zai yi amfani da su wajen ciyar da jama’a. Bari mu tattauna abin da ya faru.

6 Bayan Yesu ya yi dare yana addu’a, sai ya zaɓi manzanni 12 daga cikin almajiransa. (Luk 6:12-16) Waɗannan manzannin sun zama aminansa a sauran shekaru biyu da ya yi kafin ya mutu, don ya koyar da su ta kalamai da kuma misalansa. Ya san cewa suna da abubuwa da yawa da za su koya, hakika an ci gaba da kiransu ‘almajirai.’ (Mat. 11:1; 20:17) Yesu ya ba su shawara kuma ya koyar da su sosai a hidima. (Mat. 10:1-42; 20:20-23; Luk 8:1; 9:52-55) Yana shirya su don aiki mai muhimmanci da za su yi bayan ya mutu kuma ya koma sama.

7. Ta yaya Yesu ya ambata aikin da manzanninsa za su fi mai da wa hankali?

7 Wane aiki ne manzannin za su yi? Sa’ad da ranar Fentakos ta shekara ta 33 ta kusa, ya kasance a bayyane cewa waɗannan manzannin ne za su zama masu kula. (A. M. 1:20) Amma, wane aiki ne za su fi mai da wa hankali? Yesu ya ɗan ambata hakan a taɗinsa da manzo Bitrus bayan ya tashi daga matattu. (Karanta Yohanna 21:1, 2, 15-17.) Sa’ad da suke tare da sauran manzannin, Yesu ya ce wa Bitrus: “Ka yi kiwon ’ya’yan tumakina.” Ta hakan, Yesu ya nuna cewa manzanninsa suna cikin ƙalilan da zai yi amfani da su wajen yin tanadin abubuwa da za su taimaka wa mutane da yawa su kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Hakika, abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa yana ƙaunar ‘’ya’yan tumakinsa’ sosai.b

YA SOMA CIYAR DA SU DAGA RANAR FENTAKOS

8. Shin sababbin Kiristoci sun san waɗanda za su koyar da su kuwa? Ka bayyana.

8 Tun daga ranar Fentakos ta shekara ta 33, Yesu ya ci gaba da yin amfani da manzanninsa don koyar da sauran almajiransa shafaffu. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:41, 42.) Yahudawa da kuma sauran ’yan al’ummai da suka zama shafaffun Kiristoci a ranar sun fahimci cewa Yesu yana amfani da waɗannan manzannin. Saboda haka, sun ci gaba da “lizima a cikin koyarwar manzanni.” Hakan yana nufi cewa sun ci gaba da bin koyarwar da aminci. Sababbin Kiristocin sun san cewa suna bukatar su ci gaba da koyon gaskiya, kuma sun san waɗanda za su iya koyar da su. Sun amince da manzannin sosai, kuma sun ci gaba da neman bayani game da ayyukan Yesu da kuma annabcin da aka yi a kansa.c—A. M. 2:22-36.

9. Ta yaya manzannin suka nuna cewa ba su yi watsi da aikinsu na kula da tumakin Yesu ba?

9 Manzannin ba su taɓa yin watsi da aikinsu na kula da tumakin Yesu ba. Alal misali, ka yi la’akari da abin da suka yi sa’ad da wata matsala da za ta iya jawo tsatsaguwa ta taso a wannan sabuwar ikilisiya. Sa’ad da ake rarraba wa gwauraye abinci, ana mai da hankali ga mata Ibraniyawa fiye da mata Helenawa. Ta yaya manzannin suka warware wannan matsalar? ‘Su goma sha biyun’ sun naɗa ƙwararrun maza bakwai don su kula da harkar rarraba abinci. Yawancin manzannin sun rarraba wa jama’a abinci a lokacin Yesu, amma yanzu sun fahimci cewa ya fi muhimmanci su mai da hankali ga koyarwa. Shi ya sa suka lizima ga ‘hidimar kalmar.’—A. M. 6:1-6.

10. Ta yaya Kristi ya yi amfani da manzanni da kuma dattawa da ke Urushalima?

10 An daɗa wasu ƙwararrun dattawa ga sauran manzanni da suke da rai a shekara ta 49 a zamanin Yesu. (Karanta Ayyukan Manzanni 15:1, 2.) Manzanni da dattawa da ke Urushalima ne hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin. A matsayin Shugaban ikilisiya, Kristi ya yi amfani da wannan ƙaramin rukuni na ƙwararrun maza don ya warware wasu batutuwa na koyarwa. Ya kuma yi amfani da su don ya kula da kuma ja-goranci wa’azi da koyarwa ta bisharar Mulki.—A. M. 15:6-29; 21:17-19; Kol. 1:18.

11, 12. (a) Me ya nuna cewa Jehobah ya albarkaci tsarin da Ɗansa ya bi don ya ciyar da ikilisiyoyi a ƙarni na farko? (b) Ta yaya tsarin da Kristi ya bi ya kasance a bayyane?

11 Shin Jehobah ya albarkaci tsarin da Ɗansa ya bi don ya ciyar da ikilisiyoyi a ƙarni na farko? Babu shakka! Ta yaya muka sani? Don littafin Ayyukan Manzanni sura ta 16:4, 5 sun ce: “[Manzo Bulus da abokansa] suna cikin tafiyarsu, suna bibbiyan birane, sai suka yi ta baba su hukunce-hukunce, waɗanda manzanni da dattiɓai da ke cikin Urushalima suka hukunta, domin su kiyaye su. Ikilisiyai fa suka ƙarfafa cikin imani, yawansu yana ƙaruwa kowace rana.” Waɗannan ikilisiyoyi sun samu ci gaba don sun ba da haɗin kai ga hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin. Hakan tabbaci ne cewa Jehobah ya albarkaci tsarin da Ɗansa ya yi amfani da shi don ya ciyar da ikilisiyoyi. Ya kamata mu tuna cewa idan Jehobah bai albarkace mu ba, ba za a samu ci gaba a tanadin da ya yi don a bauta masa ba.—Mis. 10:22; 1 Kor. 3:6, 7.

12 Mun tattauna cewa Yesu ya bi wani tsari don ya ciyar da mabiyansa, wato ya ciyar da jama’a ta hannun mutane ƙalilan. Tsarin a bayyane yake sarai ga mutane. Manzanni da suke cikin hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin sun nuna tabbaci cewa Jehobah yana goyon bayansu. Littafin Ayyukan Manzanni 5:12 ya ce: “Aka gudana da alamu da al’ajibai dayawa ta hannuwan manzannin a cikin jama’a.”d Saboda haka, waɗanda suka zama Kiristoci ba za su yi mamaki ba suna tambaya, ‘Su waye ne Kristi yake amfani da su don ya ciyar da tumakinsa?’ Amma, yanayin ya canja a ƙarshen ƙarni na farko.

SA’AD DA CIYAYIN SUKA FI ALKAMAR YAWA

13, 14. (a) Wane gargaɗi ne Yesu ya ba da, kuma a wane lokaci ne kalamansa suka soma cika? (b) Ta yaya za a yi wa ikilisiyar hamayya? (Ka duba ƙarin bayani.)

13 Yesu ya annabta cewa ikilisiyar Kirista za ta fuskanci hamayya. A annabcin da ya yi game da alkama da ciyayi, ya ce za a shuka ciyayi (jabun Kiristoci) cikin gonar alkama (Kiristoci shafaffu). Yesu ya kuma ce za a bar rukunin su yi girma tare har lokacin kaka, wato a “matuƙar zamani.” (Mat. 13:24-30, 36-43) Annabcin Yesu bai daɗe ba kafin ya soma cika.e

14 A ƙarni na farko, wasu ’yan’uwa sun zama ’yan ridda amma manzannin Yesu masu aminci sun ‘hana’ su yaɗa koyarwar ƙarya. (2 Tas. 2:3, 6, 7) Bayan manzo na ƙarshe ya mutu, sai koyarwar ƙarya ta yi jijiya kuma ta yaɗu har na tsawon shekaru da yawa. Ƙari ga hakan, a wannan lokacin ne ciyayi suka fi alkama yawa, kuma babu tsarin da ake bi don koyar da Kalmar Allah. Hakan zai canja, amma a wane lokaci?

WANE NE ZAI CIYAR DA MUTANE A LOKACIN KAKA?

15, 16. Mene ne sakamakon nazarin Nassosi da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi, kuma wace tambaya ce hakan ya sa aka yi?

15 Yayin da ƙarshen lokacin girmar alkamar da ciyayin ya yi kusa, mutane da yawa suka soma son koyarwar Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1870 zuwa 1879, wani ƙaramin rukunin mutane masu son gaskiya suka kafa azuzuwa na koyon Littafi Mai Tsarki. Wannan azuzuwan ba na cocin Kiristendom ba ne. Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun bincika Nassosin sosai.—Mat. 11:25.

16 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun samu sakamako mai kyau don nazarin Nassosi da suka yi. Sun fallasa koyarwar ƙarya kuma suka yaɗa na gaskiya, sun wallafa da kuma rarraba littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a dukan duniya. Aikinsu ya daɗaɗa zuciyar mutane da yawa masu son gaskiya kuma ya tabbatar musu cewa koyarwar Allah ne. Amma tambayar ita ce: Shin Kristi ya yi amfani da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da ke duniya kafin shekara ta 1914 don ya ciyar da tumakinsa? A’a. Ciyayi da alkama suna girma tare a lokacin, kuma ana kan kafa tsarin yadda za a riƙa gudanar da koyarwar Allah. Lokaci bai yi ba da za a ware jabun Kiristoci daga Kiristoci na gaskiya.

17. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne suka soma faruwa a shekara ta 1914?

17 Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, lokacin kaka ya soma a shekara ta 1914. A wannan shekarar, abubuwa da yawa masu muhimmanci sun soma faruwa. Yesu ya zama sarki a shekarar, kuma aka shiga kwanaki na ƙarshe. (R. Yoh. 11:15) Daga shekara ta 1914 zuwa farkon shekara ta 1919, Yesu ya bi Ubansa don su yi bincike da kuma tsabtace tsarin bauta.f (Mal. 3:1-4) An soma tattara alkamar, wato Kiristoci shafaffu a shekara ta 1919. Shin lokaci ya yi da Kristi zai kafa tsari na koyar da kalmar Allah? Ƙwarai kuwa!

18. Mene ne Yesu ya ce zai yi, kuma wace tambaya m ai muhimmanci game da kwanaki na ƙarshe aka yi?

18 A annabcin da Yesu ya yi game da kwanaki na ƙarshe, ya ce zai kafa tsari na ba da ‘abinci a lotonsa.’ (Mat. 24:45-47) Ta wace hanya ce Yesu zai yi hakan? Kamar yadda ya yi a ƙarni na farko, zai ciyar da jama’a ta hannun mutane ƙalilan. Amma yayin da aka shiga kwanaki na ƙarshe, tambaya mai muhimmanci ita ce, Su waye ne mutane ƙalilan? Za mu tattauna wannan tambayar da kuma wasu game da annabcin Yesu a talifi na gaba.

a Sakin layi na 3: A wani lokaci kuma da Yesu ya ciyar da maza 4,000 tare da mata da yara, ya miƙa wa almajiran su kuma suka raba wa “taron.”—Mat. 15:32-38.

b Sakin layi na 7: A lokacin da Bitrus yake da rai, ‘’ya’yan tumakin’ suna daraja begensu na zuwa sama.

c Sakin layi na 8: Da yake sababbin almajirai sun ci gaba da “lizima a cikin koyarwar manzanni,” hakan ya nuna cewa manzannin suna koyarwa a kai a kai. A yanzu, wasu koyarwa da manzannin suka yi yana rubuce a cikin hurarrun littattafan Nassosin Helenanci na Kirista.

d Sakin layi na 12: Kiristoci ma da ba manzanni ba ne sun samu baiwar ruhu ta hanyar mu’ujiza. Amma kamar dai a yawancin lokaci, manzon ne da kansa ya ba wasu baiwar ko kuma hakan ya faru a gabansa.— A. M. 8:14-18; 10:44, 45.

e Sakin layi na 13: Furucin manzo Bulus da ke Ayyukan Manzannin 20:29, 30 ya nuna cewa ikilisiyar za ta fuskanci hamayya ta hanyoyi biyu. Na farko, jabun Kiristoci (ciyayi) za su ‘shiga wurin’ Kiristoci na gaskiya. Na biyu, ‘daga cikin’ Kiristoci na gaskiya wasu za su zama ’yan ridda, suna faɗin “karkatattun zantuttuka.”

f Sakin layi na 17: Ka duba talifin nan “Ga Shi, Ina Tare da Ku Kullayaumi” a cikin wannan mujallar, shafi na 11, sakin layi na 6..

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba