AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU
Shin zai dace iyaye Kiristoci su zauna tare da ɗansu da aka yi wa yankan zumunci a taron ikilisiya?
Babu wani dalilin da zai sa mu damu da inda wanda aka yi wa yankan zumunci ya zauna a cikin Majami’ar Mulki. Littattafanmu sun ƙarfafa iyaye su taimaki ’ya’yansu da aka yi wa yankan zumunci da har ila suna zama tare da su a gida a batun ibada idan suna ganin yin hakan ya dace. Kamar yadda aka bayyana a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1988, shafuffuka na 19 da 20, iyaye za su iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yaransu ƙanana da aka yi wa yankan zumunci. Ta hakan, wataƙila yaron ya sami ƙarfafa da za ta sa ya daidaita halayensa.a
Ba laifi ba ne yaron da aka yi wa yankan zumunci ya zauna shiru tare da iyayensa a Majami’ar Mulki. Tun da yake ba a ajiye kujerar baya a Majami’ar Mulki don waɗanda aka yi wa yankan zumunci ba, ba laifi ba ne yaron da aka yi wa yankan zumunci ya zauna kusa da iyayensa ko da a gaba suka zauna. Yayin da iyaye suke ƙoƙarin taimaka wa ɗansu ya daidaita dangantakarsa da Jehobah, babu shakka, za su kuma so ya amfana sosai daga taro. Saboda haka, iyayen za su iya taimaka wa ɗansu idan ba su ƙyale shi ya zauna a wani wuri dabam ba.
A ce yaron da aka yi wa yankan zumunci ba ya zama tare da iyayensa, shin hakan yana nufi cewa ba zai iya zama tare da su a Majami’ar Mulki ba? A dā littattafanmu sun tattauna irin halin da ya kamata Kiristoci su kasance da shi idan ya zo ga batun tarayya da danginsu da aka yi wa yankan zumunci da ba ya zama a gida tare da su.b Amma, akwai bambanci tsakanin waɗannan yanayi biyu: Na farko, mutumin da aka yi wa yankan zumunci ya zauna ba tare da damun kowa ba kusa da danginsa sa’ad da ake taro da kuma na biyu, danginsa suna yin cuɗanya da bai dace ba da shi. Bai kamata kowa ya damu kansa ba, idan dangin mutumin da aka yi wa yankan zumunci suna da ra’ayin da ya dace game da shi, kuma suna ƙoƙari su bi gargaɗin da ke cikin Nassosi game da yin cuɗanya da shi.—1 Kor. 5:11, 13; 2 Yoh. 11.
Saboda haka, kada kowa ya dami kansa idan mutumin da aka wa yankan zumunci ya zauna kusa da danginsa ko kuma wani mai shela a cikin Majami’ar Mulki idan bai damu kowa ba. Hana mutum zama a duk inda yake so zai iya jawo matsaloli dabam-dabam, dangane ga yanayin. Amma, idan danginsa suna ƙoƙartawa su bi ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki game da yankan zumunci kuma hakan ba ya sa wasu tuntuɓe, bai kamata kowa ya damu da yadda ’yan’uwan suka zauna sa’ad da ake taro ba.
a Ko da yake wannan talifin yana magana game da namiji da aka yi wa yankan zumunci, amma batun ya shafi ta mace ma.
b Ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” shafuffuka na 207-209.