ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WANE SAƘO NE KE LITTAFI MAI TSARKI?
Me Ya Sa Zai Dace Ka San Abin da Ke Littafi Mai Tsarki?
Littafi Mai Tsarki ne littafin da mutane suka fi sani a cikin duniya duka. Me ya sa? Ɗaya daga cikin dalilan shi ne, labaran da ke ciki abubuwa ne da mutane da yawa a yau suke shaidawa. Yana ɗauke da labaran gaskiya game da mutane da suka rayu a dā, dangantaka da ke tsakanin su da juna da kuma Allah. Waɗannan labaran da aka rubuta da kalmomi masu sauƙin fahimta suna koya mana darussa da yawa. Ƙari ga haka, ana iya fassara su zuwa ɗarurruwan harsuna da mutane da yawa a wurare dabam-dabam suke ji. Kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna da amfani a kowane lokaci.
Mafi muhimmanci ma, Littafi Mai Tsarki littafi ne daga wurin Allah kuma yana tattauna batutuwa da yawa game da Allah. Ya bayyana sunan Allah da halinsa da kuma nufinsa da ba zai canja ba ga duniya da ’yan Adam. Littafi Mai Tsarki ya kuma bayyana yadda Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehobah tun da daɗewa, da kuma yadda Jehobah zai tabbatar cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, sa’an nan ya kawar da mugunta. Karanta Littafi Mai Tsarki da niyyar koyo zai taimaka wa mutane su kasance da bangaskiya da kuma bege.
A cikin Littafi Mai Tsarki, muna iya samun bayanai da ba za mu taɓa samu a wani wuri ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana gaskiya game da batutuwa kamar waɗannan:
Yadda muka soma wanzuwa da kuma dalilin da ya sa muke shan wahala
Abin da Allah ya yi don ya ceci ’yan Adam
Abin da Yesu ya yi mana
Abin da zai faru da duniya da kuma ’yan Adam a nan gaba
Don Allah ka karanta abin da ke shafuffuka na gaba don ka san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.