AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Matattu za su sake rayuwa kuwa?
Mutuwa tana kama da barci domin matattu ba su san kome ba, kuma ba za su iya yin wani abu ba. Amma Mahaliccinmu zai iya sake ta da waɗanda suka mutu. Domin ya nuna cewa hakan zai iya yiwuwa, Allah ya ba Yesu iko ya ta da mutane da dama.—Karanta Mai-Wa’azi 9:5; Yohanna 11:11, 43, 44.
A wace hanya ce mutuwa take kama da barci?
Allah ya yi alkawari cewa zai ta da matattu da yake tuna da su don su zauna a cikin sabuwar duniya da ke cike da adalci. Waɗanda suka mutu za su ci gaba da kasancewa hakan har sai Allah ya ta da su. Allah Maɗaukaki yana ɗokin yin amfani da ikonsa wajen ta da su daga mutuwa.—Karanta Ayuba 14:14, 15.
Mene ne tashin matattu zai ƙunsa?
Idan Allah ya ta da mutane, za su iya gane kansu da abokansu da kuma iyalansu. Ko da jikin mutum ya ruɓe, Allah zai iya ta da wannan mutumin da wani sabon jiki kuma.—Karanta 1 Korintiyawa 15:35, 38.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a cikin waɗanda za a ta da, wasu za su zauna a duniya, wasu kuma za su je sama. (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Amma, mafi yawan mutane da za a ta da su za su zauna a cikin aljanna a duniya. Waɗannan za su sami damar sake soma rayuwa, kuma za su iya yin hakan har abada.—Karanta Zabura 37:29; Matta 5:5; Ayyukan Manzanni 24:15.