Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 10/15 pp. 31-32
  • Za Ka Iya Daɗa Ƙwazo a Yi wa Mutane Gargaɗi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Daɗa Ƙwazo a Yi wa Mutane Gargaɗi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YESU BAI TAƁA KASALA A WA’AZI BA
  • SUN YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI
  • KA YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI
  • Kuɗi Yana Kawo Farin Ciki na Gaske Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 10/15 pp. 31-32

Za Ka Iya Daɗa Gargaɗar da Mutane da Ƙwazo?

A somawar ƙarni na ashirin, mutane sun ji daɗin wani fim marar sauti mai suna A Trip Down Market Street. Fim ɗin ya nuna yadda ake rayuwa a farkon ƙarni na 20 a birnin San Francisco da ke Amirka. Waɗanda suka shirya fim ɗin sun yi amfani da kyamarar da aka kafa a gaban wani irin motar sufuri kuma suka saita kyamarar a kan wani titi mai cike da mutane. Fim ɗin ya nuna karusa da motoci na zamanin dā da mutane suna saye-saye da kuma yara masu sayar da jaridu.

Abin da ya daɗa sa fim ɗin ya zama abin tausayi shi ne wataƙila an shirya wannan fim a watan Afrilu na shekara ta 1906, wato kafin a yi wata mummunar girgizar ƙasa da wuta da ta halaka fiye da mutane dubu uku a ranar 18 ga Afrilu na wannan shekarar. Kuma bala’in ya kusan halaka wannan ɓangaren birnin. Wataƙila wasu da aka nuna a cikin fim ɗin, kwanaki kaɗan ne kawai ya rage musu a duniya. Wani dangin waɗanda suka shirya fim ɗin mai suna Scott Miles ya ce: “Ina kallon waɗannan mutanen kuma suna ba ni tausayi don ba su san abin da zai faru da su ba.”

Za mu iya kwatanta abin da ya faru a lokacin da zamaninmu. Yanayin maƙwabtanmu, abin tausayi ne a gare mu. Suna al’amuransu na yau da kullum ba tare da sanin bala’in da ke tafe ba, wato halakar wannan mugun zamani. Amma wannan bala’in ba kamar girgizar ƙasa ba ne da ke aukuwa ba zato ba tsammani. Muna da ɗan lokaci na yi wa mutane gargaɗi game da ranar hukunci na Jehobah. Wataƙila ka keɓe lokaci don yin wa’azi gida-gida kowane mako, shin za ka iya daɗa ƙwazo a yi wa mutane gargaɗi?

YESU BAI TAƁA KASALA A WA’AZI BA

Yana da kyau mu yi la’akari da misalin Yesu don bai taɓa kasala a wa’azi ba. Ya yi wa dukan waɗanda ya haɗu da su wa’azi, wannan ya haɗa da mai karɓan haraji da ya haɗu da shi a hanya da kuma wata mata da ya haɗu da ita a bakin rijiya yayin da yake hutawa da rana. (Luk 19:1-5; Yoh. 4:5-10, 21-24) Yesu ya yi amfani da dukan zarafin da ya samu don ya koyar da mutane, har a lokacin hutunsa. Yesu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya koyar da maƙwabtansa don yana tausayinsu. (Mar. 6:30-34) Ta yaya masu shela a yau suke bin misalin Yesu a yin wa’azi da gaggawa?

SUN YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI

Wata ’yar’uwa mai suna Melika tana zama a wani gida mai tsaro sosai. Yawancin maƙwabtanta ɗalibai ne daga ƙasashen waje. Suna amfani da wayar selula kuma sunayensu da lambobin wayarsu ba sa cikin takardar da ke ɗauke da jerin sunayen waɗanda ke zama a gidan da ake ajiyewa a zauren. Tana amfani da dukan zarafin da ta samu don tattaunawa da su game da saƙon Littafi Mai Tsarki sa’ad da ta haɗu da su a zauren gidan ko kuma a cikin lif. Ta ce, “A wani fannin, na ɗauki wannan gidan a matsayin yankina na yin wa’azi.” Melika tana kasancewa da littattafanmu da aka wallafa a harsuna dabam-dabam a kowane lokaci, kuma maƙwabtanta da yawa sukan karɓi warƙoƙi da mujallu. Ƙari ga haka, takan nuna musu yadda za su shiga dandalinmu na jw.org. A sakamakon haka, ta soma yin nazari da mutane da dama.

Wata ’yar’uwa mai suna Sonia ma tana amfani da duk zarafin da ta samu don yin wa’azi. Tana aiki a wani asibiti mai zaman kansa kuma ta ƙudurta cewa za ta yi wa dukan abokan aikinta wa’azi. Da farko ta yi ƙoƙari ta gano abin da kowannensu yake bukata da kuma abin da suke son tattaunawa a kai. Kuma tana amfani da lokacin hutun rana don yi wa kowannensu wa’azi game da Littafi Mai Tsarki. A sakamako, ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane biyu. Ƙari ga haka, tana shirin yin amfani da hutunta na rana don tattaunawa da waɗanda suka zo ganin likita.

KA YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI

Wani mutumin da ya tsira daga wannan girgizar ƙasa da aka ambata a sama da ta auku a shekara ta 1906 ya ce: “Wannan shi ne bala’i mafi muni da ya taɓa addabar wani jiha ko kuma birni.” Duk da haka, babu irin bala’in da zai kai hukuncin da za a yi wa “waɗanda ba su san Allah ba.” (2 Tas. 1:8) Jehobah yana son mutane su saurari gargaɗin da Shaidunsa suke yi.—2 Bit. 3:9; R. Yoh. 14:6, 7.

Za ka iya yin amfani da dukan zarafin da ka samu don yi wa mutane wa’azi sa’ad da kake harkokinka na yau da kullum?

Kana da gatan taimaka wa mutane su fahimci cewa muna rayuwa ne a miyagun zamanu, saboda haka, ya kamata su soma bauta wa Jehobah maimakon biɗan bukatunsu. (Zaf. 2:2, 3) Shin za ka iya yin amfani da dukan zarafi da ka samu don yin wa’azi ga abokan aikinka da maƙwabtanka da kuma waɗanda kake haɗuwa da su sa’ad da kake harkokinka na yau da kullum? Za ka daɗa yin ƙoƙari don ka yi wa mutane gargaɗi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba