Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/10 pp. 1-3
  • Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Soma Taɗi da Burin Yin Wa’azi
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 8/10 pp. 1-3

Za Ka Iya Yin Wa’azi Sa’ad da Ka Samu Zarafi!

1. (a) Menene ma’anar yin wa’azi sa’ad da aka samu zarafi? (b) Mutane nawa ne da suke wannan taron suka fara sanin gaskiya ta hanyar yin wa’azi sa’ad da aka samu zarafin yin hakan?

1 A cikin ikilisiyarku, mutane nawa ne suka san gaskiya don wani ya yi musu wa’azi sa’ad da ya samu zarafin yin hakan? Adadin zai ba ka mamaki. Yin wa’azi sa’ad da aka samu zarafi ya ƙunshi yi wa mutane da muke saduwa da su a rayuwarmu ta yau da kullum magana game da bishara, wato, sa’ad da muke tafiya, ziyartar ’yan’uwa ko maƙwabta, ko yin sayayya, a makaranta, a wurin aiki da sauran su. A wani rukuni na Masu Shela fiye da ɗari biyu da suka yi baftisma, an soma yi wa kashi arba’in cikinsu magana ne sa’ad da aka samu zarafi! Saboda haka, wannan hanya ta yin wa’azi tana da amfani sosai.

2. Waɗanne misalan yin wa’azi sa’ad da aka samu zarafi ne suke cikin Nassosi?

2 Masu wa’azin bishara a ƙarni na farko sukan yi wa’azi sa’ad da suka samu zarafin yin hakan. Alal misali, sa’ad da yake wucewa ta garin Samariya, Yesu ya yi wa wata mata da take ɗibar ruwa a rijiyar Yakubu wa’azi. (Yoh. 4:6-26) Filibus ya soma tattaunawa da Bahabashe ma’aikacin kotu da ke karanta littafin Ishaya ta wurin tambayarsa: “Ka fahimci abin da ka ke karantawa?” (A. M. 8:26-38) Sa’ad da manzo Bulus yake cikin kurkuku a ƙasar Filibi, ya yi wa ma’aikacin kurkukun wa’azi. (A. M. 16:23-34) Daga baya, sa’ad da yake tsare a gida, Bulus “yana karɓan dukan waɗanda suka shigo wurinsa, yana wa’azin mulkin Allah, yana koyarwa da al’amura na wajen Ubangiji Yesu Kristi.” (A. M. 28:30, 31) Ko da kana jin kunya, za ka iya yin wa’azi sa’ad da ka samu zarafin yin haka. Ta yaya?

3. Me zai iya taimaka mana mu daina jin kunya?

3 Somawa: Yana yi wa mutane da yawa a cikinmu wuya mu soma yi wa baƙi wa’azi. Yi wa waɗanda ba mu sani ba sosai wa’azi zai iya kasance da wuya. Za mu iya samun gaba gaɗin yin magana, idan mun yi bimbini a kan alherin Jehobah, gaskiya mai tamani da ya ba bayinsa, da kuma yanayi marar kyau na mutane a duniya. (Yun. 4:11; Zab. 40:5; Mat. 13:52) Ƙari ga hakan, za mu iya gaya wa Jehobah ya taimaka mana mu samu “ƙarfin hali.” (1 Tas. 2:2) Wani ɗalibin makarantar Giliyad ya ce: “Na fahimci cewa yin addu’a tana taimako sa’ad da ya kasance mini da wuya na yi wa mutane magana.” Idan kana jinkirin yin wa’azi, ka yi gajeriyar addu’a a zuciyarka.—Neh. 2:4.

4. Wane maƙasudi ne za mu iya soma kafa wa kanmu, kuma me ya sa?

4 Kamar yadda sunan ya nuna, ba a bukatar soma yin wa’azi sa’ad da aka samu zarafin yin hakan da gabatarwa ko kuma da nassi kamar yadda ake yi sa’ad da ake yin wa’azi a gida zuwa gida. Za mu iya ganin amfanin kasancewa da maƙasudin soma tattaunawa ba tare da jin cewa lallai sai mun ba da shaida nan take ba. Masu shela da yawa sun faɗi cewa yin hakan yana ba su gaba gaɗin da suke bukata don gabatar da bishara. Ba a bukata a tilasta wa mutumin idan ba shi da niyyar tattaunawa. Ka kammala tattaunawar da fara’a kuma ka tafi.

5. Menene ya taimaki wata ’yar’uwa mai jin kunya ta yi wa’azi sa’ad da ta sami zarafin yin hakan?

5 Sa’ad da wata ’yar’uwa da ke jin kunya take sayayya a kasuwa, ta fara da haɗa ido da mutumin sai ta yi murmushi. Idan mutumin ma ya yi murmushi, sai ta ɗan yi magana. Idan mutumin ya amsa da kyau, yana ba ta gaba gaɗin yin ƙarin bayani. Sai ta saurara sosai kuma ta nemi fahimtar ɓangaren bisharar da zai dace da mutumin. Ta yin hakan, ta samu damar ba da littattafai masu yawa da kuma soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.

6. Ta yaya za mu iya soma tattaunawa sa’ad da muka samu zarafin yin hakan?

6 Soma Tattaunawa: Me za mu iya faɗa don soma tattaunawa? Sa’ad da Yesu yake tattaunawa da macen a bakin rijiya, ya soma ne ta roƙonta ta ba shi ruwa ya sha. (Yoh. 4:7) Saboda haka za mu iya soma tattaunawa ta yin gaisuwa cikin fara’a ko kuma yin tambaya. Yayin da kuke tattaunawa za ka iya samun zarafin gabatar da wata Nassi kuma wataƙila ka shuka iri na gaskiya. (M. Wa. 11:6) Wasu sun yi nasara ta wajen yin magana mai ta da marmari da zai sa a yi tambaya. Alal misali, sa’ad da kake jiran ganin likita, za ka iya soma tattaunawa ta cewa, “Zan yi farin ciki sosai sa’ad da ba zan ƙara yin ciwo ba.”

7. Ta yaya lura da abubuwan da suke faruwa kusa da mu za su taimaka mana mu yi wa’azi sa’ad da muka samu zarafin yin hakan?

7 Lura da abubuwan da ke faruwa kusa da mu zai kuma taimaka mana mu soma tattaunawa. Idan mun lura da iyaye da suke da yara masu biyayya sosai, za mu iya yaba wa iyayen, kuma mu tambaye su, “Menene ya taimake ku ku zama iyaye masu nasara?” Wata ’yar’uwa ta lura da batun da mutane suke yawan tattaunawa a wurin aiki, da hakan sai ta ba da ainihi bayani a kan batun da ke zuciyar abokan aikinta. Sa’ad da ta samu labari cewa wata mata da suke aiki tare tana son ta yi aure, sai ta ba ta mujallar Awake! da ke magana a kan yadda za a iya yin shirin aure. Hakan ya sa suka daɗa tattauna Littafi Mai Tsarki.

8. Ta yaya za mu iya yin amfani da littattafanmu don soma tattaunawa?

8 Wata hanya kuma da za mu iya soma tattaunawa ita ce ta karanta littattafanmu a inda wasu za su iya ganin mu. Wani ɗan’uwa ya buɗe wani talifi na Hasumiyar Tsaro ko Awake! wanda jigonsa ke ta da marmari sai ya soma karantawa. Idan ya lura da wani da ke kusa da shi yana kallon mujallar, sai ya yi tambaya ko kuma ya yi ’yan kalamai a kan talifin. Yin hakan yana yawan kai ga soma tattaunawa da kuma ba da shaida. Ajiye ɗaya daga cikin littattafanmu inda wasu za su iya ganinsa zai iya ta da marmarin abokan aikinmu ko abokan ajinmu kuma ya motsa su su yi tambaya game da littafin.

9, 10. (a) Ta yaya za mu iya neman zarafi don yin shaida sa’ad da muka samu damar yin hakan? (b) Ta yaya ka samu damar yin hakan?

9 Neman Zarafi: Domin gaggawar aikin wa’azi, bai kamata mu ɗauki yin wa’azi sa’ad da muka samu zarafi kamar abin da za mu iya yi sa’ad da muka ga dama ba. Maimakon hakan, ya kamata mu nemi zarafi don yin wa’azi yayin da muke ayyukanmu na yau da kullum. Ka yi tunani game da mutane da wataƙila za ka iya saduwa da su, kuma ka yi la’akari da yadda za ka iya soma tattaunawa da fara’a. Ka riƙe Littafi Mai Tsarki da mujallu da za ka iya amfani da su don tattaunawa da waɗanda suke da marmari.—1 Bit. 3:15.

10 Ta kasancewa masu hikima, masu shela da yawa sun samu hanyoyi na neman zarafin ba da shaida sa’ad da suka samu zarafi. Wata ’yar’uwa da take zama a gida mai tsaro sosai ta ajiye hoton yanayi mai kyau a wurin shaƙatawa da ke gidan. Idan masu wucewa sun tsaya suka yi kalamai a kan kyaun hoton, sai ta yi amfani da zarafin ta soma tattaunawa kuma ta gaya musu game da alkawarin Littafi Mai Tsarki na “sabuwar sama da sabuwar duniya.” (R. Yoh. 21:1-4) Za ka iya yin tunanin hanyoyin da za ka nemi zarafi don ba da shaida sa’ad da ka samu zarafin yin hakan?

11. Ta yaya za mu iya ci gaba da tattaunawa da wanda muka yi wa wa’azi sa’ad da muka samu zarafi?

11 Ka Koma Ziyara: Idan ka sadu da mai son saƙon, ka koma ziyara wurinsa. Idan ya dace, za ka iya gaya wa mutumin: “Na more tattaunawa da kai sosai. A ina zan iya sake ganinka don mu ci gaba da tattaunawa?” Wasu masu shela suna ba mutumin adireshinsu da lambar wayarsu sai su ce: “Na ji daɗin tattaunawarmu. Idan za ka so ka samu ƙarin bayani game da abin da muka tattauna, ga inda za ka iya sake gani na.” Idan ba za ka iya koma ziyara wurin wanda ke son saƙon ba, ka yi shiri don wata ikilisiya da ta dace ta yi hakan ta wurin cika fam ɗin nan Please Follow Up (S-43) kuma ka ba sakataren ikilisiyarku.

12. (a) Me ya sa ya dace mu riƙa rubuta lokacin da muka yi wa’azi sa’ad da muka samu zarafi? (b) Wane sakamako ne aka samu don yin wa’azi sa’ad da muka samu zarafin yin hakan? (Duba akwatin nan “Sakamakon Yin Wa’azi Sa’ad da Aka Samu Zarafi!”)

12 Ya dace mu ba da rahoton lokacin da muka yi amfani da shi don yin wa’azi sa’ad da muka samu zarafi. Saboda haka, ka tabbata cewa ka rubuta lokacin a cikin takarda, ko da ’yan mintoci ne a rana. Ka yi la’akari da wannan: Idan kowanne mai shela ya yi wa’azi na minti biyar sa’ad da ya samu zarafi a kowacce rana, za a samu adadin awoyi miliyan sha bakwai a duk wata!

13. Menene ya kamata ya motsamu mu ba da shaida sa’ad da muka samu zarafin yin hakan?

13 Muna da dalili mafi kyau na ba da shaida sa’ad da muka samu zarafi, wato, ƙaunar Allah da maƙwabta. (Mat. 22:37-39) Idan muna nuna godiya ga halayen Jehobah da ƙudurinsa, hakan zai motsamu mu yi magana game da ‘ɗaukakar mulkinsa.’ (Zab. 145:7, 10-12) Kulawa da maƙwabtanmu sosai zai motsamu mu yi amfani da kowacce zarafi don shaida bishara yayin da akwai ɗan sauran lokaci. (Rom. 10:13, 14) Da ɗan yin natsuwa da kuma shiri, dukanmu za mu iya ba da shaida sa’ad da muka samu zarafin yin hakan kuma wataƙila za mu samu farin cikin yi wa mai zuciyar kirki wa’azi.

[Bayanin da ke shafi na 2]

Za ka iya ganin amfanin kafa maƙasudin saduwa da mutane da kuma soma tattaunawa da su

[Bayanin da ke shafi na 3]

Ta kasancewa da hikima, masu shela da yawa sun gano hanyoyi masu yawa na ba da shaida sa’ad da suka samu zarafin yin hakan

[Akwati da ke shafi na 3]

Shawarwari Na Soma Tattaunawa

◼ Ka yi addu’a don samun damar somawa

◼ Ka zaɓi masu fara’a da kuma waɗanda ba su shagala ba

◼ Ku haɗa ido, ka yi murmushi, kuma ka yi magana a kan abin da yake marmari

◼ Ka kasance mai saurarawa sosai

[Akwati da ke shafi na 3]

Sakamakon Yin Wa’azi Sa’ad da Aka Samu Zarafi!

• Sa’ad da wani ɗan’uwa yake jira a gyara motarsa a gareji, ya yi wa’azi ga waɗanda suke kewaye da shi kuma ya ba su takardar gayyata zuwa jawabi ga jama’a. Da ya halarci taron gunduma bayan shekara guda, wani ɗan’uwa da bai gane ba ya gaishe shi sosai. Ɗaya daga cikin mutanen da ya ba takardar gayyata zuwa taro shekara da ta gabata ne. Mutumin ya je ya saurari jawabi ga jama’ar kuma ya ba da sunansa don ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Da shi da kuma matarsa sun yi baftisma yanzu.

• Sa’ad da wani ma’aikacin kamfanin inshora ya ziyarci wata ’yar’uwa, ta yi amfani da zarafin don ta yi masa wa’azi. Ta tambaye shi ko zai so ya samu koshin lafiya, farin ciki, da rai na har abada. Ya amince kuma ya tambaye ta ko wane irin inshora ne take nufi. Ta nuna masa alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ta ba shi ɗaya daga cikin littattafanmu, kuma ya kammala karatun a yamma guda. Sun yi shirin yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ya soma halartar tarurruka, kuma daga baya ya yi baftisma.

• Wani ɗan’uwa makaho mai shekara ɗari wanda ke zama a gidan da ake kula da shi yana yawan cewa, “Muna bukatar Mulkin.” Hakan ya sa nas da majiyyata su yi masa tambayoyi kuma da hakan ya samu damar bayyana ma’anar Mulkin. Wata mace da ke aiki a wurin ta tambaye shi abin da zai riƙa yi a cikin Aljanna. Ya amsa, “Zan riƙa gani da kuma tafiya kuma zan ƙona keken guragu na.” Tun da shi makaho ne, ya ce mata ta karanta masa mujallun. Sa’ad da ’yar ɗan’uwan ta ziyarce shi, nas ɗin ta nemi izini ta kai mujallun gidanta. Wata nas ta gaya wa ’yar mutumin, “Sabon jigonmu a wannan gidan kula da majiyyata shi ne: ‘Muna bukatar Mulkin.’”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba