Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Soma Taɗi da Burin Yin Wa’azi
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: A yawancin lokatai, ba ma samun mutane a gida sa’ad da muke wa’azi gida-gida. Amma, mukan haɗu da su sa’ad da muke motar haya ko asibiti ko sa’ad da muka fita shan iska a wurin aiki ko a makaranta da dai sauransu. Jehobah yana so mu ba waɗannan mutanen damar jin saƙon Mulkinsa. (1 Tim. 2:3, 4) A yawancin lokatai, wajibi ne mu soma taɗi da su idan muna so mu yi musu shelar bishara.
Ku Bi Shawarar Nan Wannan Watan:
A kowane mako, ku yi ƙoƙari ku soma taɗi da mutane da burin yin wa’azi a duk inda kuka sami zarafi.