Ka Kasance A Faɗake Domin Yin Addu’a
‘Ku natsu cikin hankalinku da lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.’—1 BIT. 4:7.
1, 2. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a”? (b) Waɗanne tambayoyi game da addu’a ne ya wajaba mu yi wa kanmu?
WANI mutumi da ya taɓa aikin dare ya ce, “Lokacin da ya fi wuya mutum ya kasance a faɗake daddare shi ne sa’ad da gari ya kusan wayewa.” Babu shakka, waɗanda sukan kasance a faɗake har sai gari ya waye ma za su amince da hakan. Hakazalika, haka yanayin zamanin nan yake. Muna rayuwa ne a ƙarshen duniyar Shaiɗan. Kiristoci a yau suna bukatar su ƙoƙarta su kasance a faɗake, domin wannan zamanin ya yi kama da lokacin da muka ambata ɗazun, wato lokacin da gari ya kusan wayewa. (Rom. 13:12) Zai zama mugun kuskure idan muka yi barci a ibadarmu ga Jehobah. Wajibi ne mu ‘natsu cikin hankalinmu’ kuma mu ci gaba da “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.”—1 Bit. 4:7.
2 Da yake ƙarshen duniyar Shaiɗan ya yi kusa, zai dace mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Shin ina kasance a faɗake kuma ina yin addu’a kuwa? Ina yin dukan ire-iren addu’a a kai a kai kuwa? Shin ina addu’a a madadin wasu ne, ko kuwa ina yin hakan don abubuwan da nake bukata ne kawai? Ta yaya yin addu’a yake da alaƙa da cetona?
KA RIƘA YIN DUKAN IRE-IREN ADDU’A
3. Waɗanne ire-iren addu’o’i ne muke bukata mu riƙa yi?
3 Manzo Bulus ya ambata “kowace irin addu’a” sa’ad yake rubuta wa ’yan’uwa da ke Afisa wasiƙa. (Afis. 6:18) Idan muna yin addu’a, mukan roƙi Jehobah ya tanadar mana da bukatunmu kuma ya taimake mu mu shawo kan matsalolinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce shi “mai-jin addu’a” ne, kuma da yake yana ƙaunarmu, yana amsa addu’o’in da muka yi na neman taimako. (Zab. 65:2) Amma sa’ad da muke addu’a, zai dace mu roƙi wasu abubuwa dabam da bukatunmu. Hakan zai haɗa da addu’ar yabo da godiya da kuma roƙo.
4. Me ya sa ya kamata mu yabi Jehobah a kai a kai sa’ad da muke addu’a?
4 Akwai dalilai da yawa da suka sa muke bukata mu yabi Jehobah sa’ad da muke yin addu’a. Alal misali, za mu so mu yabe shi sa’ad da muka tuna da ‘ayyukansa masu-iko’ da kuma “mafificin girmansa.” (Karanta Zabura 150:1-6.) An yabi Jehobah sau goma sha uku a ayoyi shida na littafin Zabura sura 150 kaɗai. Wani marubucin zabura kuma ya yi wata waƙa don ya nuna ƙaunarsa ga Jehobah, ya ce: “So bakwai rana ɗaya ni kan yi yabonka, Saboda shari’unka masu-adalci.” (Zab. 119:164) Hakika, Jehobah ya cancanci a yabe shi. Saboda haka, zai dace mu riƙa yabon Jehobah a addu’o’inmu har “so bakwai” a rana, wato a kai a kai.
5. Ta yaya yin godiya a addu’o’inmu yake kāre mu?
5 Wata irin addu’a ita ce godiya. A wasiƙar da Bulus ya aika wa Kiristoci da ke Filibi, ya ce: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” (Filib. 4:6) Tun da yake muna zamani na ƙarshe a duniyar Shaiɗan kuma muna zama cikin mutane “marasa-godiya,” yana da muhimmanci mu riƙa gode wa Jehobah da dukan zuciyarmu don dukan abubuwan da yake yi mana. (2 Tim. 3:1, 2) Halin rashin godiya ya zama gama gari a wannan duniyar. Idan ba mu mai da hankali ba, za mu soma yin koyi da irin wannan halin. Amma idan muna yin godiya ga Allah a addu’o’inmu, ba za mu zama ‘masu-gunaguni, masu-ƙunƙuni’ ba. (Yahu. 16) Sa’ad da mai-gida yake addu’a tare da iyalinsa kuma ya yi godiya ga Allah, hakan zai taimaka wa matarsa da ’ya’yansa su riƙa yin godiya.
6, 7. Wace irin addu’a ce roƙo, kuma waɗanne abubuwan ne ya kamata mu roƙi Jehobah?
6 Roƙo addu’a ne da ake yi da dukan zuciya kuma cikin natsuwa ƙwarai. Waɗanne batutuwa ne ya kamata mu roƙa sa’ad da muke addu’a ga Jehobah? Za mu iya roƙon taimakon Jehobah sa’ad da ake tsananta mana ko kuma idan muna rashin lafiya mai tsanani. A irin waɗannan yanayi ne zai dace mu roƙi Jehobah ya taimake mu. Shin a irin waɗannan yanayin ne kawai ya kamata mu roƙi Jehobah?
7 Ka yi la’akari da abin da Yesu ya ce game da sunan Allah da Mulkinsa da kuma Nufinsa a addu’arsa na misali. (Karanta Matta 6:9, 10.) Ana mugunta sosai a wannan duniyar kuma gwamnatoci ba sa iya tanadar da bukatu na musamman ga ’yan ƙasarsu. Saboda haka, ya kamata mu riƙa yin addu’a cewa a tsarkake sunan Allah kuma Mulkinsa ya kawar da na Shaiɗan. Wannan kuma lokaci ne da ya dace mu roƙi Jehobah ya sa nufinsa ya tabbata a duniya kamar yadda yake a sama. Saboda haka, bari mu kasance a faɗake kuma mu riƙa yin dukan ire-iren addu’a.
KA RIƘA ‘YIN ADDU’A’
8, 9. Me ya sa bai dace mu kushe Bitrus da sauran manzannin don sun yi barci a lambun Jatsaimani ba?
8 Ko da yake manzo Bitrus ya aririci Kiristoci su “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a,” amma akwai wani lokacin da shi da kansa ya ƙasa yin hakan. Yana cikin almajiran da suka yi barci yayin da Yesu yake addu’a a lambun Jatsaimani. Yesu ya ce su ‘zauna a faɗake, su yi addu’a,’ amma ba su yi hakan ba.—Karanta Matta 26:40-45.
9 Maimakon kushe Bitrus da kuma sauran manzannin don ba su kasance a faɗake ba, zai dace mu tuna cewa sun yi hidimomi a ranar kuma hakan ya gajiyar da su sosai. Sun yi shirye-shiryen Idin Ketarewa kuma sun yi idin da yammar. Sai Yesu ya ba su umurni game da Jibin Maraice na Ubangiji, don su san yadda za su riƙa tunawa da mutuwarsa. (1 Kor. 11:23-25) Littafi Mai Tsarki ya ce bayan sun “raira waƙa, suka fita zuwa dutsen Zaitun.” Kafin su isa wurin, suna bukatar su yi tafiya mai nisa sosai ta titunan Urushalima. (Mat. 26:30, 36) Wataƙila ma lokacin tsakar dare ne. Da a ce mu ne ke lambun Jatsaimani a wannan daren, wataƙila da mun yi barci. Maimakon Yesu ya tsauta wa manzanninsa gajiyayyu, ya fahimci cewa “ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”
10, 11. (a) Wane darasi ne Bitrus ya koya daga abin da ya faru a lambun Jatsaimani? (b) Mene ne ka koya daga labarin Bitrus?
10 Barcin da Bitrus ya yi a lambun Jatsaimani ya sa shi baƙin ciki, amma ya koyi wani darasi mai muhimmanci sosai. Da farko Yesu ya ce: “A cikin daren nan dukanku za ku yi tuntuɓe saboda ni.” Amma Bitrus ya ce: “Ko duka za su yi tuntuɓe saboda kai, ni ba zan yi tuntuɓe ba daɗai.” Sai Yesu ya daɗa ce wa Bitrus zai yi musun saninsa sau uku. Amma Bitrus bai amince da hakan ba, ya ce: “Ko ya zama dole in mutu tare da kai, ba ni musunka ba.” (Mat. 26:31-35) Daga baya, Bitrus ya yi tuntuɓe kamar yadda Yesu ya faɗa. Sa’ad da Bitrus ya ga cewa ya yi musun sanin Yesu, sai “ya yi ta kuka mai-zafi.”—Luk 22:60-62.
11 Babu shakka, Bitrus ya koyi darasi daga abubuwan da suka faru kuma ya daina fahariya. Hakika, addu’a ce ta taimake shi a wannan yanayin. Yaya muka san da hakan? Bitrus ne ya rubuta cewa mu “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.” Shin muna bin wannan gargaɗin Littafi Mai Tsarki kuwa? Bugu da ƙari, shin muna dogara ga Jehobah ta yin addu’a a kai a kai kuwa? (Zab. 85:8) Bari kuma mu bi gargaɗin da manzo Bulus ya yi mana cewa: “Domin wannan fa, wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.”—1 Kor. 10:12.
AN AMSA ADDU’O’IN NEHEMIYA
12. Me ya sa ya dace mu yi koyi da misalin Nehemiya?
12 Ka yi la’akari da Nehemiya, wanda shi ne mai-shayarwa Sarkin Farisa, wato Artaxerxes a shekara ta 450 kafin zamaninmu. Nehemiya ya kafa misali mai kyau a yin addu’a ga Jehobah da zuciya ɗaya. Ya yi kwanaki da yawa yana “azumi da addu’a a gaban Allah,” don yanayi mai wuya da Yahudawa suke ciki a Urushalima. (Neh. 1:4) Sa’ad da Sarki Artaxerxes ya tambaye shi abin da ya sa yake baƙin ciki, nan da nan sai Nehemiya ya “yi addu’a ga Allah na sama.” (Neh. 2:2-4) Mene ne sakamakon hakan? Jehobah ya amsa addu’arsa kuma ya taimaki mutanensa. (Neh. 2:5, 6) Babu shakka, hakan ya ƙarfafa imanin Nehemiya sosai!
13, 14. Me ya kamata mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu yi tsayayya da Shaiɗan sa’ad da yake so ya sa mu sanyin gwiwa?
13 Idan muka yi addu’a a kai a kai kamar yadda Nehemiya ya yi, za mu kasance da bangaskiya sosai. Shaiɗan mugu ne, kuma yakan kawo mana hari sa’ad da muke sanyin gwiwa. Alal misali, idan muna rashin lafiya mai tsanani ko kuma muna baƙin ciki, wataƙila mu soma gani kamar Allah ba ya daraja sa’o’in da muke yi a wa’azi. Wataƙila wasu cikinmu suna baƙin ciki sanadin wani abu da ya taɓa faruwa a rayuwarsu. Shaiɗan yana so mu riƙa gani kamar ba mu da daraja. Yana amfani da irin waɗannan abubuwa masu sa baƙin ciki don ya sa bangaskiyarmu ta yi sanyi. Amma idan muna “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a,” za mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Hakika, “garkuwa ta bangaskiya” za ta taimaka mana mu “ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun.”—Afis. 6:16.
14 Idan muna “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a,” za mu kasance a faɗake kuma sa’ad da aka gwada mu za mu kasance da aminci ga Jehobah. Sa’ad da aka gwada ko tsananta mana, mu tuna misalin Nehemiya kuma mu yi addu’a ga Jehobah nan da nan. Sai da taimakon Jehobah ne kaɗai za mu iya shawo kan gwaji kuma mu jimre sa’ad da ake tsananta mana.
KA RIƘA YIN ADDU’A A MADADIN WASU
15. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi game da yin addu’a a madadin wasu?
15 Yesu ya roƙi Allah ya taimaki Bitrus da sauran almajiran su ci gaba da kasancewa da bangaskiya. (Luk 22:32) Wani Kirista mai suna Abafras ya yi koyi da Yesu sa’ad da ya duƙufa a yin addu’a a madadin ’yan’uwansa da ke Kolosi. Bulus ya rubuta musu wasiƙa, ya ce: “Kullum [Abafras] yana ƙwazo dominku cikin addu’o’insa, ku tsaya cikakku masu tabbatawa cikin dukan nufin Allah.” (Kol. 4:12) Ya kamata mu tambayi kanmu, ina duƙufa a yin addu’a domin ’yan’uwana da ke faɗin duniya? Ina yin addu’a game da ’yan’uwana maza da mata da bala’i ya addabe su? Yaushe ne na yi addu’a a madadin ’yan’uwa da ke kula da ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah kamar su, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe da dai sauransu? A kwanan nan, shin na yi addu’a game da wani ko wata a cikin ikilisiya da ke fuskantar matsala?
16. Shin ya dace mu yi addu’a a madadin wasu? Ka bayyana.
16 Yin addu’a a madadin wasu zai iya taimaka musu sosai. (Karanta 2 Korintiyawa 1:11.) Ko da yake ba wajibi ba ne Jehobah ya ɗauki mataki don bayinsa da yawa suna yin addu’a a kai a kai, amma yana farin ciki cewa suna ƙaunar juna kuma domin hakan yana amsa addu’o’insu. Saboda haka, bai kamata mu yi wasa da wannan gatan yin addu’a a madadin wasu ba. Ya kamata mu bi misalin Abafras kuma mu nuna ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu ta wajen yin addu’a a madadinsu. Hakan zai sa mu yi farin ciki domin “bayarwa ta fi karɓa albarka.”—A. M. 20:35.
CETONMU YA ƘUSA
17, 18. Ta yaya “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a” zai taimake mu?
17 Kafin Bulus ya ambaci cewa “dare ya tsāla, gari ya kusa wayewa” ya rubuta cewa: “an san wokacin nan, sa’a ta yi sarai da za ku farka daga barci: gama yanzu ceto ya fi kusa da mu bisa ga lokacin da muka fara bada gaskiya.” (Rom. 13:11, 12) Sabuwar duniya ta kusa kuma cetonmu ya kusa fiye da yadda muke tsammani. Yanzu ba lokacin yin sanyin gwiwa ba ne, kuma kada mu yarda harkokin duniyar nan su hana mu samun lokacin yin addu’a ga Jehobah. A maimakon haka, bari mu “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.” Yin hakan zai taimaka mana mu “zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada” yayin da muke jiran ranar Jehobah. (2 Bit. 3:11, 12) Salon rayuwarmu zai nuna ko muna a faɗake kuma mun yi imani cewa ƙarshen wannan mugun zamanin ya kusa. Wajibi ne mu “yi addu’a ba fasawa.” (1 Tas. 5:17) Bari mu bi misalin Yesu ta wajen neman wurin da ba kowa don yin addu’a. Idan muka ɗauki lokaci sosai don yin addu’a ga Jehobah, za mu kusace shi sosai. (Yaƙ. 4:7, 8) Babu shakka, hakan zai yi albarka sosai!
18 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Cikin kwanakin jikinsa kuwa, [Kristi] ya miƙa addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai-zafi da hawaye ga wanda yana da iko ya cece shi daga cikin mutuwa, da aka amsa masa kuma saboda tsoronsa mai-ibada.” (Ibran. 5:7) Yesu ya yi addu’a tare da roƙo, kuma ya kasance da aminci ga Allah har ƙarshen rayuwarsa a duniya. A sakamakon hakan, Jehobah ya ta da Ɗansa daga mutuwa kuma ya ba shi rai marar mutuwa. Hakika, za mu sami lada ta rai na har abada idan muka ci gaba da “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.”