MASU KARATU SUN YI TAMBAYA . . .
Me ya sa Allah yake barin masu iko su zalunci talakawa?
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan masu iko da suka zalunci talakawa. Wani da ya ɗanɗana zalunci shi ne Naboth. A ƙarni na goma kafin zamaninmu, Ahab, wani sarkin Isra’ila ya yarda matarsa Jezebel ta sa a kashe Naboth da kuma ’ya’yansa. Me ya sa? Don sarkin yana so ya kwace gonar Naboth. (1 Sarakuna 21:1-16; 2 Sarakuna 9:26) Me ya sa Allah ya bar mutane su yi amfani da ikonsu wajen zaluntar talakawa haka?
‘Allah . . . ba ya yin ƙarya.’—Titus 1:2
Bari mu tattauna wani babban dalili: Allah ba ya ƙarya. (Titus 1:2) Wace alaƙa ce ke tsakanin wannan dalilin da kuma zalunci? Ka tuna cewa tun farko Allah ya gargaɗi Adamu da Hawwa’u cewa idan suka yi tawaye da shi, za su fuskanci mummunan sakamako, wato mutuwa. Tun daga lokacin da suka yi tawaye a lambun Adnin, mutane sun ci gaba da mutuwa. Hakan tabbaci ne cewa maganar Allah gaskiya ce. Hakika, zalunci ne sanadin mutuwa ta farko a tarihin ɗan Adam, wato a lokacin da Kayinu ya kashe ɗan’uwansa Habila.—Farawa 2:16, 17; 4:8.
Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da ’yan Adam tun daga wannan lokacin: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Shin, hakan ba gaskiya ba ne? Jehobah ya ja kunnen al’ummarsa Isra’ilawa da cewa sarakunansu za su wulaƙanta su, kuma hakan zai sa su yi kuka ga Allah. (1 Sama’ila 8:11-18) Ko Sarki Sulemanu mai hikima ma ya wahal da mutanensa ta wajen sa su yi ayyukan da suka fi ƙarfinsu. (1 Sarakuna 11:43; 12:3, 4) Mugayen sarakuna kamar Ahab sun zalunci mutane sosai. Ka yi la’akari da wannan: Da a ce Allah ya hana zalunci aukuwa a duniya, da hakan bai nuna cewa shi maƙaryaci ba ne?
“Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya cuce shi.”—Mai-Wa’azi 8:9
Ƙari ga haka, Shaiɗan ya yi da’awa cewa ’yan Adam suna bauta wa Allah ne kawai don amfani da suke samu daga yin hakan. (Ayuba 1:9, 10; 2:4) Idan Allah ya kāre dukan bayinsa daga kowane irin zalunci, ai hakan zai zama kamar gaskiya ce Shaiɗan ya faɗa, ko ba haka ba? Kuma idan Allah ya shinge ’yan Adam baki ɗaya daga ayyukan zalunci, da hakan bai nuna cewa yana goyon bayan wani babban ƙarya ba? Idan Allah ya yi hakan, mutane da yawa za su zata cewa ’yan Adam za su iya yin mulkin kansu da kyau. Amma Kalmar Allah ta bayyana cewa ɗan Adam ba zai taɓa iya ja-gorar kansa da kyau ba. (Irmiya 10:23) Muna so Mulkin Allah ya zo don ya kawo ƙarshen rashin adalci.
Shin hakan yana nufin cewa Allah ya naɗa hannunsa ne kawai yana kallo yayin da ’yan Adam suke zalunta juna? A’a. Ka lura da abubuwa biyu da ya yi. Na farko, ya ba da cikakken bayani game da zalunci. Alal misali, Kalmarsa ta fallasa makircin da Jezebel ta ƙulla wa Naboth. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa wani masarauci mai iko, wanda ba ya so a san da shi ne yake zuga mutane su aikata waɗannan munanan ayyukan. (Yohanna 14:30; 2 Korintiyawa 11:14) Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan Iblis ne wannan masaraucin. Ta wajen fallasa mugunta da ainihin tushenta, Jehobah ya taimaka mana mu guji aikata mugunta, kuma hakan yana buɗe mana hanyar yin rayuwa har abada.
Na biyu, Allah ya ba da tabbaci cewa zai kawo ƙarshen zalunci. Allah ya fallasa, ya shari’anta kuma ya hukunta Ahab da Jezebel da kuma mutane da yawa da suka yi koyi da su. Saboda haka, muna da tabbaci cewa zai cika alkawarinsa na halaka masu mugunta. (Zabura 52:1-5) Allah ya kuma yi alkawari cewa jim kaɗan, zai kawar da kowace irin wahalar da bayinsa suke sha saboda mugunta.a A lokacin da duniyar nan za ta zama aljanna inda babu rashin adalci, Naboth mai aminci da kuma ’ya’yansa za su rayu a cikinta har abada.—Zabura 37:34.
a Ka duba babi na 11 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.