Kana da Ra’ayin Jehobah Game da Yin Adalci?
“Gama zan yi shelar sunan Ubangiji . . . , Allah mai-aminci ne, marar-mugunta.”—K. SHA. 32:3, 4.
1, 2. (a) Wane irin rashin adalci ne Naboth da yaransa suka fuskanta? (b) Waɗanne halaye guda biyu ne za mu bincika a wannan talifin?
KA YI tunani a kan wannan yanayin. Wasu mugayen mutane biyu sun zargi wani mutum cewa ya zagi Allah da kuma sarki. Ko da yake abin da suka faɗa ƙarya ce, an hukunta mutumin da yaransa. Ka yi tunanin yadda mutane masu son adalci suka ji sa’ad da aka yanke wa mutumin da bai yi kome ba hukuncin kisa. Wannan ba tatsuniya ba ce. Amma abu ne da ya faru da gaske ga wani bawan Jehobah mai suna Naboth da ya yi rayuwa a zamanin Sarki Ahab.—1 Sar. 21:11-13; 2 Sar. 9:26.
2 A wannan talifin, za mu yi la’akari da abin da ya faru da Naboth da kuma labarin wani dattijo mai aminci da ya yanke hukuncin da bai dace ba a ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko. A waɗannan misalan Littafi Mai Tsarki, za mu ga cewa tawali’u yana da muhimmanci idan muna son mu kasance da ra’ayin Jehobah na yin adalci. Ƙari ga haka, za mu koyi yadda gafartawa take nuna cewa muna da ra’ayin Jehobah sa’ad da aka yi rashin adalci a ikilisiya.
YIN RASHIN ADALCI
3, 4. Wane irin mutumi ne Naboth, kuma me ya sa ya ƙi ya sayar wa Sarki Ahab gonarsa?
3 Naboth ya riƙe amincinsa ga Jehobah sa’ad da Isra’ilawa suke bin mugun tafarkin Sarki Ahab da matarsa Jezebel. Waɗannan mutane da suke bauta wa Baal ba sa daraja Jehobah da ƙa’idodinsa. Amma Naboth ya ɗauki dangantakarsa da Jehobah da muhimmanci sosai.
4 Karanta 1 Sarakuna 21:1-3. Da Ahab ya nemi ya saya gonar Naboth ko kuma su canja gonar da wata, sai Naboth ya ƙi. Me ya sa? Naboth ya bayyana wa Ahab cewa: ‘Ubangiji ya sawwaƙa mani, da zan ba da gādon ubannina a gareka.’ Naboth ya ƙi ne don Jehobah ya hana Isra’ilawa sayar da gādonsu. (Lev. 25:23; Lit. Lis. 36:7) Babu shakka, Naboth ya bi umurnin Jehobah.
5. Mene ne Jezebel ta yi don mijinta ya sami gonar Naboth?
5 Sa’ad da Naboth ya ƙi ya sayar da gonarsa, Sarki Ahab da matarsa sun yi wasu abubuwan da ba su dace ba. Don Jezebel ta ba wa mijinta gonar Naboth, sai ta ɗora wa Naboth sharri, kuma hakan ya sa aka kashe shi da yaransa. Mene ne Jehobah zai yi saboda irin wannan rashin adalcin?
ALLAH YA YI ADALCI
6, 7. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi mai son adalci ne, kuma ta yaya hakan ya ta’azantar da abokan Naboth da iyalinsa?
6 Nan da nan, Jehobah ya tura Iliya ya tsauta wa Ahab. Iliya ya gaya wa Ahab cewa ya yi kisan kai kuma ya yi sata. Wane hukunci ne Jehobah ya yanke? Abin da ya sami Naboth da yaransa zai sami Ahab da matarsa da kuma yaransa.—1 Sar. 21:17-25.
7 Ko da yake iyalin Naboth da abokansa sun yi baƙin ciki sosai don abin da Ahab ya yi, sun yi farin ciki sa’ad da suka san cewa Jehobah ya san irin rashin adalcin da aka yi musu, kuma bai ɓata lokaci wajen magance matsalar ba. Babu shakka, abin da ya faru bayan hakan ya shafe su sosai da kuma amincinsu ga Jehobah.
8. Mene ne Ahab ya yi sa’ad da ya ji hukuncin da Jehobah ya yanke masa, kuma da wane sakamako?
8 Sa’ad da Ahab ya ji hukuncin da Jehobah ya yanke, ‘sai ya yayyage tufafinsa, ya sa buhu a bisa jikinsa, ya daina cin abinci, ya kwanta cikin buhu, ya riƙa tafiya sanu sanu.’ Babu shakka, Ahab ya ƙaskantar da kansa! Mene ne ya faru don wannan abin da ya yi? Jehobah ya gaya wa Iliya: “Tun da ya ƙasƙantadda kansa a gabana, ba ni kawo masifan a cikin zamaninsa; sai dai cikin zamanin ɗansa zan kawo masifan a bisa gidansa.” (1 Sar. 21:27-29; 2 Sar. 10:10, 11, 17) Jehobah wanda yake bincika “zukata” ya nuna wa Ahab jin ƙai.—Mis. 17:3.
ZAMA MASU TAWALI’U YANA KĀRE MU
9. Ta yaya tawali’u ya taimaka wa abokan Naboth da kuma iyalinsa?
9 Ta yaya wannan hukunci ya shafi waɗanda suka san abin da Ahab ya yi? Wataƙila hakan ya dami abokan Naboth da kuma iyalinsa sosai. Amma idan suna da tawali’u, za su ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci kuma su kasance da tabbaci cewa Allah ba ya rashin adalci. (Karanta Kubawar Shari’a 32:3, 4.) A nan gaba, Naboth da yaransa za su ga juna sa’ad da aka ta da su daga mutuwa. (Ayu. 14:14, 15; Yoh. 5:28, 29) Ƙari ga haka, mutum mai tawali’u ya san cewa “Allah za ya kawo kowane aiki wurin shari’a, da dukan asirin rai, domin shi raba, ko nagari ne, ko mugu.” (M. Wa. 12:14) Babu shakka, sa’ad da Jehobah yake yanke hukunci, yana yin la’akari da wasu abubuwa da mu ba za mu iya sani ba. Don haka, zama masu tawali’u zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya ga Jehobah.
10, 11. (a) Wane irin yanayin ne zai iya sa mu ga kamar ba a yi adalci ba? (b) A waɗanne hanyoyi ne tawali’u zai taimaka mana?
10 Mene ne za ka yi idan dattawa sun yanke wata shawarar da ba ka fahimta ba ko kuma ba ka amince da shi ba? Alal misali, me za ka yi idan kai ko kuma wani abokinka ya rasa gatarsa? Idan aka yi wa matarka ko ɗanka ko abokinka na kud da kud yankan zumunci fa, shin za ka yarda da hakan? Me za ka yi idan kana ganin cewa dattawan sun yi rashin adalci? Irin wannan yanayin zai iya jaraba amincinmu ga Jehobah da kuma yadda ya tsara ƙungiyarsa. Ta yaya kasancewa mai tawali’u zai taimaka maka idan ka tsinci kanka a irin wannan yanayin? Bari mu yi la’akari da hanyoyi biyu.
Mene ne za ka yi idan dattawa sun yi wata sanarwa da ba ka yarda da ita ba? (Ka duba sakin layi na 10, 11)
11 Da farko, tawali’u zai taimaka mana mu fahimci cewa ba mu da cikakken bayani game da batun. Ko da a ce mun san abin da ya faru, Jehobah ne kaɗai zai iya sanin ainihin abin da ke zuciyar mutum. (1 Sam. 16:7) Sanin wannan zai taimaka mana mu zama masu tawali’u kuma mu san kasawarmu har mu daidaita ra’ayinmu. Na biyu, zama masu tawali’u zai taimaka mana mu jira da haƙuri har sai lokacin da Jehobah ya kawar da rashin adalci. Kamar yadda mutumin nan mai hikima ya ce: “Waɗanda ke tsoron Allah za su zama lafiya . . . , amma babu lafiya ga miyagu, ba kuwa za su tsawanta kwanakinsu ba.” (M. Wa. 8:12, 13) Babu shakka, idan muka zama masu tawali’u za mu amfana har ma da waɗanda aka yi masu rashin adalcin.—Karanta 1 Bitrus 5:5.
WANI MISALIN MUNAFUNCI
12. Wane labari za mu bincika yanzu, kuma me ya sa?
12 A ƙarni na farko, Kiristocin da ke Suriya ta Antakiya sun fuskanci jarabawa da ya nuna ko su masu tawali’u ne da kuma gafartawa. Bari mu bincika wannan labarin don mu koyi wasu darussan da za su taimaka mana mu bincika kanmu ko muna gafarta wa mutane. Ban da haka ma, za mu fahimci abin da ya sa Jehobah yake amfani da mutane ajizai ba tare da ya taka ƙa’idodinsa ba.
13, 14. Waɗanne gata ne Bitrus ya samu, kuma ta yaya ya nuna cewa yana da gaba gaɗi?
13 Manzo Bitrus dattijo ne da aka sani sosai a ikilisiyar Kirista. Ya yi tarayya sosai da Yesu, kuma an ba shi aiki mai muhimmanci sosai. (Mat. 16:19) Alal misali, a shekara ta 36 bayan haihuwar Yesu, Bitrus ya sami gatan yi wa Karniliyus da iyalinsa wa’azi. Me ya sa wannan gata ne babba? Saboda Karniliyus ba Bayahude ba ne. Amma da ruhu mai tsarki ya sauko wa Karniliyus da iyalinsa, sai Bitrus ya ce: “Akwai mai iya hana ruwan da za a yi wa mutanen nan baftisma, waɗanda suka sami Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda mu ma muka samu?”—A. M. 10:47.
14 A shekara ta 49 bayan haihuwar Yesu, manzanni da dattawa da ke Urushalima sun yi taro don su tattauna ko Kiristocin da ba Yahudawa ba suna bukatar su yi kaciya. A wannan taron, Bitrus ya yi magana da gaba gaɗi kuma ya tunawa ‘yan’uwa da suke wurin cewa, a shekarun da suka shige, Kiristocin da ba Yahudawa ba sun sami kyautar ruhu mai tsarki. Abin da Bitrus ya faɗa ne ya taimaka wa hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni farko ta wajen yanke shawara mai muhimmanci. (A. M. 15:6-11, 13, 14, 28, 29) Babu shakka, Kiristoci Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba, sun ji daɗin abin da Bitrus ya faɗa. Kuma hakan ya sa sun amince da wannan dattijon.—Ibran. 13:7.
15. Wane irin kuskure ne Bitrus ya yi sa’ad da yake Suriya ta Antakiya? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)
15 Bayan taron da aka yi a shekara ta 49 bayan haihuwar Yesu, Bitrus ya ziyarci Suriya ta Antakiya. Da yake wurin, Bitrus ya yi tarayya da Kiristocin da ba Yahudawa ba. Babu shakka, Bitrus ya koya wa ‘yan’uwan abubuwa da yawa kuma sun amfana sosai. Amma da Bitrus ya daina cin abinci da su, hakan ya ɓata musu rai. Hakan ya sa wasu ma har da Barnaba su bi misalin Bitrus na daina yin tarayya da Kiristocin da ba Yahudawa ba. Me ya sa wannan dattijon da ya manyanta ya yi irin wannan kuskuren da zai iya raba kan ikilisiyar? Mene ne za mu iya koya daga misalin Bitrus da zai taimaka mana sa’ad da wani dattijo ya yi ko faɗi abin da ya ɓata mana rai?
16. Ta yaya aka yi wa Bitrus gyara, kuma waɗanne tambayoyi ne mutum zai iya yi?
16 Karanta Galatiyawa 2:11-14. Bitrus ya bar tsoron mutum ya zama masa tarko. (Mis. 29:25) Duk da cewa, Bitrus ya san ra’ayin Jehobah game da batun, ya ji tsoron abin da Kiristoci Yahudawa da suke ikilisiyar da ke Urushalima za su ce. Da yake manzo Bulus yana wurin taron da aka yi a Urushalima a shekara ta 49 bayan haihuwar Yesu, ya ja kunnen Bitrus kuma ya gaya masa cewa abin da ya yi munafunci ne. (A. M. 15:12; Gal. 2:13) Mene ne Kiristocin da ba Yahudawa ba da Bitrus ya musu kuskuren suka yi? Shin za su bar hakan ya sa su yin sanyin gwiwa ne? Ko kuwa Bitrus zai rasa gatan da yake da shi domin kuskuren da ya yi?
KU RIƘA GAFARTAWA
17. Ta yaya Bitrus ya amfana don Jehobah ya gafarta masa?
17 Hakika, Bitrus ya amince da gyarar da Bulus ya yi masa. Kuma Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Bitrus ya rasa gatan da yake da shi ba. Ban da haka ma, an hure shi ya rubuta wasiƙu guda biyu da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma a cikin wasiƙarsa ta biyu, Bitrus ya kira Bulus “ƙaunatacen ɗan’uwanmu.” (2 Bit. 3:15) Yesu wanda shi ne kan ikilisiya ya ci gaba da yin amfani da Bitrus ko da yake Kiristocin da ba Yahudawa sun ji zafin kuskuren da Bitrus ya musu. (Afis. 1:22) Hakan ya ba wa membobin ikilisiyar damar yin koyi da Yesu da kuma Jehobah ta wurin gafartawa. Abin farin ciki shi ne cewa, wataƙila babu wani cikinsu da ya bar wannan kuskuren ta sa ya yi sanyin gwiwa.
18. A wane irin yanayi ne muke bukatar mu yi koyi da halin Jehobah na yin adalci?
18 Kamar yadda yake a ikilisiyar ƙarni na farko, babu kamiltaccen dattijo a yau, domin “dukanmu mukan yi tuntuɓe.” (Yaƙ. 3:2) Sanin hakan yana da sauƙi, amma me za mu yi idan kuskuren da wasu suka yi ya shafe mu? A irin wannan yanayin, shin za mu bi misalin Jehobah? Alal misali, me za ka yi idan wani dattijo ya yi wani furucin da ya nuna cewa yana nuna wariya? Shin za ka yi sanyin gwiwa ne idan wani dattijo ya faɗi abin da ya ɓata maka rai? Maimakon ka yi tunanin cewa wannan ɗan’uwan bai cancanci zama dattijo ba, zai dace ka jira sai Yesu wanda shi ne kan ikilisiya ya ɗauki mataki, ko ba haka ba? Maimakon ka mai da hankali ga kuskuren, shin za ka tuna da shekarun da ɗan’uwan ya yi yana bauta wa Jehobah? Idan wanda ya ɓata maka rai ya ci gaba da yin hidima a matsayin dattijo ko kuma ya sami ƙarin gata, shin za ka yi farin ciki don hakan? Idan ka nuna cewa kai mai gafartawa ne, hakan zai nuna cewa kana bin misalin Jehobah na yin adalci.—Karanta Matta 6:14, 15.
19. Me za mu ƙuduri aniyar yi?
19 Masu son adalci suna marmarin ganin lokacin da Jehobah zai kawar da rashin adalcin da Shaiɗan da duniyarsa suke yi wa mutane. (Isha. 65:17) Kafin wannan lokacin, idan muka fuskanci rashin adalci, muna bukata mu zama masu tawali’u kuma mu fahimci cewa ba kome game da batun ne muka sani ba, ƙari ga haka, mu ci gaba da gafartawa waɗanda suka yi mana laifi da zuciya ɗaya.