ABIN DA KE SHAFIN FARKO
Akwai Wanda Zai Iya Sanin Gobe?
Dukanmu muna tunanin gobe. Muna tunani a kan yadda rayuwarmu da na danginmu da kuma na abokanmu za ta kasance. Ƙari ga haka, muna tambayoyi kamar su: ‘Yarana za su yi rayuwa da ta fi tawa inganci? Wani bala’i zai halaka wannan duniyar ne? Akwai abin da zan iya yi yanzu da zai kyautata rayuwata a nan gaba?’ Dukanmu muna sha’awar sanin abin da zai faru nan gaba, muna jin daɗin kasancewa da tabbaci da kwanciyar rai kuma muna so abubuwa su zama da tsari. Idan ka san abin da zai faru a nan gaba, za ka iya yin shiri da kuma tanadi domin gobe.
To, me zai faru da kai a nan gaba? Akwai wanda zai iya sani? Masana da suke ƙoƙarin sanin abin da zai faru gobe sukan yi nasara a wasu lokatai, amma mafi yawan abubuwa da suka faɗa ba su cika ba. Duk da hakan, ana cewa Allah yana iya annabta daidai abin da zai faru kafin hakan ya faru. Kalmar Allah ta ce shi ne “mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma alamuran da ba a rigaya an aika[ta] ba tukuna.” (Ishaya 46:10) Annabce-annabcen da Allah ya yi sun cika kuwa?
ANNABCE-ANNABCEN ALLAH SUNA CIKA
Me ya sa zai dace ka yi sha’awar sanin sakamakon annabce-annabcen da Allah ya yi a dā? Idan ka gano cewa akwai wani masanin yanayi da duk abin da ya faɗa a kan yanayi yana faruwa, za ka ɗaga masa tuta, ko ba haka ba? Mai yiwuwa za ka yarda da abin da ya faɗa game da yanayin gobe. Hakazalika, idan ka san cewa annabce-annabcen da Allah ya yi a dā sun cika, za ka so ka san annabcin da ya yi game da rayuwarka, ko ba haka ba?
HALAKAR WANI BABBAN BIRNI:
Idan wani ya yi annabci cewa ba da daɗewa ba za a halaka wani babban birni mai iko sosai, kuma hakan ya faru, wannan zai zama abin a zo a gani, ko ba haka ba? Ta bakin wani wakilinsa, Allah ya annabta cewa abin da zai faru da Nineba ke nan. (Zafaniya 2:13-15) Mene ne ’yan tarihi suka faɗa game da cikar wannan annabci? Wajen shekaru 15 bayan Allah ya yi wannan annabcin, wato a shekara ta 632 kafin zamanin Kristi, Babiloniyawa da mutanen Midiya sun kai wa birnin Nineba hari kuma suka ci su da yaƙi. Ƙari ga haka, Allah ya bayyana cewa Nineba zai zama “kango, busashiya kamar jeji,” tun ma kafin hakan ya faru. Wannan annabcin ya cika kuwa? Hakika. Ko da yake wannan birnin da karkararsa yana da girma, waɗanda suka kai ma birnin hari sun ci birnin da yaƙi kuma sun halaka shi gaba ɗaya. Shin, akwai wani masanin siyasa da zai iya yin irin wannan annabcin kuma hakan ya cika daidai wa daida?
ZA A ƘONA ƘASUSUWAN MUTANE:
Wa ya isa ya yi annabci tun shekaru 300 kafin ya cika cewa za a ƙona ƙasusuwan mutane a kan bagadi, har ya ba da ainihin sunan wanda zai yi hakan da zuriyarsa da kuma garin da za a gina wannan bagadin? Idan wannan annabcin ya cika, lallai wanda ya yi annabcin zai yi suna. Wani wakilin Allah ya sanar cewa: “Za a haifa ma gidan Dauda yaro sunansa Josiah,” kuma ya ce yaron zai “ƙona ƙasusuwan mutane” a kan bagadi a garin Bethel. (1 Sarakuna 13:1, 2) Wajen shekaru ɗari uku bayan annabcin, an yi wani sarki a zuriyar Dauda mai sunan da ba a cika amfani da shi a dā, wato Josiah. Kamar yadda aka annabta, Josiah ya sa aka “kwaso ƙasusuwa daga cikin kusheyin [kabari], aka ƙone su a bisa bagadi” a Bethel. (2 Sarakuna 23:14-16) Shin zai yiwu ɗan Adam ya yi annabci da cikakken bayani haka ba tare da taimakon wani da ya fi ’yan Adam ba?
ƘARSHEN WATA DAULA:
A ce wani ya annabta cewa za a tumɓuke gwamnatin da ke mallakar duniya kuma ya ambata sunan mutumin da zai yi hakan har da dabarar da zai yi amfani da ita tun kafin a haifi mutumin, kuma hakan ya faru. Hakika wannan zai zama abin mamaki, ko ba haka ba? Allah ya sanar cewa wani mutum mai suna Cyrus zai ja-goranci rundunar da za ta ƙwace mulkin wata daula. Ya daɗa da cewa Cyrus zai ’yantar da Yahudawa daga bauta kuma zai tallafa musu su sake gina haikalinsu mai tsarki. Sai Allah ya nuna cewa dabarar da Cyrus zai yi shi ne, zai janye ruwan kogin da ya kewaye babban birnin daular kuma za a bar ƙofofin birnin a buɗe a ranar da za a kai harin. Ta haka, ƙwace mulkin zai zama kamar cin tuwo. (Ishaya 44:27–45:2) Dukan waɗannan abubuwa da Allah ya annabta sun cika kuwa? ’Yan tarihi sun yarda cewa Cyrus ya ci birnin Babila wanda shi ne masarautar daular Babila da yaƙi, kuma hakan ya kawo ƙarshen ikon Babila. Cyrus da rundunarsa sun janye ruwan kogin Babila ta wajen buɗe ma ruwan wata hanya dabam. Bayan haka, suka shiga birnin cikin sauƙi domin an bar ƙofofinsa a buɗe. Sai Cyrus ya ’yantar da Yahudawa kuma ya ba su izini su koma Urushalima don su gina haikalinsu. Hakika hakan abin mamaki ne, domin Cyrus ba bawan Allahn Yahudawa ba ne. (Ezra 1:1-3) Wane ne ya isa ya yi annabci da cikakken bayani haka, in ba Allah ba?
Mun tattauna annabce-annabce guda uku da Allah ya yi kuma suka cika. Ba waɗannan ne kaɗai annabce-annabcen da Allah ya yi da suka cika ba. Wani shugaban Yahudawa mai suna Joshua ya faɗi wani abin da masu sauraronsa ba su yi shakkarsa ba. Ya ce: ‘Kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya tsare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya tsare daga ciki.’ (Joshua 23:1, 2, 14) Mutanen Joshua ba su yi shakkar cewa Allah mai cika alkawari ne da kuma annabci ba. Amma yaya Allah yake cim ma hakan? Iyawar Allah ba ɗaya yake da na ’yan Adam ba. Zai dace ka san da hakan, domin Allah ya yi wasu muhimman annabce-annabce da za su cika a nan gaba, kuma tabbas za su shafe ka.
ANNABCIN ALLAH DA HANGEN ’YAN ADAM
Mutane suna faɗin abin da suke ganin zai faru bisa ga binciken kimiyya ko tabbatattun bayanai ko abin da ya daɗe yana faruwa. Wasu kuma suna yin hakan domin suna da’awa cewa sun san gaibi. Bayan mutane sun faɗi abin da suke ganin zai faru a nan gaba, sukan naɗe hannu su ga ko hakan zai faru.—Misalai 27:1.
Akasin haka, Allah ya san kome; ya san ’yan Adam da tafarkinsu ciki da waje. Saboda haka, yana iya hangen abin da zai faru da mutum ko kuma al’umma gaba ɗaya a duk lokacin da ya ga damar yin hakan. Ban da haka ma, Allah yana iya sarrafa al’amura don ya tabbata cewa nufinsa ya cika. Ya ce: “Maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina . . . ba za ta koma wurina wofi ba, amma . . . za ta yi albarka,” ko kuma nasara. (Ishaya 55:11) Saboda haka, wasu annabce-annabcen Allah suna sanar mana da abin da Allah zai yi nan gaba ne kawai. Allah yana ba mu tabbaci cewa kowane annabcin da ya yi zai cika.
ABIN DA ZAI FARU DA KAI A NAN GABA
Shin akwai annabcin da aka yi game da rayuwarka da kuma na iyalinka da tabbas zai cika? Idan aka sanar da kai tun da wuri cewa za a yi wata mahaukaciyar guguwa mai ɗauke da ruwa, babu shakka za ka ɗauki mataki don ka tsira. Irin wannan matakin ne ya kamata ka ɗauka game da annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Allah ya sanar cewa ba da daɗewa ba duniyar nan za ta shaida gagarumin canji. (Ka duba akwatin nan “Abin da Allah Ya Bayyana Game da Nan Gaba.”) Abin da zai faru a nan gaba ya sha bambam da abubuwan da masu hangen nesa suke faɗa.
Za ka iya kwatanta rayuwar ’yan Adam da rubutaccen labari. Da yake an riga an rubuta labarin, za ka iya sanin yadda ƙarshen zai kasance. Allah ya ce: “[Ni ne] mai-bayyana ƙarshe tun daga mafarin, . . . Ina cewa, Ƙudurina za ya tabbata, zan kuma cika dukan nufina.” (Ishaya 46:10) Kai da iyalinka za ku iya more rayuwa mai kyau a nan gaba. Ka tambayi Shaidun Jehobah su gaya maka abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce za su faru a nan gaba. Shaidun Jehobah ba masu dūba ba ne, ba sa sha’ani da ruhohi kuma ba sa da’awa cewa suna da baiwar sanin abin da zai faru nan gaba. Su ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne da za su iya bayyana maka shiri masu kyau da Allah yake yi game da nan gaba da za su amfane ka.