“Ka Daidaita Tafarkin Ƙafafunka” don Ka Yi Nasara
SA’AD DA Isra’ilawa suka bar ƙasar Babila a shekara ta 537 kafin zamaninmu, Jehobah ya damu da yanayin komawar su Urushalima. Ya ce musu: “Ku shirya hanyar mutane; ku gina, ku gina tafarki; a ciccire duwatsu.” (Isha. 62:10) Shin mene ne suka yi don su bi wannan umurnin? Wataƙila wasu cikinsu sun wuce gaba don su rufe ramuka kuma sun gyara hanyar don ta yi sumul. Hakan ya sa komawar su Urushalima ta kasance da sauƙi.
Za mu yi amfani da wannan wajen kwatanta yadda ake cim ma maƙasudai a bautar Jehobah. Jehobah yana so dukan bayinsa su bi hanyar da za ta sa su cim ma maƙasudanmu ba tare da tangarɗa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka daidaita tafarkin ƙafafunka, Dukan al’amuranka kuma su kafu.” (Mis. 4:26) Za ka iya amfana daga wannan shawara mai kyau ko da kai matashi ne ko a’a.
KA SHIRYA TAFARKINKA TA YIN SHAWARWARI MASU KYAU
Wataƙila ka taɓa ji wani ya ce: ‘Tana jin daɗin rayuwa,’ ko kuma ‘Yana sha’aninsa.’ Matasa suna da ƙoshin lafiya da saurin fahimta da kuma burin yin nasara. Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla-dalla cewa: “Fahariyar samari ƙarfinsu ne: jamalin tsofaffi kuma furfura ne.” (Mis. 20:29) Matashin da ya yi amfani da baiwarsa a bautar Jehobah zai cim ma maƙasudai da za su faranta wa Jehobah rai kuma zai yi farin ciki ƙwarai.
Wasu mutane a duniya suna lura da baiwa da kuma iyawar matasanmu. Idan wani matashi da Mashaidi ne yana ƙoƙari a makaranta, malamansa ko abokan makaranta za su iya ba shi shawara cewa ya je jami’a don ya yi nasara a wannan mugun zamanin. Ko kuma za a iya ƙarfafa wani matashi ko matashiya da ta iya wasanni ta biɗi hakan a rayuwa. Wataƙila kai ko kuma wani da ka sani yana fuskantar irin wannan yanayin. Mene ne zai taimaka wa Kirista ya tsai da shawara mai kyau?
Koyarwar Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka wa mutum ya bi tafarki da zai sa ya yi nasara a bautar Jehobah. Littafin Mai-Wa’azi 12:1 ya ce: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.” Ta yaya kai ko kuma wani matashi da ka sani zai ‘tuna da Mahaliccinsa’?
Ka yi la’akari da abin da ya faru da Erica da ke Afirka ta Yamma. Ya iya buga kwallon kafa sosai. Sa’ad da Eric ya kai shekara 15, an zaɓe shi ya buga wa ƙasarsu ƙwallo. Hakan zai sa a kai shi ƙasar Turai don a horar da shi kuma ya zama tauraro a wasan ƙwallo. Amma ta yaya wannan shawarar da ta ce: ‘Ka tuna da Mahaliccinka’ zai taimaka masa? Kuma wane darasi ne za mu koya daga wannan labarin?
Ana nan, sai Shaidun Jehobah suka soma nazarin littafi mai tsarki da Eric sa’ad da yake makaranta. Daga wannan nazarin, ya koyi cewa Mahaliccinsa zai magance matsalolin ’yan Adam gaba ɗaya. Ƙari ga haka, Eric ya koyi cewa yin amfani da kuzarinsa da kuma lokacinsa don yin nufin Allah yana da muhimmanci sosai. Saboda haka, ya ƙi biɗan wasanni. A maimakon haka, ya yi baftisma kuma ya biɗi maƙasudai a bautar Jehobah. Da shigewar lokaci, ya zama bawa mai hidima kuma aka gayyace shi zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure.
Da a ce Eric ya ci gaba da yin wasanni da wataƙila ya sami arziki kuma da ya shahara. Amma ya fahimci gaskiyar wannan ƙa’idar Littafi Mai Tsarki: “Wadatar mai-arziki ƙaƙarfan birninsa ne, kamar ganuwa mai-tsawo kuma ga ganinsa.” (Mis. 18:11) Hakika, kāriya da ake gani arziki yake tanadarwa wasiƙar jaki ce. Ƙari ga haka, waɗanda suka sa biɗan arziki kan gaba sukan “jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukan rai.”—1 Tim. 6:9, 10, Littafi Mai Tsarki.
Matasa da yawa sun biɗi hidima ta cikakken lokaci kuma ta hakan, sun sami kwanciyar rai da farin ciki. Eric ya ce: “Na shiga babban ‘rukunin’ bayin Jehobah masu hidima ta cikakken lokaci. Wannan shi ne rukuni mafi kyau kuma ina godiya ga Jehobah a kan yadda ya nuna mini hanyar samun farin ciki da kuma nasara a rayuwa.”
Kai kuma fa? A maimakon ka biɗi maƙasudai a wannan duniyar, za ka iya kafa “al’amuranka” a gaban Jehobah ta wajen yin hidimar majagaba.—Ka duba akwatin nan “Na Cim ma Abubuwan da Ba A Koyarwa a Jami’a.”
KAWAR DA ABUBUWAN DA ZA SU HANA KA CI GABA
Yayin da wasu ma’aurata suka ziyarci ofishin reshe na Amirka, sun ga yadda ’yan’uwa da suke hidima a Bethel suke farin ciki. Daga baya, ’yar’uwar ta ce: “Mun ɗauka cewa rayuwar da muke yi a dā ba laifi.” Saboda haka, ma’auratan suka yi shawara cewa za su yi amfani da lokacinsu don biɗan wasu maƙasudai a bautar Jehobah.
Canje-canjen da waɗannan ma’auratan suke bukata su yi ba su da sauƙi. Amma wata rana sai suka yi tunani a kan Nassin yini da suka bincika a ranar. Nassin daga littafin Yohanna 8:31 ne inda Yesu ya ce: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske.” Sai suka fahimci cewa ɗaukan duk wani matakin da ya dace don su sauƙaƙa salon rayuwarsu haƙa ce da za ta cim ma ruwa.” Suka sayar da babban gidansu da wasu mallakarsu kuma suka soma hidima a wata ikilisiya da ke bukatar taimako. Yanzu suna hidimar majagaba. Ban da haka, suna ba da kansu don taimakawa a gina Majami’un Mulki kuma suna ba da kansu a taron gunduma. Yaya suke ji game da canje-canjen da suka yi? “Muna mamakin irin farin cikin da muke yi sa’ad da muka yi abin da ƙungiyar Jehobah take ƙarfafa mu mu yi, wato sauƙaƙa rayuwarmu.”
KA RIƘA BIƊAN ABUBUWAN DA ZA SU SA KA YIN NASARA A IBADARKA
Sulemanu ya rubuta cewa: “Bari idanunka su duba gaba sosai, Maƙibtanka kuma su tafi rankai.” (Mis. 4:25) Ya kamata mu guji duk wani abin da zai hana mu kafa da cim ma makasudai da za su faranta wa Jehobah rai.
Waɗanne maƙasudai ne za ka iya kafawa? Za ka iya kafa maƙasudin zama mai hidima ta cikakken lokaci. Wani kuma shi ne yin hidima a wani ikilisiya da ake bukatar ƙwararrun masu wa’azi. Idan kai ɗan’uwa ne, za ka iya yin hidima a ikilisiya da ke bukatar ƙarin dattawa da kuma bayi masu hidima. Za ka iya samun ƙarin bayani daga wajen mai kula mai ziyararku. Idan kuma za ka iya yin hidima nesa da gida, za ka iya neman bayani game da ikilisiyoyin da suke bukatar taimako.b
Bari mu sake tunani game da labarin Isra’ilawa da aka yi maganarsu a Ishaya 62:10. Wasu daga cikin su sun yi aiki tuƙuru don gyara hanyar da ke zuwa Urushalima don ’yan’uwansu su isa gida lafiya. Idan kana aiki tuƙuru don cim ma wasu maƙasudai a bautar Jehobah, kada ka karaya. Jehobah zai taimake ka ka cim ma waɗannan maƙasudan. Ka ci gaba da roƙan Jehobah ya ba ka hikima sa’ad da kake ƙoƙarin kawar da tangarɗa da suke gabanka. Da shigewar lokaci, za ka shaida yadda zai “daidaita tafarkin ƙafafunka.”—Mis. 4:26.