Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 12-16
  • Matasa Ku Tuna Da Mahaliccinku A Yanzu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa Ku Tuna Da Mahaliccinku A Yanzu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ka Dogara ga Ubangiji da Dukan Zuciyarka”
  • Matasa, Ku Kasance Masu Hikima!
  • Sun Faɗi Sa’ad da Suka Kusa Cika Makasudinsu
  • Ku Zaɓi Makasudinku da Hikima
  • Ku Saurari Waɗanda Suke Ƙaunarku
  • Ka Bi Misali Mafi Kyau
  • Jehobah Yana Dubanmu Don Amfaninmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehovah Yana Yi Wa Waɗanda Suke Biyayya Albarka Kuma Yana Kāre su
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 12-16

Matasa Ku Tuna Da Mahaliccinku A Yanzu

“Ka tuna da Mahaliccinka kuma kwanakin ƙuruciyarka.”—M. WA. 12:1.

1. Ta yaya ne Jehobah ya nuna cewa ya amince da matasa da suke bauta masa?

JEHOBAH yana ɗaukan Kiristoci matasa da tamani kamar raɓa. Hakika, ya ce a “ranar ikon” Ɗansa, matasa maza da mata za su “bada kansu” ga hidimar Kristi. (Zab. 110:3) Wannan annabci zai cika a lokacin da yawancin mutane suka ƙi yin biyayya ga Allah, suka kasance masu yin abin da ransu yake so, masu son kuɗi kuma masu rashin biyayya ga Allah. Duk da haka, Jehobah ya san cewa matasa da suke bauta masa za su bambanta. Ya amince da ku ’yan’uwa maza da mata.

2. Menene tuna Jehobah ya ƙunsa?

2 Ka yi tunanin farin cikin da Allah yake yi sa’ad da ya ga matasa suna tuna cewa shi ne mahaliccinsu. (M. Wa. 12:1) Hakika, tuna Jehobah ya kunshi fiye da yin tunaninsa kawai. Yana nufin yin abubuwan da za su faranta masa rai, da kuma bin ka’idodinsa a rayuwarmu ta yau da kullum. Yana kuma nufin mu dogara da Jehobah, da sanin cewa yana son ci gabanmu a ruhaniya. (Zab. 37:3; Isha. 48:17, 18) Haka ake ji game da Mahaliccinka?

“Ka Dogara ga Ubangiji da Dukan Zuciyarka”

3, 4. Ta yaya ne Yesu ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah, kuma me ya sa yana da muhimmanci mu dogara ga Jehobah?

3 Wani misali mai kyau na mutumin da ya dogara ga Allah shi ne Yesu Kristi. Ya bi umurnin da ke cikin Misalai 3:5, 6: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” Bayan baftismarsa Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya jarabci Yesu ya karɓi sarautar duniya da ɗaukakarsa. (Luk 4:3-13) Shaiɗan bai rinjayi Yesu ba. Ya san cewa “dukiya [ta gaskiya], da girma, da rai” su ne “ladar tawali’u da tsoron Ubangiji.”—Mis. 22:4.

4 A yau wannan duniya tana cike da haɗama da kuma son kai. A irin wannan yanayin duniya, ya kamata mu bi misalin Yesu. Ka tuna cewa Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya rinjaye bayin Jehobah daga hanyar samun rai. Yana son ya ga kowa yana tafiya a kan hanya mai faɗi da za ta kai ga halaka. Kada ka yarda ya rinjaye ka. Maimakon haka, ka tsai da shawarar tuna Mahaliccinka. Ka dogara gare shi ɗungum, kuma ka riƙe rai ‘wanda shi ne hakikanin rai,’ da zai zo bada daɗewa ba.—1 Tim. 6:19.

Matasa, Ku Kasance Masu Hikima!

5. Yaya kuke ji game da abin da zai faru da wannan duniyar a nan gaba?

5 Matasa da suke tuna Mahaliccinsu suna fin tsaransu hikima. (Ka karanta Zabura 119:99, 100.) Saboda suna da sanin Allah, sun san cewa wannan duniya za ta shuɗe. A cikin ɗan shekaru da ku ka yi a rayuwarku, babu shakka kun lura cewa abin ban tsoro da damuwa sun ƙaru. Mai yiwuwa a makaranta kun ji game da gurɓata mahalli, ƙaruwar zafi, kwararowar hamada, da kuma wasu matsaloli. Mutane suna damuwa domin waɗannan abubuwa da suke faruwa, amma shaidun Jehobah ne kawai suka fahimci cewa waɗannan suna cikin alamun da suke nuna cewa muna ƙarshen duniyar Shaiɗan.—R. Yoh. 11:18.

6. Ta yaya ne aka rinjayi wasu matasa?

6 Abin baƙin ciki, wasu matasa bayin Allah ba su kula ba kuma sun mance cewa wannan duniya ta kusa shuɗewa. (2 Bit. 3:3, 4) Abokanan banza da hotunan batsa sun rinjayi waɗansu su yi zunubi mai tsanani. (Mis. 13:20) Zai kasance abin baƙin cikin mu rasa tagomashin Allah yanzu da muke kusa da ƙarshen duniya. Maimakon haka, ku koya daga abin da ya faru da Isra’ilawa a shekara ta 1473 K.Z. sa’ad da suka kafa sansani a Filayen Moab, kusa da Ƙasar Alkawari. Me ya faru a wurin?

Sun Faɗi Sa’ad da Suka Kusa Cika Makasudinsu

7, 8. (a) Wane tarko ne Shaiɗan ya yi amfani da shi a Filayen Moab? (b) Wane tarko ne Shaiɗan yake amfani da shi a yau?

7 A zamanin Isra’ilawa, Shaiɗan ya nuna cewa yana son ya hana su su sami gadōnsu. Da ya ga cewa ya kasa sa annabi Bala’am ya la’ance su, sai ya yi amfani da wani tarko dabam; ya yi ƙoƙari ya ga cewa ba su cancanci samun tagomashin Jehobah ba. Ya sa matan Moab suka rinjaye su, a wannan karon kuwa Shaiɗan ya yi nasara. Mutanen suka soma yin lalata da ’yan matan Moab kuma suka yi sujada ga Ba’al na Peor. Ko da yake sun kusa shiga Ƙasar Alkawari, Isra’ilawa guda 24,000 sun rasa ransu. Lalle wannan rashi ne sosai.—Lit. Lis. 25:1-3, 9.

8 A yau, mun kusa shiga ƙasar alkawari da ta fi ta dā, wato, sabuwar duniya. Kamar dā, Shaiɗan yana amfani da lalata ya lalata mutanen Allah. Ɗabi’ar mutane yanzu ya lalace sosai har ana ɗaukan fasikanci ba wani abu ba ne, luwaɗi kuma ganin daman mutum ne. Wata ’yar’uwa Kirista ta ce: “A gida da Majami’ar Mulki ne kawai yarana suke koyon cewa luwaɗi da fasikanci ba su da kyau a gaban Allah.”

9. Menene zai iya faruwa a lokacin ƙuruciya, kuma ta yaya matasa za su bi da wannan abu?

9 Matasa da suke tuna Mahaliccinsu a yau sun san cewa jima’i kyauta ce mai tsarki da ta shafi rai da haihuwa. Saboda haka, sun fahimci cewa ma’aurata ne kaɗai suka cancanci su yi jima’i. (Ibran. 13:4) Amma, ƙuruciya a lokacin da shawarar jima’i take da ƙarfi tana rinjayar tunanin kirki, hakan zai iya kasance da wuya a tsaya da tsarki. Me za ka iya yi idan ka ga cewa ka soma tunanin da bai dace ba? Ka yi addu’a ga Jehobah ya taimake ka ka mai da hankali ga abubuwa masu tsarki. Jehobah yana sauraran waɗanda suke roƙonsa. (Ka karanta Luka 11:9-13.) Taɗi game da abubuwa masu tsarki za su iya taimakawa wajen mai da hankalinka ga abubuwa masu tsarki.

Ku Zaɓi Makasudinku da Hikima

10. Wane irin mugun tunani ya kamata mu guje wa, kuma wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?

10 Abin da ya sa matasa sukan yi abin da suka ga dama kuma su nemi nishaɗi na jiki shi ne ba su da bege ko ja-gora daga Allah. (Mis. 29:18) Suna kama da Isra’ilawa marasa ibada na zamanin Ishaya waɗanda suke rayuwa domin “farinciki da murna, . . . cin nama da shan ruwan anab.” (Isha. 22:13) Maimakon ku yi sha’awar waɗannan mutane, me zai hana ku yi tunanin alkawarin da Jehobah ya yi wa amintattunsa? Idan kai matashi ne mai bauta wa Allah, kana ɗokin sabuwar duniya? Kana ƙoƙari ka ‘rayu cikin hankalinka . . . yayinda kake sauraron begen’ da Jehobah ya yi alkawarinsa? (Tit. 2:12, 13) Amsar da ka ba da zai ƙarfafa ka bisa makasudin da ka zaɓa.

11. Me ya sa ya kamata matasa Kiristoci da suke makaranta su sa ƙwazo sosai a makaranta?

11 Duniya tana son matasa su sa kuzari a kan makasudai na duniya. Yana da kyau waɗanda suke makaranta su yi ƙoƙari don su sami ilimi mai kyau. Tun da ma, manufarka ba kawai ka sami aiki mai kyau ba ne, amma don ka taimaka a cikin ikilisiya kuma ka zama ƙwararren mai shela. Don ka cim ma wannan makasudai, ya kamata ka iya tattaunawa da mutane da kyau, ka iya tunani mai kyau, kuma ka kasance mai saurarar mutane kuma mai daraja su. Duk da haka, matasa da suke yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suna ƙoƙari su yi amfani da ka’idodinsa a rayuwarsu suna samun ilimi mafi kyau kuma suna ƙafa tushe mai kyau na yin nasara da kuma na rayuwa a nan gaba.—Ka karanta Zabura 1:1-3.a

12. Wane misali ne ya kamata iyalan Kiristoci su bi?

12 A Isra’ila, iyaye ba sa wasa da ilimantar da ’ya’yansu. Iyaye suna koyarwa ’ya’yansu kowacce fannin rayuwa, mafi muhimmanci ma abubuwa na ruhaniya. (K. Sha 6:6, 7) Hakazalika, matasa Isra’ilawa waɗanda suka saurari iyayensu da wasu dattawa masu tsoron Allah za su sami ilimi, hikima, basira, fahimi, da kuma hankali, wato halaye masu muhimmanci da ake samu daga sanin Allah. (Mis. 1:2-4; 2:1-5, 11-15) Ya kamata iyalan Kiristoci a yau su kula da irin wannan ilimantarwa.

Ku Saurari Waɗanda Suke Ƙaunarku

13. Wace shawara ce wasu matasa suke samu, kuma me sa ya kamata su kula?

13 Matasa suna samun shawara daga mutane dabam dabam, kamar malamai da suke ba wa daliɓai shawara a makaranta, waɗanda shawarar su game da yadda za su yi nasara ne a duniya. Don Allah ku roƙi Jehobah ya taimake ku sa’ad da kuke tunani a kan waɗannan shawarwari da taimakon Kalmar Allah da kuma littattafan da bawan nan mai aminci mai hikima ya yi tanadinsu. Daga nazarin Littafi Mai Tsarki da kuke yi, kun fahimci cewa matasa marasa wayo su ne ainihi abin fakon Shaiɗan. Alal misali, a lambun Adnin, Hauwa’u marar wayo ce ta saurari Shaiɗan, wani baƙo da bai nuna ma ta ƙauna ba. Da a ce ta saurari Jehobah wanda ya nuna yana ƙaunarta a hanyoyi dabam dabam, da yanayin bai kasance haka ba.—Far. 3:1-6.

14. Me ya sa ya kamata mu saurari Jehobah da kuma iyayenmu masu bi?

14 Mahaliccin ku ma yana ƙaunarku, kuma yana yin haka da zuciya mai kyau. Yana son ku yi farin ciki har abada. Saboda haka, da ƙauna irin ta iyaye masu kula, ya ce muku da kuma dukan waɗanda suke bauta masa: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.” (Isha. 30:21) Idan kuna da iyaye da suke ƙaunar Jehobah, kuna da ƙarin gata. Ku saurare su sa’ad da kuke zaɓan abin da ya fi muhimmanci a rayuwarku da kuma makasudanku. (Mis. 1:8, 9) Saboda suna so ku sami rai, wani abin da ya fi arziki ko kuma ɗaukaka a wannan duniya.—Mat. 16:26.

15, 16. (a) Wane tabbaci ne muke da shi ga Jehobah? (b) Wane darassi mai muhimmanci ne muka koya daga labarin Baruch?

15 Waɗanda suke tuna da Mahaliccinsu suna sauƙaƙa rayuwarsu, da tabbacin cewa Jehobah ba ‘zai tauye’ musu ba ‘kuwa ba zai’ yashe su ba. (Ka karanta Ibraniyawa 13:5.) Saboda irin wannan rayuwa ya bambanta da na duniya, kada mu yarda ra’ayin duniya ya rinjaye mu. (Afis. 2:2) Ka yi la’akari da misalin Baruch sakataren Irmiya, wanda ya rayu a lokacin da Urushalima take cikin wahalar ranakun ta na ƙarshe da ya kai ga halaka birnin a shekara ta 607 K.Z.

16 Mai yiwuwa ne Baruch yana so ya sami abin duniya. Jehobah ya lura da hakan sai ya gargaɗi Baruch kada ya biɗa ma kansa ‘mayan abubuwa.’ Baruch ya nuna tawali’u da hikima, saboda ya saurari Jehobah kuma ya tsira sa’ad da aka halaka Urushalima. (Irm. 45:2-5) A wani ɓangare kuma, abokanan Baruch da suka nemi ‘manyan abubuwa’ wato, abin duniya, suka saka bautar Jehobah a baya, ba da daɗewa ba suka yi hasarar kome a lokacin da Kaldiyawa suka ci Urushalima. Da yawa kuma suka rasa ransu. (2 Laba. 36:15-18) Labarin Baruch ya koya mana cewa dagantaka mai kyau da Allah ya fi arziki da ɗaukaka a wannan duniya.

Ka Bi Misali Mafi Kyau

17. Me ya sa Yesu, Bulus, da kuma Timothawus misalai ne masu kyau ga bayin Jehobah?

17 Kalmar Allah ta yi mana tanadin misalai masu kyau da za su taimaka mana mu bi tafarkin samun rai. Alal misali, Yesu shi ne mutum mafi baiwa da ya taɓa rayuwa a nan duniya, duk da haka ya mai da hankali ga abin da zai taimaki mutane har abada, wato, “Bishara ta mulkin Allah.” (Luk 4:43) Don ya yi aikin Jehobah sosai, manzo Bulus ya bar aikin da yake yi, ya yi amfani da lokacinsa da ƙarfinsa a wajen shelar bishara. Timothawus, ‘ɗa na gaske cikin bangaskiya,’ ya bi misali mai kyau na Bulus. (1 Tim. 1:2) Yesu, Bulus, da Timothawus sun yi nadamar tafarki da suka bi a rayuwar su ne? Ko kaɗan! Maimakon haka, Bulus ya ce abubuwan duniya suna kama da “najasa” idan aka kwatanta su da gatar bauta wa Allah.—Filib. 3:8-11.

18. Wane canje-canje ne wani ɗan’uwa matashi ya yi, kuma me ya sa bai yi nadama ba?

18 Matasa da yawa a yau suna bin gurbin Yesu, Bulus, da Timothawus. Alal misali, wani ɗan’uwa matashi wanda yake da aikin da yake samun kuɗi sosai ya ce: “Na sami ƙarin girma saboda ina bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Duk da kuɗin da nake samu, sai na ji kamar ina cin iska ne kawai. Sa’ad da na gayawa shugabanni kamfanin cewa zan bar aikina in zama mai hidima na cikakken lokaci, sun ce za su ƙara mini albashi don in ci gaba da aiki. Amma na riga na tsai da shawara. Mutane da yawa ba su fahimci abin da ya sa na bar aikina zuwa hidima na cikakken lokaci ba. Amsa ta ita ce ina son in cika keɓe kaina da na yi wa Allah. Saboda yanzu na sa zuciyata a abubuwa na ruhaniya, ina samu farin ciki da kuma gamsarwa da arziki ko ɗaukaka ba za su iya ba ni ba.”

19. Wane zaɓe ne mai kyau ake ƙarfafa matasa su yi?

19 A duniya duka matasa da yawa sun yi irin wannan zaɓe mai kyau. Saboda haka, matasa, sa’ad da kuke tunanin rayuwarku, ku tuna da ranar Jehobah. (2 Bit. 3:11, 12) Kada ku yi kishin mutanen da suke samun abin duniya. Maimakon haka, ku saurari waɗanda suke ƙaunarku da gaske. Yin ‘ajiya a sama’ shi ne ajiya mafi kyau da za ku iya yi kuma shi kaɗai ne mai albarka ta har abada. (Mat. 6:19, 20; Ka karanta 1 Yohanna 2:15-17.) Hakika, ku tuna da Mahaliccinku. Idan ku ka yi hakan, Jehobah zai albarkace ku.

[Hasiya]

a Don kari bayani game da ƙarin ilimi da kuma aiki, ka dubi Hasumiya Tsaro, na 1 ga Oktoba, 2005, shafofi na 26-31.

Za Ka Iya Tunawa?

• Ta yaya ne za mu iya nuna mun dogara ga Allah?

• Menene ilimantarwa mafi kyau?

• Wane darassi ne za mu koya daga wurin Baruch?

• Su wanene suka kasance da misalai masu kyau, kuma me ya sa?

[Hotuna a shafi na 13]

Jehobah yana bada ilimi mafi kyau

[Hoto a shafi na 15]

Baruch ya saurari Jehobah kuma ya tsira sa’ad da aka halaka Urushalima. Menene za mu koya daga wannan labarin?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba