Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 5/1 pp. 21-26
  • Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Mori Ƙuruciyarka
  • “Ku Kusato ga Allah”
  • Ka Yi Zaɓe Mai Kyau
  • Ka Daraja Abubuwa na Ruhaniya
  • Ka Yi Zaɓi Mai Kyau a Ƙuruciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Matasa Ku Tuna Da Mahaliccinku A Yanzu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yaya Za Ka Iya Taimakon Ɗa “Mubazzari”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 5/1 pp. 21-26

Matasa, Kuna Shiri Don Nan Gaba Kuwa?

“Na san irin tunanin da ni ke tunaninku da su, . . . tunani na lafiya, ba na masifa ba, domin in ba ku bege mai-kyau a ƙarshe.”—IRMIYA 29:11.

1, 2. A waɗanne hanyoyi ne za a iya ɗaukan ƙuruciya?

YAWANCIN mutane suna ɗaukan ƙuruciya lokaci ne na ban sha’awa. Suna tuna da kuzari da ƙwazo da suke da shi lokacin da suke matasa. Suna tuna da lokacin da ban sha’awa, lokacin ba su da hakki da yawa, lokaci ne da suke ɓatar da yawancin lokacinsu a morewa kuma suna da zarafi da yawa da ke a gabansu.

2 Ku da kuke matasa ƙila kuna ganin abubuwa dabam suke. Kana iya samun matsalolin bi da canje-canje na tsotsuwar zuciya da kuma na jiki a ƙuruciya. A makaranta, za ka iya fuskanci matsi na tsara. Kana bukatar ka ƙudura niyya a ƙoƙarinka ka yi tsayayya wa shan mugun ƙwayoyi, giya, da kuma yin lalata. Da yawa cikinku ma suna fuskantar batun tsaka tsaki ko wasu batutuwa da ke dangane da imani. Hakika, ƙuruciya lokaci ne mai wuya. Amma, lokaci ne na zarafi. Tambayar ita ce, Yaya za ka yi amfani da waɗannan zarafi?

Ka Mori Ƙuruciyarka

3. Wane gargaɗi da faɗaka Sulemanu ya ba matasa?

3 Tsofaffi za su iya gaya maka cewa ƙuruciya ba ta daɗewa, kuma gaskiyarsu. A ’yan shekaru kawai, sai ka ga ka shige ƙuruciya. Saboda haka, ka more ta sa’ad da kake ciki! Gargaɗin da Sarki Sulemanu ya yi ne da ya rubuta: “Ka yi murna, ya kai saurayi, a cikin ƙuruciyarka; zuciyarka kuwa ta yi fari a kwanakin ƙuruciyarka, ka bi muradin zuciyarka, da sha’awar idonka.” Amma kuma Sulemanu ya gargaɗi matasa: “Ka kawarda baƙinciki daga zuciyarka, cuta kuma daga jikinka.” Sai ya daɗa cewa: “Ƙuruciya da zaman mutum, duk banza ne.”—Mai-Wa’azi 11:9, 10.

4, 5. Me ya sa hikima ce matasa su yi shiri don nan gaba? Ka ba da misali.

4 Ka fahimci abin da Sulemanu yake nufi? Ga misali, ka yi tunanin wani matashi da aka ba shi wata babbar kyauta, wataƙila gadō. Me zai yi da kyautar? Yana iya more shi wa kansa—yadda ɗa mubazzari na almarar Yesu ya yi. (Luka 15:11-23) Amma me zai faru sa’ad da kuɗin ya ƙare? Hakika zai yi nadama cewa ya yi wauta! A wata sassa kuma, idan ya yi amfani da kyautar don ya yi shirinsa na nan gaba, ƙila ya zuba jari da shi. A ƙarshe, sa’ad da yake samun ribar jarinsa, kana tsammanin zai yi nadama cewa bai kashe dukan kuɗinsa a more ƙuruciyarsa ba? Sam!

5 Ka yi tunanin ƙuruciyarka cewa shekarun kyauta ce daga wurin Allah, kuma haka take. Yaya za ka yi amfani da su? Kana iya gama da kuzari da ƙwazon wa sha’awoyinka kawai, kana shan moriya a nan da can, ba tare da tunanin nan gaba ba. Idan ka yi hakan nan, to, “ƙuruciya da zaman mutum” a gare ka zai zama “banza.” Ya kuwa fi albarka ka yi amfani da lokacin ƙuruciyarka ka yi shiri don nan gaba!

6. (a) Wane gargaɗi na Sulemanu ne yake wa matasa ja-gora? (b) Menene Jehovah zai so ya yi wa matasa, kuma ta yaya matashi zai iya amfana daga wannan?

6 Sulemanu ya ambata wata ƙa’ida da za ta iya taimaka maka ka more ƙuruciyarka. Ya ce: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma [a] kwanakin ƙuruciyarka.” (Mai-Wa’azi 12:1) Sauraron Jehovah da kuma yin nufinsa—ita ce mabuɗin nasara. Jehovah ya gaya wa Isra’ilawa na dā abin da yake son ya yi musu: “Na san irin tunanin da ni ke tunaninku da su, . . . tunani na lafiya, ba na masifa ba, domin in ba ku bege mai-kyau a ƙarshe.” (Irmiya 29:11) Jehovah kuma za ya so ya ba ka “bege mai-kyau a ƙarshe.” Idan ka tuna da shi a halayenka, tunaninka, da shawarwarinka, za ka sami ƙarshen nan da kuma begen.—Ru’ya ta Yohanna 7:16, 17; 21:3, 4.

“Ku Kusato ga Allah”

7, 8. Ta yaya matashi zai iya kusaci Allah?

7 Yaƙub ya ƙarfafa mu mu tuna Jehovah sa’ad da ya aririce mu: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yaƙub 4:8) Jehovah shi ne Mahalicci, Mamallaki na samaniya, da ya cancanci dukan sujjada da yabo. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Duk da haka, idan muka matsa kusa da shi, za ya matso kusa da mu. Irin wannan so da yake da shi wajenmu ba ya daɗaɗa zuciyarka ne?—Matta 22:37.

8 Muna matsa kusa da Jehovah a hanyoyi da yawa. Alal misali, manzo Bulus ya ce: “Ku lizima ga addu’a, kuna tsaro a cikinta da godiya.” (Kolossiyawa 4:2) A ce, ka koyi halin yin addu’a. Kada ka gamsu da ce amin kawai bayan da babanka ko kuma ’yan’uwa Kirista suka yi addu’a a cikin ikilisiya. Ka taɓa gaya wa Jehovah dukan damuwarka kuma ka gaya masa abin da kake tunani, kake tsoro, da kuma ƙalubalen da kake fuskanta? Ka taɓa gaya masa abubuwan da idan za ka tattauna da wani ne za ka ji kunyar yin haka? Addu’o’i da zuciya ɗaya suna sa mu kasance da salama. (Filibbiyawa 4:6, 7) Suna taimaka mana mu kusaci Jehovah kuma mu fahimta cewa yana matso kusa da mu.

9. Ta yaya matashi zai saurari Jehovah?

9 Ga wata hanya kuma da za mu kusaci Jehovah cikin hurarren kalmominsa: “Ka ji shawara, ka karɓi koyarwa, domin ka yi hikima a ƙarshen kwanakinka.” (Misalai 19:20) Hakika, idan ka saurari Jehovah kuma ka yi masa biyayya, kana shirinka ke nan don nan gaba. Ta yaya za ka nuna cewa kana saurarar Jehovah? Babu shakka kana halartan taron Kirista a kai a kai kuma kana sauraron tsarin da ke ciki. Kana kuma “girmama ubanka da uwarka” ta kasancewa a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali. (Afisawa 6:1, 2; Ibraniyawa 10:24, 25) To, yana da kyau. Amma ban da haka, kana ‘rifta zarafi’ don ka shirya taro, ka karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, kuma ka yi bincike? Kana ƙoƙari kuwa ka yi abin da kake karantawa, don ka yi tafiya ta ‘mai hikima’? (Afisawa 5:15-17; Zabura 1:1-3) Idan kana haka, kana kusatar Jehovah ke nan.

10, 11. Waɗanne amfani masu yawa matasa suke samu sa’ad da suka saurare Jehovah?

10 A kalmomin da suka fara littafin Misalai, hurarren marubuci ya bayyana ƙudurin littafin nan na Littafi Mai Tsarki. Ya ce, domin “a san hikima da koyarwa. A gane zantattuka na fahimi kuma: domin a karɓi koyarwa cikin aikin hikima, da cikin adalci da shari’a da daidaita: domin a bada azanci ga marasa wayo, ilimi da hankali ga saurayi.” (Misalai 1:1-4) Saboda haka, sa’ad da kake karatun kalmomin Misalai—da sauran littattafan Littafi Mai Tsarki—za ka koyi adalci da daidaita, kuma Jehovah za ya yi farin ciki cewa ka kusace shi. (Zabura 15:1-5) Idan kana koyon sanin ya kamata, fahimi, sani, da basira, za ka tsai da shawarwari masu kyau.

11 Abu mai girma ne a yi tsammanin matashi ya yi hikima haka? A’a, domin Kiristoci matasa da yawa suna yin haka. Saboda haka ne wasu suke daraja su kuma ba sa ‘rena ƙuruciyarsu.’ (1 Timothawus 4:12) Iyayensu suna fahariyar wannan kuma Jehovah ya ce suna faranta masa rai. (Misalai 27:11) Ko da su matasa ne, suna da gaba gaɗin cewa waɗannan hurarren kalmomi dominsu ne: “Ka lura da kamili, ka duba kuma adali: Gama ƙarshen wannan mutum salama ne.”—Zabura 37:37.

Ka Yi Zaɓe Mai Kyau

12. Waɗanne muhimman zaɓe ne matasa za su yi, kuma me ya sa wannan zaɓe ke da sakamako mai daɗewa?

12 Ƙuruciya lokaci ne na yin zaɓe da yawa, wasu suna da sakamako mai daɗewa. Wasu zaɓe da kake yi yanzu za su shafe ka nan da shekaru da yawa. Zaɓe mai kyau na kawo farin ciki a rayuwa. Munanan zaɓe za su iya ɓata dukan rayuwar mutum. Ka yi la’akari da gaskiyar wannan game da zaɓe biyu da kake bukatar ka yi. Na farko, Wa ka zaɓa ya zama abokinka? Me ya sa hakan ke da muhimmanci? To, hurarren karin magana ta ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Misalai 13:20) A wata sassa, a kwana a tashi sai mu zama kamar mutanen da muke abokantaka da su—masu hikima ko wawaye. Wanne za ka so ka zama?

13, 14. (a) Ban da yin sha’ani da mutane, mecece tarayya ta ƙunsa? (b) Wane kuskure ya kamata matasa su kauce masa?

13 Idan aka yi zancen tarayya, za ka yi tunanin mutane. Gaskiya ne, amma ya wuci haka. Sa’ad da kake kallon tsarin telibijin, kake sauraron waƙa, kake karatun wani littafi, sa’ad da ka je gidan siliman, ko kuma wani waje cikin Intane, tarayya kake yi. Idan tarayyar ta zama ta mugunta, lalata, ko kuma tana ƙarfafa shan muguwar ƙwaya, maye, ko kuma yin wani abin da ya saɓa da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kana tarayya ne da “wawa” da yake aikatawa sai ka ce babu Jehovah.—Zabura 14:1.

14 Wataƙila kana jin cewa tun da yake kana halartan taron Kirista kuma kana da ƙwazo cikin ikilisiya, za ka iya ka magance mugun siliman ko waƙa da take da daɗin ji amma kalmomin masu ƙyama ne. Wataƙila kana jin babu abin da zai faru idan ka ɗan duba hotunan tsiraru cikin duniyar Gizo na Intane. Manzo Bulus ya ce ra’ayinka ba daidai ba ne! Ya ce: “Zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) Abin baƙin ciki, wasu matasa Kiristoci da suke da kirki sun yarda wa muguwar tarayya ta ɓata halayensu na kirki. Saboda haka, ka ƙuduri niyyar ka ƙi irin wannan tarayyar. Idan ka yi haka kana bin gargaɗin Bulus ke nan: “Kada ku kamantu bisa ga kamar wannan zamani kuma: amma ku juyu bisa ga sabontar azancinku, da za ku gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.”—Romawa 12:2.

15. Wane zaɓe na biyu ne matasa suke da shi, kuma waɗanne matsi suke fuskanta game da wannan?

15 Ga wani zaɓe kuma. Lokaci zai kai da za ka zaɓi abin da za ka so ka yi bayan ka gama makaranta. Idan kana zama a ƙasa da bai da sauƙi a samu aikin yi, za ka iya fuskantar matsi na son ka samu aikin da ya fi kyau. Idan kana ƙasa mai ni’ima, kana da abubuwa da yawa da za ka so ka yi, wasu ma da ban jaraba. Malamanka ko iyayenka da nufin kirki za su so ka samu aikin da za ka sami isashen kuɗi, har ma ka yi arziki. Amma, yin koyon domin wannan zai iya cin lokacinka ƙwarai da za ka yi amfani da shi a bauta wa Jehovah.

16, 17. Ka ba da bayanin yadda nassosi dabam dabam za su iya taimakon matashi ya daidaita ra’ayinsa game da aiki.

16 Ka tuna ka bincika Littafi Mai Tsarki kafin ka tsai da shawara. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi aiki domin rayuwa, wannan ya nuna mana cewa muna da hakkin kula da kanmu. (2 Tassalunikawa 3:10-12) Har ila, ya ƙunshi wasu abubuwa. Muna ƙarfafa ka ka karanta waɗannan nassosi na gaba kuma ka yi tunanin yadda za su iya taimakon matashi ya daidaita a batun zaɓen makasudi: Misalai 30:8, 9; Mai-Wa’azi 7:11, 12; Matta 6:33; 1 Korinthiyawa 7:31; 1 Timothawus 6:9, 10. Bayan da ka karanta waɗannan ayoyi ka ga yadda ra’ayin Jehovah yake game da batun?

17 Bai kamata aiki ya zama abu mafi muhimmanci har ya sha kan hidimarmu ga Jehovah ba. Idan za ka iya samun aiki ta wurin zuwa babban makaranta, yana da kyau. Idan za ka bukaci ƙarin koyo bayan babban makaranta, abin da za ka tattauna ne da iyayenka. Amma, kada ka ƙyale “mafifitan al’amura”—abubuwa na ruhaniya. (Filibbiyawa 1:9, 10) Kada ka yi kuskure irin na Baruch, marubuci na Irmiya. Ya yi rashin godiya ga gatarsa ta hidima kuma ya ‘soma biɗan manyan abubuwa wa kansa.’ (Irmiya 45:5) A ɗan lokaci ya manta cewa babu ‘manyan abubuwa’ cikin wannan duniya da za su sa ya kusaci Jehovah ko su taimake shi ya tsira wa halakar Urushalima. Abu ɗaya ne za a iya faɗi game da mu a yau.

Ka Daraja Abubuwa na Ruhaniya

18, 19. (a) Menene yawancin maƙwabtanka suke wahalarta, kuma yaya ya kamata ka ji game da su? (b) Me ya sa mutane da yawa da suke yunwa ta ruhaniya ba sa jin suna yunwa?

18 Ka taɓa ganin hotunan yara cikin labarai a ƙasashe mayunwata? Idan ka taɓa gani, lallai ka ji tausayinsu. Haka kake jin tausayin maƙwabtanka? Me ya sa? Domin yawancinsu suna jin yunwa. Suna yunwa da Amos ya yi annabcinsa: “In ji Ubangiji Yahweh, kwanaki suna zuwa inda zan aike yunwa a cikin ƙasan, ba yunwar gurasa ko ƙishin ruwa ba, amma na jin maganar Ubangiji.”—Amos 8:11.

19 Gaskiya ne cewa yawancin waɗanda suke yunwa ta ruhaniyar nan ba waɗanda suka san talaucinsu na ruhaniya ba ne. (Matta 5:3) Mutane da yawa ba sa jin suna yunwa ta ruhaniya. Wasu suna ma jin sun ƙoshi ainu. Idan haka ne, watau suna ci ne daga “hikimar duniya,” da ta haɗa da son abin duniya, kame kame na kimiyya, ra’ayin ɗabi’a, da sauransu. Wasu suna jin cewa “hikima” ta zamani ta sa koyarwar Littafi Mai Tsarki ta zama yayin dā. Amma, “duniya, ta wurin hikimarta, ba ta san Allah ba.” Hikimar duniya ba za ta taimake ka ka kusaci Allah ba. Ba kome ba ne, “wauta ce ga Allah.”—1 Korinthiyawa 1:20, 21; 3:19.

20. Me ya sa bai da kyau mutum ya so ya yi koyi da mutane da ba sa bauta wa Jehovah?

20 Sa’ad da ka kalli hotunan waɗannan yara mayunwata, kana son ka zama kamar su ne? Sam! Amma wasu matasa cikin iyalan Kirista sun nuna suna son mutane da suke yunwa a ruhaniya da ke kewaye da su. Wataƙila waɗannan matasa suna tsammanin matasa da suke cikin duniya ba su da damuwa, rayuwa suke mora. Sun manta cewa waɗannan matasa a ware suke daga Jehovah. (Afisawa 4:17, 18) Sun kuma manta da mummunan sakamakon yunwa ta ruhaniya. Wasu sakamakonsu sune ɗaukan cikin shege, da ciwon jiki da na tsotsuwar zuciya domin lalata, shan taba, maye, da kuma shan muguwar ƙwaya. Yunwa ta ruhaniya tana jawo ruhun tawaye, rashin bege da rashin ja-gora a rayuwa.

21. Ta yaya za mu tsare kanmu da kasancewa da mugun halaye na waɗanda ba sa bauta wa Jehovah?

21 Saboda haka, sa’ad da kake makaranta tsakanin waɗanda ba sa bauta wa Jehovah, kada ka yarda halayensu su shafe ka. (2 Korinthiyawa 4:18) Wasu za su furta ƙyama game da abubuwa na ruhaniya. Ban da haka, hanyar watsa labarai tana fito da mugun labarai, suna nuna cewa yin lalata, maye, ko kuma magana ta ban ƙyama ba laifi ba ne. Ka yaƙi wannan tasirin. Ka ci gaba da yin tarayya a kai a kai da mutane da suke “riƙe da bangaskiya da managarcin lamiri.” Kullum suna “yawaita cikin aikin Ubangiji.” (1 Timothawus 1:19; 1 Korinthiyawa 15:58) Ka taƙure da aiki a Majami’ar Mulki da kuma hidimar fage. A lokacin makarantarka, ka yi majagaba na ɗan lokaci a wasu lokatai. Ka sake ƙarfafa ra’ayinka game da ruhaniya a wannan hanyar kuma kada ka kasala.—2 Timothawus 4:5.

22, 23. (a) Me ya sa matashi Kirista zai yi wani zaɓe da wasu ba za su fahimta ba? (b) Menene aka ƙarfafa matasa su yi?

22 Domin ra’ayinka game da abubuwa na ruhaniya zai sa ka tsai da shawara da wasu ba za su fahimta ba. Alal misali, wani matashi Kirista yana da baiwar zama mawaƙi, ɗalibi da ake daraja shi ne a kowane fasalin koyo a makaranta. Da ya sauke karatu, ya bi babansa a aikin da yake yi na sharan taga don ya ci gaba da aikinsa na mai wa’azi na cikakken lokaci ko majagaba. Malamansa ba su taɓa fahimtar dalilinsa na wannan shawarar ba, amma idan ka kusaci Jehovah za ka fahimci hakan.

23 Sa’ad da kake bincika yadda za ka yi amfani da ƙuruciyarka, ‘ka ajiye wa kanka tushe mai kyau domin wokaci mai zuwa da za ka ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.’ (1 Timothawus 6:19) Ka ƙudura niyyar ka ‘tuna da Mahaliccinka’ a ƙuruciyarka—har kuma a dukan rayuwarka. Hanya ce ke nan kaɗai da za ta shirya maka nan gaba mai kyau, wadda ba ta ƙarewa.

Me Ka Kammala?

• Wane hurarren gargaɗi ne zai taimaki matasa a shirinsu na nan gaba?

• Waɗanne hanyoyi ne matashi zai iya ya “kusato ga Allah”?

• Ina wasu shawarwari da matashi zai yi da zai shafe shi nan gaba?

[Hotuna a shafi na 23]

Za ka yarda wa biɗan abin kanka duk ya sha kan kuzari da ƙwazonka na ƙuruciyarka?

[Hoto a shafi nas 24, 25]

Kiristoci matasa masu hikima suna daidaitawa a ruhaniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba